Skip to content
Part 51 of 54 in the Series Abinda Ka Shuka by Khadija S. Moh'd (Matar J)

Ana saura kwana biyu dangin ta suka zo wajen suna, ranar suna yaro ya ci sunan Ahmad, sosai abun ya ba ta mamaki, ita dai ba ta zaɓi sunan ba, haka nan kawai ta ji an sanyawa yaro sunan, Sai kawai ta share ta ci gaba da sabgoginta.

Shagali aka yi sosai, abun da ta fahimta AG  yana son bidi’a sosai, shi  dai a yi Nishadi yauwa.

*****

HAFSAT

Kamar ko wane term, wannan term din ma haka su Hafsat suka kare exam din 2nd term successfully, Sai dai a bangarenta ba dadi take ji, abubuwan da suke shirin tunkararta bayan Exam din sabbin abubuwa ne kuma baƙi a gare ta.

Da ya kama bayan gama exam din ta da sati biyu ne daurin auranta, sai kuma ga shi daga gidansu Ahmad an nemi alfarmar a dawo da bikin baya, saboda an tura Ahmad wani course, wanda ya kama zai tafi a ranar daurin auran nasu.

Bayan tsugunne tashi dole aka mayar da auran bayan da sati daya da gama jarabawarta, shi ya sa lokacin da take murnar kammala jarabawa, da jiran ranar hutu, bangaren su Mama Halima da Malam Ayuba kuma kokarin fita kunyarta suke yi. Yayin da bangaren su Ahmad suke ta shirin biki, saboda ta kammala Exam Friday, Asabar aka kawo lefe, lefen da ya dauki hankalin mutanen garin, ba a taba kawo ma wata yarinya irin lefen da aka kawo ma Hafsat ba.

A lokacin da ake karbar lefe a can cikin gari Hafsat tana nan zaune kan dutse tare da Tukuro, kuka take yi sosai, kukan da ba ta san dalilin yin shi ba, saboda ba za ta ce ba ta son Ahmad, kuma ba za ta ce tana son shi ba, abun da ta sani kawai shi ne abun alfahari ne a gare ta Ahmad ya kasance yana mijinta, ya tattara komai da ko wace mace za ta iya son shi don su. Ilmi, sura, kyau, kudi ga kuma sarauta.

Amma zuciyarta ba ta yi mata dadi sam game da batun auran, kuma da za ace za a fasa ba za taso hakan ba.

Hawayen ta dauke tana kallon kullin maganin da Tukuro ke miko mata tare da fadin “Wannan ma kamar sauran da nono za ki rika shan shi, shi ma dai na farin jini ne, Sha Allah kowa zai soki a zuriyar Galadima, haka za su duk wani abu da za ki haifa. Shi ma ba zai taba iya kwatanta soyayyarki da ta ko wace mace ba a zuciyarsa. Zai soki, zai kauna ce ki, ba zai taba jin kin fita a kanshi ba. Ko ina zai je tunaninshi da hankalinshi yana kanki, zai rika ganin fuskarki kamar farin nono”

Duk da hawayen da ke sakko mata hakan bai hana ta murmusawa ba, duk lokacin da Tukuro ya ba ta wasu magungunan yana fada mata ma’anarsu ba ta sanin lokacin da take yin murmushi, wani lokaci kuma dariya take yi sosai har da ƙyaƙyatawa

Wani lokaci ya kan taya ta, wani lokaci kuma ya share ta, kamar yanzu ma da ya murmusa kadan kafin ya ce “Ke yarinya ce Hafsat, ba za ki san dalilina na ba ki wadannan magungunan ba. Na san ina za ki je, sannan na san cikin su wa za ki yi rayuwa. To ina son ki rayu tamkar wata a tsakiyar taurari, ina son ki ji dadin rayuwa har karshen numfashi. Shi ya sa ki ga ina ba ki duk wasu nau’in magunguna na kariya da kuma farin jini “

Kai ta jinjina alamar gamsuwa.

