Skip to content
Part 9 of 54 in the Series Abinda Ka Shuka by Khadija S. Moh'd (Matar J)

Rumasa’u.

Abin da su Alaramma suia guda shi ne ya faru, domin kuwa ango Aibo, idonshi ya murzawa toka ya ce aure ba da shi za a daura ba.

Duk yadda wakilanshi suka juya shi dambu ya taliya ya ki amincewa, wannan ya sa dole aka dakata da dauran auran Ruma. Ba da son ran wakilanshi, saboda sosai suna ganin girman duk wani ahlin na Baba Malam.

Tun maganar fasa auran ana yin ta iya masallaci, har ta tsallake mutane ta leko waje, ba iya nan ta tsaya ba, Sai da ta kuma tsallake mutanen waje ta leka cikin gida

Dan-da-nan murna ta koma ciki, ƴan biki musamman dangin Ruma na wajen uwa suka yi tsuru cike da jimami.

Jama’argari kuma aka shiga kasa zance, wasu su ce ango ya fasa auran ne saboda ba ita ya ce yana so tun farko ba.

Wasu su ce kudi aka cika mishi, wasu su ce ba zai iya jure mulkin mallakar da Alaramma ke yi wa wanda duk ya ba aure ba ne, wasu su ce Alaramma ne ya raina abun da Aibo ya kawo, kowa dai da abin da yake fada.

Wadanda abun ya shafa dai hankalinsu a tashe yake hade da ɓacin rai, musamman Alaramma da yake ganin Aibo zai tozarta shi a bainar jama’a.

Bai taɓa tsammanin wannan maganar za ta tashi ba, duba da yadda su ka yi aiki a kanta sosai (To ai dama an ce asiri kwana arba’in yake ya karye, Sai dai a kuma dorawa, kila sun manta hakan ne) a ture batun aikin ma, bai taɓa tsammanin Aibo zai yi mishi wannan abun ba, ya dauka Aibon mai rufa mishi asiri ne, musamman yadda ya raine shi tun yana yaro, a hannunshi ya yi karatu har ya yi sauka, ya kuma ɗauki ƴa ba shi, ya ɗauka yana da alfarma a wurin Aibo. Amma yau Aibon ya goge mishi wancan tunanin. A gaban idonshi Aibo ke cewa shi fa ba zai auri Ruma ba, ko kunyarshi ba ya ji.

Haka wakilan ango da na Amarya suka fito daga cikin masallaci zuwa cikin zauren Baba Malam, aka shiga tufkawa, amma Sam Aibo ya ce shi fa ba zai karbi wannan auran ba.

Alaramma ya kalli mutanen da ke cikin zauren, Ya ce su ɗan ba shi wuri zai yi magana da Aibo.

Bayan sun fice daga cikin zauren ya kalli Aibo cike da ɓacin rai ya ce “Na ɗauka kai me rufa min asiri ne Sha’aibu, sai ga shi yau a bainar jama’a, cikin baƙi da ƴan gari kake son tona min asiri.

Kake son tono abin da muka binne, wadanda ko ƴaƴan cikinmu basu san da lamarin ba. Na gode sosai da wannan. “

Sha’aibu ya cuskune fuska kamar zai yi kuka, yayin da Alaramma ya cika mishi ido, baya ganin kowa sai fuskar Alaramma da ta hade kamar hadari ya taso tsabar ɓacin rai.

Aibo kam nutsuwa ya yi hade da shiga taitaiyinshi, saboda karami aiki ne a wajen Alaramma ya tashi ya mai shegen duka a cikin zauren nan, shi ya sa bai so aka bar su su biyun ba.

“Ka fada min ko nawa ka kashe, zan mayar ma da kudinka har da ƙari, Sai dai ka sani ko karbi kudinka, ko ba ka karbi abin da ka kashe ba, a yammacin nan za a daura auranka da Ruma.

Kai ba ka isa ka sanya ni a kunya ba, ka yi kadan ka tozarta ni Sha’aibu, waye kai don ubanka? “

Sha’aibu ya kara nutsuwa tare bai kufce mishi ba, saboda a ko wane lokaci zai iya jin saukar duka ta ko ina.

