Skip to content
Part 53 of 54 in the Series Abinda Ka Shuka by Khadija S. Moh'd (Matar J)

Cikin bacci wani ciwon ciki mai azaba ya tashe ta, zumbur ta mike a tsakiyar gadon hannayenta dafe da cikin nata, Sai da ciwon ya lafa ne ta, ta ga Ahmad kwance kan sofa, laptop din a kan kirjinshi.

Da ta fara bacci sai ciwon cikin ya farkar da ita, tun tana daurewa har ta sakko daga saman gadon zuwa inda yake kwance.

Cikin matsakaicin hasken take karewa fuskarshi kallo, sosai bacci yake yi

Hannunshi da ya yi filo ta shiga bubbugawa a hankali, ya bude idanunshi a nutse masu dauke da bacci ya dora a kanta.

Kamar za ta yi kuka ta ce “Cikina ne ke ciwo”

“kin ci wani abu ne?”

Ya yi tambayar da alamun bacci a muryar shi

“Ban ci ba, sai dai tuwon…” Dole ta yi shiru saboda yadda cikin ya murɗa mata. Ba ta san lokacin da ta kankame damtsen hannunshi, cike da azabar ciwo take fadin “Wash Allahna! Wayyyo cikina!!”

Dole ya tashi zaune, ba ta san lokacin da ta kwantar da kanta a kan cinyoyinshi ba, har zuwa lokacin da cikin ya lafa mata

“Sannu” ya fada lokaci daya kuma yana shafa kwantancen gashin kanta, hakan ba karamin dadi ya yi mata ba, Sai ta ji kamar yana rage mata ciwon ne.

Time ya duba karfe biyu saura na dare, ba ya jin zai kira Asad, idan har ba ciwon ne ya yi worst ba

“Dama kina ciwon ne?” daga kwancen ta girgiza kai alamar a’a

Ya shiga laluben me ya kamata ya ba ta, musamman yadda ya ga ciwon ya kara motsawa sai dai bai tuna komai ba, cak ya dauke ta zuwa saman gadon ya kwantar, ya ci gaba da kallon yadda take murkususu hannayenta dafe da cikin.

Sai bayan da ya lafa ne ya kuma cewa mata “Sannu”

Kai kawai ta daga alamar amsawa.

A hankali ta ce “Ina kafafuna wai?” ya bi ta da kallo har zuwa kan kafafun kafin ya ce “Ga su a jikinki”

“Taɓa su in ji” ta, kuma fada.

Gefen gadon ya zauna saitin kafafun nata ya taba, Sai cewa ta yi “Don Allah matsa min su, sun yi sanyi kamar basu a jikina”

A hankali ya shiga matsawar, shi da kanshi ya ji ƙafar tata ta fi ko ina sanyi a jikinta.

Tasowar ciwon kuma sai ta janyo hannun na shi ta dora a kan marar cikin kuka ta ce “Danna min nan da karfi. Wayyo Allahna!”

Bai biye ta ya danne mata da karfin ba ya dai danna daidai yadda za ta ji dadi, Sai ko ga shi har bacci yana daukar ta.

Ba ta samu barci ba sai gab asuba, Ahmad ma a dakin ya yi sallah, bayan ya idar da sallahr ne ya kira Asad

Bayan sun gaisa ne Asad ka  ya yi tsokana sannan Ahmad ya ce “Queen ba ta da lafiya”

“Subhnallah! Zazzabin ne ya dawo?” cike da damuwa Asad ya tambaya

“A’a, cikinta ne ke ciwo, kuma sosai fa”

“Subhnallah! Amma ciwon daga sama ne, tsakiya ko can karshe wajen mara?”

Shiru Ahmad ya yi, a kokarinshi na gano amsa, Sai, kuma ya tuna inda take cewa ya danne mata da karfi, don haka, ya ce “Marar ce”

“To an ya ba period ba, ka, tambaye ta ka ji, ko idan tana period tana ciwon ciki”

“Ta ce ba ta taɓa yin ciwon cikin ba” Ahmad ya yi saurin amsawa

“Amma bayan marar sai ina kuma take yawan yi ma complain?”

“Sai kafafunta, wai suna mata sanyi kamar ba a jikinta ba”

“Gaskiya period ne, kuma ka san zai iya canjawa ta rika ciwon cikin idan da can baya ba ta yi. Zan rubuto ma magani sai a ba ta”

“OK” Ahmad ya amsa, idanunshi a kan Hafsat da take baccin wuya.

Sai 6:30am ta tashi, har zuwa lokacin Ahmad na dakin, kuma laptop din Shi yake tabawa, har ta yi alwala hade da yin sallah bai kalle ta ba, Sai da ta ce “Ina kwana?”