” Kada ki yi wasa da duk abin da na ba ki. “kan ta kuma jinjinawa alamar eh

” Akwai abubuwan alkairi masu tarin yawa da suke shirin tunkaro ki Hafsat, za ki yarda da ni nan gaba”

Murmushin kawai ta yi ba tare da ta ce komai ba.

Tukuro yana da baiwa masu yawa, tun ba ta yarda da hakan ba, har ta fara yarda yanzu. Idan ya ce abu, zai wahala abun da ya ambata bai kasance ba, yana da baiwar sanin magunguna. Tsiro guda daya sai ya fada maka magungunan da yake yi sama da ashirin.

Kamar ko wane lokaci sai yamma ta dawo gida, tun da ta iso kuwa hirar kayan lefen take ji, kannen ta caaaa, Tatuuwa akwai ka za da kaza, Tatuwa har da kaza, har ta gaji da hirar. Safiyar Lahadi ba ta samu zuwa ruga ba, saboda zuwan Mama Halima. Saboda jiyan da aka kawo lefe Ɓurma suka je wajen Ruma daba ta da jiki.

A lokacin ne Hafsat ta samu damar ganin kayan lefenta a lokacin da Goggo Amarya ke nunawa Mama Halima. Kallo kawai take yi, amma har ga Allah wasu abubuwan ma ba ta san amfaninsu ba.

Mama ce da kanta ta ce Hafsat ta aikawa kawayenta su zo su ga lefe kafin a dauke shi, saboda yau Mama Halima za ta tafi da shi Dawuri, ba iya lefen ba har da Hafsat.

Danladi kanenta ta aika zuwa gidansu Farida da Na’ima ya kira su, ba su dau lokaci ba kuwa suka zo, sosai suka yaba da yiwa Hafsat fatan alkairi.

Duk abin da ke faruwa Hafsat hankalinta na kan Tukuro ba su yi wata kyakkyawar sallama ba, ga shi kuma Mama na maganar tafiya da ita yau, sannan ta ji tana fadin wai duk hidimar biki a can za a yi, daurin aure ne kawai za a yi a nan Maƙera, tana jin ma Maman tana fadawa su Na’ima wai ranar Laraba za a fara shagalin biki, idan suna ganin babu damuwa za a turo mota ta dauke su zuwa Dawurin a matsayin kawayenta.

Duk abin da suke tattaunawa ba ta ce komai ba, har sai lokacin da suka kasance daga ita sai Maman a daki sannan ta ce “Mama don Allah ba za a bar ni zuwa Larabar ba sai in taho, ban yi sallama da Ya Tukuro ba?” yadda ta karasa maganar kamar za ta yi kuka, sosai Mama ta ji tausayinta, ta san akwai shakuwa sosai tsakaninsu da Tukuro. Cikin rashin jin dadi Mama ta ce “Da zai yiwu Hafsat da an yi hakan, amma komai ya zo a kurarren lokaci, gyaran jiki nake so a yi miki, idan ya kai Laraba kuma ai ba amfani, yanzu haka ma mun yi late.”

Shiru Hafsat ta yi, ba ta kara cewa komai ba, Sai ma kayan amfaninta da Maman ta ce ta hada, su ta shiga haɗawa, zuwa karfe shida na yamma Tajuddeen ya zo, saboda Mama a motar haya ta zo da farko.

Lokacin da Hafsat ta fahimci lallai barin gidan za ta yi, Sai ta nufi Malam Ayuba ta rungume hade da fashewa da kuka, kuka sosai, wanda ya saka Malam Ayuba hawaye, duk da yadda ya so danne su

Sai ga shi ya tsinci kansa yana mai zubar da hawaye, wata irin sabuwar kaunar Hafsat din ce irin ta Ƴa da Uba ke ratsa duk wata gaɓa tashi. Komai sai ya kasa cewa. Illa Goggo da ta janye shi daki, Mama kuma ta kama Hafsat zuwa motor. Tajuddeen kuma sai ya samu abun tsokana.

Har suka kusa isa Dawuri hawaye take dauke a hankali, bangare daya kuma tana jin kamar mafarki, wai ita ce za ta yi aure, kuma za ta auri ɗan Galadiman Dawuri ikon Allah.