” Kai ni za ka yi wa iskanci, ka manta waye ni ko? Ubanwa ke ta ka ni a garin nan, Sai kai da kake a tafin hannuna, to bari ka ji, ko da sonka ko ba sonka sai an daura auranka da Ruma. Ba amincewarka nake bukata, umurni nake ba ka, a matsayina na malaminka ba rokonka ko shawartarka nake yi ba. Ka dai sanni, ka san kuma waye ni, idan ka bari na kunyata Sha’aibu, lallai za ka kunyata a duniya fiye da irin kunyar da ka sanya ni a ciki. Na fada ma wannan kar ka ce ban fada ma ba”

Hausawa sun ce ba fada da Malam ba dare.

Saboda lokaci daya jikin Aibo ya yi la’asar, ya san waye Alaramma ya kuma san ɗanyen aikin shi, idan har ya saba daga abin da ya umurce shi, ya tabbata zai yi da na sani, ya fi mishi ya amince kawaiin kawai a daura auran. Taro ya tashi lafiya ya na mai wasa da macijin tsumma, ƴan kallo lafiya mai wasa ma lafiya.

“Nawa ka kashe?” cikin tsawa Alaramma ya yi maganar.

Murya ciki-ciki ya ce “Naira dubu ɗari na kashe”

“Na kara ma dubu hamsin, kuma gidana na can kan tudu zan sanya a yi mishi shafe yau ku zauna a ciki”

Yana maganar yana zaro rafa din kudi a aljihunshi, ya jefawa Sha’aibu a kan kirjinshi

“Allah Ya kara daukaka” cewar Aibo kamar ba ya so.

 Alaramma bai amsa ba ya fice daga cikin zauren.

Duk da yamma ta yi sosai, amma har lokacin akwai ragowar mutane da yawa, musamman maroka da ƴan gulma.

Ba ɓata lokaci aka lalubo liman ya ɗaura auran Ruma.

Lokacin da ake ta hada-hadar kai Amare ne Auwalu ya samu ya saɓe daga daurin huhun goron da ya sha, ya bi dare.

Wannan kenan.

*****

AG ne da Hacker zaune a gaban mota, dukkansu idanunsu a kan screen din wayar da ke rike a hannu Hacker, yayin da suke karanta post din da Mk Bashir (Kb) . “On my way to Maafa in Sha Allah” haka ya rubuta hade da dora hotonshi da ya ci kwalliya.

AG ya janyo wayarshi cikin sauri ya aikawa layin Cinnaka kira hade da komawa can gefe.

Ba jimawa Cinnaka ya dauki kiran,AG bai jira wani surutu daga Cinnaka ba ya ce “Target din mu zai je Maafa, kar ka sake wannan damar ta kucce mana”

“An gama Oga” cewar Cinnaka cikin kakkausar murya.

AG ya yanke kiran hade dadawo inda Hacker yake tsaye.

Bangaren Cinnaka, kiran AG na yankewa, ya shiga kiran wani layin shi ma.

“Gatari, gayen nan zai je Maafa, lallai ka yi kokarin bin shi, kana kuma bamu bayani a kanshi gani nan zan dakko tawaga”

Ba tare da Gatari ya ce wani abu ba, Cinnaka ya yanke kira tare da cusa wayar aljihu ya nufi wajen yaranshi

Ba jimawa suka shirya hade da ficewa cikin wata jeef mai dauke da tinted glass.

Bangaren Mk kuwa  a bakin hanya ya tare mota, Sai dai abin da bai sani ba, tare suka shiga motar da Gatari, saboda cikin hanzari Gatari ya fito inda ya tabbatar a nan Mk zai hau mota zuwa Maafa.

Tun da motar ta fara tafiya Gatari ke turawa Cinnaka information har zuwa lokacin da suka isa garin Maafa, haka Gatari ya rika bin Mk a boye ba tare da ya sani ba,   su Cinnaka ma tuni suka iso   garin Maafa, a mafarkarsu, suke  karbar information daga Gatari.

Misalin karfe biyar Mk ya nufi inda zai samu mota, yanzu kam su Cinnaka ne ke bin sawayenshi ba tare da sanin shi ba.

Zuwa 5:30pm ya samu mota ya dau hanyar komawa gida, yayin da su Cinnaka ke bin su a baya, wani lokaci su wuce motar su Kb wani lokaci kuma motar su Kb ta zo ta wuce su haka suka rika tafiya ku san a jere , har zuwa lokacin da suka isa wani matsakaicin daji mai tsaunuka.

