Skip to content
Part 43 of 48 in the Series Akan So by Lubna Sufyan

Fu’ad ya kaisu gida da kanshi. Nana ma bacci take, don haka ya saɓeta a kafaɗa ya kaita har ɗakin Sofi ya kwantar da ita.

Yana fitowa ya samu Sofi tsaye bakin ƙofar. Idanuwanshi ya ke yawatawa kan fuskarta ba tare da yasan abinda yake son gani akai ba. Kallon nata na nutsar da shi ta fannoni da ya ke kasa fahimta. Da duk wani abu da ke jikinshi yake son sake jin ɗuminta ko na minti biyu ne.

Baya son takura mata. Yarda da aurenshi da ta yi bayan ta san bashi da abinda zai bata kaɗai ya ishe shi. Beside zuciyarshi ciwo take kamar me. Lumshe idanuwanshi ya yi yana fitar da wani numfashi mai nauyi kafin ya ce mata,

“Zan yi tafiya gobe in sha Allah. Zan dawo maybe zuwa next week ko kafin…”

Yana buɗe bakinshi ya fara magana ta ji zuciyarta na wani irin dokawa cike da tsoro. Zai sake tafiya, zai sake barinsu.

Yanzun kam sam zuciyarta ba za ta iya ɗaukar wani rashin nashi ba. Katse shi ta yi da faɗin,

“Karka tafi…”

Idanuwanta ta sauke cikin nashi ta tabbata ya ga tsoro da shakkun da ke cikinsu. Kasa haƙuri ya yi da sauri ya taka ya haɗe tazarar da ke tsakaninsu.

Hannu yasa ya tallabi fuskarta yana jin jikinshi ya ɗauki wani irin ɗumi. Sosai ya kalleta.

“Zan ƙare komai ne Sofi. Zan dawo gaba ɗaya. Ki yarda da ni, ƙarshen abinda zuciyata za ta yi shi ne nisanta da ke.”

Hawayen da ke riƙe cikin idanuwanta suka zubo. Muryarta a sarƙe ta ce mishi,

“Usman ya rasu…”

Kallonta yake da mamaki yana juya maganarta cikin kanshi yana tunanin inda ya taɓa jin sunan da alaƙar sunan da ita. Lokaci ɗaya ya tuna. Ware idanuwanshi ya yi kafin ya ce,

“Allahu Akhbar! Sofi. O. M. G. Sofiiii!”

Ya rasa me ya kamata ya ce mata. Langaɓe kanta da ke cikin hannuwanshi ta yi gefe cikin wani irin sanyin murya ta ce,

“Na gode…”

Ji yake kamar ya ɗauke mata ciwon da ya san take ji. Ciwon da har yanzun bai san asalin ɗacin shi ba sai dai ya kamanta. Riƙota ya yi jikinshi ya rungumeta. Tsam ta yi a jikinshi tanajin sanannen yanayin da ke tattare da hakan da ta yi tunanin ya ɓace mata. Hannuwanta ta zagaya tana sake riƙe shi. Da kaɗan-kaɗan ta ke ji yana hura mata wajajen da ke mata zafi ba tare da wata iska na fita daga bakinshi ba. Sun kai mintina biyar a haka.

Kafin ta ɗan zame jikinta ta ɗago tana ware idanuwanta a kanshi.

“Ka kwana tare da mu yau.”

A tausashe ya ke kallonta.

“You don’t have to… Bana son takura ku Sofi. Za mu iya bin komai a hankali.”

Girgiza mishi kai ta yi,

“Nana za ta so hakan. In dai za ka kwana ba tare da ka zaci wani abu da ya wuce hakan ba banda matsala.”

Kai ya ɗaga mata. Ya fahimci komai.

“Zan je gida sai in dawo. Ki kula da ke da Nana.”

Kai ta ɗaga mishi kawai tana jinta daban ta wajaje da dama. Yanayin ba baƙo ba ne a wajenta amma ya mata wani iri. Sai da ya sumbaci kumatunta, yana jin son yin fiye da hakan ya danne sannan ya juya ya nufi ƙofar yana ficewa.

Sauke numfashi Safiyya ta yi ta wuce cikin ɗaki inda Nana take.

*****

A gida ya ci abinci da sallar isha’i. Ya yi sallama da kowa don ba ya jin zai biya da safe sannan ya wuce daga can zai tafi.

Komai da ya ke buƙata ya ɗauka ya sa a mota ya wuce gidan su Safiyya. Yana shiga Nana ta rugo da gudu ta riƙe mishi ƙafafuwa.

