Skip to content
Part 42 of 48 in the Series Akan So by Lubna Sufyan

Wayarshi ke ringing. Ya ɗan ja ƙaramin tsaki saboda sam ba ya jin magana koma wace iri ce. Hannunshi yasa ya tallabi goshin shi. Wayar ta sake ɗaukar ringing. Ɗaukota ya yi da niyyar kashewa gaba ɗaya. Ganin sunan da ke jiki ya sa har hannunshi ke rawa wajen picking. Wani irin dokawa zuciyarshi ta ke yi. Da ƙyar ya nemo muryarshi ya iya faɗin,

“Nuriyya.”

Shiru ta ɗan yi. Ya san tana jin shi, don haka ya sake cewa,

“Are you okay?”

Maimakon ta amsa tambayarshi sai cewa ta yi,

“Mafarki nake ko da gaske ne ka ce min ba Anty bace mahaifiyata?”

Ya san yanayin da ta ke ciki. Ba ya son ƙara mata damuwa.

“Please mu yi wannan maganar idan kin ƙara nutsuwa kin…”

Katse shi ta yi da faɗin,

“Ka faɗa min kawai. Ina son sani ne.”

Muryarshi a dakushe ya ce,

“Ba ita bace mahaifiyarki Nuriyya. Ta tsince ki ne ta riƙe ki.”

Yana jin kukan da ya ƙwace mata. Taɓashi take ta ko’ina na jikinshi ba tare da ta yi amfani da hannayenta ba. Kukanta na shiga har ƙasan zuciyarshi yana yawo.

“Nuri…”

“Karka sake kirana da Nuri please…Na… Haka ya ke cemin…”

Ta ƙarasa maganar muryarta na rawa da alamun kukan da ta ke yi. Gaba ɗaya ba ya jin daɗi. Ya buɗe baki zai yi magana ta kashe wayar. A hankali ya cire wayar daga kunnenshi ya bita da kallo. Ajiyewa ya yi yana sauke numfashi.

*****

Kan gado ta saki wayar ta kwanta. Kuka take mai taɓa zuciya. Abu ɗaya ne ya ke mata yawo akai.

A da ta sha ɗauka cewar Anty ce mahaifiyarta. Ya fi a ƙirga tana tambayarta waye mahaifinta tana shan jibga har ta haƙura ta daina.

Duk tsawon lokacin nan tana ma kanta kallon wadda aka samu ta hanyar banza. Ta daɗe da making peace ɗinta da wannan ɓangaren.

A da ta san wacece mahaifiyarta. Yanzun komai ya canza mata. Bata san wacece ita ba. Bata san ina aka samota ba.

Har yanzun tabon samu ta hanyar banza bai ɓace mata ba. Shin yarda ita aka yi? Ko me ya faru da ita. Wani tsoro ne ya ke shigarta.

Jan ƙafafuwanta ta yi ta haɗe jikinta sosai kan gadon. Nawaf ɗin da take kallo take tunanin tana da wani a faɗin duniya shi ma baya nan. Ya tafi inda ba zai taɓa dawowa ba sai dai ita ta je ta same shi. Bata da inda za ta kama. Bata da inda zataje. Ba za ta ce ga makomarta ba idan ta gama takaba. Ta san darajar hakan take ci a gidansu Nawaf.

Faɗar sunanshi kawai wani ciwo ta ke ji marar misaltuwa. Wanda bai san yadda ɗacin mutuwa ya ke ba ba zai fahimci halin da ta ke ciki ba.

Text ta ji ya shigo wayarta. Hannu ta kai ta ɗago da wayar ta duba. Farhan ne don haka ta buɗe.

‘Idan kina buƙatar wani abu. Ina nan. Kirana kawai za ki yi. Please ki kula da kanki.’

Ajiye wayar ta yi ta lumshe idanuwana, ta rasa exact abinda ta ke ji.

*****

Zuciyarshi wani irin dokawa take tun da su Abba suka tafi ya kasa samun nutsuwa. Ji yake kamar ƙaddara za ta sake ƙwace mishi Safiyya. Ji yake kamar ba za a ɗaura auren nan ba. Ya kasa zama. Sai kai kawo ya ke yi cikin ɗakinshi. Kama handle ɗin ƙofar ya yi zai fito wayarshi ta kama ringing.

Zarota ya yi daga cikin aljihunshi. Ganin Lukman ne ya ƙara ma zuciyarshi gudu da dukan da take yi. A sanyaye ya ɗaga tare da faɗin,

“Lukman…”

“An ɗaura Fu’ad. An mayar da aurenku da Safiyya.”

Lumshe idanuwa Fu’ad ya yi ya jingina jikinshi da ƙofar ɗakin yana jero ma Ubangiji godiya. Muryar Lukman ta katse shi da faɗin,

“Fu’ad…”

“Ina jinka Lukman.”

