Skip to content
Part 52 of 54 in the Series Abinda Ka Shuka by Khadija S. Moh'd (Matar J)

Da wannan taku na za a, ba za a ba, suka isa wurin wata kayatattar kujera, ta  hannunta da ke cikin hannunshi ya fahimci kokarin zama take yi, don haka ya yi saurin matsa hannu. Sai ko ta ankare don haka ita ma ta yi tsayen, kamar yadda ya yi.

Yin da sojojin nan suka shiga miko gaisuwa da wani irin salo na parade mai burgewa.

Hafsat kam sosai ta ware idanunta da ke cikin mayafi tana shan kallo. Kara   godewa Allah ta yi, da Ya sa ta auri soja, yau kam auran soja ya burgeta, ta kuma san zai burge mutane da yawa.

Yadda Ahmad ya tsaya ƙyam yana karɓar gaisuwar ba ƙaramin mamaki ta yi ba. Za Ta iya rantsewa ko yatsan kafarshi bai motsa ba

Ta cikin mayafin take satar kallon fuskar shi, wacce ta canja zuwa ta sojojin, ba ta taɓa kura da idanunshi jajaye ne ba sai yau.

Tun tsayawar na yi mata dadi har ta gaji ta fara mutsu-mutsu, saboda wasa-wasa sun kwashe wajen awa daya a tsaye.

Ba ƙaramin dadi ta ji ba, da ta ji Ahmad ya yi mata alamun zama, Sai ko ta zauna din ba jira, yayin da suka ci gaba da kallon parrade din kala-kala har da a kan doki, wanda ya sha ado da kayan sojoji.

Abu daya ne ke damunta karar gangar nan, duk lokacin da aka bugata sai kanta da kirjinta sun amsa, saboda gangar ta kosa a tashi, amma don parrade din idan za a kwana ana yi ba za ta gaji da kallo ba.

Sai da aka kira sallahr magriba taron ya tashi, wannan karon kam ba mota daya suka shiga ita da Ahmad, tare da kawayenta aka kwashe su, haba labari sai in ba a yi, kowa fadin abin da ya fi burge shi yake yi

Cikin dariya Nabila ta ce “Allah Hafsat yau kin ban dariya lokacin da aka buga gangar nan wlh ina kallon ki za ki ruga da gudu”

Gabadayansu suka kwashe da dariya, hatta Hafsat sai da ta dara, cikin dariya Juwairiyya ta ce “Ashe kin lura ke ma. Yau kam da ta bamu kunya”

“Ni kuma ban lura ba Sam” cewar Farida cikin dariya

Ni’ima ma ta ce “Allah ni ma ban lura ba”

“Saboda hankalinku baya kanta ne” cewar Nabila tana ci gaba da dariya.

“To ya aka yi ta tsaya?” Farida ta tambaya har lokacin dariya take yi

“Yo Angon ne ya riko ta” Juwairiyya ta amsata

Sai ko suka kara kwashewa da dariya

“Allah Ya Tajuddeen ma ya gani, lokacin da ya kira ni din nan sai da ya ce min kin ga Hafsat za ta gudu ta ganga ba irin ta kauyensu ba” cewar Nabila

Cikin dariya Hafsat ta ce “Ki ce na bani da sharri kuma”

“Amma fa kin yi kyau, ko in ce kun yi kyau, kai wlh har sai na ji Ina son auran soja. Ke kin ga wata ƙamewa a wurin Ahmad, fuskar nan kamar bai taɓa dariya ba. Yasin shi nai ta kallo ina mamakin yadda ya canja lokaci daya” Cewar Juwairiyya

Nabila ta amshe “Ashe ba ni kadai ya ba mamaki ba, kuma sosai kayan sun yi mishi kyau wlh”

Farida ma ta ce “Gaskiya duk sun yi kyau, Hafsat tana ban dariya idan na kalle su na ganta can a kasan shi, wai duk tsawonta fa ba ta gama kamo kafadarshi ba”

Suka kuma tuntsirewa da dariya.

Haka su kai ta tattaunawa har sai da direban ya ajiye su kofar gida.

