Hannunta take ƙoƙarin ƙwacewa daga cikin na Fu’ad amma gam ya riƙeta Fuskarta cike da kunya ta ce mishi, “Mama Indo fa na kitchen.”
Ɗaga mata gira ya yi da ke nuna cewar sai me? Shi bai damu ba. Ɗayan hannunta ta sa ta cire nashi daga nata. Wani shagwaɓe fuska ya yi.
“Gobe warhaka sai kin nemi hannuwana kin rasa Sofi.”
Da sauri ta kamo hannuwanshi duka biyun ta riƙe. Har ranta ta ke jin tafiyar nan. Idanuwanta da suka ciko da hawaye ta sauke masa.
Da sauri yace,
“Yi haƙuri. Na daina.”
“Ina sane da tafiyar nan. Ba sai ka tuna min ba…”
Hannunshi ya zame daga nata ya kama kunnuwanshi duka biyun.
“Afuwan. Na daina amma kar hawayen nan ya zubo. Ba na son ganinsu.”
Murmushin ƙarfin hali ta yi masa. Ta dai kasa cewa komai. Don tana yin magana kuka za ta yi.
Dab da ita sosai ya ƙarasa. Ya tallabi fuskarta cikin hannuwanshi yana kallon cikin idanuwanta.
“Ki kira Laurat. Ba lesson yau.”
Ware idanuwanta ta yi cikin nashi tana son ce mishi ba ta yarda ba. Goshin shi ya haɗa da nata.
Kusan laɓɓan shi kan nata suke. Wani miyau da ba ta san da shi ba cikin bakinta ta haɗiye.
Yana ganin yadda idanuwanta ke yawatawa kan fuskarshi. Hucin numfashinta na ƙaruwa kan fuskarshi. Kan laɓɓanta ya yi magana da faɗin,
“Yau ba lesson. Lokacina ne duk yau. Kin ji?”
Kai ta ɗaga masa gwiwarta na yin sanyi. Wata sumba mai taushi ya manna mata a leɓe sannan ya saki fuskarta. Wannan karon shi ya ke maida numfashi yana ƙoƙarin maida yanayin da ke son ƙwace masa.
“Bari in yo alwala in je in yi la’asar. ki shirya kafin in dawo mu fita.”
“Ni ma bari in yi sallar. Ina za mu je?”
Yatsun shi yai running kan fuskarta. Yana bin inda duk suka taɓa da kallo kafin ya yi ƙasa da idanuwanshi kan laɓɓanta ya tsayar da su a nan.
“Sirri ne.”
Idonshi ya mayar cikin nata ya ɗora da,
“You are gonna be dah’ death of me Sofi.”
Fuskarta ta ɗan daƙuna tana maimaita kalamanshi cikin kanta tana so ta gane ma’anarsu.
Wucewa ya yi ya barta nan tsaye. Numfashi ta sauke wani son shi na shigarta. Ƙarasawa ta yi ta ɗauki wayarta a kan kujera ta kira Laurat. Bayani ta yi mata cewar za su fita da Fu’ad, in sun dawo da wuri za ta kirata.
Bedroom ta shiga. Sai da ta watso ruwa tukunna ta yi alwala ta fito ta yi sallar la’asar. Mai ta shafa. Ta murza hoda. Kallon fuskarta ta ke yi a mudubi. Yadda ta yi wani haske ta yi ɓulɓul. Kamar ba ita ba.
Miƙewa ta yi kafin tunani ya haye mata. Ta ɗauko wata doguwar riga ta atamfa ta saka.
Ɗinkin ya zauna mata. Simple ta ɗaura ɗankwalinta ta ɗauko mayafi kalar kayan ta ajiye.
Sanda mamansu Fu’ad ta aiko mata da kayayyakin kusan kowanne da mayafinshi da takalmi da jaka.
Kayan kaɗai ta yi amfani da su. Tunda babu inda ta ke zuwa. Koda ta ke jajen mai kitso wa Laurat cewa ta yi ta kwance ta wanke za ta yi mata.
Haka kuwa aka yi. Banda makaranta. Ta kwana biyu ba ta je ko ina ba. Sallamar Fu’ad ta ji yana turo ƙofar.
Ta amsa tare da faɗin,
“Sannu da dawowa.”