Ɗago ta ya yi zuwa jikinshi.

“Princess baki yi bacci ba?”

Girgiza mishi kai ta yi tana daƙuna fuska.

“Mumy ta ce min za ka kwana a nan. Shi ne na ke ta jiranka.”

Murmushi ya yi yana cire takalman ƙafarshi kafin ya ƙarasa da ita tsakiyar falon. Idanuwanshi ya sauke kan Safiyya da take sanye da doguwar riga ta farar shadda.

Ta mishi kyau ba kaɗan ba.

“Sannu da gida.”

Ya ce mata yana zama gefe tare da Nana da ya zaunar kan cinyarshi.

“Ya su Momma?”

Safiyya ta buƙata.

“Suna lafiya, suna gaishe ki.”

Kafin ta amsa shi Nana ta ce,

“Dady za ka tafi gobe?”

Ya jinjina kai alamar eh. Ya ɗora da faɗin,

“Da wahala in yi sati ɗaya. Idan na dawo shikenan ba zan sake komawa ba.”

Dariya Nana ta yi alamar ta ji daɗin hakan kafin kuma ta daƙuna fuska.

“Zan yi missing ɗinka kuma.”

Shima ɗan daƙuna fuska ya yi. Ba don yana tunanin Safiyya ba da ya fasa tafiya gobe ya yi booking musu waje ya tafi da Nana.

“Ko za ku raka ni?”

Nana ya tambaya amma idanuwanshi na kan Safiyya. Murmushi kawai ta yi.

“Nikam bana son jirgi fa. Ba zani ba dady.”

Ware idanuwa Fu’ad ya yi da ke tambayar da Safiyya ko da gaske Nana take. Kai ta ɗan ɗaga mishi.

Dariya ya yi.

“Da gaske? Me ya sa?”

Ɗan ɗaga mishi kai ta yi.

“Kawai tunanin hawa ina ciki can sama. Owww a daina maganar jirgi please.”

Ɗan ja mata hanci ya yi yana dariya.

“An daina Princess.”

Hira suke a hankali tana jikinshi. Safiyya kam kallonsu take, shi kaɗai ya isheta nishaɗi.

Har Nana ta yi bacci a jikinshi don magungunan da ta sha ma sun isa ɗaukarta. Safiyya ya kalla. Sannan ya miƙe da Nana.

Bayanshi ta bi. Ya kwantar da Nana kan gado. Yana gyara mata kwanciya ta juya ta riƙe mishi hannu gam. Ƙoƙarin zamewa ya ke amma yanayin riƙon da ta yi mishi in ya motsa ta sosai za ta iya tashi. Zama ya yi kan gadon yana jan ƙafafuwanshi a hankali ya kwanta gefenta. Safiyya ya kalla.

“Bana so in tashe ta.”

Kai ta ɗaga mishi. Ta zagaya ɗayan gefen Nana ta zauna tana jingina bayanta da gadon ta lumshe idanuwa. Ba don Fu’ad ɗin ba da sun manta da sun yi bacci. Don Nana ta koya mata bacci da wuri sai dai ko in sun zauna kallo ne. Kwanciya ta yi tare da gyarawa idanuwanta a rufe tana faɗin,

“Bacci na ke ji fa.”

Dariya ta bashi.

“Ina ne ɗakina?”

Ya tambaya, shiru ya ji ya sake faɗin,

“Sofi.”

“Umm.”

“Ina zan kwanta?”

Da alamar bacci da takura a muryarta ta ce,

“A kwance kake fa. Ni ka bar ni bacci nake ji.”

Murmushi ya yi.

“Good night to.”

“Oww ka daina Magana.

Dariya ya yi. Yana jin ta sauke ajiyar zuciya tana ƙara gyara kwanciya. Hannunta ɗaya ta ɗora kan Nana da alamun ta saba da hakan. Nana na jin hannun safiyya kanta ta saki na Fu’ad ta juya kwanciya tana ƙara matsawa jikin Safiyya ɗin. Kallonsu ya yi yana jin daban.

Ƙaunarsu mai girma ce. Alaƙar da ke tsakaninsu ba zai taɓa kamo shi ba. Matsawa ya yi kusa da Nana ya zagaya da hannunshi ya Riƙo su ita da Safiyya yana sauke wani numfashi.

Addu’a ya yi musu su dukansu ya tofa musu kafin ya lumshe idanuwanshi cike da ƙaunarsu.