Ba ta san borin namiji ba ne, Sai da ta zo ta yi karo da manyan bokitan da aka cika su da kayan gara, irin Dublan, cincin, alkaki, da kuma nakiya, kaf dinsu an yi saletapping nasu.

Kayan kitchen kam gasu nan, wasu ma ba ta san yadda ake amfani dasu ba, sai dai ta yi ta kallonsu.

Sosai Mama ke shirin biki, take away da catoons na minerals gami da ruwa ga su nan kamar za a bude shago.

Abin da ba ta gani ba sune furnitures, su kuma tun a mota ta ji Tajuddeen yana fadawa Mama wai masu hada furnitures sun ce Laraba ko Alhamis za su zo.

Tun da ta zo gidan take ci hade da cin abubuwa da yawa, masu dadi da marasa dadi, turarurruka kam kullum cikin tu’ammali take dasu, wasu a cikin ruwan wanka, wasu ta tsugguna wasu kuma a turare ta dasu.

Ga wata mata da take zuwa shafa mata wani abu kullum, wannan ya sa fatar ta ta ƙara garai-garai kamar ana hango ruwan jikinta, saboda hasken fatarta ba mai ja ba ne, irin mai farin nan ne.

Ga wani kamshi mai shegen dadi da kwantar da hankali da ke fita a jikinta. Duk abin da ta taɓa ko ta raɓa sai ya canja zuwa kamshinta.

Ango dai bai iso gida ba, Sai ranar Talata da yamma shi da tawagar abokonshi sojoji da kuma yaranshi, saboda za su yi sword cross ranar Laraba

Can ma gidan Mama a ranar su Nabila suka iso, aka ci gaba da shirye-shirye.

Safiyar Laraba Ahmad ya kawo ma Hafsat kayan da za ta sanya a wajen shagalin biki, Sai dai bai ganta ba, Nabila ya ba, saboda a lokacin tana wurin kunshi da gyaran kai.

Ba kuma a gama mata ba sai 3am, daga nan kuma suka shiga shirin tafiya wurin Sword cross, Wanda aka ce za a yi a babban stadium din garin mai suna Galadima Stadium.

Mai kwalliya ta musamman aka dakko, ta tsarawa Hafsat light kwalliya mara nauyi, saboda kusan duk wani abu da za a yi wa Hafsat ado da shi Allah Ya ba ta, shi ya kadan aka dora kwalliyar sai ta fita fes, don ma ta ɗan yi rama sosai a cikin kwanakin.

Wata doguwar riga  irin ta amare ta sanya pink colour amma mai haske, jikin rigar duk wasu irin duwatsu ne masu walainiya, duk yadda ta motsa sai duwatsun su shiga walkiya.

Duk irin ramar da ta yi hakan bai hana rigar yi mata kyau ba, hade da fita da aurar jikinta. Saboda ana adjusting dinta ta baya. Gashin kanta ado aka yi mishi da wasu furanni kamar a Indiya, sai kuma aka lulluba bata pink colour veil na rigar.

Shi kam plain ne, sannan garai-garai mara nauyi, Sai dai yana da yashi-yashi. Bakin shi kuma an cishi da wani abu mai kama da cuku-cuku. Duk wata kwalliya da aka yi wa gashinta gyalen bai ɓoyeta ba, wannan ya sa tarin gashinta da aka parker a baya ya fito dam gwanin sha’awa.

Farin takalmi ta sanya mara tsini sosai, amma ya ɗan kara daga ta, yayin da hannayenta gami da wuyanta suka sha gwala-gwalai, sai ta fito tamkar amaryar Indiya, daidai lokacin ne kuma kawayenta Farida da Ni’ima suka iso.

Abu na farko da ya faranta ran Hafsat a ranar, duk yadda ake mata gargadin za ta ɓata kwalliyarta, hakan ai hana ta buga tsalle ta rungume su Ni’ima ba, suka shiga murnar ganin juna, yayin da suka rika yaba kwalliyar tata, saboda sosai Hafsat ta canja, kamar ba ita ba.