Kallonta ya ke yi. A hankali ya taka zuwa inda ta ke tsaye. Tun daga ƙafafuwanta ya soma yawo da idanuwanshi har fuskarta.
Wani numfashi ya ke ja ya na fitarwa ta bakinshi.
“Ƙin yi kyau. Kin yi kyau sosai.”
Murmushi ta yi mishi. Ta ɗauki mayafinta tana faɗin,
“Mu je ko?”
Fito da idanuwa ya yi yana wani tura baki gaba.
“Um um. Kin ga kyan da ki ka yi? Nima sai na sake kaya.”
Yadda yakan yi mata ta yi mishi. Ta sa hannuwa ta tallabi fuskarshi tana ɗaga ƙafafuwa saboda ya mata tsayi. Dariya ya dinga yi mata. Hannunshi ya ɗora kan ƙugunta ya ɗan yi sama da ita.
Har mamakin yadda ya ke ɗaga ta ta ke yi. Ko numfashi bai mayar ba. Sai ka ce ɗaga ta ɗin wani abu ne mai sauƙi.
“uhum Sofi…”
Ya ce yana kallonta. Maƙalo masa wuya ta yi ta na ɓoye kanta cikin kafaɗarshi saboda kunyar da ta kamata. Cikin kunne ta raɗa mishi.
“Ka yi kyau sosai. Ko ba ka sake kaya ba.”
Dariya ya yi ya na sake gyarata a jikinshi. Muryarshi can ƙasa ya ce,
“Indai kin ce na miki a haka. Za ki iya fita da ni. Fine mu je.”
Ka ji shi fa. Wai in za ta iya fita da shi ma yake faɗi.
“Kai ba ka ji kunyar jerawa da ‘yar karkara ba..wayyoo.”
Ta ƙarasa saboda cizon da ya yi mata a gefen kafaɗa. Sauketa ya yi. Fuskarshi babu alamar wasa yace,
“Wa ya faɗa miki ba zan yi rigima da duk wanda ya raina min ke ba? Ko da kuwa ke ɗin ce da kanki.”
Kanta ta sadda ƙasa tare da faɗin,
“Na daina…”
Hannu ya sa ya ɗago mata da haɓa,
“Kar in sake ji. Ke matar Fu’ad ce. Kin wuce raini a ko’ina.”
Kai ta ɗaga mishi. Fuskarshi ya kai ya sumbace ta sannan ya ce,
“Good. Mu je.”
Mayafinta ta ɗauko tana maimaita yadda ya faɗi ‘good’ cikin kanta. Saboda ta ji kalmar ta fi a ƙirga a makaranta, amman yanayin da ya lanƙwasa ta ya mata daɗi. Maimaitawa ta ke ta yi. Bakinta da ke motsi ya ke kallo. Da mamaki ya ce,
“Magana ki ke yi?”
Da sauri ta girgiza masa kai tana yafa mayafinta.
“Sofi..?”
Ya kirata yana jan sunan. Murmushi ta yi a kunyace sannan ta ce,
“Kalmar da ka faɗa na ke maimaitawa saboda ta min daɗi.”
Dariya ya yi kawai a ranshi ya ke faɗin ya ma za a yi da duk lokutan da suke wucewa son Sofi ba zai ƙaru a zuciyarshi ba.
“She is fucking amazing.”
****
Suna mota ya kira wayar Anty Fatima ya faɗa mata ga su nan a hanyar gidanta. Shi kanshi ya manta rabon shi da gidan.
Zai ma iya ƙirga zuwanshi gidan Anty Fatima. Ko me zai siyo sai dai ya ba wa Momma a aika mata da shi.
Sai da suka yi parking cikin gidan suka fito sannan Safiyya ta ce mishi,
“Tsoro na ke ji.”
Dariya ya yi mata.
“Karki damu. Anty Fatima ba ta da matsala.”
Shiru ta yi ta bi bayanshi. Da sallama suka shiga gidan. Aikam Safiyya ta ga ba ta da matsala don da fara’a ta tarbe su.
Ta ja Safiyya suka zauna. Fu’ad ta kalla ta ce,
“Ina nan ai ƙule da kai wallahi. Tunda Momma ta faɗa min shi ya sa ka ga ban kira ba.”