Wani numfashi Lukman ya ja kafin ya ce,

“Ka kula da ita. Zai wahala in ta kufce maka ta sake dawowa. Ba kowa ba ne ya ke sa’a irin taka a rayuwarshi.”

A sanyaye ya amsa da,

“In sha Allah. Na gode Lukman.”

“Allah ya sanya alkhairi.”

Lukman ya faɗi yana kashe wayar kafin Fu’ad ɗin ya amsa. Bai san me ya sa ya ƙi zuwa ba.

Babu yadda Babban Yaya bai yi ba ya ce kanshi ciwo yake. Abba ya ce a ƙyale shi ai ba dole sai ya je ba.

Takawa ya yi ya ƙarasa kan gadonshi ya zauna. Safiyya ya yi wa text kamar haka,

‘Na gode. ‘

Bata yi mishi reply ba. Bai kuma saka ran ɗaya ba. Don haka bai damu ba. Nan ya yi zamanshi yana jin dawowar su abba bai fita ba. Yana son kasancewa shi kaɗai ɗin ne na wani lokaci. Ko da na iya ranar ne. Bai fito ba sai da ya ɗauro alwalar sallar magrib tukunna.

*****

Tunda Baba ya dawo ya faɗa mata an sake ɗaura auransu da Fu’ad ya fice da Nana take kwance ɗaki tana kukan da bata san dalilinshi ba. Inda ance rayuwa za ta sake maidata matsayin da ta daɗe da goge shafinshina zuciyarta ba za ta yarda ba. Tana jin sallamar Inna ta shigo ɗakin. Da sauri ta miƙe tana goge fuskarta tare da amsa sallamar a sanyaye. Gefen gadon Inna ta zauna da wata leda a hannunta.

Ta ɗora ledar kan gadon ta buɗeta. Atamfofine guda biyu a ciki. Takalma sai abin hannu da sarƙa. Da hawaye cike taf idanuwan Inna muryarta na rawa ta ce ma Safiyya,

“Bayan Usman ya kammala aji shida jarabawarshi ba ta yi kyau ba. Aka ce sai ya gyara wata shekarar. Sai ya buƙaci zai dinga zuwa aikin kafinta da ya soma yi, tun dawowarmu makaranta ta sa dole ya ajiye. Cikin kuɗin da ya kan samu yana mana siyayya dasu. Kama daga kaya zuwa abubuwan ciye ciye…”

Shiru Inna ta yi tana goge hawayen da suka zubo mata. Tun da Inna ta kira Usman wasu sabbin hawaye ke zubo ma Safiyya. Nata zaman makokin ne ta ke yi yanzun. Ciwon mutuwar Usman sabo ne a wajenta. Su Inna suna da shekara uku su ririta nasu ciwon. Ita kam yau kwana ɗaya kenan da samuwar nata.

Tura wa Safiyya kayan Inna ta yi.

“Ko da muka haƙura da nemanki. Usman ya fi kowa sa ran dawowarki. Shi ya siyo kayan nan ya ban in ajiye. Da ɗaiɗai ya siyo yana sa ran za ki dawo ko yaushe karya zamana kin dawo bai siya miki komai ba. Yakan ce kuna hirar sana’a tare, yakan faɗa miki ba shi da sha’awar karatu…”

Kasa ƙarasawa Inna ta yi, don haka ta miƙe kawai ta fice daga ɗakin. Kayan Safiyya ta sa hannu akai. Kamar taɓa kayan da ta yi ya buɗe mata hotunan Usman a zuciyarta. Fuskarshi ta ke kallo. Murmushin shi ta ke gani.

So ta ke ta tuna yadda sautin dariyarshi yake. Yadda muryarshi ta ke cikin kanta ta ƙasa. Wani irin tsoro ta ji ya shigeta.

Sosai take jin tsoron har cikin tsokar jikinta. Lokaci ya ƙwace mata wannan ɓangaren na Usman.

“Ya Allah…”

Ta faɗi wasu irin hawaye masu ɗumi na zubo mata. Da gaske ta manta yadda sautin muryar Usman yake. Atamfofin ta janyo jikinta hannuwanta na rawa.

Fuskarta ta haɗa da kayan tana kuka marar sauti tana faɗin,

“Allah ya kai haske kabarinka Usman. Ban samu bankwana da kai ba balle in roƙi gafararka…”

Sosai ta ke kuka tana riƙe kayan a jikinta. A haka yayanta ya shigo ya sameta. Ba ta ji sallamarshi ba saboda gaba ɗaya duniyar a birkice ta ke jinta a lokacin.

Sai da ta ji ya zauna gefen gadon sannan ta ɗago fuskarta da ke jikin kayan da Usman ya siya mata ta sauke su kan yaya.