Gidan ba kowa sai Mama  kadai, da alama sune suka fara isowa, daga baya ne mutane suka fara shigowa, da yawansu ƴan’unguwa ne da abokan huldar Mama. Sai 10pm gidan ya kasance daga Mama, Goggo, Ya Tajuddeen, Juwairiyya, Farida,, Nabila da kuma Ni’ima

Hafsat dai kwance take kan 3 sitter tana sauraron hirarsu, har ta gaji da dariya, saboda duk kauyencin da ta yi suke lissafawa, musamman Tajuddeen kamar mistake din ta ya je gani

Goggo ce kawai mai yaba komai, tun da ita ma ba ta taɓa gani ba sai ranar. Hira sosai suka yi, Sai 12am suka kwanta.

Safiyar Alhamis kuma aka ci gaba da karbar baki, saboda ranar Juma’a za a daura aure.

Ranar dai kowa ya ci tuwon gidansu aka yi

Can gidansu Ahmad iya su suka cashe, nan ma su Nabila sai suka kira DJ ya zo ya, sakar musu kida a farfajiyar tsakar gidan suka cashe sosai, sai magariba aka tashi.

Safiyar Juma’a kuma aka nufi Maƙera inda za a daura aure.

Ranar dai garin Maƙera sun ga baƙi, sun ga manyan motocin da basu taba gani ba, tun daga kofar gidan Maigari, kofar gidan Malam Ayuba, masallacin juma’a, cikin kasuwa, da filin kwallon da ke kusa da kasuwar motoci ne, abun ne ya hadu biyu, saboda a ranar kuma za a ba Ahmad Sardaunar Samarin Dawuri, shi ya sa jama’a kamar ana arfat.

Malam Ayuba dai kuka kawai yake yi, bai taba tunanin zai iya tara wadannan mutanen ba, Sai ga shi ta dalilin shi manyan mutanen da bai san iyaka ba sun taru.

Ana idar sallahr juma’a aka daura auran Hafsat, auran da tun da aka tsiri garin Maƙera ba a taba daura irinshi ba.

Ana gama daura auran suka juyo zuwa Dawuri inda kofar fada take cike da makaɗan fada ga algaita ana ta busawa.

Ahmad dai ranar ba ya taruwa, mutane sun yi mishi yawa, duk rashin son hayaniyarshi ranar kam dole ya haƙura.

Bangaren Hafsat ma ana yin sallahr la’asar motoci suka zo daukar ta, wai so ake yi tana gidan a ɗaurawa Ahmad rawani.

Tun tana jin dadin game din har ta ajiye, saboda kanta ya fara ciwo, misalin karfe 8:30am ta ji ana knocking kofa, Asabe ta gani tsaye hannayenta du biyun rike da basket, cikin girmamawa ta gaishe ta, Hafsat ta amsa hade da amsar basket daya suka shiga ciki, kan dinning suka ajiye Asaben na fadin “Hajiya ta ce a gaishe ki”

“Na gode sosai” Hafsat ta amsa cikin murmushi, Kafin Asabe ta kara yin godiya ta fice.

Hafsat kuma ta shiga bude kwanukan, flask na farko kunun gyada ne, flask na biyu black tea ne mai ƙamshin wani abu da ba ta sani ba.

Flask na farko kuma pepesoup ne na kayan ciki sai turiri yake yi, ga kamshi mai dadi, dayan flask din Kuma yamballs ne ya ji kwai sosai.

Cikin rike baki Hafsat ta ce “Masu kudi sun ji dadinsu”

Kunun gyadar ta tsiyaya hade da zuba yamballs din mai yawa, saboda ba za ta yi fulako ba.

To fara ci kenan sai kuma ta ji zuciyarta na tashi, dalilin da ya, sanya ta komawa kan pepesoup din, ba ta jima da fara ci ba, dole ta yi toilet da gudu ta shiga kwarara amai, a galabaice ta fada kan kujera ta kwanta, cikin kankanen lokaci zazzabi ya rufe ta.

Zuwa 10am kuma baƙi suka fara zuwa yi mata sallama, ciki har da su Farida, sosai jikinsu ya mutu ganin yadda take kwance sharkaf, Juwairiyya ce ta turawa Ahmad sako, a kan Hafsat ba ta da lafiya sosai.

Bai yi reply ba, sai dai bayan shigar sakon da kamar 20mns, sakon shi ya shigo wayarta, inda yake shaida mata ta kamo ta zuwa waje.