Dariya Fu’ad ya yi. Haƙuri ta ke so ya ba ta bai kawo mata Safiyya sun gaisa ba. Ta kuma san sai dai ta gaji da mitarta don ba samu za ta yi ba.
Gaisawa suka yi sosai da Safiyya don ma ta na jin kunya. Ko lemo da soyayyen nama da meat pie ɗin da ta kawo musu kasa ci ta yi.
Miƙewa Fu’ad ya yi yana faɗin,
“Anty wucewa za mu yi. “
Buɗe baki ta yi sannan ta ce,
“Kai Fu’ad ka sa Allah a ranka. Tun yanzun?”
Dariya ma ta ba shi.
“Ba kun gaisa ba?”
Miƙewa Anty Fatima ta yi. Da ido ta nuna mishi alamar ta na son magana da shi in private.
Daƙuna fuska ya yi. Bai dai musa mata ba ya bi bayanta zuwa wani ɗan corridor.
Ba wani ɓata lokaci Anty Fatima ta ce,
“Bazan judging ko me ya faru da ku ba Fu’ad saboda na san ƙaddara kowa da tashi.
Allah kuma ya riga ya rubuta taku tun kafin a haife ku.”
Wani juya idanuwa Fu’ad ya yi tare da faɗin,
“Sai na yi kewar Islamiyya…”
Harararshi ta yi don ta san rainin wayau ne ya sa shi faɗar haka. Ganin ta yi shiru tana kallonshi ya sa shi faɗin,
“Ina ji. Just cut it short.”
“Hmm. Kawai ka riƙe ta amana.
Don Allah karka mata butulci.”
Haɗe hannyenshi ya yi waje ɗaya kawai. Sannan ya juya ya wuce. Ya gaji da jin kalaman nan da kowa ke faɗa mishi.
Safiyya ya samu zaune inda suka barta ya ce mata,
“Taso mu tafi.”
Miƙewa ta yi. Anty Fatima ta ƙaraso tana faɗin,
“Ku ɗan jira in zo.”
Lumshe idanuwa Fu’ad ya yi alamar jiran da za su yi an takura shi. Bata fi mintina sha biyar ba ta fito da leda a hannunta ta miƙa wa Safiyya tare da faɗin,
“Ban san za ku zo ba.”
Hannu biyu ta sa ta karɓa ta yi mata godiya sannan suka tafi. Suna shiga mota Fu’ad ya ce,
“Anty Fatima ta fi son ki da ni. Ba ta taɓa ba ni komai ba.”
Dariya ya ba ta.
“Ai mu biyu ta ba.”
Turo baki ya yi ya ce,
“Oh-OH ban ji ta ce da ni ba.”
Ya tashi motar suka fita daga gidan. A hanya ta ce,
“Na gode.”
Da mamaki ya ce,
“Godiyar me fa?”
“Yadda ka ke ƙoƙarin ‘yan uwanka su karɓe ni.”
Shiru ya yi don bai san me zai ce mata ba. Tsayawa suka yi ya siya musu take away sannan suka wuce gida.
*****
Yau a gida ya ja musu sallar Isha’i bayan sun ci abinci sannan ya kulle musu ƙofar su ya dawo ya kama hannunta suka yi bedroom.
Ce mata ya yi ta watso ruwa. Zai wuce ɗakin shi ya watsa ruwa don so ya ke su gama tare su kwanta.
Haka kuwa aka yi. Ba ta jima da fitowa ba ya shigo ɗakin. Ƙamshin turarukanshi na wani kashe mata jiki.
Kwanciya ya yi kan gadon ya kamota ya ɗago ya kwantar kan jikinshi ya lumshe idanuwanshi.
“Kewarki na ke ji sosai Sofi. Tun kafin in tafi na ke jinta har raina.”
Ita ma lumshe idanuwanta ta yi tana sake ƙanƙame shi. A hankali zuciyarta ke haɗa mata kalaman yanayin da ta ke ji kafin ta ce,
“Lokaci zai tsaya min in ba ka kusa. Komai zai canza. Ba na tunanin zan gane hanya ni kaɗai a duniyarka in ba ka tare da ni.”