A daidai wurin ne Motar su Cinnaka da ke gaban ta su Mk ta gangara gefen hanya alamun akwai matsala.

Cikin hanzari Wizi ya fi  hade da dagawa motorsu Mk hannu alamun ta tsaya.

Ba tare da wani tunani ba, direban ya rage gudu tare da gangarawa gefen hanya

Tsayawarsu ke da wuya su Cinnaka suka nufo motar su hudu, kamar masu son labarta musu matsalarsu.

Lokacin da direban su Mk kokarin fitowa domin fuskantar su Cinnaka, Disko ya mayar da shi ciki, cikin ƴan sakanni suka tsaya jikin ko wacce kofa yayin da suka zira kansu ta glass din suka fito musu da bindigu, sannan suka umarci Mk ya fito.

Motsin kirki a motar babu wanda ya yi, har Mk ya fita, suka tura shi cikin motarsu suka yi ribas baya, wannan ya faru ne a cikin abin da bai wuce minti daya ba.

*****

ASMA’U

8:00am

Cikin bacci ta ji wayarta na vibration alamun kira.

Ganin sunan Hajiya Babba surukarta, da sauri ta dauki kiran .

Daga can Hajiyar ta ce “Na san bacci kike yi, yi hak’uri likita ne ya zo duba ki”

“To” Asma’u ta amsa hade da mikewa ta saka hijab din da ta yi sallah ta nufi bangaren Hajiyar ba tare da tunanin komai ba.

Saboda Hijiya irin mutanen nan ne da basu raina ciwo, komin kankantar ciwo za ta ce a kira likita, bare ita da ku san sati kenan take fama da ciwon kai, tun kuma da Hajiyar ta fahimci haka kwana uku baya ta dage lallai sai likita ya duba ta.

Lokacin da ta shiga falon Hajiyar ce zaune a daya daga cikin kujerun falon sanye da dogon hijab, Sai Dr Sadiq dake zaune a kan kujerar dining suna taɓa hira kadan-kadan.

Shigowarta ya sa duk suka mayar da idanunsu a kanta.

Cike da girmamawa ta gaishe da Hajiya, sannan ta juya kan Dr Sadiq, ya amsa har lokacin yana kare mata kallo.

Hajiya ta mike zuwa cikin bedroom tana fadin “Ga ta nan Dr a duba ta”

Bayan tafiyar Hajiyar Dr Sadiq ya shiga jerowa Asma’u tambayoyi tana amsawa har lokacin da ya jefo mata tambayar da ta hana mata yawun bakinta wucewa.

Ta kafe Dr Sadiq da ido kamar tana jiran amsar tambayar daga bakinshi, a can cikin zuciyarta kuma lissafi take na yaushe ne ma ranar  ta karshe da ta ga period dinta. Kamar yadda Dr Sadiq din ya tambaya

Ana saura kwana biyu ta dawo nan ta yi wanka, kenan bayan wankanta da kwana biyu ta hadu da Kb.

Daga wancan lokacin ba ta kara ganin jini ba, ya kamata ace tun kwanaki goma baya ta ga period din, amma shiru har yanzu da Dr Sadiq ke mata tambayar yaushe na last period din ta.

“Ba zan iya tunawa ba” ta amsa a hankali ba tare da ta kalle shi ba.

“To idan ba damuwa ki kawo min fitsarinki zan tafi da shi lab”

Babu yadda ta iya haka ta karbi bottle din hannunshi ta shiga toilet na ɗakin ƴanmatan Hajiya da suka yi aure, ta yi fitsarin hade da kawo mishi.

“Za ki iya tafiya” ta juya salo-salo  cike da tashin hankali da ta kasa biye shi a saman fuskarta zuwa bangarenta.

Shigarta babban falon ke da wuya ta kwashe hijabin jikinta ta wurga kan kujera, ji ta yi kamar ta lulluba bargo, wani zufan tashin hankali ne ke tsiyayo mata, ta shiga lissafa kwanakin da ta yi rabon ta da period, ta lissafa ya fi kafa dari har wayarta ta dakko ta lissafa da ita, kwanaki talatin da biyar cif-cif dai yake ba ta.

