Skip to content
Part 57 of 60 in the Series Abinda Ka Shuka by Khadija S. Moh'd (Matar J)

HAFSAT

Sanye take cikin gogaggun uniform , siket tummy shirt Mai dogon hannu, white mini hijab, hade da eyes glass, Wanda ya karawa fuskarta kyau, Allah duk da ba wata kwalliya ta yi ba.

Halin damuwar da ta shiga kwanaki ukun nan, hakan bai sa ta rame ba, sosai uniform din suka yi mata kyau.

Falon kam ya fara  cika  da iyalan Galadima, kuma duk suna hallara ne saboda zuwa makaranta graduation din Hafsat.

Tun da ta shigo suke kallon ta, ta kara zama silent Kamar ba ta farin ciki.

Aunty B ta ce “Aunty Queen ya da sanyi haka kuma?”

“Wlh kam, tun shekaranajiya nake ganinta haka, kuma ta ce min lafiya ƙalau.” Cewar Hajiya idanunta a kan Hafsat

Cikin salon boye damuwarta ta ce “Kawai stress ne Hajiya, amma ina lafiya”

“To Madalla” Cewar Hajiya, kafin ta dora da “Shafi’u ya fitar da motar ai, ki yi gaba muna nan zuwa sha Allah”

“Hajiya don Allah ku zo da wuri” kamar za ta yi kuka ta yi maganar.

“Kar ki damu za mu zo sha Allah” cewar Hajiya cikin alamun lallashi

Sai kuma ta kama hannun Hafsat din zuwa wajen cikin falon, kafadarta ta dafa sannan ta ce “Akwai labari mai dadi idan kin dawo”

Murmushi Hafsat ta yi, ba tare da ta ce komai ba, Hajiyar kuma ta ci gaba da karfafa mata gwiwa da maganganu masu dadi, har sai da ta saka ta cikin mota, saboda a kwanakin nan ta fahimci akwai abin da ke damun Hafsat din, kawai dai ba ta fada ba ne.

Sosai kam abubuwa da yawa suna damun Hafsat, abu na farko dai a, yanzu shi ne kwana uku ba ta yi magana da Ahmad ba, kwata-kwata ma baya online. Abin da ta fahimta kuma kamar duk ƴan gidan hankalinsu bai kai wajen rashin samun Ahmad din ba.

Abu na biyu shi ne mummunan mafarkin da ta yi a kanshi daren jiya, wai ta ganshi cikin wani duhun ciyayi duk ya rame ya yi baƙi, yana cikin halin jinya.

Wai wata mata a gefen shi tana treating din shi. Yadda ta ganshi a mafarkin ba ƙaramin tayar mata da hankali ya yi ba. Abu na uku kuma shi ne idan ta tuna yaƙi ya tafi, Sai ta ji komai baya yi mata dadi.

Da wannan tunanin suka shiga harabar makarantar, wacce ta fara karbar bakuncin manyan motoci kala-kala.

Cikin sauki ta hango motarsu Mama wannan ya sa tana shiga wurin taron ta rika ware ido, har sai da kwayar idanunta ta cafko mata abin da take nema, kai, tsaye kuwa ta doshi wurinsu cike da murna

Ganinsu sai ya dan rage mata damuwar da take ciki, musamman da ya kasance akwai su Nabila.

Hira suke yi sosai, har sai da MC ya fara announcing za a fara program sannan Hafsat ta mike zuwa hall, daidai lokacin kuma motocin gidan Galadima suka shigo.

Wuri na musamman aka ba su, duk da babu Galadiman, amma ya samu wakilci.

Bayan bayanin manyan baƙi, Hafsat ce ta fito, domin gabatar da welcoming speech.

Idan akwai abin da Hafsat ta fi kwarewa shi ne speech da debate, sosai tana da kwarewa a wannan fannin, kowa ya shaida haka a makarantar. Ga murya mai tsaki hade da sanyi.

Microphone din ta karɓar daga hannun MC din lokaci daya kuma tana fuskantar mutanen wajen cike da kwarewa ta ce “My name is Hafsat A Ayyub. From Great Ambassador secondary school.

Ladies and gentlemen, esteemed guests, distinguished dignitaries, and honored colleagues,

It is my great pleasure to welcome you all to our occasion

Firstly, I would like to extend my heartfelt gratitude to each and every one of you for taking the time to join us. Your presence here is a testament to the importance of this event and the value… “

Kamar wacce aka dannawa pause haka ta yi cak! Idanunta zube a kanshi, ta kasa gasgatawa, ta kuma kasa ƙaryatawa, kamar yadda ta kasa ci gaba da speech din. Haka ta kasa janye idanunta a kanshi, kallon shi take yi with shock.