Wani nauyi ƙirjin shi ya yi mishi. Ya na jin yadda zuciyarta ke bugawa a jikinshi.
“Duniyata da taki iri ɗaya ce yanzun Sofi. Ba na tunanin nisa zai canza haka. Ba kya jin yadda bugun zuciyata ke tafiya dai dai da naki?”
Nutsuwa ta yi ta na ƙoƙarin jin abinda ya ke cewa. Hannunshi ta kamo ta dumtse.
“Ban ce nisa zai canza yadda bugun zuciyar mu ya ke ba. Sai dai zai canza yanayin komai a tare da ni.”
Jan numfashi ya yi. In ta ci gaba da magana haka ba zai iya tafiya ya bar ta ba.
“Ki faɗi sunana Sofi. Sau ɗaya na taɓa jinshi a laɓɓanki. Ban manta yanayin shi ba. Ina son ƙari ne.
Ina son tattara duk wani yanayi in tafi da shi ko zai rage min kewarki.”
Hawayen da ta ke riƙewa suka zubo. A hankali ta sumbaci wuyanshi saboda daidai nan kanta ya tsaya.
Baisan lokacin da ɗan sauran control ɗin shi ya ƙwace ba. Sosai ya ke nuna mata yadda sonta ya gama zauna mishi.
Yadda zai yi kewarta. Jikinta ya hau ɓari saboda baƙuwa ce sosai a wannan salon soyayyar nashi.
Riƙeta ya yi. Cikin kunnuwanta ya ke gaya mata kalaman da sirri ne a tsakaninsu. Haka ya riƙe ta a jikinshi yana saukar mata da nutsuwa.
Duk yadda ya ke ji bai danne rashin son tsorata ta ba. Ya fi son ya bi komai a hankali.
Kamar yadda zuciyarshi ke faɗa mishi. Bai samu lokaci a soyayyarta ba. Lokaci ɗaya ta yi masa illa. Shi ya sa ya yi alƙawarin ba wa nuna mata ita dukkan lokacin da ta ke buƙata.
****
“Sofi da kin shirya na kai ki makaranta.”
Girgiza masa kai ta yi.
“Na haƙura da zuwa yau. Ina son ganin tafiyar ka.”
Ƙyaleta ya yi. Tunda suka tashi ya ke fama da ita ta shirya ya kai ta makaranta ta ƙi. Ita a dole sai ta ga tafiyarshi ba za ta makaranta ba. Tare suka yi breakfast. Ya shiga ya sake yin wanka.
Lukman ya kira a waya. Don driver ɗin da aka samo musu sun yi sai gobe zai fara zuwa. Saboda haka shi zai sauke shi airport.
Tana zaune tana kallonshi yana ta kaikawo. Har ya gama shirin shi tsaf. Kukan da take ta daurewa tun ɗazun ya ƙwace mata.
Lumshe idanuwanshi ya yi. Sannan ya ƙarasa wajenta ya riƙo ta. Muryarshi ɗauke da wani yanayi ya ce,
“Na ce ba na son kukan nan. Kullum fa za mu yi waya. Ko so ki ke in tafi zuciyata da hoton fuskarki jiƙe da hawaye?”
Girgiza mishi kai ta yi. Hannu ya sa yana goge mata fuska. Da ƙyar ta iya samu hawayen suka tsaya.
“Na ce miki ko me ki ke so ki kirani ko? Zan sa Lukman ya kawo miki. Kuɗi na nan in da na nuna miki. Don Allah banda yawan damuwa.”
Muryarta a dakushe saboda kukan da ta yi ta ce masa,
“Duk na riƙe fa.”
Dariya ya ɗan yi. Wayarshi ya ji tana ringing. Ya san Lukman ne da ƙyar ya samu ya janyeta daga jikinshi ya ɗauki ‘yar jakar shi.
Miƙewa ta yi ta riƙe hannunshi ta na buɗe wani sabon shafin kuka. Rungume ta ya yi. Gaba ɗaya kalamanshi sun ƙare.
Shi kanshi buƙatar lallashin ya ke. Sun jima a haka yana riƙe da ita ta na kuka. Wayarshi da ta sake ɗaukar ihu ya sa shi ɗago Safiyya daga jikinshi.
