Skip to content
Part 54 of 54 in the Series Abinda Ka Shuka by Khadija S. Moh'd (Matar J)

Cikin bacci ta rika jin iskar da take shaƙa gami da fesarwa ta canja kamshi, shi ya sa a hankali ta shiga bude idanunta har ta bude su kaf a kanshi, kasancewar ba ta kashe hasken falon ba ta yi bacci, shi ya, ba ta damar ganin fara ƙal din jallabiyar da ke jikinshi, wacce aka yi wa ado da golden colour din zare.

Cikin dafe kanta wanda yake mata ciwo har zuwa lokacin ta miƙe zaune.

“Ba kowa a gidan ne?”

Kai ta daga alamar eh.

“Kan na ciwo ne?” ya kuma tambayarta, saboda kallo daya za ka yi mata ka fahimci ba ta da lafiya

Kan ta kuma dagawa alamar eh.

Hannun nata ya janye, haɗe da dora na shi a kan goshiinta, sai kuma ya yaye hajabin da ke jikin ya mayar da hannun na shi saman wuyan ta, tare da fadin “Kin sha magani ne?”

Kai ta girgiza alamar a’a

Hannun nata ya rika, suka rika haurawa saman a hankali.

Gefen gado ya zaunar da ita, hade da hado mata tea ya mika mata. Ta shiga sipping a hankali, sai da ta yi rabi kafin ta mika mishi, shi kuma ya mika mata pcm, Sai ta kuma karbar tea din ta sha maganin da shi.

Kafadunta duk biyun ya kama hade da kwantar da ita, kafin ya rage karfin AC din.

Shi kuma ya koma kan sofa ya kwanta.

Tun Hafsat na kin yi bacci na bakunta har ya dauke ta, ba ta farka ba sai ana sallame sallahr asuba, ganin baya dakin, Sai ta biyo kofar da ya shigo da ita, ta koma dakin ta, a can ta yi alwala haɗe da yin sallah,ta yi azkhar din safe da kuma karatun qur’ani, zuwa lokacin ba ta jin zazzabin sosai, shi ma ciwon kan sai kadan.

Katon gadonta ta haye, tana karewa bedroom din kallo, wai ita Hafsat mai kwana a dakin kaji, yau ita ce a wannan bedroom din, saman wannan gadon, ko nawa Mama ta kashe wajen fitar da ita wannan kunyar oho.

Saboda ta san dai ita ce karfin duk wannan hidimar. Daki kamar ba na ta ba

Ba ta iya komawa baccin bayan sallahr asuba ba, shi ya sa ta dakko wayarta ta shiga sana’arta ta game.

Arround 6:30am ta ji ana taba kofar shigowa, shi ya sa ta mayar da hankalinta kai, ganin kuma shi ne ya shigo, kan ta dauke hade da mayar da shi kan wayar.

Sai da ya zauna gefen gadon ne, ta mike zaune tare da fadin “Ina kwana?”

“Lafiya kalau, ya jikin naki?”

“Akwai sauki Alhamdulillah. Na gode”

Komai bai ce ba, saboda bai san godiyar me take yi ba.

Sai ma ya daga kiran da ya shigo a wayar tashi, shiru ya yi yana sauraron abin da ake fada, kafin cikin zafin da Hafsat ba ta san yana da shi ba ta ji ya ce “Are you stupid Daniel?”

Ba ta san me aka fada ba a dayan bangaren, ta ga dai ya kara hade fuska sosai, dalilin da ya sanya ta pause na game din da take yi.

Tsoki ya ja hade da yanke kiran, lokaci daya kuma yana kiran wata lamba, bayan a daga kiran ne ya ce” Amos, akwai wata mota tana nan za ta wuce ta checking point na ku Mai lamba(ya shiga karanto lambar) kar ka bari su wuce “

Ba ta san me aka fada ba, ta ga dai ya yanke kiran haɗe da kiran wani layin.

” A/o kana ji na ko, sojojin da suke standby din a samu mota uku, yanzun nan a tura su Zungur, akwai alamun samun rikicin kabilanci. Saboda yanzu haka motocin da muke zargi, daya ta wuce”

Ya jima shiru, almar yana saurare, kafin daga bisani ya yanke kiran, hade da kara kiran wani layin yanzu kam hands-free ya saka, cikin fada ya ce “Daniel!”

