AG
Bayan fitar Hacker wayarshi ya fita ya shiga wurin kira.
Kiran bai jima da shiga ba aka daga kiran.
Bayan gajeruwar gaisuwa AG ya ce “Kana ina?”
Daga can ɓangaren Cinnaka ya amsa da “Ina Area Oga, ko ta samu ne?”
“Ka jira ni, Ina zuwa.” cewar AG tare da yanke kiran, ya kuma juya kan motar tashi don fita daga layin.
Kamar 30mns ya isa Arear da Cinnaka ya shaida mishi suna can.
Tsayawarshi ba da jimawa ba Cinnaka ya fito sanye cikin kananun kaya riga da wando na jeans ya dora wata coat a sama duk da zafin da ake yi.
Kannan kamar an ci giginya ba waƙa, yatsunshi biyar na hannun hagu wasu kwama-kwaman zobuna ne.
“Oga ka dade kai karko!” cewar Cinnaka lokacin da ya bude motar ya zauna.
Komai AG bai ce ba, dalilin da ya sa Cinnaka fadin “Waye ya tabaka Oga yanzu lahira tai baƙo Allah kuwa!”
Wayar da ke hannunshi ya mikawa Cinnaka tare da fadin “Wannan na jikin hoton a jami’ar Maiha yake karatu, ina son ku kamo min shi zuwa By pass amma ku kula da kyau . Iyakar information din da na sani a kanshi kenan. Abin da zan iya kara maku a kai shi ne ɗan garin Dawaki ne.”
“Fada ta ka cikawa tamu Oga, ka san zan yi fiye da kula ma, don haka ka sanya ranka a Inuwa ya zo hannu. Sauran information kuma da kaina zan nemo shi.”
“Da kyau” Cewar AG
“An gama kawai”
Cinnaka ya kuma jaddadawa.
“Zan tura ma issassun kudi a account din ka, sannan an ji ma ka je ka dauki motor nan da kuka taba fita aiki da ita”
“An gama Oga, Sai Oga.” cewar Cinnaka hade da yi wa AG jinjina.
Daga haka suka rabu. Bari mu leka Rumasa’u.
*****
Auwalu ne zaune cikin wani ƙarami daki mai cike da turbaya, yayin da kafafunshi suke sanye cikin mari.
Jikinshi kuwa babu inda baya ciwo, wani irin bugu Alaramma ke yi mishi mai kama da fyadin shinkafar makafi, rabon da a yi mishi duka irin wannan ya manta ranar, zai ce ma ba a taba yi mishi ba. Saboda ɓarawon da aka kama jihar da suke zuwa neman kudi ne kawai zai hadu da irin wannan hukuncin, saboda su a can babu imani.
Bai taba tunanin Rumasa’u na da ciki ba, bai taba jin labarin cikin ba sai labarin haihuwarta, abin ya zo mishi da mamaki
Ban da ya san shi ne yake amfani da ita da ya karyata.
Sai dai ya san babu wani mahaluki da zai kusanci Ruma.
A Ina ma zai gan ta?
Shi kanshi ta samu damar ne saboda shi ne babban abokin Aibo (wanda Ruma za ta aura)
Aibon yana ba shi sako duk lokacin da zai zo gida ya kawo ma Ruma, ita kuma Rumasa’un ta kan fito farfajiyar gidan daga waje inda dakunan almajirai suke ta karbi sakon.
Wannan ya sa Shaidan ya rika kai kawo a zuciyar Auwalu a kanta.
Sanin ba zai samu abin da yake so cikin sauki ba, ya yi musu siddabarunsu na malamai, sai ko ga shi a ruwan sanyi ya samu Ruma yake yin duk abin da ya ga dama da ita, duk lokacin da ya kawo mata sako sai ya ja ta dakin almajiran ya biya bukatarshi.
Yanzu kam ba iya kanshi matsalar ta tsaya ba, zai iya cewa ta shafi duk wani makusancinshi da kuma Ruma.
yayarshi da ke auran Alaramma sai da ta karbi kason na ta dukan, da barazanar saki.
Mahaifiyar Ruma kam sai da saki ya tabbata a kanta, yanzu haka ba ta gidan.
Shi kuwa tsawon kwanakin uku da aka tsare shi, kullum sai Alaramma ya jibgeshi da katuwar gora abinci ko sau biyu ko sau daya kacal ake ba shi.
Bangaren Ruma ma ba karamin bugu ta ci a, hannun Alaramma ba, sannan ya kara saka mata takunkumi ba ita kadai ba, duk ƴanmatan gidan.
