Skip to content
Part 2 of 6 in the Series Addininmu by Salis M. Reza

Zainab ta ce “To yanzu Mama haka zan barshi ya cigaba da cin mutuncin mu al’halin kuma duk abun da yake fad’a ‘karyane? Mama ta ce “Zainab karki bari malam yaji zancennan domin kinsan Shima baya ‘kaunar su, saboda haka kibar komai a gurina, kinga yanzu in kika biye masa al’ummar gari zasu samu abun fad’a dukda dama batin yanzu akasa ba jin kanku dashi ba, dukda ke ba beye masa kikeyiba, yanzuma kiyi haguri karkice komai kiyi abun dake gabanki…

Yabon Annabi Muhammad sallalahu a w s ne kuma babu Wanda  ya isa ya hanaki domin kuwa da albarkar uwa da uba a kanki, kuma ga soyayyar Nana batula ‘Yar manzan Allah wanda shine silar saninn ki da al’umma sukaye, kinga ko iya haka ai kinci riba sosai ko?

Cikin jin dad’i Zainab ta ce “Sallahu a’lahi wasallam, tana mai shafa wa a fuskarta, sannan ta shiga rera wata ‘kasida da tayiwa Nana fad’ima Yar ma’aikin Allah Mai taken *(NANA YAR MA AIKI UWAR GIDAN ALIYU SADAUKIN DA FAYA TSORO)

A J. VOP

Yana shigowa gidan ya tarrar har nana ta gama shanya masa kayan sannan ta ‘dora musu girki, Yana shiga ciki inah ta ce “Wai Abdul jabaru meya had’a ka da wasu mutane yanzu suka turo wai ana neman ka? shine na tura Nana kadija akan ta dubo, tazo tacemin Wai wani saurayi ne a cikin mota! Kafin Innah ta rufe baki Nana ta ce “Yaya wanine yazo Wai yace min in kazo nace maka sunan sa salis yazo bai gankaba ka sameshi a gida.

Da sauri AJ ya ce “Wa kikace? Nana ta sake cewa “Wai Salis. Ai da sauri AJ ya rungumeta yana cewa “Innah in Sha Allah arzi’ki ne yake kirana, ina wannan gidan da nake baki labarin cewa in na mallaki gidan nahuta, tofa yaron gidanne ranar juma’ar da ta huce muka had’u dashi  to shekaran jiya ya gaiyaceni gidansu har mukaci abinci, shima baban sa ya rasu daga shi sai ‘kanwar sa sai mamarsu agidan Wallhi Innah in kiga ga gidan sai kin godew Allah!.

Innah ta ce “Auda bana gode masa har sai naga gida? Ta cigaba da cewa “wallhi Abdul jabaru kari’ke maraicin ka karka dinga saka kanka a gurin da Allah bai sakakaba, i’na kai i’na abota da d’an masu kud’i har kana fad’a.

AJ ya ce “Yanzu Innha dan Allah kallemufa? yana ri’ko  hannun Nana yana cewa… Yanzu dan Allah Innah munyi Kama da y’ay’an talakawa, ai wallhi ko daga gani kinsan huce nann, Koda mud’in bamu da kud’i amma ai Muna Kyu ko, saboda haka mude ki dinga mana addu’a kawai. Innah tayi salati ta sanarwa da uban giji kafin ta ce “To dan gidan ku kyu d’in da kake alfahari dashi ai duk nawane shima uban naku ai ni ya gado kukuma kuka gajeshi, Kai Allah dai ya ji ‘kan Rabu’u!! Tafad’a kamar tayi kuka.

Duk suka amsa da amin. Sannan Nana ta ce “Yaya  sabulun wankanafa ya ‘kare ga kuma a islamiya ance a kawo kud’in wata? AJ Ya kalli Innah ya ce “To kingani yanzu da bana tare dasu a Ina Zan samu wannan kud’ad’an. Nifa wallhi Inna duk wata sana’ar da zata kawomin kud’i Zan iyayi domin Naga na inganta rayuwar Nana da kuma taki…

Sannan kuma akan kud’i zan iyayin duk wani Abu in dai ADDINIMU bai haramtaba. Kede inna kinsan bana sata bana shaye-shaye bana neman mata, duk abun da kukaga inayi to nasan menakeyi. Karatunnan fa nayi, nasan dai-dai da kuma a kasin hakan, shima wannan d’in da yake kirana aiki zan samu a gurinsa shine yasa.