Sama sama ta ji numfashinta na yi . Jiya ta yi ta sa ranshi ya kira Inna ya ce mata ba zai samu zuwa ba.

“Yayaa…”

Ta kirashi cikin yanayin ciwon da zuciyarta ta ke yi. Da sauri ta sakko daga kan gadon ta zauna a ƙasa. Hannuwanshi ta kama.

“Yaya ka yafe min. Yaya babu Usman yau. Usman ya tafi ya bar mu…”

“Shhhhhhh Safiyya ya isa. Ya isa haka.”

Ai kamar ma ya sake buɗe mata wani sabon shafin kukan. Tana riƙe da hannuwanshi.

“Don Allah Safiyya ki yi shiru. Soyayyarmu Usman ya ke buƙata ta hanyar addu’a.”

Ɗago jajayen idanuwanta ta yi.

“Ba za ka gane me nake ji ba yaya. Kai ka mishi sallama…”

Kallonta yake. Shi kuwa zai gane me ta ke ji fiye da ita. Ɗan uwa ɗaya ta san ciwon rashin shi.

“Karki fara Safiyya. Karki sake ki yanke wa abinda ba ki sani ba hukunci. Ba za ki taɓa sanin me ake ji ba lokacin da mutuwa ta ɗauke maka dan uwanka guda ɗaya. Ƙaddara ta watsa ‘yar uwarka duniyar da ba ka sani ba. Karki yanke wa abinda ba ki sani ba hukunci.”

Fuskarshi ta ke kallo. Hannuwanshi ta saki ta sa hannu ta goge tata fuskar.

“Ka yafe min yaya. Na ji rashin ku fiye da zatonka. Wallahi na horu da rashinku. Ciki har da ɓacewar muryar usman daga gareni.

Na rasa abubuwa da yawa…”

Wayarshi ta ga ya ɗauko yana daddanawa. Miƙa mata ya yi ta karɓa hannunta na rawa. Videos ne. Da sauri ta danna play. Idanuwanta lokaci ɗaya suka sake cikowa da hawaye. Usman ne yana dariya.

Da alama shi ya ke ɗaukar kanshi video ɗin yana faɗin,

“Ban san me ya sa na ke ji a jikina ba zan sake ganinta ba. Koma menene Allah ya fini sanin shi.”

Murmushi ya yi cike da wani yanayi da ya sa Safiyya miƙa wa yaya wayar tana haɗe kanta da gwiwa. Muryar yaya a dishe ya ce mata,

“A wayarshi na ɗauka bayan ya rasu. Date ɗin jiki ya nuna ya yi recording kwana biyu kafin rasuwarshi. Da ke a zuciyarshi ya rasu Safiyya. Usman na ƙaunarki fiye da yadda ki ke zato.

Mu duka munyi rashin shi. Addu’ar mu yakee buƙata a yanzun.”

Ai bata jin nasihar yaya. Ya barta kawai ta yi kukanta. Ya barta ta ji mutuwar Usman saboda shi ya riga da ya ji tashi.

Tana jin ya miƙe bata ɗago da kanta ba.

“Na ji daɗi da na sake ganinki kafin mutuwa ta gifta mana. Allah ya sanya alkhairi.”

Bata amsa shi ba. Tana jin ya fice daga ɗakin ta koma kan gadon ta ci gaba da kukanta. Sai da ta daina jin hawaye na fita sannan. Tana kwance tana tunanin yadda rayuwa da duka duniyar ma ba komai bace text ɗin fu.ad ya shigo.

Dubawa ta yi ta ajiye wayar. Ta rasa abinda ya kamata ta ji.

*****

Har ya tashi da safe ba zai ce ga abinda ya ke damunshi ba. Kawai yanajin wani irin yanayi ne da ya kasa fassarawa. Ko da Anty Fati ta zo gidan gaisawa suka yi. Ita da Momma suka shirya suka tafi gidansu Safiyya su taho da ita.

Haneef zai kira ya je su yi magana sai gashi ya shigo gida. Kallo ɗaya ya yi ma Fu’ad ya karanci yanayin fuskarshi. Sai da ya zauna sannan ya ce mishi.

“Me ke faruwa?”
Gyara zama Fu’ad ya yi ya fuskanci Haneef sosai.

“Em’ quitting?”

Cike da rashin fahimta Haneef ya ke kallonshi.

“Me kenan? Ban gane ba.”

Jan nunfashi Fu’ad ya yi ya sauke shi a hankali.

“Football. Zan yi quitting…”

Katse shi Haneef ya yi da faɗin,

“No. No Fu’ad ba za kayieabinda zakae zo kai da na sani ba.”

