Skip to content
Part 58 of 60 in the Series Abinda Ka Shuka by Khadija S. Moh'd (Matar J)

Mk

Yanzu kam a familynsu babu wanda bai san yana da yaro a waje ba, tun ana ɓoye-ɓoye har maganar ta fito fili kowa ya sani. Shi kanshi tun yana jin nauyi har ya saki jiki, ya karbi Abdallah da hannu bibbiyu, saboda yanzu duk hutu anan yake yin shi, shi kanshi Abdallahn wani lokaci har tambaya yake yi, ya ce yaushe za a kai shi wurin Uncle Mk, haka yake kiran shi. Yanzu kam ba Abdallah ne damuwar Mk ba, damuwarshi a yanzu shi ne bayanin da likita ya yi musu asibiti, sakamakon wani barin da Ruma ta kuma yi.

Likitan ya tabbatar musu da Ruma na dauke da rukunin jini negative ne, shi Kuma yana dauke da rukunin jini Positive, Shi ya sa idan ta samu ciki ya zubewa ko ta haifi dan babu rai. Maganin wannan matsalar kuma shi ne yin wata allura a duk lokacin da aka sadu kuma aka tabbatar da akwai ciki, wannan allurar za ta ba yaron kariya sha Allah.

Sai dai allurar tana da tsada sosai, ta kai 50k, wannan abu sosai ya tayarwa da Mk hankali ga shi, Allah Ya jarrabe shi da son Ruma, baya son ganin bacin ranta. Shi ya sa ya dauki shawarwarin likita, suke ziyartar asibiti domin ganin sun kiyaye kansu da kara yin barin ciki na gaba. Abu daya ya yanke shawara shi ne Ruma na samun yara biyu to za ta yi planing, saboda duk wani nemanshi a kan a asibiti yake karewa.

Bangaren Alaramma kuwa tuni ya fahimci ilimin boko shi ma yana da na shi ranar, shi ya sa shirin ilimin tsangaya da gwamnati ke ba makarantun tsangayu kyauta Alaramma ya kai sunan makarantarshi.

Yanzu duk ranar Alhamis da juma’a da yamma ake tara almajiran wajen koya musu karatu da rubutu.

*****

Hafsat

Watansu daya a Hong suka juya zuwa Dawuri, wannan karon kam a jirgi suka biyo, daga Nasara zuwa Dawuri ne suka hawo mota.

Tun da suka iso gidan ba ta da lafiya sai zazzabi, shi ya sa ma ta dawo nan babban gidan wurin Hajiya.

Gidan Mama ma dakyar ta samu ta je, kowa cewa yake tafiya ce a jirgi kasancewar ba ta saba ba.

Yau kam da ta tashi da zazzabin sosai, kai tsaye Ahmad ya nufi asibiti da ita.

Ɗakin gwaji suka tura ta, daga dakin gwajin kuma waiting room ta shiga hade da kwanciya, yayin da Ahmad ke zaune a office din Asad suna hirarsu da ba ta karewa

Kamar 30mns aka turowa Asad result din Hafsat ta computern office din.

Ya zubawa computer ido, Sai kuma ya ce “Bala’i”

Ahmad ya tattara hankalinshi a kan Asad ba tare da ya ce komai ba.

Asad din ne ya ce “Yarinyar nan fa ciki gare ta wlh, har sati uku”

Ido da baƙi Ahmad ya bude kafin ya ce “Queen?”

“ita fa!”

Har zuwa lokacin Ahmad bai rufe bakin shi ba alamun firgici ya ce “Akwai matsala ne?”

Kai Asad ya shiga girgizawa kafin ya ce “Mu a likitance babu wata matsala sha Allah. A wurinka ne da akwai matsalar, saboda har yanzu yarinya ce ga shi ko universityn ma ba ta shiga ba bare ta yi shekara biyun ma”

Yanzu kam Ahmad ya fahimci magana Asad ya fada mishi, shi ya sa ya mike hade da nufar kofar fita, zuciyarshi wadai, ashe shi ma zai ga wannan ranar da za a ce matarshi na da ciki, ikon Allah.

Asad kuma dariya yake ta yi, irin dariyar tsokanar nan.

A reception Ahmad ya sa aka kira mishi Hafsat don su tafi.