“Lafiya, Ya jikin?” har zuwa lokacin idanunshi a kan laptop din ne.

“” Da sauki “ta amsa.

” Idan za ki yi period kina ciwon ciki? “ya, yi, tambayar ba tare da ya kalle ta ba

Ita ce ta kalle shi, yadda fuskarshi take ne ya sanya ta saurin girgiza kai alamar a’a

Saboda ita ba ma ta taɓa yin period din ba.

” Ba kya yi? “

Kai ta kuma dagawa alamar eh

” Sai me kike ji, na alamun zuwanshi?”

“Ai ban taɓa yi ba” yanzu kam ya dago kai yana kallon ta, Sai dai komai bai ce ba ya mayar da kan a kan laptop, a zuciyarshi Kuma yana kara jinjina kankantarta, kawai garin jiki ne ashe, yanzu da ya yi gajen hak’uri ya haike mata tun jiya fa, da shi kenan ya kusanci macen da ko period ma ba ta taɓa yi ba.

“Ina zuwa” ya fada lokacin da yake daga wayar shi.

Komai bai ce ba ya fice, Hafsat kuma ta bi shi da kallo, hade da nazarin maganarsu ta yanzun

Kamar 2mns sai ga shi rike da leda a hannunshi “Akwai magangana ki sha su da tea yanzu”

Bai jira amsar ta ba ya dauki laptop din ya fice.

Ledar ta bude, magunguna ne da pad packaged daya Sai pant guda 12.

Tuwon ta ta duma ragowar na jiya, ta ci hade da pepesoup din nan, sannan ta sha maganin, babu dadewa tsakanin shan maganin nata da kawo musu  abinci break din su.

Har 11am Ahmad bai fito ba, daidai lokacin ne kuma Hafsat ta ji kamar wani abu na zubo mata, da, sauri ta ajiye wayar hannunta ta shige toilet, sai kuwa ta ga jinta.

Cikin iyayenta mata na dangin Babanta wadanda suka biyo ƴan daurin aure aka fara kai ta, suka yi mata fada, sannan aka kai ta na wurin dangin mahaifiyarta su ma suka yi mata, sai kuma Alhaji Aminu da wakilci Malam Ayuba, shi ma fada ya yi mata mai ratsa jiki, wannan ya sa Hafsat ta rika dauke hawaye, hawaye na tuna abubuwa da yawa suke zubo mata, ji take ina ma Inna na raye ta ga wannan rana, ina ma ace a Ya Nasir na raye ya ga wannan rana, ta tabbata za su yi farin ciki, za su yi alfahari. In Sha Allah sune mutane biyu da take fatan Allah Ya ba ta ikon yi musu sadakatul jhariya, yadda za su san a bayansu akwai wata halitta da suka bari ta gari.

Motoci ne manya-manya na gani na fada, a kofar gidan jere, kamar yadda kowa ya sani mota ma fi kyau ita ce ta dauki amarya, tafiya suke yi a jere gwanin sha’awa ba tare da wani ganganci ba.

Ta cikin mayafin da aka lullubata ta rika kallon doguwar katangar ginin gidan Galadima.

Yau ce rana ta biyu da ta ga gidan, rana ta farko dai ita ce ranar da Tajuddeen ya kawo ta, a wancan karon daga nesa ta rika kallon gidan cike da burgewa, a wancan karon a mashin aka a kawo ta, a wancan karon ko kofar gidan ba ta samu damar tsayawa ba, hangen shi ta rika daga nesa. A wancan karon ta bar kofar gidan ne da sanin cewa har abada ba za ta shiga gidan ba, saboda ba ta da wani dalili na yin hakan…

Yau kuma ga ta a mota ma fi tsada, tare da rakiyar wasu motocin, za ta shiga cikin gidan a matsayin matar gida…

“Allah mai iko!” ta fada a, hankali lokacin da aka wangale musu gate din gidan, take kuma Dogarawa da Fadawa suka shiga fadanci, kirari suke zabga mata kamar an ba ta sarautar Tunga.

Hannunta cikin na Goggo Hanne kanwar Babanta suka shiga dakin Hajiya Babba

Wacce take kinshingide cikin tuntaye ga wata alkyabba ta alfarma ta sha.

Kallo daya Hafsat ta yi mata ta cikin mayafin ta fahimci ita ce mahaifiya Ahmad. Saboda akwai kamaninshi a jikinta.

Dattijuwa ce sosai, da ta tasarwa shekaru 60-65. Sai dai kwanciyar hankali da samun kulawa su boye shekarun nata.

A gabanta a tsugunnar da Hafsat, yayin da Hajiya ta tashi daga kishingiɗar da ta yi, lokaci daya kuma cikin nutsuwa ta daga mayafin da aka ɗorawa Hafsat. Da gudu Hafsat ta lumshe idanunta wadanda suka jiƙe da hawaye.