Murmushi Fu’ad ya yi. Muryarshi ƙasa-ƙasa ya ce,

“Ba zan yi da na sani ba Haneef. Ko ban dawo ba na kusan ajiyewa. Ko da ban kai inda nake da buri ba. Na yi. Na kuma ji daɗinta.

Yanzun kun fi min komai muhimmanci. Ina son kasancewa tare da ku. Na rasa shekaru sha ɗaya. Bana son rasa kwanaki ba a kusa daku ba. Contract ɗin da na yi signing ya ƙare. Sabo ne zan yi signing ƙarshen watan nan.  Em’ done.  Zan je in ƙare komai in dawo.”

Sosai Haneef ya ke kallonshi da alamun maganganun Fu’ad ɗin ba su zauna mishi daidai ba.

“Are you sure?”

Ya buƙata. Kai Fu’ad ya dagar mishi yana murmushi. Haneef ya lumshe idanuwanshi ya buɗe su.

“Allah ya tabbatar da alkhairi to.”

“Amin ina Khadee?”

Murmushi ya ƙwace wa Haneef da jin sunan ‘yar tashi.

“Tana Islamiyya.”

Hira suke kafin Hassan ya shigo. Da murmushi a fuskarshi ya gaishe da su ya nemi waje ya zauna. Yanayin zaman ya sake ƙarfafa niyyar Fu’ad. Yadda ya ke ji a zuciyarshi bai taɓa jin hakan akan ball ba.

‘Yan uwanshi sun fi mishi komai muhimmanci.

*****

“Da ka shigo ciki.”

Cewar Aina bayan sun gaisa da Jabir. Girgiza mata kai ya yi.

“Wucewa zan yi na biyo mu gaisa. Ba jimawa zan yi ba.”

Murmushi ta yi a kunyace.

“Ina su Ikram da Anty?”

Murmushin ya mayar mata.

“Duk suna lafiya. Jana tana gaishe da ke.”

Ɗagowa ta yi ta ɗan ware mishi idanuwanta da alamun mamaki. Ya ɗaga mata girarshi duka biyun tare da faɗin,

“Kina mamakine? In bata ce ba ba zan faɗa miki ba.”

“Kawai dai…. Bansan ma me zan ce ba.”

Murmushi Jabir ya sake yi.

“Jana mutuniyar kirki ce Aina. Ina sonta fiye da yadda zan iya faɗa miki. Zan aure ki ne saboda ina sonki ba don na rasa komai a wajenta ba. Banda haufin za ta girmamaki duk da ta girmeki. Bance ki tayani son Jana ba. Sai dai ina son ki taya ni girmamata saboda tana da muhimmanci a rayuwata.”

Sauke ajiyar zuciya Aina ta yi. Wani son Jabir da ƙimarshi na ƙara shigarta. Cikin fuska ta kalle shi.

“Kai ma mutumin kirki ne Jabir. Daga lokacin da maza suke neman aure sai ka ji suna kushe matansu na gida don su burge ‘yan matan da za su aura ɗin. Da ace ka buɗe bakinka da mummunar kalma akan Anty ƙimarka za ta ragu a idanuwana. Ban san ko ƙaddararka akan mata biyu ta tsaya ba. Saboda zan ji a raina yadda kake faɗa akan Anty haka za ka faɗa akaina. Allah ya ba ni ikon tayaka bata girma gwargwadon iyawata.

Ba zan maka alƙawarin komai ba saboda ba na so ka ɗaga zatonka fiye da yadda zan iya.”

‘Yar dariya Jabir ya yi. Hankalin Aina da yanayinta shi ne abinda ya fara so tattare da ita kafin ya kula da kyawunta. Ba fara ba ce kamar Janarshi.  Baƙa ce kuma ba ta da dogon hanci kamar na Jana sai dai idanuwanta na burge shi sosai. In ta yi murmushi yadda dimples ɗinta ke fitowa yana mishi kyau. Komai nata ya sha banban da na Jana. Yana sonsu su duka biyun.

“Nagode Aina. Na gode da karamcinki. Zan wuce sai mun yi waya ko?”

Kai ta ɗaga mishi tana murmushi.

“Ka kula da kanka. Ka gaishe da su Ikram.”

“Za su ji in sha Allah. Ki kula min da kanki.”

Ya faɗi yana buɗe murfin motarshi. Addu’a ta yi mishi da ya ji daɗinta kafin suka yi sallama.

*****

Fita ya zo yi daga motar ya ga deposit slip a ajiye. Janyo su ya yi da mamaki don ya san bai je banki ba duk satin nan. Yana niyyar zuwa biya wa su Ikram kuɗin makaranta bai samu zuwa ba ya bari sai weekend.

Dubawa ya yi. Ya ware idanuwanshi. Girgiza kai yayi ya fito daga motar yana shiga cikin gidan. A kitchen ya samu Jana tana soya doya da ƙwai. Ya shiga da sallama ta amsa shi.

