Skip to content
Part 55 of 60 in the Series Abinda Ka Shuka by Khadija S. Moh'd (Matar J)

Tsakaninta da Ahmad kuma sai chat ko video call, mutanen da ke kewaye da ita, suka hana ta kewar shi. Dama ba wani sabawa ta yi da shi ba.

Satinshi daya da tafiya ta fara zuwa makaranta, Sai take jin ina ma ace tun farko a haka ta fara karatunta, makaranta ce da komai cikin tsari ake yin shi. Babu wata maganar seniority, duka class dinsu, su 20 kacal, ko wanne da lokar shi. Daukar darasi a nutse, babu hayaniya, ga Ac, ga kuma kayan aiki. Ko ba ka so dole ka iya.

Zulaihat Mustapha Sandamu (Hana) ita ce wacce tasu ta fi zuwa daya da Hafsat, shi ya sa ko wane lokaci suna tare har sai an tashi. Amma Hana tana bangaren Boarding school ne. Saboda ta shaidawa Hafsat daga Abuja aka kawo ta, amma asalin su yan Sandamu ne a jihar Katsina.

Hafsat ji take kamar an kwatota daga hannun kidnappers idan ta kwatanta rayuwarta ta baya da ta yanzu. Za a kai ta school a mota, a dakko ta a mota, ta yi karatu a cikin Ac. Ta dawo gida ta iske abinci lafiliyayye. Iya ka ci ta ci kawai ta kwanta ta yi bacci.

Duk bayan sati biyu ranar Friday ake kai ta wurin Mama, su Nabila kam tun da aka gama biki suna school, Sai dai a chat da video call suke haduwa. Maƙera kuwa da Babanta kadai take waya, Tukuro ba shi da waya sai dai Mp yake da ita, ta shan kida a cikin daji. Amma sosai take kewarshi

Cikin wata daya  jikinta ya fara karbar canjin da yake samu, ta yi yar Kiba, fatar nan ta kara gogewa. Gashi luf-luf ya fara kwanciya a jikinta.

Yau ma kamar kullum around 2:30pm ta shigo gidan, stress din gajiyar makarantar kaɗan ne.

Kai tsaye kuma sashen Hajiya ta yi wa tsinke.

A babban falon ta cimma Hajiyar zaune da waya a hannunta, da alama kira ta gama amsawa.

Hajiyar ta amsa sallamarta hade da yi mata sannu da dawowa.

Ta amsa daidai tana zama daya daga cikin luntsuma-luntsuman kujerun alfarma da suke falon.

socks din kafarta ta shiga zarewa a hankali, yayin da Hajiya ke kallon ta, wani lokaci idan tana abu sai ta ga kamar Ahmad, sosai ita ma akwai nutsuwa a tare da ita, mini hijab din jikinta ta zare, take kwantancen baƙin gashinta ya bayyana. Ido ta lumshe hade da shakar iska ta kuma furzar.

“Akwai yunwa ne?” Hajiya ta tambaye ta

“Kadan” Hafsat ta amsa hade da mikewa ta nufi dining, abinci ta zubo cikin plate, ta dawo wurin da ta zauna, ta aje abincin hade da wucewa dakin Hajiya inda ta ajiye wayarta a lokacin da za ta tafi school, saboda basu zuwa da waya.

Ƙasa ta zauna hade da nade kafafunta, ta fara cin abincin a nutse, lokaci daya kuma suna taba yar hira da Hajiya sai kuma idanunta da ke kan screen din yawarta tana kallon sakonnin da aka tura mata a WhatsApp.

Kiran Ahmad ya shigo wayar, ta kasan ido ta saci kallon Hajiya, Sai kuma ta mike hade da dakko earpiece ta Jonas Sannan ta daga kiran.

Fuskarshi ta bayyana garai-garai kamar yana gabanta, ta cikin earpiece din ya ce “Sai yanzu kika dawo school din?”

Kai ta daga alamar eh, lokaci daya kuma tana cin abincinta a nutse

“Ya school din?”

Hannunta na dama ta daga irin na kurame alamar lafiya.

Kallon da ya yi mata ne ya sanya ta murmusawa, sai kuma ta juya camera zuwa kan Hajiya da take zaune hankalinta a kan waya. Bayan ta tabbatar ya ga Hajiyar sannan ta mayar da cameran kanta.

Siririn murmushi ya yi kafin shi ma ya daga hannunshi ya yi mata sannu irin na kurame sannan ya yanke kiran.

Friday.

Kai tsaye gidan Mama ta ce direba ya wuce da ita, saboda yau tashi ta yi zuciyarta Sam babu dadi, kila ta dan warware idan ta je gidan.