Shi kanshi ya kasa janye idanun na shi a kanta, sosai ta canja, zallar kyawunta da dirinta ya kara fita, sanadiyyar yar Kibar da ta yi.

Yadda take speech din kuma ba tare da jin wani tsoro ba; ba karamin burge shi ta yi ba. She make him proud.

Wani abu da ke tafiya da duk wani kuzarin shi hade da sanya mishi shauki, shi ne reaction dinta, a lokacin da ta tsorata ko abu ya ba ta mamaki, komai na jikinta ya kan saki ne, yadda take sakin lebenta na kasa ba karamin tafiya da shi hakan yake yi ba.

Tun mutane suna dauka Hafsat ta kakare ne, har suka fara bibiyar abin da ya dauke mata hankali, bangaren malamai kam, inkiya kawai suke mata ta ci gaba, kar ta basu kunya. Amma sam ta kasa ci gaban, ga Ahmad ya yi fuska cikin kayan sarauta kamar bai gane shi take kallo ba.

Sai da wani Uncle nasu ya baro wurin zamanshi zuwa inda take, sannan ta tuna me take yi, sai dai dole ta kuma sakowa daga farko.

Har zuwa lokacin kuma idanunta na a kan Ahmad, bayan ta kammala mic din ta mikawa Mc din hade da komawa wajen zaman ta. Yayin da program ya ci gaba da gudana,.

Ba ta iya barin kallon Ahmad ko na minti daya ji take kamar zai bace. Duk wasu program da take a ciki haka ta rika yin su idanunta a kan Ahmad.

Bangaren Ahmad wata irin soyayyarta ce ke kara shiga zuciyarshi, ji yake kamar ya fita ya rungume ta, musamman lokacin da suke gabatar da debate da kuma quiz, amma ba dama yin hakan, kasancewar yana cikin kayan sarauta ne.

Taro ya ci gaba da gudana cike da sha’awa gami da kayatarwa, inda aka fannin bayar da kyauta. Ahmad shi ya mika kyautar First position wa Zulaihat Mustapha Sandamu.

Hafsat kyautar 3rd position ta samu, Sai kuma aka ba ta kyautar health prefect, Wacce Asad ne ya mika mata kyautar.

Aka juya kiran sunayen best student in subject.

Ahmad ne ya mikawa Hafsat kyautar best student in English language

Lokacin da ta zo karbar kyautar ne a hannun shi, ya zuba mata idanunshi da wani kalar kallon da ita kadai ta san tasirin da ya yi a jikinta, shi ya sa ta janye idanunta.

A hankali ya motsa labbanshi ya ce “You make proud, thank you so much my queen” ba kowa ne zai fahimci magana ya yi ba, idan ba, wacce ya yi maganar domin ta ba. Ita din ma kuma reaction dinta Bai nuna an yi mata magana ba ne.

Bayan mai hoto ya dauke su ne ta juya da zummar komawa wurin zaman ta, Sai kuma aka kara kiranta best in Biology studies. Yanzu din ma Ahmad ya mika mata kyautar. Sauran kyautar in Agricultural science, wani bakon ne ya ba ta.

Sai kuma aka shiga raba certificate Hafsat ta samu Certificate na MSS, English club, best in debate presenter and quiz presenter.

Taron dai ba ta shi ba sai la’asar.

Duk tawagar gidan Galadima sun ri ga ta komawa, saboda ta tsaya hotuna da sallama da kawaye.

Shi ya sa sai biyar na yamma suka shigo gida, sallah ta fara yi a dakin Hajiya, saboda falon cike yake da iyalan Galadima.

Zaune ke kan salallaya hade da bitar abin da ya faru, Sai ta na jin kamar mafarki ta ga Ahmad sai kuma ta ji kamar gaske, tana tsaka da tunanin kamshinshi ya rika shiga hancinta, kamar 5mns Hajiya ta shigo dakin tana fadin “Ki je ga Ahmad can ya shigo, ki, tafi mishi da abinci”

Wani gingirin ta ji, yayin da farin ciki ya cika mata zuciya jin dai da gasken shi ne.

Aunty Sadiya ce ta jera mata abincin a kan tire Asabe ta dauka, Sai da suka isa kofar shiga part din Hafsat ta amsa hade da yi mata godiya. Tana tsaka da jera abincin a, kan dinning ya fito daga dakinshi, yanzu kam, kananan kaya ne a jikinshi, sun dan fito mishi da ramar da ya yi kadan.