Ta baya ya rungumeta jikinshi. Ta yi dariya tana ture shi.

“Honey J aiki nake yi.”

Gam ya riƙeta jikinshi. Cikin kunnenta ya ce,

“Ban hanaki aikinki ba ai.”

Harararshi ta yi duk da ba ya ganinta.

“Please. Ka sakeni in ƙarasa.”

Dariya ya yi. Ya saketa yana matsawa suka jera. Kwanon ƙwan ya ja gabanshi ya shiga zuba mata wata yankakkiyar doyar a ciki.

“Ina ka je haka?”

Ba tare da tunanin komai ba ya ce mata.

“Wajen saminu naje saina biya muka gaisa da Aina. Ta ce tana gaishe da ku ma.”

Wani tafasa ta ji zuciyarta na yi ga wani irin kishi da ya turnuƙeta. Shiru ta yi tana jero addu’o’i cikin kanta. Tana jin idanuwan Jabir na yawo a fuskarta. Ta ƙi bari su haɗa idanuwa ta kafe su kan aikin da take. Sai da ta tabbatar za ta iya magana ba tare da kishin da ta ke ji ba cikin muryarta kafin ta ce,

“Muna amsawa mun gode. Tana lafiya dai ko?”

Kai kawai ya ɗaga mata. Sai da ta ƙarasa kwashe doyar ta rufe warmer ɗin ta sauke man sannan ya sake janyota jikinshi.

Slips ɗin ya zaro daga aljihunshi ya kamo hannunta yasa su a ciki.

“Janaaa…”

Ya kira da wani irin yanayi. Dubawa ta yi. Ta lumshe idanuwanta babu inda ba ta neme su ba. Sai yanzun ta tuna da motar Jabir ɗin ta fita ranar.

“Jana hidimar tana yawa.”

Hannuwanshi ta zame daga jikinta ta juya suka fuskanci juna. Idanuwanta ta sauke cikin nashi.

“Meye hidimar a ciki? Biya wa yaranmu kuɗin makaranta? Honey J ba ka bari na in taya ka da komai. Ko mai na zubama motata sai ka yi faɗa. Please ina so in taimaka nima.”

Hannu ya sa ya murza goshin shi.

“Bawai taimakawa bane bana so ki yi Jana. Ba na so ki sangartani ne da yawa. Kar inzo in kasa sauke nauyin da Allah ya ɗora min.

Haƙƙin kula da ku akaina yake.”

Sumbatarshi ta yi a hankali kafin ta janye da faɗin,

“Na sani. Kuma kana yi, ina son yin wani abu ne nima. Meye amfanin aikin da nake in ba ka bari ina kashe kuɗin?”

Murmushi ya yi. Ya ɗora hannuwanshi kan kafaɗarta.

“Na gode Jana. I love you kin sani ko?”

Kai ta ɗaga mishi da murmushi. Har ranta ta ke jin sonshi.

“Kafin yara su dawo zo mu siyo ice cream.”

Ya ƙarasa maganar yana jan hannunta. Riƙo shi ta yi.

“Honey J. Ice cream kawai. Promise?”

Ɗan daƙuna fuska ya yi. Ta ja iska mai nauyi ta na fitar da ita tare da girgiza kai. Ta san shi sarai. In har za ta siyi wani abu sai ya kashe mata rabin kuɗinta.

Ba yadda za ta yi da halin Jabir.

“Allah ya shirya min kai.”

Dariya ya yi yana jan hannunta suka fita daga kitchen ɗin tare.

*****

Ya fara damuwa kuma. Su Momma sun kusan awa huɗu yanzun. Bai san me yasa suka daɗe ba. Shi kewar Nana ma ta dame shi. Wayarshi ya ɗauko ya kira Safiyya. Ringing ɗin farko ta kashe. Da mamaki yake kallon wayar. Zai sake kira text ɗinta ya shigo.

‘Ina tare da su Momma.”

Murmushi ya yi. Yasan sarai kunyar ɗaga wayarshi take gabansu Momma, don haka ya sake kira wannan karon ko ringing ɗin farkon bata yi ba ta sake kashewa. Text ɗinta ya sake shigowa.

‘Please mana.’

Reply ya mayar mata.

‘Kun taho?’

Bata ba shi amsa ba ya sake tura wani.

‘Zan ta kira har sai kin ɗaga Sofi.’

Reply ta yi mishi. Ya yi murmushi.

‘Muna hanya.’

Ajiye wayar yayii ya lumshe idanuwanshi. Tattare da wata nutsuwa da take saukar masa akwai wani irin yanayi da ya kasa fahimtar ko na mene ne.

Yanajin kamar wani abu mai girma zai faru dashi.