Yadda ya zauna a motar shiru, idanunshi a lumshe sai abun ya fara ba ta tsoro, ko cewa aka yi tana da wata cuta mai girma ne, don haka ta ce”Ya Amad lafiya? “

Ka na shi ya dago hade da bude idanunshi a kanta, Sai kuma ya janyota jikinshi, rungume ta ya yi sosai for some minutes a hankali ya ce” Kina da ciki Queen, ina jin kamar mafarki, na dauka irin wannan ranar ba za ta zo ba. Alhamdulillah Ya Rabbb “ya fada hade da yin kissing din ta

Hafsat kam mamaki ne gami da tsoro ya kamata, tana da ciki, ciki dai irin na haihuwa. Ikon Allah. Tsoron kuma shi ne ranar haihuwar, amma yadda ta ga yana farin ciki, sai ta ji duk tsoron ya gushe.

Ba karamin dadi ta ji ba, da bai fadawa kowa tana da ciki ba, satinsu daya suka koma Hong.

Wata irin tarairaya Hafsat ke samu, duk da cikin bai sanya mata laulayi ba. Komai ci take yi, shi ya sa cikin kankanen lokaci ta kara zama Tubarakhallah. Kiri-kiri take kin bin Ahmad gida, wai kar aje a ganta da ciki. Shi ya da ranar da ta isa gidan a matsayin ta zo haihuwa ba karamin mamaki mutane suka sha ba. Babu wanda ya san tana da ciki sai yanzu da ta zo.

Hajiya har da hawayen farin ciki, haka labarin ma da ya isa kunnen Galadima ba karamar murna ya yi ba hade da addu’ar Allah Ya raba lafiya.

Nauyin cikin bai hana ta zuwa Makera ba, har Rugga ta je wajen Tukuro. Suka sha hira sannan ta dawo gida.

Satinta uku da dawowa Dawuri safiyar juma’a ta zuba ƴan tagwayenta duk maza, farare tas sai dai duk kama suke da Ahmad. Wannan rana ahlin Galadima sun kasance cikin farin ciki. Kar ma Ahmad ya ji labari, har da kukan farin ciki ya yi.

Nan da nan gida ya fara karbar yan barka, karon farko da su Inna Kuluwa suka zo gidan Hafsat, a nan suka kara tabbatar da cewa Hafsat ta yi nisan da su dai ba za su iya kamo ta ba.

Ranar suna yara suka ci sunan Hibban da Affan, ranar kam shagali aka yi sosai, har da wasa dawaki kamar ranar sallah.

Gidan Mama Hafsat ta koma don zaman arba’in. Kulawa sosai Mama ke ba ta, duk wasu magunguna na gyara mace, Mama ba ta sanya wajen ba ta su. Yan biyu kam Tubarakhallah girmansu suke yi hankali kwance.

Duk lokacin da Ahmad ya zo ya gansu sai ya rika jin kamar ba nashi ba, idan kuma ya tuna lallai nashi ne, wani irin dadi farin ciki yake ji, baya sanin lokacin da yake daga hannu ya gode ma Allah.

Hafsat na yin arba’in ta je Makera, daga nan kuma aka maido ta gidan mijinta, duk yadda Ahmad ya so tafiya da ita zuwa Hong Hajiya hanawa ta yi.

Wai yara basu yi kwari ba, sannan babu wanda zai rika taimaka mata a can.

Ita kanta Hafsat din ba karamin jin dadin wannan shawarar ta yi ba, duk da yaran basu da rigima amma rainon yan biyu kam akwai wahala. Sannan kuma ga bikinsu Nabila da aka sanya, Juwairiyya a Nasara ta samu miji, yayin da Nabila ta samu nata a nan Dawuri.

Duk bayan sati biyu Ahmad ke zuwa weekend, wani lokaci kuma sai ya zo a sati daya.

Kamar yau ma da ya sanar mata yana hanya, shi ya sa suka hadu ita da Shamsiyya yarinyar da ke taimaka mata, suka gyara gidan tsaf hade da yin abincin da Ahmad din ya fi so.

Zuwa biyar na yamma suka kammala komai, ciki har da shirya ƴan biyu, wadanda suke koyon zama, family house ya fara isa, shi ya, sa sai da aka yi magariba ya shigo gidan.

Time din Hafsat zaune take kan kujera tana shayar da Hibban, tun da ya shigo take kallonshi fuskarta dauke da murmushi.

Shi ma murmushin yake yi, bag din da ke sagale a bayanshi ya fara saukewa, ya dauki Affan lokaci daya kuma yana zama daf da ita, wuyanta ya sumbuta kafin ya ce “I really missed you”

“I missed you too”

Murmushin ya kuma yi kafin ya ce “Kin ji ni shiru ko? Na ɗan biya gida ne. I’m sorry”

“Ba komai”

“Thank you”

Ya, yi maganar hade da mika mata Affan ya dauki Hibban.