Da sauri ta dago kai idanunta a kanshi. Lallausan murmushi ya sakar mata hade bude hannayenshi yana fadin “Come on my Queen, you make me proud today, I really love you” ƴa karasa maganar hade da janyo ta jikinshi, saboda tsaye ta yi kamar hoto.

Hijab din jikinta ya zare, hade da cusa fuskar shi a cikin wuyanta, yana shakar kamshinta mai dadi, duk yadda ya so controlling kanshi ya kasa, Sai da ya hada bakinta da na shi for some minutes, ba shiri ya zauna a kan kujerar dinning din, saboda ji ya yi kafafunshi ba za su iya daukar shi ba. Saman cinyarshi ya dora ta hade da kwantar kanta a kan kirjinta, da wata irin murya ya ce “What do you want as your gift” yadda ya yi maganar a cikin kunnenta ba ta san lokacin da ta kara tura kanta cikin jikinshi ba.

Dalilin da ya sanya shi dago fuskarta da hannayenshi biyu ya shiga laluben kwayar idanunta, Sai dai ta ki bude idon, wannan ya sa ya kuma yin kissing din Lallausan lebenta a karo na ba adadi.

Shi da kanshi ya daga ta daga jikinshi, yana dariyar yadda take ta sunƙe kai kasa, neman hanyar gudu ma take yi, shi ya sa ya riko hannunta tare da fadin “Ba ki yi murnar ganina ba?”

Da sauri ta ce “” Na yi”

“Na gani ai, kina son sanya ni rungume ki cikin mutane”

Kasa ta yi da kai hade da murmushi. Hannunta da ke cikin na shi ya saki, yana fadin “Sanya min abinci, ina jin yunwa sosai.”

A nutse ta sanya mishi abincin, ita ma sai ta zuba kadan ta ja kujerar kusa da shi. Abincin suke ci, hade da yar taɓa hira, wacce kaf din ta a kan taron makarantarsu Hafsat ne sai kuma zuwan shi gida.

Sai da aka kira magriba sannan ya fita zuwa masallaci, a lokacin ne kuma Hafsat ta samu ta yi wanka hade da yin alwala. Ba ta daga akan sallayar ba, sai da ta yi sallahr isha’i.

Wayarta ta janyo ta shiga WhatsApp, maganganun tsokana ne su Nabila suka tara mata, shi ya sa hankalinta kaf ya tattara a kan wayar, yayin da fuskarta ke dauke da murmushi.

Fige wayar da aka yi ne ya sanya ta saurin dawowa cikin hankalinta.

Sakonni ya rika karantawa, yayin da kunya ta rufe ta, saboda akwai maganganun da bai kamata ya ji ba.

Wayar ya mika ta tare da fadin “Tashi mu tafi gida”

“Wane gidan?”

Ta yi saurin tambaya

“Namu mana”

Ido ta waro hade da sakin bakin da yake so kafin ta ce “Me ya samu nan din? Nan ya fi dadin zama”

“Idan babu abin da za ki dauka ki same ni a waje” ya karasa maganar hade da ficewa.

Cikin rashin jin dadi ta mike tsaye, sosai ta saba da gidan, ba a rayuwar kaɗaici, mutane wannan ya shigo wannan ya fita, ga katon lambu idan ta yi marmarin daji, ga kuma bangaren dabbobi. Amma can ba komai, dama-dama ma lambun shi ma bai kai girman na babban gidan ba. Duk da ba ta taba shiga ba, ta windows kawai take kallon shi.

Rai babu dadi ta nufi bangaren Hajiya, ita kanta Hajiyar ta lura da haka sai dai ta yi fuska kamar ba ta gani ba. Illa addu’a da ta bi ta da ita.

Yau kam sarautar yake ji, saboda a back seat ta same shi, driver na gaba, kusa da shi ta zauna, Sai da ya ba drivern umurni, sannan ya yi wa motar key…

*****

Har suka isa gidan lallausan hannunta yana cikin na shi, murzawa yake a hankali, from time to time, yayin da sakon ke shiga duk wani sassa da yake son aika shi.

Motar na gama tsayawa ta fice dama komai ba ta dakko ba a wancan gidan

, ita a dole fushi take yi. Ta dauka za ta samu gidan da dattin rashin zama, ga mamakinta tsab ta same shi, ga kamshi daɗaɗan turare ɗaki yana tashi.