“Allah kai ka san iya abinda za mu iya ɗauka. Allah ka ba mu juriya a duk lokacin da za ka jarabcemu.”

Ya faɗi yana sauke muryarshi ƙasa-ƙasa. Yana ganin ‘yan aikin gidan na ta hidima. Hussaina ce da wannan rigimar. A dole sai sun yi walima iya su kawai.

*****

Ƙarfe 4:00

Ko’ina ka duba na gidan cike ya ke da farin ciki. Zainab da Safiyya zaune suna ta hira. Za ka rantse sun yi shekaru tare ba wai ranar kawai suka haɗu ba.

Nana ta ƙaraso wajen Safiyya.

“Mummy aramun wayarki in kira Anty Jana.”

Lokaci ɗaya Safiyya ta mayar da hankalinta kan Nana. Hannuwa ta sa tana taɓa fuskarta da wuyanta. Murmushi Nana ta yi tare da faɗin,

“I am ok mummy. Kawai ina son tambayarta abu ne.”

Sauke ajiyar zuciya Safiyya ta yi.

“Kin tabbata?”

Kai Nana ta ɗaga mata kafin ta miƙa mata wayar. Wucewa Nana ta yi da ɗan saurinta tana barin area ɗin gaba ɗaya.

Ƙasan kafar benen da zai kaika sama ta shiga ta zauna. Number ɗin Dr. Jana ta nemo ta kira ta kara a kunnenta. Zuciyarta dokawa ta ke yi. Ta so ace tana kusa da dadynta za ta yi kiran nan saboda tana jin wani ƙwarin gwiwa idan tana tare da shi. Sai dai wannan abu ne da take buƙatar yin shi ita kaɗai.

Hukunci ne akan rayuwarta da ta ke son yankewa ita kaɗai ba tare da kowa ba.

“Assalamu alaikum. Maman Nana.”

Aka faɗi daga ɗayan ɓangaren.

“Wa alaikumussalam. Anty ni ce ba mummy ba.”

Da mamaki a muryar Jana ta ce,

“Nana lafiya dai ko? Ba jikin ba ne ba?”

Girgiza kai nana ta yi kamar tana ganinta kafin muryarta a sanyaye ta ce,

“Ina so in tambayeki ne kawai.”

“Ina jinki Nana.”

Numfashi Nana ta ja tana son zuciyarta ta rage dukan da take kafin ta ce,

“Na san dady is not a match. Na ji suna maganar zuwa gobe a auna kowa agani. Ina so in tambayeki. In an samu match. Zan warke ne gaba ɗaya?”

Shiru Jana ta yi na ɗan mintina kafin ta ce,

“Ki kaima mumynki wayar Nana mu yi magana da ita.”

Girgiza kai Nana ta ke yi.

“A’a please. Ki faɗa min kawai ina son sani ne. Baki san yadda nake ji ba amman kinsan me yake damuna fiye da mummy.

Ina so in sani ne. Zan fahimta idan ba za ki gayamun ba.”

Da wani irin rauni a muryar Jana ta ce,

“A’a. Zaki ji sauƙi sosai ne.”

“Amman zan ci gaba da rashin lafiya irin wannan?”

Tana jin yadda Jana ke fitar da numfashi alamar a wahalce take amsa tambayoyin nan. Itama a wahalcen take saurarenta.

“Ba kodayaushe ba.”

Ɗaga kai Nana ta yi alamar ta fahimta.

“Thank you Anty Jana. You are the best doc.”

“Hmm.”

Kawai ta iya faɗi kafin Nana ta kashe wayar. Lumshe idanuwanta ta yi kafin ta tashi ta fice daga falon zuwa harabar gidan.

Hango su Fu’ad ta yi suna zazzaune su dukansu suna hira. Babban Yaya ne kawai ba ya wajen. Ko takalmi babu a ƙafarta ta ruga da gudu. Kamar ance Fu’ad ya ɗago idanuwa ya kuwa sauke su kan Nana. Ita ta ke gudun shi zuciyarshi ke dokawa karta faɗi. Da alama ganin yadda gaba ɗaya hankalin Fu’ad ya bar kansu ya sa gaba ɗayan su suka maida kallonsu inda na Fu’ad ɗin yake.

Tana ƙarasowa jikin Fu’ad ta faɗa ta ƙanƙame shi. Riƙeta ya yi yana shushing ɗinta da alamar lallashi duk da bai san abinda ya sameta ba ji yake har zuciyarshi.

Ko’ina na jikinta kyarma yake. Yana jin yadda hawayenta ke jiƙa mishi riga. Ya sake riƙeta yana rocking ɗinsu tare da lumshe idanuwanshi.

“It is ok princess. Ina tare da ke. Faɗa min menene?”