Daga can Daniel ya ce “Sir!”

“Idan sauran motocin sun taho, ka kara bari su wuce”

“, sorry Sir!” cikin muryar sojoji Daniel ya fada.

Shi kuma ya yanke kiran. Hade da jan tsoki, har zuwa lokacin fuskarshi ba ta warware ba.

“Ina zuwa” ya fada lokacin da yake daga wani kiran, bayan ya yanke kiran ne ya dube ta sai kuma ya kawar da kai, saboda yadda take kallon shi da damuwa a fuskarta sai ya ji bai ji dadi ba, ga shi kuma ya kasa warware fuskarshi, sosai ranshi ya baci

“Ki tabbatar kin ci abinci idan an kawo, zan je in sallami baƙi” ya yi maganar lokacin da yake miƙewa zuwa kofa

“To” ta amsa

Shi kuma ya fita.

A hankali yake sauka daga stairs din entrance din, tun kafin ya karasa Asad ya bude mishi kofar motar, shi ya sa yana isa motar kawai ya shige, hade da jingina bayanshi jikin kujera.

Wata katuwar leda Asad ya aje mishi a kan cinyarshi, ba tare da ya ce komai ba. Ahmad kuma ya shiga bincike ledar, kayan makarantar Hafsat ne a ciki, komai akwai, uniform Kala biyu, sandals, school bag da kuma exercise book da text books.

“Yanzu goben ne za ka koma?” cewar Asad cikin rashin jin dadi

Ajiyar zuciya ya sauke a, hankali kafin ya ce in Sha Allah.

Cikin rashin jin dadi Asad ya ce ” Sam ban so zuwan ka Isreal din nan ba, Haba don Allah, just 1 week after marriage”

“To ya zan yi?”

“kana da wlh, idan ka ce ba ka so ya zauna saboda kana da hanya”

Murmushi Ahmad ya yi kafin ya ce “Wai idan na zauna a nan din me zan yi?”

Wani kallo Asad ya aika mishi, wanda ya sanya Ahmad murmusawa Asad din kuma ya ce “Ban gane me za ka yi ba, kai da kake da amarya ɗanya shakaf.”

“Har sau nawa zan fada ma she is very young, Zaitun din ma fa ta girme ta. Ko ka san sai a nan ta fara period”

“To shi ne me?”

Ido Ahmad ya fitar kafin ya ce Let’s assumed na kusanci yarinyar nan Asad, da shi kenan na kusance ta ko period ba ta fara ba. Haba da Allah. Kamar mutum fa ya ci ɗanyen abinci ne”

Wata irin dariya Asad ya gaggaɓe da ita, cikin dariyar ya ce “Gaskiya kam, ya kamata a bari ta, nuna”

“You see! Six months zan yi, 3 months for course and 3 months for peace keeping. Ka ga Lokacin da zan dawo ta gama school, Sai a nemar mata university mai kyau, a cigaba da rakawa ko year 2 ta kai”

Kai Asad ya jinjina alamar yana fahimta har zuwa lokacin akwai murmushi a kan fuskar shi

Hakan ya sa Ahmad bude kofar motar ya fito rike da ledar bayan ya ja dogon tsoki, dariyar da Ahmad yake ta faman riƙewa ita ce ta fito, don haka ya shiga yin ta, har sai da ya ji ya gaji, sannan ya fice daga gidan yana ganin wauta irin ta Ahmad. Kai yau kam ya yarda ƴan fari basu da wayau, yo idan ba rashin wayau ba, waye zai yi wannan abun.

Hafsat kam murna ba a magana, abun har mamaki ya ba shi, saboda a gaban shi ta yi tsalle hade da daga kayan, wannan na daya daga cikin abin da ya sa yake kara yi mata kallon yarinya.

Ko irin tsoron mazan nan da sabbin amare ke yi ita ba ta yi, kai tsaye take abun ta. Abin da ya fahimta kallon shi take kamar Yayanta.