A kofa ta hadu da Ya Tajuddeen, hannunshi rike da sallaya da alama masallaci zai tafi, kallon da yake yi mata ne, ya sanya dora hannunta a kan bakinta tana dariya.

Gefenshi ta raɓa da zummar wucewa, Sai ya daga sallayar hannunshi hakan ya sa ta zubara da gudu tana dariya sosai. Shi ma cikin dariyar ya ce “Na sace ki wlh. Kullum kina ta wani kara kumbura kamar ana saka miki yeast”

Dariyar ta kara saki hade da shigewa cikin gidan da gudu. Goggo da ke tsaye kofar dakin Mama ta juya da sauri kafin ta ce “Ah’aha! Hafsat ce, ke da wa kike gudu?”

Daga cikin dakin Mama ta ce “Wace Hafsat din?”

Shigowarta ne ya sanya Mama fadin “Ba cewa aka yi duk bayan sati biyu za ki rika zuwa nan ba, ba yau sati daya da kika zo ba?”

Raɓewa ta yi jikin kofar hade da kyaɓe fuska kamar za ta yi kuka.

Cikin dariya Goggo ta ce “Tun da ta riga da ta zo ai sai a yi hakuri”

“Amma ai babu dadi, mutanen nan suna Iyakar bakin kokarinsu, ban son kure mutum”

Mama ta kai karshen maganar tana kiran layin Hajiya.

Daga inda Hafsat take tsaye ta ji muryar Hajiya na amsa gaisuwar Mama.

Maman ta dora da “Wai sai ga Hafsat kuma”

Cikin dariyar manya Hajiya ta ce “Haka direba ya ce min ta ce ya kawo ta nan”

“To ai wannan shirme ne, ina laifi duk bayan sati biyu ana kawo ta, shi ne za ta fara gaban kanta, don Allah ku yi hak’uri, Tajuddeen idan ya dawo masallaci zai kawo ta.”

“Haba dai! Don Allah ki kyale ta, tana ma kokari ai, gida ma nake son a kai ta ta ga ƴan’uwanta in Sha Allah. Dole a rika yi mata abun da zai debe mata kewa, kin ga mijinta baya nan, mune ma ya kamata mu ba ku hak’uri ai.”

Mama ta ce “Haba ba komai, ai yanayin aikinsu ne ya zo da haka, ba ga shi har an yi wata biyu ba.”

“Haka ne kam, amma du da haka ai ba dadi” cewar Hajiya

“Allah ba komai Hajiya” Mama ta amsa, daga nan suka yi sallama, lokaci daya kuma ta dire idanunta a kan Hafsat wacce har lokacin take tsaye.

“Ai sai ki shigo, kike yi da wasu kumatunki, wai ni kam abincin da kike ci a kumatu yake tsayawa ne?”

Sosai Goggo ta saki dariya, Hafsat kuma ta shigo cikin falon sosai, hade da yaye ƙaramin hijabinta, Sai kuma ta shiga cire socks din

“Me ya faru to?” Mama ta tambaya idanunta a kan Hafsat din

“Babu komai, ni na gaji da can din ne” ta amsa hade da tura baki

“Ma Sha Allah! Hafsat wace irin ƙiba ce kike yi ne, kin ga wuyanki kuwa?”

Hannu ta kai hade da shafa wuyan ba tare da ta ce komai ba.

Sai ma hannun da ta sanya tana karbar abincin da Goggo ke mika mata.

“Ya makarantar?” Mama ta kuma tambaya.

“Lafiya kalau, ranar Monday za a fara Exam din 2nd term”

“Har da ku?”

“Ban da mu” Hafsat ta amsa hade da kai loma bakinta

“Su Nabila kuma ranar Laraba zasu fara” cewar Mama

“Haka ta fada min jiya”

“Hafsat kina ƙiba wlh, kar fa mutanen nan su zagemu su ce ba ma ba ki abinci da”

Dariya sosai Hafsat ta yi, sai dai komai ba ta ce ba.

“Allah! Wannan ƙiba haka, kin ganki kuwa?”

“Amma dai ai ban yi ƴar lukuta ba Mama”

“Ba ki yi ba kam, amma duk wanda ya sanki baya, ya kalle ki yanzu ya san an samu canji. Wuyanki  ƙashi fa ya ɓata”

“Ya, kamata ki yi kitso Hafsat, kamar wacce aka yi wa baki, wata biyu kanki ba kitso”

“Yauwa Mama, ki fadawa Hajiya wai zan zo kitso wurin Goggo ranar Sunday”

“Ba ruwana, daga ni har Goggon ma ranar Sunday bamu nan”

“Ina za ku je?” Hafsat ta y saurin tambaya

“Ɓurma”

“Me ake yi Mama?”