“Har yanzu bassa shan madarar ne?”

“Suna sha kadan amma, dama-dama ma Affan ya kan dan sha yawa.”

“Amma hakan baya affecting dinki”

Kai ta shiga girgizawa kafin ta ce “A’a kawai dai ina yawan jin yunwa ne”

“To ki bar bari kina ji, ki yi ta cin abinci.”

Dariya ta yi mai sauti kafin ta mike tsaye bayan ta kwantar da Affan don ya yi bacci.

Dinning ta nufa tare da fadin “Bismillah, ko ka ci abinci?”

“Na dai sha fura wajen Abbah”

“Abincin sai an jima kenan?”

“Eh sai dai zan yi wanka”

Bag din da ya ajiye ta dauka, ta nufi stairs din, shi kuma ya biyi bayanta sabe da Hibban.

Sai da ta hada mishi ruwan wankan ta fito, duk da yadda ta so taimaka mishi Hibban bai bari ba, saboda bacci yake son yi, Sai ko da ya yi baccin ta samu ta yi sallahr isha’i.

A lokacin ne kuma ta zubawa Ahmad abinci. Yana cin abincin ne ya ce “Kwanaki can na tambaye ki, me kike son yi a garinku a matsayin sadakatul Jhariya wa Inna, me kake ce ma?”

Zama Hafsat ta gyara hade da fadin “Ce maka na yi akwai wani fili nata, idan so samu ne, zan, yi katuwar makarantar Islamiya hade da masallaci, a tona rijiya ko borehole, in rinka daukar responsibility din makarantar”

Kai ya shiga jinjinawa alamar gamsuwa, lokaci daya kuma yana tauna abincin a nutse.

Kafin ya ce “Na yi maganar da Asad, kuma ya je an nuna mishi filin, sai dai ba zai isa a yi yadda kike son ba, kuma ya yi tsakiyar gari sosai, babu yadda za a yi a kara filin tun da tsakiyar gidaje yake”

Shiru Hafsat ta yi, da yanayin sanyin jiki.

“So shi ya sa muka sanya aka bincika mana fili mai kyau babba, jiya ya kira ni ya ce an samu, a nan bakin hanya, amma miliyan goma aka yi mishi kudi”

Ido Hafsat ta fitar kafin ta ce “Miliyan goma? Ya yi tsada Ya Aamad”

“Amma kuma yana da kyau da girma ai”

“To ai kudin ne damuwar wancan filin ba zai kai 10m ba, bare in ce ko a siyar sai a sayi wannan din. Amma akwai wasu filaye da gonaki sai a sayar (sai kuma ta yi shiru alamun tunani, kafin ta ce) to kuma idan aka siyar da su da me za a yi ginin?”

Bai san lokacin da ya yi murmushi mai sauti ba, yana daya daga cikin abin da ya sa yake son Hafsat tana da zurfin tunani sosai. Komai bai ce ba ya ci gaba da cin abincin. Ita din ma sai ta saki maganar ta koma wata” Ya Aamad maganar karatun nawa fa? “

A shagwabe ta yi maganar

Cikin ido ya kalle ta, kafin ya ce” I don’t know. Dole sai kin yi karatun ne wai? “

” Ina son yi dai, kawayena duk sun fara ga su Aunty Ju har sun gama”

Kai ya jinjina kamar ba zai yi magana ba sai kuma ya ce “Jira ki yaye twins Sai mu ga abin da za a yi.”

“Na gode” ta fada hade da kokarin tattara plates din da ya ci abinci, saboda a daki ta kawo mishi.

Yau dai a dakinshi suka yi bacci, safe kam tare suka yi duk aikin gidan da shi, idan har yana gida to 80% na ayyukan gidan tare suke yi, Shamsiyya ita kanta ba ta faye aiki ba idan yana nan.

Kwananshi uku ya kuma komawa, yayin da Hafsat ta ci gaba da rainon yaranta, tare da shirin bikinsu Nabila.

Su Affan na da wata takwas aka yi bikin su Aunty Jhu, duk yadda Hafsat ta so zuwa Nasara raka Aunty Jhu Ahmad hanawa ya yi, shi ya sa iyakarta Dawuri.