Innah tayi shiru tana tinani tabbas abun da yafad’a hakane, baya sata sannan Kuma komai na rayuwa shine yake musu daga ita har Nana d’in, Yana yin duk wata sana’a in dai zata rufa masa asiri. Bata mantawa, yayi san’ar okada, yayi yaron mota, yayi jiran shago ya iya d’in ki, ga ya ta’ba zama Dreban wani mutumi Kuma duk saboda su, to amma abun tambayar ba kullum yake zuwa aikiba kuma kullum baya rabuwa da kud’i, in na tambayeshi yace sana a yayi.

Tana cikin tinani taji Yana cewa, yanzu in naje gurin sa zan samu aiki wanda daga yau mun daina cin tuwo a gidanan , ya kalli Nana ya ce “kilissafa min duk abun da kikeso in nadawo zan siyo miki, cikin murna Nana ta sake rungumshi tana ji kwanar yayan nata sosai,  ta ce “Allah ya dawo da Kai lafiya Yaya. Itama Innah ta ce “dan Allah kadinga tinawa damu tik inda kashiga karkabarmu. AJ yace karki damu Innata abar alfahari na.

Yana fita ya tuno da Zahrah sai yayi dariya ya ce “In banda mahaukaciya ina ta ta’ba jin ana aure tsakanin musilmi da arne! Wai ita aure takeso muyi, baride na gama samun Yan canjina na barki da nemana. Yanzufa wannan yarinyar ta satomin kud’ad’e sunfi dubu d’ari shida, anya kuwa in baban ta ya kamata bazan shiga damuwa ba!? Sai kuma yace kodan ai tana sona bazata ce nine nake sakataba, kumafa babanta soja ne! Ta’b gaskiya rabuwa zanyi da yarinyar nann Yasin kafin ta sakani a  matsala, haka ya tare me mashin zuwa gidan su Salis, yana tinanin tayaya zai rabu da ita.

*ZAHRAH* *VOP*

Take ta zubar da kud’in a gurin ta shiga dukan ‘kofar amma bata ko motsi, tin tana d’aukar lamarin wasa har abun yazama gaske, wasa wasa zahrah takai a’wa uku acikin d’akin amma ba wanda ya shigo gidan, nann take tafara rusar kuka domin kuwa ta tsorata sosai ga yunwa dake addabar cikinta ga tsoran abunda Daddy zaimata in ya kamata, domin kuwa tasan da cewa ta kamu.

Tana cikin hakane taji dawowar su, harda Samuel da Daddy harda Mommy, da sauri ta kwashe kud’in ta mayar gurin da ta d’auka sannan ta tashi ta koma ‘kar’kashin gado ta sake ‘boyewa.

Ai kuwa cikin sauri Daddy ya shigo d’akin yana shiga ya tsaya cak yana mai bin d’akin da kallo…sai ya nufi gurin da ya ajiye kud’in yana mai bud’e abun ya zubawa kud’in ido kamar mai son gano wani abu, sai Kuma ya koma bakin kofar d’akina yana dubawa kodai bai rufe da Kyu bane, domin kuwa Tabbas an shigo d’akinnan. Kayansa ya cire ya rage daga shi sai gajeran wando na sojoji, Wanda Zahrah tana ganin sa a haka ta rufe ido cikin tsoro, toilet ya fad’a ya rufo ‘kofar, ai kuwa yana shiga itama ta fito, har zata fita sai kuma ta dawo da baya ta bud’e gurin ta kwaso kud’in ta saka a cikin jins d’in dake jikinta dama ya katseta, sannan tayi hanyar barin d’akin Amma ta sake jin ‘kofar a rufe.