Tun da suka fito ya bude kofar front seat, dakyar Hafsat ta iya shiga, sosai jikinta ba ƙwari.

Juwairiyya kuma ta koma ciki.

Sai da suka fita daga farfajiyar gidan ne ya kalle ta tare da fadin “Zazzabin dawowa ya yi?”

Kai ta jinjina a hankali

“Shi ne ba za ki iya kirana ba kuma?”

Komai ba ta ce ba, Sai ma kanta da ta kwantar jikin kujerar hade da lumshe idanunta

Shi ma koman bai ƙara cewa ba.

Ba ta bude idanun ba, Sai da ta ji ya yi parking, maimakon parking space na asibitin yau a kofar shiga reception ya yi, yana bude mata kofar motar sister Larai ta fito, cikin murmushi ta ce “Sannu da zuwa yallaboi, ya mai jikin”

“Da sauki” ya fada, lokaci daya kuma yana kamo hannun Hafsat ya fito da ita.

Daidai lokacin da Sister Hassana ta turo Keken daukar marasa lafiya, da kanshi ya zaunar da ita cikin Keken, sister Hassana Kuma ta shiga turawa. Zuciyarta na mata zafin rainin hankalin da Hafsat ta yi mata. Saboda zuwa yanzu ta san Hafsat matarshi ce, ba ta jin akwai wanda yake social media kuma bai ga videon auran nasu ba, saboda yanzu haka shi ne abin da yake trending. Mutane sai sharhi suke yi.

Da gaske ne duk wanda yake tu’ammali da social media ko yana so ko bai so sai ya ci karo da different videos na bikin Ahmad, Asma’u na daya daga cikin wadanda suka ci karo da videos din, duk da yadda ba ta son kalla, amma haka nan take kallo, ita kanta ba ta san ta wace hanya za ta kushe halittar Hafsat ba. Idan dai kyau shi ne sa ar aure to tabbas Ahmad Allah Ya yi mishi babbar sakayya da mace kyakkyawa. Tun daga lokacin da ta fara cin karo da videon shagalin ba ta kara samun nutsuwa, kawai dai tana dannewa ne ko don saboda AG.

Special ɗaki aka shiga da Hafsat din, yayin da Sister Larai ta shiga duba ta, Ahmad kuma yana tsaye ya yi tare da kallon yadda sauran nurse din ke taimaka mata. Sai bayan da ta sanyawa Hafsat drip ne sannan nurses din suka fita.

“Stress Ne kawai, In Sha Allah da zarar ta farka Zazzabin zai sauka, saboda malaria babu yawa” Sister Larai ta fada tana kallon Ahmad

Kai ya jinjina alamar fahimta.

“Allah Ya sanya alkairi Yallaboi, Ya sa abokiyar arziki ce, ya bayar da zuriya dayyiba” Sister Larai ta kuma fada cikin murmushi.

“Amin” ya amsa a, takaice.

Ita kuma ta fice, tun Hafsat na ganin duhu-duhunshi har bacci ya dauke ta.

Ba ta farka ba sai wajen biyu da rabi na rana, haka ta farka garas sai rashin karfin jiki kawai, amma ciwon kai da ciwon jikin nan duk babu.

Tana zaune a tsakiyar gadon suka shigo, a zuciyarta ta ce “Tip da Taya kenan” maganar dai suke yi, duk lokacin da suke wata hira sosai yadda suke tattara hankalinsu a kan juna ke ba ta mamaki, suna masifar ba juna attention din su.

Jikin durawa Ahmad ya tsaya hade da ajiye ledar hannunshi, yayin da Asad ya kara so wurin gadon, idanunshi a kan file din ta

Cikin tsokana ya ce “Amarya kin sha hayaniya akwai bukatar ki huta.”

Murmushi kawai ta yi tare da cewa “Ina wuni?”

“Lafiya kalau, ya jikin naki?”

“Da sauki”

“Ma Sha Allah”

Sai kuma ya juya kan Ahmad tare da fadin “Gidan za ku wuce ko?”

“Zai fi ai, idan ba damuwa” Ahmad ya masa after some seconds

“Kai ma ka je ka yi bacci don Allah, yanzu dai babu sauran wasu baƙi ai, you, have to rest”

Komai Ahmad din bai ce ba, Asad ne ya kuma cewa “You can go”

Ya yi maganar lokaci daya yana fita daga dakin hannunshi rike da file.