Hasashen Ahmad din gaskiya ne, Hafsat ta na yi mishi kallon marigayi Nasir ne, duk da akwai bambancin halaye da dabi’u sosai a tsakaninsu, hakan bai sa ya daina yi mata kama da Nasir din ba

Ahmad ko very giant ne gallon officer and very young soldier. Dirinshi da ƙirar da Allah Ya yi mishi kadai ya isa ka fahimci ya cancanci zama soja.

Dogo ne sosai, irin dai tsawon nan na kyau, yana da ƙiba ta cika ido, saboda jikinshi a murɗe yake alamar karfi. Haka kirjin nan a bude faffaɗa. Yana da ɗan hasken fata kadan, doguwar fuska mai dauke da dogon hanci gami da gazar-gazar din gashin gira.

Fuskar suɓul take babu gashi ko ɗaya, haka kanshi ma bai faye barin gashi ba, ba dai a aske tal, haka kuma baya cika

Ko man shi gently yake yin sa a nutse. Idan kuma ya canja fuska sai ya zama kamar wani zaki a tsakiyar kananan dabbobi.

Sam baya son hayaniya ko kara mai karfi, shi ne ya mayar mata da waya a vibration, sannan duk lokacin da zai same ta tana kallo sai ya rage ƙarar Tvn ko ba zai zauna ya kalla ba

Nan ya bar ta a falon tana ta tsalle sai ta ji ɗokin zuwa makarantar ya kore jimamin da take yi na tafiyarshi

Dama tun da ya ce wurin Hajiya za ta koma ta ɗan ji sauki, amma yaushe za ta rayu nan shiru daga ita sai dogarawa da jimi’an tsaro.

Tun da ya tafi masallaci magriba bai dawo ba sai wajen tara saura, wannan ya tabbatar mata da gida ya je.

Zaune take tana kallo ta ji karar kofa alamun ya shigo, sai da ya ɗan murɗa kunnenta a hankali sannan ya dauki remote haɗe da rage ƙarar Tvn. “

Basket din hannunshi ya aje mata lokaci daya kuma yana haurawa sama

Kamar kullum dai yau ma tuwon ne, sai da ta ci ta koshi, sannan ta kai ragowar fridge, ta koma dakinta, wanka ta yi gami da brush ta yi kwanciyarta

Bangaren Ahmad wani abu ne ke yi mishi zillo a zuciya, babu abin da yake bukata irin ya ji Hafsat a jikinshi, ba yau ne ya fara jin hakan ba, kullum sai ya yi da gaske yake iya danne feeling din shi a kanta.

Yau ɗin ma dakyar ya danne feeling din zuwa lokacin da aka kira sallahr asuba, kasancewa jirgin 11am zai bi shi ya sa bai bata lokaci ba ya shirya komai na shi, Hafsat ma haka ta shirya duk abin da za ta bukata a can, sosai wani irin abu mara dadi take ji, yau kwanansu tara da aure, amma ta dan saba da shi, yana da hakuri hade da kawaici.

A can gidan suka yi break, zuwa lokacin duk ƴan’uwa na kusa sun zo, misalin 9am motar da za ta kai shi Nasara ta fito, abun da ya ba Hafsat mamaki shi ne yadda da yawan ƴan’uwanshi suke kuka, musamman mata, Hajiya ma haka ta rika dauke hawaye, shi kuma idanun nan suka kaɗa suka yi jawur, fuskar nan a cunkushe.

Duk rubibin da suke yi na yi mishi rakiya wurin mota ita ba ta je ba, Sai kawai ta yi kwanciyarta, zuciyarta babu dadi, ta rasa abin da ya fi daga mata hankali yanzu tsakanin tafiyar Ahmad da koke-koken da ƴan’uwanshi ke yi.

Ita ba ta ga wani abu sabo ba, ba yau ya fara tafiya wurin aiki ba, ko dama haka suke yi, sui ta kuka idan zai tafi, saboda ita dai ce mata ya yi kawai zai koma aiki, kuma ba zai jima ba zai dawo, amma za ta koma gida wurin Hajiya. A nan ba ta ga wani abun tayar da hankali ba, har su tayar ma wani. Ta karshen maganar hade da jan siririn tsoki, tana kwance suka fara dawowa ɗakin, ba kunya kuma sai suka warware aka shiga hira har da dariya da shewa.