A ka ba Yaya aikin kula da lafiyarta, sannan aka kara daga bikinsu saboda ta warke sarai.
Rubutu kam da magunguna tana kan shansu.
Maganar abin da ya faru kam tuni Malam Balarabe ya danne bakin kowa, ba iya familyn ba, kowa da kowa aka daurewa baki, shi ya sa babu mai daga maganar.
Ango Aibo kam yana can neman kudi bai san wainar da ake toyawa ba.
Wannan kenan.
*****
HAFSAT.
Misalin karfe tara na safe Hafsat ce cikin garken awakin Inna, ba ta jima a ciki ba ta share shi tsab, hade da fitar da dattin waje. Sai kuma ta shiga gyara zaman igiyar ko wace akuya.
Daidai lokacin kanenta Magaji ya shigo a guje jiki na rawa
“Me ya faru magaji?” cewar Kuluwa da sauri.
Ya ci burki a tsakiyar gidan lokaci daya kuma yana kallon kofar shigowa
“Wai me ya faru?” Luba ta amshe tana kallon shi.
“Wani soja ne a kofar gidanmu kuma ya ce Tatuwa (haka suke kiran Hafsat) ta zo”
Duk suka juyo inda Hafsat ke tsaye tana watsawa kaji abinci, yayin da ita kuma ta aje poster, gabanta na faduwa.
Kar dai ko ɗansanda aka dakko musu, to laifin me kuma suka kara yi?
Ta aje kwanon hannunta a hankali kan dakin kajin da ke kusa da ita, sannan ta shiga dakin Inna don dakko hijabinta.
Inna da ke kwance cikin halin jinya ta yunkura dakyar ta mike zaune tana kallon Hafsat da ke kokarin sanya hajabinta.
“Me kuma ya faru soja ke neman ki Hafsah?”
Da sauri Hafsat ta juyo, ba ta dauka idon Inna biyu ba, saboda tun daga ranar da wancan tozarcin ya faru, ba ta kara lafiya ba. Ciwo ya yi sauki ya dawo.
Ganin Hafsat din ba ta ce komai ba Inna ta kuma cewa “Ko wani abun ya kara faruwa aka ce ni ce?”
Idon Hafsat ya cika da hawaye na tausayin mahaifiyarta, ta kai bayan hannunta a hankali ta dauke hawayen.
“Ina zuwa Inna” ta yi maganar hade da ficewa daga dakin.
Lokacin da ta fita tsakar gidan su Kuluwa ne da sauran yaran gidan ke tsaye jikin katanga, wannan ya tabbatar mata da sojan da aka ce yana nemanta suke leke.
Lokacin da ta yaye yabudadden murfin kofar ne idanunta suka hango mata Najib tsaye cikin kayan bautar kasa, ya jingina da katuwar bishiyar katuwar cediyar da ke daura da gidansu.
Ido ta lumshe hade da hadiyar wani busasshen yawu, koma dai menene ta san sha Allah zai zo da sauki.
Tun da ta taho ya zuba mata idanu yana nazartar yanayinta.
Duk da ko wane lokaci yanayinta yana nuna akwai abin da ke damunta, to wannan yanayin ya sha bam-bam sosai da sauran.
Saboda har rama ta danyi, ta kara fayau, hancin nan ya kara fita ziri kamar an zaro tsamiya.
Dab da shi ta tsugunna a kan kafarta tare da fadin “Good morning Uncle!”
“Tashi tsaye.” cewar Najib ba tare da ya amsa gaisuwarta ba, baki bude cike da mamaki ta mike tsayen
Ba ta taba jin ya yi Hausa ba, ta dauka ba ya ji, ko, kuma dai yana ji kadan amma baya iya mayarwa.
“How are you?” ya katse mata tunaninta
“I’m fine”
“A haka din?” ya kuma tambayarta idanunshi zube a kanta yana kallon yadda take wasa da zara-zaran fararen yatsunta.
“Sati biyu ba ki je makaranta ba, me ya sa?”
“Ba ni da lafiya ne.” ta yi saurin amsawa.
“Me ya sa ba ki aiko ba?”
Shi ma ya tare ta da wata tambayar
“Babu wanda zan aiko ne.”
“Ba ki da kawaye?”
Wannan karon kai ta daga alamar Eh
“Ai kin ji sauki yanzu ko?”
Ta kuma daga kai alamar eh.
“To ki tabbatar gobe kin je makaranta”
Kan dai ta kuma dagawa sama alamun ta ji.