Karon na biyu da Ruma ta zo Dawuri, dauke da danyen goyonta, na yarinya mace wacce aka sanyawa sunan Hajiya Fatee, shi ya sa suke kiranta da Mama. Sai kuma Abdallah da ya tasarwa shekaru takwas, sosai ya yi girma.

A wurin bikin ne Ruma da Hafsat suka kuma kulle sosai, shi ya sa har Ruman ta yi alkawarin zuwa gidan Hafsat kafin ta tafi.

Haka kuwa aka yi, washegarin tashin biki Ruma ta zo gidan Hafsat hannunta rike da Abdallah. Da Ahmad suka fara haɗuwa a farfajiyar gidan, suka gaisa sannan suka shige ciki.

Sosai Hafsat ta ji dadin ziyarar Ruma, sun sha hira kamar sun dade da sanin juna, yayin da Ahmad ya fita da Abdallah da su Hibban, ba kuma su dawo gidan ba sai la’asar. Tsaraba ta musamman ya yi wa Abdallah.

Misalin karfe biyar Hafsat ta yi wa Ruma rakiya.

Bayan kwana biyu da biki kuma Makera Ahmad ya kai ta , sakamakon aikin ginin Islamiyar da za a fara.

Yadda mutane ke gaishe ta hade da ba ta girma sai take jin ta kamar baiwar da aka  ƴanta. Yanzu kowa ma so yake ya nuna ita din tashi ce, amma kuma ta ƙi ba kowa wannan kofar idan ka dauke Babanta da Mama. Sai Farida da Na’ima, amma kam duk sauran mutane irin dai zaman da take yi da su a shekarun baya shi ta kuma dorawa.

Ko su Inna Kuluwa tsakaninta da su gaisuwa, sai ihsanin da Ahmad ke yi musu. Ita kam ta fi yi wa kannenta ma. Idan kuwa ta zo gida dakinta take budewa ta shige ta wuni da yaranta.

Da kyar ta samu damar zuwa wurin Tukuro, saboda shi ba ya shigowa gari, koda ta yi mishi korafi ma cewa ya yi, wai ya taba zuwa kofar gidan Galadima sau daya da zummar zuwa wurinta, ya ga Dogarawa na ta yi mishi mazurai sai ya koma

Yanzu kuma da take zaune a gidanta, cewa ya yi sojoji yake tsoro. Saboda akwai sojoji masu duty a kofar gidan.

Duk lokacin da ya fadi haka dariya take hade da karfafa mishi gwiwar zuwa, amma sai ya ce shi fa a’a

Yau ma sai yamma lis suka dawo gida.

Washegari kuma Ahmad ya wuce wurin aikinshi tare da rakiyar canvoy din shi.

Yanzu hankalin Hafsat ya fi karkata a wurin aikin ginin Islamiyar nan, shi ya ku san duk sati sai an kai ta Maƙera, shi ma Ahmad din duk sati yana gida.

A cikin haka ta yaye twins wadanda suke da shekara daya da wata biyar. Tun da ta yaye su, Sai suka rabu biyu, bassa gidanta, bassa Family House wajen Hajiya. A wajen Hajiyar ma kullum suna fada.

Shi ya sa duk wani taro da Galadima zai je tare da su yake zuwa. Watarana kuma haka nan sai a dora saman doki su zagaye gari tun suna tsoro har suka daina.

Galadima ya kan ce sune za su gaje shi ba Ahmad, sam Ahmad babu sarauta a jininshi. Shi dai kawai a yi fafutuka.

Soyayya ba ta wasa ba, Galadima ke nunawa yaran, su din ma sosai suka shaku da shi, fiye da yadda suka shaku da Ahmad.

Sai dai safiyar wata Litinin aka tashi da mummunar labarin rasuwar Galadima, babu ciwo babu komai. Rasuwar da ta girgiza mutane, ciki har da Hafsat, saboda ba ta san tana da ciki ba, Sai da labarin rasuwar ya riske ta, jini ya balle mata tsabar fargaba, shi ya sa har aka kai Galadima makwancinsa na karshe Hafsat ba ta sani ba, tana asibiti, Sai dare aka sallamota, Sai dai an ba ta bedrest, shi ya sa part din ta na gidan Galadima ta wuce, a can take karbar gaisuwa, nan din ma ba kowa ne ke zuwa ba, sai wanda yake da muhimmanci sosai. A tare da ita Nabila ce, Maman Zsrah matar Asad, Sai kuma kannen Ahmad da su kan leko, su dan taya ta zama.

<< Abinda Ka Shuka 58Abinda Ka Shuka 60 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×