Cikin rekicewa ta saki wani ihuuu d’an ‘karami amma tayi saurin toshe bakinta da hannu, sai ta hango kin d’akin a kan kadonsa gurin da ya cire kaya, nann ta d’auko ta bud’e, sai ta dawo ta ajiye  da niyar fita sai daji alamar shigowa d’akin, ai da sauri ta koma bayan ‘kofar ta ‘boye ai kuwa Mai shigowar Yana tura ‘kofar yashiga ciki yana shiga ita kuma ta sand’a ta fita, ta nufi d’akin ta cikin rikicewa, tana shiga ta boye kud’in sannan ta saki a jiyar zuciya.

Samuel kuwa, yana shiga ya samu gefen gado ya zauna Yana jiran fitowar Daddy, ai kuwa yana  zama Daddy na fitowa. Cikin tsananin mamaki da firgici Daddy ya ke kallon Samuel ya ce “Samuel what are you doing in may room? Kafin Samuel yayi magana ya ga durowar kud’in abud’e ga kuma ‘kofar d’akin nasa ta ciki ya rufe Amma yaga Samuel aciki gakuma kofar a bud’e.

ABDALHA VOP

Zaune suke agaban Mommy dukkanin su, abdalh Maryam da Sadiya da Nusaiba sai autansu Nura… Kallon su tayi kafin ta ce “meya had’a ka da Maryam? Cikin tsananin jin haushin abun da Maryam d’in tayi ya ce “Mommy wai wannan yarinyar d’an bidi’a zata kawo mana gida a matsayin mijin aure! Saboda ita mara kunya ce, shine harda cewa Wai in Abba yazo zata sanar masa, Mommy ta ce “Wai ni abdullha kaida babanka bansa me kuka d’auki mutanan ba, sumafa musilmai ne kamar ku, Allah mu d’aya annabin mu d’aya, littafi d’aya muke karantawa wato ALQUR’ANI mai girma, kaga kenann ADDINIMU d’aya, to meyasa don an d’an samu rebewar Kai sai ku dunga ai batasu kuna kafurtar dasu!?

Kafin wani yayi magana sukaji ana cewa “Mu ba d’aya muke dasuba, domin kuwa mu bamuyin abun da Annabi Muhammad sallalahu a w s, baiyiba Kuma Allah baice a yiba, saboda haka, nidai zuria’a ta bazasu had’a jini da suba, cewar Abba yana shigowa d’akin. Kafin kowa ya sake mgn Nusaiba ta ce “Ni fa wallhi bana musu kallon musilmai domin kuwa wani lokaci in sukayi wani abun Kamar basa karanta ALQUR’ANI, .

Sadiya ma ta ce “Ni Wallhi tinma ba wannan Zainab Ambato d’inba gaba d’aya ‘kasidun ta babu wani tsari da ma’ana amma a haka zakika kowa Zainab Ambato Zainab Ambato. Mayarm ta ce…

“Ashede kina jin ‘kasidar tata da har kika san babu tsari, kafin kowa yayi magana Abba ya ce “Andullahi meya faru? Abdullha ya ce “Abba Maryam ce tazo da wani yaro Wai shi takeso kuma d’an bidi’a ne. Daddy kuwa dama yagama sakarwa abdullha ragamar gidan duk abun da ya yanke a kan ‘kannennasa to yayi. Nann shima ya tabbatar mata da cewa Babu ita bashi, in auren takeso ta nemo mari’kin sunna shi zai aura mata, Yana gamawa ya bar d’akin ya nufi nashi d’akin dama yanzu ya shigo.

Mommy ta kalli Maryam ta ce “mamana ki rabu dashi tindade Abbanku da yayanki basaso kinji? Kafin ta Kara’sa Nusaiba ta ce “Toma mommy in banda zubar mana da kima yaza’ayi ta kawo mana dan la’ilo tace yazama suriki a gidannan.