“Yarinyarta ce ta haihu, yaron ya koma”

“Allah sarki” Cewar Hafsat cike da jimami

“Wlh abun tausayi, ina jin ko haihuwarta ta uku ke nan yaran na komawa”

“Wayyyo! Allah Ya ba ta masu albarka”

“Amin”

“Mama ina son zuwa”

“Sai ki tambayi  mijin ki.” cike da gatse Mama ta yi maganar.

Hafsat kam sai ta dauka gaske.

Zuwanta gidan kam sai ta warware sosai, 6pm Tajuddeen ya mayar da ita gida.

Bayan ta gaishe da Hajiya bangarenta ta wuce, Ahmad take son kira ta shaida mishi za ta je Ɓurma.

Kasancewar ta yi wanka a gidan Mama, kayan makarantar kawai ta cire hade da sanya doguwar rigar rubber material blue, sai da ta daidaita saman gadon kafin ta bude data, cikin sa a kuma wanda take son ganin yana online, don haka ta aika mishi da kiran videon.

Kamar 5sec ya daga kiran, sanya yake cikin overall, yayin da fuskarshi ke sanya helmets. Sai dai wajen fuskar akwai glass mai garai-garai wanda za ka iya kallon fuskar mutum. Yadda ta saki baki tana kallonshi ne ya sanya shi dage hular gabadaya, da gira ya yi mata alamar kallon fa

“Ina wuni?” ta fada da dan murmushi

“Kin dawo yawon?”

“Ba fa yawo na je ba, gidan Mama na je”

“OK” ya fada a takaice

“Nan kana ina?”

Maimakon ya amsa mata, Sai ya juya mata camerar, wurin kamar Sahara kamar daji, ga sojoji nan burjuk da irin shigar da ke jikin Ahmad.

Ya dauke camerar daga kansu ya mayar kanshi, baki bude alamun mamaki ta ce “To me kuke yi a nan?”

“Aiki” ya amsa mata

Kai ta rangwadar gefe, kafin ta ce “Yaushe za ka dawo?”

“Kina so ne?”

Sai kuma duk ta daburce don haka ta ce “Na ga ka dade ne”

“Soon in Sha Allah. Just always put me in your prayers”

“In Sha Allah” ta amsa a hankali

“Me Hajiya ke ba ki ne?”

“Me ka gani?”

“Kin yi jiki sosai”

Cike da kunya ta aje kanta kasa tana murmushi.

Shi ma murmushin yake, kafin ya ce “Me ya sa kika kira, akwai wani abu ne?”

Da sauri ta dago kafin ta ce “Dama Ina son bin Mama Ɓurma ne” kamar za ta yi kuka ta kai karshen maganar

“Ki fada wa Hajiya”

“Ni ai ba zan iya ba, don Allah ka fada mata”

“Ni ɗan aikenki ne?”

Kai ta shiga girgizawa alamar a’a

“To sai ki fada mata”

“Don Allah ka fada mata.”

“Na ji”

“Yauwa na gode” ta fada cike da farin ciki.

“Je ki yi sallah, na ji an kira”

“To” ta amsa hade yanke kiran

Janye wayar ya yi a hankali hade da lumshe ido, sai kuma ya furzar da wata iska mai zafi.

Hafsat tana dauke da abubuwa masu yawa da za su tayar da hankali duk wani lafiyayyen. Musamman yanzu da take ta kara cika kullum, duk lokacin da ya kira ta sai ya ga ta canja, sosai girman jikinta ya fi karfin shekarunta, kullum ya kira ta video sai ya ga ta canja, sannan ya kan dade cikin yanayin son jin ta jikinsa, shi ya sa baya hira mai tsawo da ita.

Bangaren Hafsat Mama ta kira ta shaida mata yadda suka yi, wani irin farin ciki take yi, za ta je unguwa.

Tun daga lokacin ta bude kunnuwa tana jiran Hajiya ta yi mata maganar tafiya, sai dai shiru Hajiyar ba ta yi maganar ba har ranar Asabar da yamma , tuni  Hafsat ta fara sarewa, saboda idan har ba Hajiyar ce ta yi magana ba, ita dai ba za ta ce komai ba.

Yanzu ma zaune take a tsakiya falon Hajiyar tana amsa pass question papers na Biology, yayin da Hajiyar suke hira da Aunty Safiya da ta zo gidan.

Wayar Hafsat ta shiga vibration alamun kira, ganin Hana sai ta daga.

“Gobe za ki shigo lesson?” Hana ta tambaya

“Idan zan shigo zan sanar miki”

“ok” Hana ta amsa hade da yanke kiran wayar.

Hajiya ta ce “Gobe Ahmad ya ce za ku je Ɓurma ko?”