Su Haneef  kallonsu suke. Gaba ɗaya yanayin su ya sa jikin kowa a wajen ya yi sanyi. Ɗago Nana Fu’ad ya yi daga jikinshi yana sa hannuwa ya tallabi fuskarta.

Cikin idanuwa ya kalleta yana son ta ga yadda ya ke jin zai iya bata komai in yana da halin hakan.

“Talk to me. Mene ne?”

Muryarta na rawa ta ce,

“Bana so ku je dady. Bana so ku je asibiti gobe. Bana son transplant ɗin.”

Wani irin dokawa zuciyar Fu’ad ta yi wannan karon shi jikinshi ke kyarma. Girgiza mata kai ya ke yi.

“No…No nana. Ba za ki bar mu ba kina jina. Za a samu match in sha Allah.”

Hannunta ta sa ta ture nashi daga fuskarta. Kallonshi take da wani irin yanayi da ke nuna cewar ba zai fahimta ba. Ba zai taɓa fahimtarta ba. Ba ya son kallon da take mishi. Baya son ganin irin wannan kallon a fuskar yarinya kamarta. Hannu ya kai zai kamo nata ta ture shi tana matsawa.

“Bana so dady. Da gaske nake karku je bana so.”

Gaba ɗaya ta birkita mishi duniyar cikin ‘yan mintina.

“Nana calm down mu yi magana.”

Da ihu ta ce,

“Nooooo!”

Haneef ya kalla da yanayin neman taimako. Girgiza mishi kai ya yi don bai san me zai yi ba. Ya maida kallonshi kan Lukman. Bai ma wani tsaya ba don yasan lukmany ya fi shi rauni. Ƙasa Nana ta ke kallo kamar za ta iya samun wata mafita daga yin hakan. Muryarta can ƙasa ta ce,

“I am sorry dady. Kai kaɗai za ka faɗa wa mummy karta ɗaga burinta kamar yanda take faɗa min. Ba zan yi ba. Bana so kowa ya je.”

Fu’ad ji yake kamar zuciyarshi ta bar ƙirjinshi ya ɗan huta na wani lokaci. Ya buɗe baki zai yi magana Nana ta matsa kusa da shi. Kamo hannunshi ta yi.

“Dady ko an yi ba warkewa zan yi ba. Zai ƙara wa kwanakin mutuwata nisa ne.

Zai ƙaramin wahala fiye da wannan. Ba za ku gane me nake ji ba dady. Komai ciwo ya ke min….”

Zafi yake ji a wajaje na jikinshi da ba zai iya faɗa ba. Hannunta takai tana zame hijab ɗin jikinta.

“Kalli dady. Gashina ba zai ƙara fitowa ba. Kowa na zuwa school ni bana zuwa yanzun.

Na daina jin taste ɗin wasu abincin a bakina. Dady please bana son zama sick duka rayuwata. I want to die. I want all of it to stop in huta. Dady komai ciwo yake min don Allah kar kumin abin nan. Ku bar ni in huta dady.”

Ta ƙarasa maganar hawaye na zubo mata. Miƙewa Lukman ya yi yana barin wajen saboda yadda yake jin hawaye na shirin zubo mishi. Hassan ma barin wajen ya yi. Janta jikinshi Fu’ad ya yi yana rungumeta. Haneef kam dafe kanshi ya yi cikin hannayenshi yana fitar da numfashi da matuƙar wahala.

Cak Fu’ad ya ɗaga Nana jikinshi ya miƙe tsaye har ranshi yana jin shekarun da ya rasa tare da ita. Da wani irin yanayi ya nufi cikin gidan. Ko sallama bai yi ba ya shiga falon. Ya wuce su Fa’iza da ke tsaye suna magana ita da Anty Fati.

Ba ya ganin kowa sai Safiyya. Ita yake hangowa zaune. Ita kaɗai idanuwanshi ke gani. Zuwa yanzun hankalin kowa ya koma kanshi. Yana ƙarasawa inda Safiyya ta ke ya sauke mata Nana kan cinyarta. Ɗan dafe kanshi da hannu ɗaya ya yi yana sauke shi cike da frustration.

Kallon Safiyya ya ke yi. Muryarshi a dakushe ya ce,

“Ki kalleta Sofi. Bata son transplant ko da an samu match. Ta haƙura da rayuwa saboda ta mata wahala.”

Ware idanuwa Safiyya ta yi tana rungume Nana jikinta tare da sumbatarta. Ji yake kamar kanshi zai tarwatse. Ta samu wannan na shekaru sha ɗaya.

“Kina da wannan na shekara sha ɗaya sofi. Bani da komai da zan riƙe and fuck it!  She is dying!”

Kuka Safiyya ta ke yi. Ita Fu’ad ya ke ɗora wa laifin shekarun da ya rasa tare da Nana.