Fuskarta ya riƙe. Sumba ya ke manna mata ko ta ina a fuskarta ba tare da ya damu da hawayen da ke jiƙe a jiki ba. Yau martani ta ke mayar mishi saboda yadda ta ke jin kamar ta bi shi. Da ƙyar ta iya raka shi bakin kofar.
Kissing ɗinta ya sake yi.
“I love you. I more than a lot love you Sofi.”
Saboda yana tunanin abinda ya ke ji a zufiyarsa ya fi a ɗora shi kan kalma uku kacal.
“I love you Fu’ad.”
Wani kumburi ya ji zuciyarshi ta yi ta cika mishi ƙirji saboda wani sonta da ya ƙaru a lokacin.
“Ki kulamin da kanki sosai.”
Kai ta ɗaga mishi ba ta son kuka ya sake ƙwace mata. Tsaye ta yi har ya fice. Da sauri ta koma wajen window ta buɗe tana kallon shi. Hawaye na bi mata fuska. Har duniyar shi ta zame mata baƙuwa ko nisa bai yi ba, tsaye ta yi a wajen har ya shiga motar suka fice.
Jikin window ɗin ta haɗe kanta ta na wani irin kuka. Ba ma ta ji zuwan Mama Indo ba sai da ta dafa ta. Juyawa ta yi. Wani sabon kukan na zuwa mata. Kamata Mama indo ta yi ta kaita ɗaki tana lallashinta.
Wayarta ta ji ta ɗauki ihu. Ta lalubo ta ga shine ya kira. Miƙewa ta yi zaune tana goge fuska kafin ta ɗauki wayar.
Hakan ya sa Mama Indo bar mata ɗakin. Murya a dakushe ta yi masa sallama. Ta na jin yadda ya sauke ajiyar zuciya kafin ya ce,
“Sofi kuka ki ka sake yi ko?”
Duk yadda ta ke ji bai hanata murmushi ba.
“Tun ɗazun ne…”
“Hmm yanzun Lukman ya sauke ni a airport. Sai da na biya na yi wa Momma sallama tukunna.”
A sanyaye ta ce,
“Ai kam ka kyauta. Gidan ya yi shiru ba ka nan.”
Ya amsa da,
“Kin ga, da kinje makaranta zai rage miki kewa.”
Girgiza kai ta yi kamar yana ganinta.
“Ganinka anan kusa da ni ne kawai zai rage min kewarka.”
Hira suka yi na ɗan wani lokaci kafin ya yi mata sallama da alƙawarin zai kira da ya isa.
Sosai ta yimishi addu’ar da ba ta samu ta mishi ba ɗazu.
Da kewar shi ta kai makaranta. Duk da sun yi waya da safiyar amman jin ta ta ke kamar marar lafiya. Don da ƙyar ta iya bacci jiya. Sai da ta ci kuka ta more. Da safe ma da ta buɗe ido ta ga ba ya nan sai da ta yi wani.
Anty Laurat office ta yi abinta. Safiya kuma ta shiga aji kasancewar talata ne ba assembly suke yi ba. Da fara’a wasu daga cikin mazan ajin suka gaisa da Safiyya.
Ta ƙarasa ta zauna wajen zamanta. Sosai Khadija da Aisha suka ji daɗin ganinta.
“Anty Safiyya Allah dai ya sa lafiya. Mun yi jaje jiya mun gaji. Ga wani rashin dabara ba mu taɓa tunanin karɓar lambar ki ba.”
Cewar khadija. Aisha ta karɓa mata da,
“Wallahi kuwa. Allah dai ya sa lafiya.”
Safiyya ta ji daɗin karamcinsu. Sai ta ke jin sun rage mata kewar su Jummai. Duk da girman jikinsu zai zo ɗaya da su Khadija. Don Aisha ma da ta fi ta tsayi ta san ta girme su. Antyn nan tun tana hanasu har ta haƙura.
“Maigidana ne ya koma wajen aiki. Kuma ba na dan jin daɗi.”
Dariya Aisha ta yi.
“Umm, su Anty an samo mana baby.”
Wata kunya ta kama Safiyya. Da sauri ta girgiza musu kai.
“Ni kam dai ba wani baby.”
Khadija ta ce,
“Mu kam mun ji daɗi ko Aisha? Za mu sha suna wallahi. Har anko sai mun yi.”