Fuskar Hajiya ɗauke da murmushi ta ce “Ma Sha Allah! Alhamdulillah!” ta kai karshen maganar hade da sauke mayafin, yau kam ta yarda ta kuma amince Hafsat kyakkyawa ce kamar yadda su Aunty Safiya suka sha fada.

Saman kanta ta dora hannunta na dama, a bayyane ta ce “_Allahumma Inni As’aluka Khairaha, Wa khairah ma Jabaltaha alaihi, Wa’azubika Min Sharriha Wa Sharrah Ma Jabaltaha Alaih_”

Hannun ta dauke haɗe da lalubo Hannayen Hafsat du biyun ta sarƙafe cikin nata, a tausashe ta ce “Barka da shigowa gidan aminci, gidan karamci. Muna yi miki fatan rayuwa ta har abada a cikin gidan, muna fatan ki zame mana abun alfahari. Muna yi miki fatan samun zuriya ɗayyiba. Muna yi miki fatan ki rayu cikin farin ciki da aminci.”

Duk abin da Hajiya ke faɗa Asabe shugabar ma’aikata da sauran Fadawa mata suna fadin” Amin Ranki Ya dade, Godiya ta ke Ranki ya dade! “

A hankali ta janyo Hafsat din tare da manna ta jikinta for some seconds, Sannan ta zare ta. Sai kuma ta miƙa hannu inda Asabe take tsaye, cikin girmamawa Asabe ta miƙa mata wani ƙoƙo da ya sha kwalli an rufe shi da faifai.

Nonon da ke ciki Hajiya ta guntsa tare da fesa shi a kan jikin Hafsat.

Take fadawa matan da ke cikin falon suka rangaɗa guɗa, Hafsat kuma numfashi ta sauke a hankali.

Karo na biyu Hajiya ta kuma guntsar nonon ta fesa mata, fadawan nan suka kuerangaɗa guɗa, Sai da ta yi hakan sau uku, sannan ta miƙawa Asabe ƙoƙon, ita kuma ta koma hade da kishingiɗa.

Yayin da Asabe ta kama Hafsat zuwa wani daki da ke cikin falon, suna shiga ta yaye mayafin Hafsat, cike da annashuwa ta ce” Ma sha Allah, lallai Ibangidana ya bude idonshi sosai a wajen zabe, kin cancanta “komai dai Hafsat ba ta ce ba, Sai fuskarta da ta nuna jikinta a sanyaye yake

Wani akwatin saƙi Asabe ta dakko cikin wardrobe ta bude, take wasu kayan saƙi irin na da suka bayyana. Su Asabe ta dakko haɗe da miƙawa Hafsat tana fadin” Je ki sanya wannan Ranki ya dade”ta kai karshen maganar haɗe da nuna mata kofar toilet.

Jiki ba ƙwari Hafsat ta shiga cikin toilet din ta canja kayan, ta madubi ta ga irin kyawun da kayan suka yi mata, Sai ta koma kamar wata diyar sarki a zamanin da.

Dakin ta dawo, Asabe kuma ta naɗa mata ɗaurin ɗankwali da wani kallabin saƙi.

Yayin da ta rufa mata wani zanen na saki, hannunta ta kuma riƙawa zuwa falon inda Hajiya da tawagarta suke zaune, saboda kadan daga cikin ƴan’uwanta aka ba damar shiga wurin Hajiyar.

A gaban Hajiya Asabe ta kuma durkusar da Hafsat, wata ƴar batta Hajiyar ta bude haɗe da fiddo murjani irin na da, ta sagala a wuyan Hafsat, ta kuma kama hannayenta ta sanya mata. Sai kuma ta miƙe tsaye, wannan ya sa cikin sauri Asabe ta mikar da Hafsat, sannan ta miƙawa Hajiya Alkyabba golden colour mai kyau irin ta mata, A nutse Hajiya ta zare mayafin saƙin da ke kan Hafsat ta dora mata alkyabbar. Ta kuma lalubo hannunta na dama ta miƙa mata wata sanda Ash colour mai kyau.

Cikin maganar kasaita ta ce “Ke ce Gimbiyar wannan gida, da fatan za ki rike wannan kambun”

“Godiya take Ranki Ya dade” cewar fadawan, kafin suka koma kan Hafsat da kirari.

Sai da suka yi mai isar su, kafin Asabe ta kama hannun Hafsat, sauran Fadawan suka bi bayanta.