Itama Sadiya ta ce “Allah da nagan shi da sai na gaya masa maganar da bazai manta da itaba, “Ai kuwa kema da namiki abunda bazaki manta da niba. Ina ruwanki da saurayina? Duk abun da zakuyi ku tsaya a iya matsayinku karku shiga gonar da ba takuba domin kuwa ba tsoran aji kanmu daku nakeba. Maryam tana kaiwa nann ta fito da wayarta ta Kuna qasidar Zainab Ambato mai taken GANI ASO, tabar su a gurin ri’ke da baki.

Mommy ta ce “Nace kudaina shiga hankarta yanzu tana kan ganuwar girman balaga tanajin kanta yanzu dai-dai daku saboda haka kubarta tayi rayuwarta, Kuma karku fad’a wa yayanku tana jin ‘kasidar Zainab Ambato kunji? ceke da takaici Sadiya ta ce “Yasin Mommy Maryam ta rainamu, ace agidannan ana jin kad’e-kad’e kuma kice kar a fad’awa yaya, shida yakeyin wa’azi akan kid’a babu kyu sai Kuma a samu a gidan sa, ai dolenema yaya yaji wannan zancen, tana kaiwa ta tashi fuuu tabar d’akin izuwa nata d’akin.

Mommy ta ce “Allah dai ya sa mudace, Kuma Allah ka barmu a musulumci kuma Allah ka had’a kan al’ummar musilmi na duniya Baki d’aya. Nusaiba ta amsa da amin.

ZAINAB VOP

Kallon yayan nata tayi kafin ta ce “Wai kuwa kasan gobe zan bogowa wancan banzan wata ‘kasida mai harshen damo? Isa ya ce “Nifa Allah yaron mamaki yakebani shifa burinsa wai ace shi ma malami Kuma wallhi bai kai ya had’a kansa da keba, yanzu duk Wanda kacewa Zainab Ambato, d’an izalar da ma Yan ‘dariqar bawanda bai San dakeba, shifa, in kace… Abdalh in dai Baki had’a da sunan baban saba Wallhi za’a ce waye haka, Koda acikin masu d’an gelallan wandonne, take suka bushe da dariya dai-dai lokacin MLM wato babansu ya shigo.

Kamar yanda d’abi’ar su take ta girmama duk wani babba ta hanyar rusunawa har ‘kasa sugaishi haka yanzuma har ‘kasa suka rusa suka gaida MLM. Bayan ya amsa ne ya saka musu albarka sannan ya ce “Zainab d’azu su Alhaji Bashir sunce ranar JUMA’A suna gaiyatarki zaki musu majalasi a gidansu zai aurarr da yarinyarsa. Kuma na amince masa, ina fatan dai kinada lokaci?

Cikin girmamawa ta ce “to MLM ai koda bani da lokaci tinda suka biyo ta hannun ka ai zan samu lokaci. MLM yayi mata godiya sannan ya ce “Saide wani hanzari ba guduba… Gidan Alhaji Bashir d’in jikin gidan wannan mara kunyar yaronnanne ‘dan gidan Shek kabiru. Take isa da Zainab suka had’a baki gurin cewa, Abdalh shek kabir kenann kake nufi?

MLM ya ce “eh  wannan. gaskiya yaron bashi da kunya ahakan ya kurarin su malamaine Amma suna cin mutuncin mutane, nasan yanda kuke dashi saboda haka kisan abun da zakiyi. Zainab ta ce “to MLM nagode ranar JUMA’A ko? “Eh ranar JUMA’A.

Sannan ta tashi ta bar d’akin ciki da jin dad’in haka, Isa dake bayanta ya ce “Ashe a gurin za’a fara jin sabuwar ‘kasidar kenann? Ya cigaba da cewa “ya sunann gasidar? Itama cikin tinani ta ce “Sunann ta bud’ad’d’iyar wasi’ka…📝

A cigaba damin  uzuri… Labarinan wallhi sai ka/kin ‘karu dashi banda zagi, gaskiya ce kawai.

Bana ganinn comment d’in kufa, kodan…

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Addininmu 1Addininmu 3 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×