Gani ta yi da gaske suke yi. Da sauri ta ce,
“Kai ni ba ma mu taɓa…”
Shiru ta yi saurin yi. Ta kasa ƙarasawa. Lokaci ɗaya kunya da tuna girman riƙe sirrin aure da suka taɓa yi a Islamiyya ya zo mata. Su Khajida da sun gama gane inda ta dosa kallonta suke kamar maganar da ta yi ita ce mafi girma da ban mamaki da suka ji duk shekarar.
Da wani yanayi Khadija ta ce,
“Taɓɗi. Anty kina so wata ta ƙwace miki miji ko?”
Wani rass Safiyya ta ji gabanta ya faɗi. Ita sam ba ta taɓa wannan tunanin ba. Aisha ta jinjina kai.
“Sosai ma kuwa. Ga shi so hot.”
Duka Khadija ta kai mata. Ta yi saurin cewa,
“Ke ba kya karantawa a litattafan Hausa?”
“Wallahi kuwa. Ji cikin NI DA ƊIYATA na Anty Ayna yadda Yasmeen ta Kjwace sa Deela miji.”
Cewar Khadija. Kamar Safiyya za ta yi kuka take kallonsu. Muryarta a sanyaye ta ce,
“Ni ban taɓa karantawa ba. Ina ake samu…”
Da mamaki Khadija ta ce,
“Ba ki na da waya ba?”
Ta ɗaga musu kai.
“Kin zo da ita?”
Girgiza kai ta yi wannan karon ma. Don maganar a ƙwace mata Fu’ad. Hango Fu’ad na yi wa wata murmushi ma balle magana kawai ya sa ƙirjinta na wani zafi.
Akwai ma abubuwa da yawa da ta ke son koya. Bata iya kalar abincin shi ko ɗaya ba. A raunane ta ce musu,
“Ina son in iya kalar abubuwan da ya ke ci ma. Ban iya dafa ko ɗaya ba.”
Dafata Khadija ta yi tare da faɗin,
“Karki damu za mu koya miki. Gobe in Allah ya kaimu ki zo da wayarki da kuɗi a siya kati.
Za mu buɗe miki whatsapp mu koya miki amfani da shi. Za ki ƙaru sosai wallahi.
In shaa Allah weekend ɗin nan zan zo gidansu Aisha sai ki ba mu address ɗinki mu zo gidanki mu yini duk mu koya miki wasu girki.”
Kallonsu ta ke ta rasa bakin da za ta yi musu godiya ma.
“Allah ya biyaku da kalar karamcin da kuke nuna min.”
Dariya ta basu suka amsa da amin.
*****
Haka rayuwa ta ci gaba da tafiya wa Safiyya. Da duk rana kewar Fu’ad na ƙaruwa a zuciyarta.
Sai dai a hankali su Khadija ke wayar mata da kai. Kamar yadda suka yi alƙawari haka suka zo gidanta suka yini ranar.
Sosai ta ke ƙaruwa da su. Littafi ta samu suke rubuta mata girgike-girke ga groups na girki da suka sakata.
Duk da ba ta iya cewa komai saboda yadda typing ke mata wahala da qwerty ɗin nan. Tana buɗewa ta bi tana karantawa kuma tana ƙaruwa.
Ga litattafan hausa da ta ke samu. Suna ma rage mata kewa da daddare. Ta yi ta shan karatu.
Mama Indo na taimakawa wajen ƙara koya mata wasu girkin. Haka in taga wani a waya ta cire kunya ta nuna wa Anty Laurat.
Yanzu lesson ɗin awa ɗaya suke sauran awa ɗayan a kitchen suke yinta tana koya mata girki.
*
Kwanci tashi har satin dawowar Fu’ad ya yi. Safiyya ta ƙagu ya dawo ta tarbe shi da sababbin abubuwan da ta koya saboda shi.
Fa’iza ta zo dubata ya fi a ƙirga. Haka Lukman duk da ba ya shigowa sai dai ya tsaya a harabar gidan ta sa hijab ta fita su gaisa.
In dai zai zo sai ya kawo mata abubuwa. Wani lokacin har da kaji ko biscuit da chocolates kala-kala.
Wannan kenan.