“Kai ka tafi. Kuma na nemo ka ban sameka ba…”

Ta faɗi hawaye na sake zubo mata. Anty Fatima ce ta ƙaraso ta dafa Fu’ad a kafaɗa ya ture hannunta.

“Ba wani. Na rasa yarinyata saboda ke! Na rasa ganinta da lafiyarta. Na rasa kaita makaranta. Na rasa best moments tare da ita.”

Goge fuska Safiyya ta yi tai murmushin takaici tare da faɗin,

“Tabbas duk ka rasa wannan. Tare da shi ka rasa ganinta lokacin da ba ta da lafiya. Ka rasa ganin lokacin da she was so sick bata ko iya tashi daga gadonta.

Ka rasa ganin lokacin da gashinta ke kakkaɓewa daga kanta. Ka rasa ganin lokacin da ta ke tisa uniform dinta na islamiyya dana boko tana kallonsu saboda ita ba za ta iya zuwa ba. Ka godewa Allah da ya sa ba ka ga duk waɗannan lokutan ba Fu’ad, saboda su kaɗai sun ishi zuciyarka ciwo har ƙarshen rayuwarka.”

Tana ƙarasa magana ta sa fuskarta cikin hannunta tana fashewa da wani irin kuka. Zainab ma da ke kusa da ita kukan ta ke, balle Anty Fatima sarkin kuka. Saukowa daga jikin Safiyya Nana ta yi. Ta zo dai dai wajen Fu’ad ta tsaya. Muryarta can ƙasa ta ce,

“Stop it dady. Ka daina ba laifinta bane ba. Ba laifinta ba ne da nake da cancer. Ba ka ga nima na rasa duk abin nan da dadyna ba? Da lafiyata? Karka sake mata faɗa bana so. Ta min komai.”

Buɗe bakinshi Fu’ad ya yi yana fitar da iska saboda ta mishi wahalar fita ta hanci. Yanayin da ya ke ji babu wanda zai fahimta. Yanajin gaba ɗaya babu wanda ya kai shi son kai da rashin adalci.

In akwai wanda zai ji ba a kyauta mishi ba Nana ce. Ita ce da ciwon a jikinta.

Yasa matan da ya fi so bayan Momma kuka hankalinshi ya kwanta. Buɗe baki ya yi zai yi magana Nana ta juya wajen Safiyya ta ce,

“Gaskiya dady ya faɗi mummy. Za ki iya fiye da ƙoƙarin da kikai wajen nemo shi.”

Kai safiyya ta ɗaga mata. Itama ta san da hakan da ta kira shi ba ta same shi ba zata iya zuwa gidansu a nemo shi ba wai ta haƙura ba.

Saboda Nana ɗin ba don ita ba. Ta kowane fanni Nana akai wa rashin adalci. Takawa Nana tayi ta ƙarasa inda momma ke tsaye tana zubda ƙwalla. Kamo hannunta ta yi.

“Ki kaini in kwanta bacci nake ji.”

Goge fuskarta Momma ta yi ta kama hannun Nana suka wuce ɓangarenta. A hankali Fu’ad ya taka zuwa inda Safiyya take zaune. Tsugunnawa ya yi.

Hakan yasa Zainab dafa kujerar ta miƙe da ƙyar saboda cikinta ya shiga wata na bakwai kenan. Hawayen da ke fuskarta ta goge. Da kai ta nunama su Anty Binta da su bar musu falon.

Su dukansu ɓangaren Momma suka wuce suna barin Fu’ad da Sofi. Kamo hannuwanta Fu’ad ya yi. Wani irin abu ta ji har tsakiyar kanta. Shekaru sha biyu rabonta da Fu’ad sai yanzun da ya taɓata ta san babu abinda ya canza.

Ɗago fuska ya yi ya kalleta kafin hawaye su zubo mishi. Bai san me zai ce mata ba. Kalamai duk sun tsaya mishi. Ta karance shi tsaf.

Su dukansu suna cikin yanayi marar misaltuwa. Hannunta ta zame daga nashi ta na tallabar fuskarshi. Hawayen ta ke goge mishi tana girgiza kanta duk da ta kasa tsayar da nata.

Matsawa ya ƙara yi ya ɗora kanshi kan cinyarta hawaye na sake zubo mishi.

“Ki yafe min Safiyya. Bana nufin dukkan abinda na faɗa, don Allah ki yafe min.”

Kanta ta ɗora kan nashi da ke cinyarta.

“Na yafe maka Fu’ad. Ka yafe min daban yi trying sosai ba.”

Sake maƙalewa ya yi a jikinta yanajin yadda ya yi rashinta sosai. Kuka suke tare na shekarun da suka rasa. Na yadda ƙaddara ke gara su!

<< Akan So 41Akan So 43 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×