Sai yamma lis suka rika tafiya gida. Bayan tafiyarsu Hafsat da kanta ta shiga gyaran Hajiya sabanin Asabe, duk wani aikin gida ta iya idan ka dauke girki, shi ne kam ba ta da kwarewa a kai, saboda ba yi take yi ba.

Sosai Hajiya ta ji dadin hakan, Sai ta tuna mata da Asma’u, ita ma haka take yi, ita ke gyare ko ina fes.

Sai around 9am,Hajiya ta ce a raka Hafsat bangarenta, Asabe ce ta yi mata jagora zuwa sashen.

Bayan fitar Asabe Hafsat ta rika bin ko ina da kallo, duk girman  falon dai babu komai a ciki sai labulaye lemon green masu kyau. A karshen falon ne aka fitar da dinning Area, nan ma akwai dinning dauke da kujeru masu kyau, ta cikin dining din za ka iya shiga kitchen, da sabbin kayan kitchens ta yi arba lokacin da ta leka, bayan ta fito ta shiga corridorn da zai sada ta da dakunan gidan, haka ta rika bude kofofi har zuwa lokacin da ta bude wata kofa, royal Chairs Ne sabbi jajaye, labulayen ma jajaye ne, sosai falon ya yi kyau musamman kamshin sabbin kayan da yake fitarwa, wata kofar da bude katon gadon da ta gani ya tabbatar mata da bedroom ne, Sai da ta gama bincike ko ina, sannan ta fito zuwa dakin gaba, budewarta ke da wuya ta yi arba da fararen kujeru leather masu matakar kyau, labulayen milk ne da aka yi wa ado da wani golden abu mai walwali, komai na cikin dakin tun daga falo zuwa bedroom din farare.

Sosai ta ji wurin ya burgeta, tsaye ta yi gaban hoton Ahmad tana kare mishi kallo, da kanta ta yi murmushi hade da shafa hoton saboda abin da ta fada a zuciyarta cewa ta yi “Wai wannan mijina ne, ikon Allah!”

A yadda ta fahimta, dakin farko da ta fara gani shi ne nata, saboda har akwatinta ta gani a saman wardrobe, wannan Kuma shi ne ɗakinshi. Akwatin nata ta ɗakko hade da maido shi dakin, saboda ya fi mata kyau, a zuciyarta ta ayyana idan ta ji ya kusa dawowa, Sai ta gyara mishi na shi dakin.

Kiran da ya shigo wayarta ne ya yanke mata addu’ar baccin da take yi, da sauri ta daga ganin Ahmad ne.

“Ba ki yi bacci ba?” ya tambaye ta bayan da ya gama amsa gaisuwarta

“Zan yi yanzu. Fatan ka isa lafiya?”

“Sai da na kira za ki tambaya?”

Murmushi ta yi mai cike da kunya kafin ta ce “Ina bangaren Hajiya ne sai yanzu na dawo nan”

“Text now”

“Ban tuna haka ba”

“Na tuna miki”

“Na gode” ta amsa a hankali

“Akwai wata matsala ne?”

Kai ta shiga girgizawa a hankali kafin ta ce “Babu”

“Idan kina bukatar wani abu, ko idan akwai wani abun, ki fada min, ko Hajiya kin fahimta?”

Kai ta jinjina alamar eh, kamar yana gabanta

“Daga gobe kuma zan shiga wurin da babu network sosai, so a WhatsApp kawai za ki iya samuna.”

“To” ta amsa a hankali.

“Bacci mai kyau” bai jira cewar ta ba ya yanke kiran.

Shiru ta yi hade da kallon screen din wayar, Sai kuma ta tura ta kasan filo ta ci gaba da addu’o’inta”

Haka ta ci gaba da zama a gidan, gari na wayewa tana bangaren Hajiya, Sai dare ta dawo nata, aikinta kawai shi ne gyara inda ta kwanta da wankin bayan gida, sai kuma falo da bedroom din Hajiya, su ma duk ita ta sanya kanta, Sai kuma bin su Asabe kitchen tana dan koyon girki.

Sosai Hafsat ta saki jikinta a gidan, abu daya da ba ta wasa da shi, shi ne abinci, sakin jiki take yi ta ci sosai, ji take kamar damar da ta samu za ta kwace mata.

<< Abinda Ka Shuka 53

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.