Lumshe idon jin dadi Hafsat ta yi, kafin ta bude su a hankali ta ce “Eh”

A kasan zuciyarta kuma ta ce “Alhamdulillah Ya Allah!”

“Za ki ta fi da direba ne?”

“Ya Tajuddeen ne zai kai mu” ta amsa Hajiyar

“Me ake yi a Ɓurma?”

Aunty Safiya ta tambaya

“Goggon gidan ce ƴarta ta haihu yaron ya koma”

“Eyyah! Allah Ya jikanshi Ya mayar da amfanan ne”

“Amin” Duk suka amsa gabadaya

Hafsat kuma ta mike hade da kwashe littafanta, so take ta samu space ta yi murnar barin ta zuwa unguwa.

Bayan fitarta ne Aunty Safiya ta ce “Yarinyar nan fa sosai ta canja, kin ga yadda take wani budewa”

“Kwanaki ma na dauka ciki ne da ita,Sai kuma na ga ta yi al’ada” Cewar Hajiya

Aunty Safiya ta ce “Kai haba ciki dai”

“Ni da nake fatanshi Safiya, tun yaushe na so Ahmad ya yi aure ya ki. Sai yanzu na fahimci zaɓina ne bai yi mishi ba. Yanzu wannan yarinyar Zaitun ba ta girme ta ba. Amma sai ce min ya yi Zaitun ta yi mishi karama. Amma wannan yarinyar kam sai kin ga yadda ya damu a kanta. Kallonsu kawai nake yi. Ina kawar da kai. “

Dariya sosai Aunty Safiya ta yi kafin ta ce” Yana fa da gaskiya Hajiya, yarinyar nan tana da kyau, shi ya sa ya yi wuf da ita. Ya rufe ta a gida, ya san dai duk inda ya tafi ba shi da fargaba.”

“Ai jiranshi nake ya dawo lafiya, in ce Ahmad wannan kam ita ta yankewa duniya cibi kam, shi ya sa ka auro ta”

Wata dariyar Aunty Safiya ta kuma yi, “Amma ai tana da hankali Hajiya”

Cewar Aunty Safiyar

“Ai ko Asma’u ma tana da hankali Safiyya ke ma kin sani. Sosai Ahmad yana sa’ar mata gaskiya. Don ba Asma’u ba zan kone namanta ba, ni ba ta taɓa min komai ba sai alkairi. Allah ne dai ya kawo rabuwar”

“Gaskiya kam Asma’u na da kirki, da faram-faram da kowa, tana da hira sosai kowa nata ne, sabanin Hafsat da wanda ta sani kawai take sakin jiki ta yi hira.”

“Ita ma har da yarinta, ai kin san wayewar ba daya ba. Asma’u cikakkiyar yar tsakiyar birni, tashin bariki, ga karatu mai zurfi ta yi. Ai dole ta fi Hafsat iya mu’amala da mutane. Hafsat shigen halin Ahmad ne da ita, ba ta son hayaniya, ko ni din ma wani lokaci sai ki ji mun yi shiru. Amma tana da hira, musamman ki sako zancen kauye, to a nan za ki ji hirarta. Za ki ji sunayen tsirrai da ganyayyaki kala-kala. Za ki kalolin magunguna da sunayensu kala-kala. Sosai tana da basira a nan wajen.

Ko ita ce ta gani a faskare babu ɓawo, za ki ji ta ce wannan iccen bishiya kaza ne “

” Ikon Allah “cewar Aunty Safiyya cike da mamaki

Hajiya ta dora da” Ai kwantar da kai nake yi, in yi ta jan ta da hirar, Sai ki ji tana fada min magunguna kala-kala. In fada miki ranar da hannunta ta dakko kunama daga kitchen “

Yanzu kam ido Aunty Safiya ta waro alamun mamaki.

Hajiya ta ce” Wlh. Ta fitar da ita waje aka kashe. Nai ta lallaɓata sai ce min ta yi, ko maciji idan ta ga zai cutar za ta iya kama shi, kuma babu abin da zai yi mata”

“Kai Hajiya!” cewar Aunty Safiya da mamaki.

“Ai ni ma na yi mamaki, na ce kana tare da mutum ba ka san baiwar shi ba”

“To gadon gidansu ne?” Aunty Safiya ta tambaya.

“Ko ɗaya! Ce min ta yi wani ya ba ta maganinsu, saboda haka ko kansu ta hau sha Allah ba za su iya mata komai ba. Amma fa kafin ta fada min sai da nai ta lallaɓata da bin hanyoyi namu na manya. Abin da na fahimta yarinyar tana da tsarin jiki sosai.”

Aunty Safiya ta shiga jinjina kai alamar mamaki, tsabar mamakin ma komai ba ta ce ba.

<< Abinda Ka Shuka 54Abinda Ka Shuka 56 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×