Muryoyin al'umma ne kawai ketashi agurin ana bin wa'kar kamar sune suka rerata, ita kuwa Zainab sai kallon gurinda Abdalh yake takeyi tana son ganin wani irin yanayi zai shiga. Abdullha kuwa yana ji tasaki wannan wa'kar ya kalli abokin nasa cikin tsananin b'acin rai ya ce "Nagode da abun da kamin sannan kuma in harkana so na cigaba da zama anann to sai an kori wannan mawa'kiyar. Angon ya kalli Abdalh sannan ya ce "Haba Shek abdullha kasanfa banine na gaiyatotaba uwar amaryar ce, kuma tana gurinnan kaga kuwa banida ikon korarr ta.
Abdullha. . .