Fadar Galadima suka shiga, inda manya-manyan mutane suke zazzaune, ga kuma Dogarai da Fadawa ana ta fadanci. Shigowar ta sai kowa ya miƙe alamar girmamawa, yayin da su Asabe suka shiga miƙa gaisuwa irin ta fada, sannan ta ƙarasa da Hafsat gaban Galadima, ya sanya mata albarka, haka ta rika bin mutanen da ke cikin fadar daya bayan daya tana gurfanar masu da Hafsat. Su kuma suna sanya mata albarka haɗe da yi mata fatan alkairi.

Tun da Hafsat ta shigo Ahmad ke satar kallon ta, kyan da ta yi ko ranar da suka yi sword cross ba ta yi shi ba. Sosai ta yi kyau a cikin kayan sarautar. Wani irin dadi yake ji, Hafsat matarshi, ga ta very young, very smart, very innocent and very beautiful.

Babu wanda zai ce Hafsat ba ta hada wadannan abubuwan da ya lissafo ba, ya rasa wane irin so ne Allah Yake mishi da ya haɗa shi da Hafsat a matsayin mata. Fatanshi Allah Ya zaunar da su lafiya.

A kan wata shimfida Asabe ta zaunar da Hafsat, yayin da aka shiga hidimar naɗin Ahmad, ta kasan ido take satar kallon shi, yayin da sarkin naɗi yake shirya shi cike da ƙwarewa, kofar fadar kuma kidan sarakuna ne ke tashi hade da busar algaitu.

Cikin abin da bai fi minti goma ba, Ahmad ya fito fest cikin shigar Sarauta, shigar da ta yi mishi kyau a wurin Hafsat, sama da duk wata shiga da taba ganinshi a ciki. Shi ma alkyabbar da sanda aka mika mishi, Ya rika bin manyan mutanen da ke cikin fadar yana kwasar gaisuwa kafin daga bisani ya zame gaban Galadima.

Ba ta san me aka fada ba, ta ji dai fadawa sun dauka “Godiya take yi Ranka ya dade, Allah Ya ja da ran Galadima.”

Sai kuma ta ji Asabe ta kwalla guda, kafin daga bisani ta kama ta zuwa waje, tare da rakiyar na ta dogaran mata.

Kusa da kunnen ta Asabe ta ce “Galadima ya ba ki doki uwar ɗakina”

Komai Hafsat ba ta ce ba har zuwa lokacin da suka isa farfajiyar gidan inda ake ta shagali.

Ka doki Ahmad ya hau, yayin da sauran ƴan fada ke kawo gaisuwa tawaga-tawaga. Hafsat kam sai ido, sosai komai yake burge ta.

Sai da aka kira sallahr magariba sannan taron ya koma cikin gida. Dakin Hajiya aka kuma mayar da Hafsat, a can ta yi sallahr magariba da isha’i, ta dan ci abinci kadan, saboda wani irin ciwo kanta ke yi, ba iya kai ba jikinta ma kaf ciwo yake yi.

Sai 9am aka fito da ita daga gidan sarautar zuwa asalin nata gidan.

Tun da aka shiga ta ji mutane na ta satin gidan wai kamar ba a Dawuri ba, haka su kai ta zagaye ko ina, musamman kawayenta, duk abin da suka gano na burgewa sai su zo su fesa mata, su kuma komawa.

Sai 10am gidan ya kasance tsit, alamar babu kowa, hatta kawaye Mama cewa ta yi a mayar dasu can gidanta su kwana.

Sam Ahmad bai san mutanen gidan duk sun tafi ba, ya dauka akwai wadanda za su kwana a gidan musamman kawaye, shi ya sa sai wajen karfe daya na dare ya baro cikin mota ya shigo cikin gidan, ya san dai zuwa lokacin kowa ya yi bacci.

Sai dai kuma yana turo kofar falon  ya ci karo da Hafsat kwance saman kujera tana baccin wahala, saboda wani zazzabi ne mai zafi gami da kwankwatsar jiki ya rufe ta, sai 12 saura ta samu bacci ya dauke ta.

Shi ya sa ma sam ba ta ji shigowar shi ba, falon ya rika bi da kallo, wanda aka zubawa kaya masu kyau da tsada, duk wanda ya ga gidansu Hafsat ba zai ce za a iya yi mata wadannan kayan ba. Kodayake Hausawa sun ce fadawa mai zuciya biki ba mai dukiya ba. Amma kayan da ke cikin falon ko diyar gwamna ya auro sai haka.

Ya nufi staira din da ke cikin falon, wanda zai sada shi da dakin shi, a hankali yake takawa har ya haye saman, wanka ya fara yi da ruwa mai ɗan ɗumi, ya yi nafila hade da shafa’i da wutri, sannan ya kuma sakkowa falon, saboda jikinshi yana ba shi ba kowa a gidan sai ita kaɗai.

<< Abinda Ka Shuka 52Abinda Ka Shuka 54 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×