Ranar da za ta tafi gida period ya zo mata, kuma mijinta Ahmad ya san haka, saboda da kanshi ya fita ya siyo mata pad ta saka a karamin hand bag din ta.

Kwananta hudu a gida ta yi wanka, tana da kwanki goma sha takwas da wanka ya kuma dawowa, ta yi wanka da kwana biyu ta dakko hanya.

Wanda idan manta ba,  Ahmad da kanshi ne ya ce ta jira sai ta yi wanka sannan ta taho, saboda a lokacin bai san da tafiya course din da ya tafi ba, saura kwana daya ta taho,,  fito order ta fito a kan za su je Farang, kan dole ya tafi ba don ya so ba.

Ta kai karshen tunanin nata da fadin “Na shiga uku Ni Asma’u, Allah dai ya sa ba ciki ba ne. Wayyo Allahna!”

Ta fada a rude hade da daukar hijab dinta da ta yar a gefe ta nufi bedroom, kudi ta dakko ta nufi Chemist din da ke tsallaken kofar gidansu da kanta, duk yadda dogarawa ke tasowa a kan ta basu aiken ba ta ba kowa ba, da kanta ta siyo pt strip din.

Duk wasu mashina da motoci da suke zarya a round about din kofar gidan ba ta ganinsu, jefa kafa kawai take yi, sune suke kauce mata har ta iso part dinta

Tsabar tashin hankali a glass cup dinta ta yi fitsari ta jefa strip din ciki ta zare shi hade da zuba mishi ido ko kyaftawa ba ta yi.

A hankali ya rika canja kala, har lokacin da ya tabbatar mata akwai ciki.

Ta saki strip din kasa tare  da  glass cup din cike da tashin hankali.

Yadda ta sakesu haka ta saki baki da idanunta gabadaya kamar wawiya, zuwa can kuma ta zauna gefen gadonta a hankali tana fadin “Innalillahi Wa’inna IlaihirRaji’un!”

Haka ta rika maimaitawa ba tare da sanin ko adadi nawa ta yi ba.

Ba ta san ko minti nawa ta kwashe zaune a wurin ba, kafin ta mike jiki ba kwari ta shiga zagaye falon hawaye na mata zarya, cikin kuka take fadin “Na shiga uku Ni Asma’u, ya zan yi da wannan tashin hankali, ciki a jikina ba na mijina ba na wani. Shekarata uku a gidan nan ban samu ciki ba sai haduwa daya da Mk, wayyo Allahna! Wayyo Allahna!!”

Ta kai karshen maganar hade da fadawa saman gado ta ware muryarta sosai ta shiga kuka.

” Ina zan kai wannan abun kunyar nan, ta ya zan fara kallon idon kamilin mijina, mai sona da gaskiya, wanda ya ba ni dukkan yarda, ya yi min komai, in ce ina da ciki ba na shi ba. Ya fi min in mutu da in ga wannan ranar, ba zan iya hada ido da shi ba, kai ba shi ba duk mutanen gidan ma. Wayyo Allahna, Allah na tuba wlh, Allah ba zan kara ba, Allah ka ji kaina, wayyo Allah na mutu wlh” ta kara bude murya tana kuka wi-wi.

Kuka take yi sosai, kamar shi ne aikin da aka ba ta yau, idan ta yi kuka kuma sai ta hau sambatu, kamar yanzu ma zaune take a tsakiyar gadon hannayenta biyu a saman kanta tana fadin “Wayyyo Allahna Mommyna, wayyyo Allahna Babana, don Allah ku yi hak’uri ku yafe min. MK ka zame min bala’i, na yi danasanin haduwa da kai. Wayyo ni kaina.”

Kamar wacce aka tsikara ta duro daga gadon ta nufi babban falon a guje inda ta yasar da wayarta lokacin da take kirgen kwanaki a calendar.

Lambar Mk ta shigar, dole da shi ne ya kamata ta raba wannan tashin hankalin, cikin rashin sa a aka ce mata wayar a kashe, haka tai ta gwadawa ana ce mata a kashe, har ta gaji ta fada kan kujerar ita da wayar ta fashe da wani sabon kukan.

<< Abinda Ka Shuka 8Abinda Ka Shuka 10 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×