Shi ya sa kayan baccin kawai ta sanya ta bi lafiyar gadonta, tun tana tsammanin shigowarshi har bacci ya soma daukarta

Cikin bacci-baccin ta rika jin kamshinshi a hancinta, bude idonta ya yi daidai da kunna wutar dakin da ya yi, shi ya sa suka hada ido

“Sorry” ya yi saurin fada ganin tana yamutsa fuska alamun haske ya zo mata a bazata.

“Je ki yo alwala, ina jiranki”

Toilet din ta shiga hade da dauro alwalar, shi ne ya ja su sallah raka’ a biyu, bayan ya sallame ya juyo hade da dafa kanta, ya karanta Addu’ar _ALLAHUMMA INNI AS’ALUKI KAIRAHA, WA KAIRAHA ILAIH, WA’UZUBIKI MIN SHARRIHA, WA SHARRAH MA JABALTAHA ALAIHI_

Daga haka ya juya hade da kai goshinshi kasa, ya jima a halin sujudar sannan ya dago. Hannayenshi ya mayar sama ya shigo jero addu’o’i, bayan ya gama suka shafa tare da Hafsat, Sai ta ji duk wani danyen kai da taho da shi daga can gidan ya ƙaura. Jiki ba ƙwari ta koma saman gadon ta kwanta, bayan ta ninke zane hade da hijabin da ta yi sallah.

After 5mns ya mike daga zaunen da yake yana taba wayar shi, hasken dakin ya kashe ya bar na bacci kawai, wannan ya sa Hafsat ta lumshe ido, ta san dai fita zai yi, Sai kuma tunaninta ya canja jin shi a kusa da ita. Pillow ya jawo hade daidaita fuskarsu kafin ya ce “Na fada miki yau kin saka ni alfahari? Lallai da ban zo ba, da na yi missing din wannan ranar, wacce na san ba za ta kara dawowa ba. Allah Ya sa albarka a rayuwar ki”

Sannu a hankali ta ce “Amin, na gode”

Tun lokacin da ya hau gadon ya ji motsinta alamun ta ja baya daga jikinsa, shi ya sa ya sa yanzu ya jawo ta dab da shi sosai ta yadda kirjinsu ya hadu, cikin kasalalliyar murya ya ce “Ba ki tambaye ni ya aka yi na zo ba?”

Duk yadda ta so yin magana ta kasa, shi ya sa bai damu ba ya ce “Ka’ida sai next week muke gama documentation, na bi hanyayo da yawa don in samu in taho, shi ne suka ce sai dai in biya transport da kudina. Ni kuma na kira Tukuro na ce ya siyar min da shannunki biyar, ya turo min kudin in yi transport, tun da tafiyar taki ce “

Motsin murmushinta ya rika sauka a kan kirjinshi, wannan ya sanya shi lumshe ido, yana karbar canjin da jikin na shi ke samu.

Hafsat ta kuma ta juya mishi baya har zuwa lokacin murmushi take yi.

Da sauri ya maido yadda take, murya kasa-kasa ya ce” Da gaske nake yi miki”

Jikinta ya kuma jawo ta sosai hade rungume ta, ji yake kamar ya bude kirjin ya shigar da ita ciki.

Kasa hak’ura ya yi sai da ya nemi bakinta ya shiga aika mata da sakon da ya dade kunshe cikin zuciyarshi.

Tun yana sanin abin da yake yi, har ya fara mantawa, kawai kokarin kaiwa magaryar tuƙewa yake yi. Yayin da Hafsat ke kokarin kwatar kanta, amma Sam ya hana ta yin hakan, dole ta hakura.

Sai dai wani abu da ya ba ta mamaki shi ne, yadda ake zuzuta azabar daren farko a labari ita kam ba ta ji azabar ta kai haka, ba mamaki saboda gently ya bi ta, ita kanta ta san cewa bai shige ta da karfi ba, ya bi ta a hankali ne.

Duk da hakan dai shi ne ya yi mata komai a daren, hatta zanen gadon da ya baci, shi ne ya canja wani, ya mayar da ita ya kwantar sannan shi m ya kwanta kusa da ita.

Rashin sabo ya sa ta jima ba ta yi bacci ba, kafin daga karshe bacci mai nauyi ya dauke ta.

Sati biyu Ahmad ya yi yana cin amarci, a cikin sati biyun kam ba kananun abubuwa ya koyawa Hafsat ba, masu wuyar mantawa.

Shi da kanshi ya ji ba zai iya tafiya ya bar ta a gidan ba, shi ya sa lokacin da zai koma wurin aiki, kai tsaye ya cewa Hajiya da Hafsat zai koma , sosai abun ya ba Hajiya mamaki, saboda bai taba cewa Asma’u ta bi shi ba, ko Hajiyar ta bukaci haka sai ya zuke, yanzu kuma da kanshi wai za tafi da Hafsat.