“Je ki gida.”
Ya ce yana kara nazarinta.
Ta juya zuwa gidan lokacin ne kuma hawayen da take ta makalewa suka samu damar zirarowa.
Tana son makaranta, tana son karatu, amma ga shi kan dole za ta ginawa kanta katangar karfe da shi
Ba yanzu ne tsana da tsangwamar da mutane suke nuna mata take sanyata hak’ura da zuwa makaranta ba. Daga baya kuma Inna ta karfafa mata gwiwa komawa.
Sai dai a wannan karon ta sare, ba ta jin za ta kara shiga taron jama’a ta daga ido ta kalle su bayan abin da ya faru da mahaifiyarta.
Ita kanta Innar da take karfafa mata gwiwa a wannan karon ko aya ba ta diga ba, ba ta son ma tana fita, da zarar ta ji shiru za ta fara kwala mata kira.
Idan ta shigo sai ta ce “Hafsah kar ki fita gidan nan, yara su yi ta, tsokanarki suna fada miki maganganu marasa dadi.”
A yanzu kam ba kujera za a ware mata ita kadai ba, ko ajinta daban za a yi mata ba ta jin za ta kara zuwa makaranta.
A bangaren addini ta yi sauka, a bangaren boko kuma ta iya rubutawa ta iya karantawa, haka dan turanci bai mai yawa ba, tana ji tana kuma iya mayarwa, to wannan ya ishe ta.
Ba dole sai ta zama likitan da take fata ba. Fatan yanzu shi ne Allah Ya ba Inna lafiya. Wannan kadai ma ya ishe ta.
Da wannan tunanin ta shiga cikin gidan, ba ta damu ta goge hawayen da ke zarya a kan kuncinta ba saboda kallon da su Goggo Kuluwa ke yi mata.
Da sauri ta yi kokarin ɓoye fuskarta saboda ganin Inna zaune kamar yadda ta bar ta.
“Me ya faru?”
Inna ta yi saurin tambaya.
Muryarta ta daidaita sosai kafin ta ce “Malamin da yake koya mana turanci ne a makaranta ya zo.”
“Lafiya ko?”
Inna ta kuma tambaya tana kallon Hafsat da ke sagale hijabinta a kan kofa
“Tambayata ya yi, me ya sa ban zuwa makaranta, shi ne na ce ban da lafiya ne.”
Shiru Inna ta yi, zuciyarta na wani irin daci, ba karamin abu ne zai hana Hafsat zuwa makaranta ba, kamar yadda ita ma ba karamin abu ne zai hana ta tura Hafsat zuwa makaranta.
Hafsat na da kokari sosai, duk tsana, kyara da kuma tsangwamar da abokan karatunta ke nuna mata, hakan bai hana ta zuwa na daya ko na biyu ba, ba ta taba tsallake hakan ba kuma.
Hatta makarantar tana alfahari da Hafsat, saboda duk wani quiz ko debate da za a fita dole akwai Hafsat a ciki.
Sanin ba ta da abin cewa sai ta koma ta kwanta kan shimfidarta.
Hafsat kuma ta haye gado, tana kuka kasa-kasa.
Ba karamin takaici take ji ba, idan ta tuna irin kalubalen da ta tsallako baya a kan makaranta, har zuwa yanzu da take ss1, shekara biyu kacal ya rage mata ga shi komai ya lalace.
Tabbas ba za ta yafewa mutanen garin Makera ba, da suka jefasu cikin bakin cikin rayuwa, suka tozarta mata mahaifiya.
Da ace za a ba ta bindiga tabbas za ta iya harbe duk wanda ya shige gaba wajen wulakanta mata mahaifiya.
Idan da ace za ta samu damar ci gaba da karatu da soja ta yi, cikin dare za ta zo ta harbe Maigari, mai unguwa da kuma su Danliti.
Daga-daga za ta yi musu da kansu, Sai ta tabbatar ta ragargarza kansu kwanyasu ta fito, tun da ba ta amfana musu komai ba sai mummuna tunani.
Mikewa ta yi zaune a kan gadon tana kallon Inna da ta juya baya, kafeta da idanu ta yi kafin ta sauka gadon da sauri zuwa gadon da Inna take, da hanzari ta birkitota
Abin da take harsashen shi ne ta gani, hawaye shabe-shabe a kan fuskar Inna.
Lallausan hannunta ta sanya tana daukewa Inna hawaye, yayin da ita kuma nata hawayen ke sauka a kan kirjin Inna.