Zuwa karfe hudu da rabi na yamma motocin abokan Ango suka rika kwasar kawayen Amarya hade da Ƴan’uwanta masu sha’awar kallon zuwa Galadima Stadium.

Sai wajen biyar saura aka ce Hafsat ta fito, Juwairiyya ce ta kama mata hannu, fuskarta lullube da veil din nan har zuwa lokacin da ta shiga cikin motar, kamshin turarenshi ya dode kofofin hancinta, wannan ya tabbatar mata da yana cikin motar.

Sosai ta kara nutsuwa, duk da ta fahimci hankalinshi ya fi karkata a kan wayar shi.

Sai da motar ta tashi ne ta ji muryar Asad yana fadin “Amarya ba gaisuwa?”

Komai ba ta ce ba, Sai sautin murmushinshi da ta ji yana kara fadin “After all struggles karshe dai yau saura 2dz ki zama tamu”

Karon farko da ta ji idanun Ahmad a kanta, sosai yake kallon tulun gashinta da aka yi wa ma wani style din parking mai ban sha’awa. Sai kuma ya dawo da kallon nata saman hannunta wanda take wasa da cuku-cukun da ke gefen veil din ta. Kunshi ya rika kallo cike da mamakin yadda aka yi shi kamar da computer.

Idanunshi ya dauke zuwa kan Asad da ya dakko wata hirar, yayin da kamshin turarenta ke taya numfashinshi fitowa cikin sauki.

Hirarsu suke yi shi da Asad din, a cikin zuciyarta ta ce “2 parrot Kenan. Suka hadu bassa gajiya, kus-kus, an jima kus-kus, kullum cikin shawara suke kamar masu bayar da ƴa. Sosai take mamakin Ahmad idan suna surutu shi da Asad. A iya saninta da, shi, da Asad kawai ta san yana irin wannan hirar.

Tun da ta suka shiga Stadium din jikinta ya ba ta ba karamin mutane ne a ciki ba.

Sai da motar ta dauki Almost 2 minutes da tsayawa sannan Ahmad ya yunkura da niyyar fita, ta saci kallon shi cikin mayafin,a lokacin ta kara gasgata abin da take tsammani, sanye yake da kaya sojoji, duk da bayanshi ta kalla, hakan bai hana ta tabbatarwa da kanta, kayan ba karamin kyau  suka yi mishi ba. A zuciyarta take tambayar kanta dama soja ne.

Basu taba wannan maganar da kowa ba.

Ba ta kai karshen tunanin ba, ta ji ana taɓa murfin kofar da take.

Juwairiyya ce ta kamo ta hade da fito da ita daga cikin motar, Sai kuma ta ji ta sake ta, kafin ta ji kamshin turarenshi mai dadi yana gabato ta.

Yadda ta ga kafafunsu sun daidaita ya tabbatar mata da jerawa suka yi, “A tare za ku rika tafiya” ta ji Juwairiyya ta raɗa mata a kunne.

Daga kafar su a tare ya yi daidai da bugawar wata ganga da Hafsat ba ta taɓa jin irin ta ba, ban da ya yi saurin riƙe mata hannu lallai da ta zuwa da gudu, saboda ta dauka wani bala’in ne kuma ya sakko musu.

Sai kuma wata busa ta biyo bayan karar ganga.

Ita da kanta ta rike mishi hannu gam, tun da take ba ta taɓa ganin taron sojoji kamar yadda ta gansu yau ba. Ita soja ma sai dai a film, amma a zahiri ba ta taɓa gani ba in uniform dai, Sai dai police. Tun da suka gabato filin kowa ya mike, yayin da suka shiga tsakiyar wasu da’irar sojoji suna takawa a hankali, wannan busa na bin su. Sosai Hafsat a tsorace take, shi ya, sa koda wasa ba ta zare hannunta daga cikin nashi ba, kamar yadda ba ta yarda ta hada ido da ko wane soja ba.

Ta cikin mayafi take satar kallansu sun yi tsaye ƙiƙam! Kamar an zana su, gani take hatta idonsu baya motsawa.

<< Abinda Ka Shuka 50Abinda Ka Shuka 52 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×