Ba iya Hajiya ba, duk wanda ya san shi, ya kuma ji ya ce da Hafsat zai koma sai abun ya ba shi mamaki, don Asad har tsokanarshi yake yi, ya ce “Ai da yake ma yarinya ce.”

Ana saura kwana biyu ya koma wurin aikin ya kai Hafsat Maƙera don yi musu sallama, sosai ta ji dadin hakan, kamar wancan lokacin ma tana zuwa dakinta ta bude hade da shigewa ta hau gyara, yayin da Ahmad ke can zaure suna hira da Baba.

Sai da ta gama gyara dakin tsab, sannan ta shigo wanka, tsaye take a tsakiyar dakin daure da towel shi kuma ya shigo.

Idanunshi a kan gadajen guda biyu suka sauka, ya karaso wurin yana fadin “Wanne ne naki?” da, hannu ta nuna mishi, a nutse ya kwanta hade da lumshe ido, ya bude su a kanta, jikinshi ya janyo ta, yana murmushi, a, kunne ya rada mata, Idan mun so hutu nan zamu zo dakin ya yi kyau sosai “

Jikinta ta shiga kwacewa tare da fadin” Kar fa wani ya shigo “

Towel din ya rike idanunshi a kanta ya ce” Je ki sanyawa kofar  sakata”

Ido ta fitar waje alamun tsoro, da kanshi ya mike zuwa wurin kofar silently ya dannawa kofar key, ya dawo cikin dakin, hoton Inna ya dauka, bayan ya gama gani sai ya kifa shi jikin gini, kafin ya juyo kan Hafsat din, wacce ke da cike da mamakinshi.

Kamar wasa sai da ya biya bukatarshi da ita, a, gurguje ya yi wanka ya mayar da kayanshi tamkar komai ba faru ba.

Ya koma saman gadon ya yi kwanciyarshi, ba, jimawa kuma bacci ya dauke shi.

Ita ma sai ta kuma yin wankan tare da mayar da kayan ta, silently ta bude kofar ta fice daga gidan gabadaya. Gidansu Farida ta fara zuwa suka runguda gidansu Ni’ima, a can suka sha labari, Hafsat ta nuna musu hotunan gami da videon bikin graduation din su.

Sai da aka yi sallahr azhur sannan suka rako ta zuwa gida. Lokacin kam Ahmad ya tafi masallaci.

Tafiyarsu Farida ba jimawa, Ahmad suka dawo masallacin tare da Baba. Lokacin ne kuma Goggo Amarya ta kawo musu masa da miya, harda naman kaza. Sosai ya ci Masar.

Sai da aka yi la’asar suka tafi Rugga, nan ma basu baro Ruggar ba sai wajen 6pm, a kan hanyarsu ta komawa dai gida aka yi magariba.

Washegari kam Hafsat a gidan Mama ta wuni, Sai yamma ta dawo gida, safiyar Lahadi kuma suka dauki hanyar birnin Hong, inda Ahmad ke aiki, karon farko da Hafsat ta yi doguwar tafiya a mota har ta gaji.

Saboda Sai isha suka isa barrack din, dama Hausawa sun ce duniya a ido take, ta yarda kam, komai na barrack din ya mata kyau.

Rayuwar barrack din a wurinta rayuwa ce mai dadi, rayuwar da ba za ta taba mantawa ba. Sai take jin ina ma ace mutum tun yana yaro ake yi mishi aure, da duk ba ta sha waccan tsangwamar ta baya.

Amma yanzu kam sai dai tarihi, saboda duk wadanda suka wulakantata, yanzu rayuwarsu ta zama abun tausayi, sune a wulakance yanzu. Wadanda suka yi mata alkairi kuma, suna nan cikin ranta, musamman mahaifiyar Nasir, tana son zuwa garin da aka kai ta, saboda mutuwar Nasir ba jimawa ƴarta mai aure a Yadi ta zo ta dauke ta zuwa can.

Ahmad mijin marainiya ne, duk wacce ta same shi ta more a matsayin miji, ga ilmi, nutsuwa, kyawun hali da dabi’u. Hak’uri, wadatar zuci, arziki da kuma sarauta.

Duk lokacin da ta kalle shi a matsayin miji, Sai ta ji alfahari da shi ya kamata. Duk addu’o’inta ba ya wuce Allah ya yi musu  tsawon rai su rayu a tare ba.

<< Abinda Ka Shuka 56Abinda Ka Shuka 59 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×