Kamar hadin baki sai suka kalli juna a tare, da sauri ta janye idanunta shi kuma ya ce  ” ya Jikin?”

“Alhamdulillah!” ta amsa kanta a kasa

“Za ki iya ta shi ne?”

Kai ta jinjina alamar eh, lokaci daya kuma tana kokarin sakkowa daga saman gadon, kasa hak’ura ya yi sai da ya taimaka mata ta sakko, ya kuma rika ta zuwa wajen motar. Bayan ta zauna ne ya aje ledar da ya shiga da ita dakin dazu a back seat.

Driver seat ya shigo kunnen Shi manne da waya yana fadin “Mun wuce” ba ta san me aka fada mishi ba, ta ga dai ya yanke wayar.

Lokacin da suka isa gidan, ba kowa sai Juwairiyya da Nabila, saboda su Farida tuni suka tafi, Sai kuma wasu sabbin flask din a kan dinning, da alama abincin rana aka kawo.

Gaisuwar su Juwairiyya kawai ya amsa ya haura sama, ita ma Hafsat bedroom ta wuce, brush ta yi hade da wanka sannan ta dauro alwala ta fito, Sai da ta yi sallah sannan ta dan ci abinci, suka rika taɓa yar hira da su Juwairiyya.

Sai biyar na yamma suka tafi, har zuwa lokacin kuma Ahmad bai sakko ba.

Sai da ana kiran sallahr magriba sannan ta rika jin takun sakkowar shi.

Jallabiya ce dark blue a jikinshi mai maiko, kamshinshi mai dadi ya cika falon

“Ya jikin?”

“Da sauki”

“Sorry na dan yi bacci ne”

“Ba komai” ta amsa

Kai ya jinjina kafin ya ce “Zan je masallaci”

“Allah Ya tsare, Ya sa a dawo lafiya”

“Amin. Na gode”

Yana fita ita ma ta shiga ciki don yin alwalar, bai dawo sai karfe takwas, yadda ya shigo da basket ya tabbatar mata daga gida yake

Sai ko ga shi ya ce “Hajiya na gaishe ki”

“na gode” ta amsa cikin fara’a. Ba ta san me ya sa ba, amma duk lokacin da za a ace Hajiya na gaishe ta sai ta ji wani irin dadi.

Hannunshi ya kai kan, wuyanta kafin ya ce “Ya jikin?”

“Akwai sauki”

“Ma Sha Allah”

“ki tattara sauran flask din direba zai ta fi da su”

“To, amma akwai sauran abinci”

“Za ki ci ne?”

Kai ta girgiza alamar a’a saboda duk zarinta ba za ta iya cinyewa ba

Yana tsaye ta gama hada su cikin basket, kafin ta mika mishi, bayan fitar shi kuma sai ta bude flask din da ya shigo dasu. Daya tuwon shinkafa ne ƙal naɗe a cikin leda, Sai miyar kubewa da ta ji nama ga karamar roba an sanya yajin daddawa, daya karamar kuma manshanu ne. Sai pepesoup na kai.

A fili ta ce “Idan haka zan rika ci kullum, Anya kuwa daɗi ba zai kashe ni ba?”

Jin ana taɓa kofa alamar za a shigo ya sa ta nutsu.

Kai tsaye stairs din da zai sada shi da dakin shi ya dosa, don haka ta ce “Abincin fa?”

“Ki ci, naki ne.”

Sai da tabbatar ya haye sama, sannan ta warware leda daya ta zuba miya ta naɗe shi tas, ta kuma saka leda daya, nan ma ta cinye tas. Kafin ta koma kan pepesoup din, ci take yi kamar waccc aka kayyade mata iya kwanakin da za ta yi tana ci.

Gudun kar ya ga ɓarnar da ta yi, kitchen ta kai flask din ta rufe gam hade da zara key din ta nufi bedroom din ta da shi.

Cikin baccin da ya fara daukar ta ta ji shigowar shi, hannun shi rungume da laptop . Kan sofa ya zauna, hade da bude laptop din ya shiga yin ayyukan shi, ya ɗauka bacci take yi.

Ita din ma tun tana kallon shi, har baccin gasken ya dauke ta.

<< Abinda Ka Shuka 51Abinda Ka Shuka 53 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.