*****

Bayan Sati Ɗaya

Kallonta ya ke yi. Tana sanye da material blue mai haske da mayafi dark blue hakama takalman ƙafarta. A hankali ta tako zuwa inda yake ta hura mishi iska cikin idanuwanshi. Ya ɗago hannunshi kamar mai son kare iskar yana dariya.

“Kamar ba ka taɓa ganina ba?”

Ta faɗi tana dariya.

“Anya Jana za mu fita kuwa? Kin yi kyau bana so kowa ya kalle ki.”

Ɗaga mishi gira ta yi da faɗin,

“Eye!? Ni kam ka wuce mu tafi.”

Ɓata fuska ya yi yana kallonta. Da gaske har ranshi yana kishin wani ya ganta haka. Janyota ya yi jikinshi tana ture shi ya haɗa bakinsu. Sun ɗauki lokaci a haka kafin ya saketa yana maida numfashi.

“Honey J mana. Ka gogemun janbaki.”

Murmushi ya yi.

“Bana son kowa ya kalleki da shi a bakinki. In na ce ki goge ɓata min lokaci za ki yi.”

“Shi ne za ka shanye?”

“Ya fi min sauƙi ai. Mu je.”

Bata yi musu ba ta sa hannunta cikin nashi suka fice tare. Shi ya buɗe mata mota ta shiga sannan ya zagaya. Suna hanya ne ya ce mata,

“Kayan lefe fa za mu siyo.”

Shiru ta ɗan yi kafin cikin sanyin murya ta ce mishi,

“Ina za mu je?”

“Ban sani ba fa. Shi ya sa na taho da ke.”

“Mu shiga kantin kwari kawai. Akwai inda nake siyayyar kaya sai mu duba idan sun maka.”

Ɗan jim ya yi sannan ya ce,

“Hakan ma ya yi.”

*****

Aikuwa hakan sukayi. Sosai Jana ta ture kishin da ta ke ji gefe ta taya Jabir suka zaɓi kyayyaki daga kan atamfofi zuwa lesses zuwa shaddoji dai dai ƙarfin shi.

Shagwaɓe mata ya yi ya gaji za su dawo su ƙarasa wani lokacin. Don haka suka juyo suka dawo gida. Wanka ya shiga. Jana kam ta yo alwala ta yi sallar la’asar sannan.

Yana fitowa ita ma wankan ta shiga. Yana kwance kan gado sanda ta fito. Ta kalle shi ya wani taɓare fuska.

“Na gaji fa.”

“Taɓara kawai kake ji. Ba yawo muka yi ba waje ɗaya ne muka tsaya.”

“Ni kam sauran ke za ki ƙarasa please.”

Girgiza mishi kai ta yi.

“Zan dai rakaka in kana so.”

Baice komai ba. Ba ya son ƙure haƙurin da ta ke yi. Hakanma ya gode. Hannuwanshi ya buɗe.

“Zo mu yi magana.”

Ba musu ta ƙarasa ta zauna gefen gadon. Kama hannunta ya yi ya kwantar da ita. Gidan ya yi shiru kasancewar yaran suna gidan Hajiya weekend. Juyawa ya yi suka fuskanci juna. Ya kama hannunta ya sumbata kafin ya ce,

“Please I need you to be honest with me. Ki faɗa min ra’ayinki kan wannan. Ni na baki zaɓi.”

Kai ta ɗaga mishi da ke nuna za ta yi yadda ya ce kafin ya ɗora da faɗin,

“Yawwa. Kin ga ɓangarena ba amfani nake da shi ba. Kusan komai anan nake yi. In ba ki da matsala Aina za ta zauna anan.

In kina da matsala da hakan za ta zauna a gidana na dakata.”

Shiru tayie tana nazarin maganarshi kafin ta ce,

“Zan baka amsa. Me kake so a ranka kai?”
Ganin alamar gardama zai yi mata ya sa ta faɗin,

“Please ka amsani. Ina son sani ne.”

Sauke ajiyar zuciya ya yi.

“Zan so ganinku waje ɗaya. Rabakun ba matsala bane a wajena. Bana son takura ki ne kawai.”

Matsawa ta yi ta ɗora kanta a ƙirjinshi. Ta ji daɗin wannan karamcin da ya yi mata har ranta. Ba kowanne namiji bane ya ke baka zaɓi irin wanda Jabir ya bata. Sosai take juya maganarshi a ranta. Bata son ta kasa cika roƙon da ya yi mata na ta faɗa mishi gaskiya.

“Bakomai in ta zauna anan ɗin. Roƙo ɗaya nake maka. Addu’a ɗaya nake maka Honey J. Allah ya baka ikon yi mana adalci.”

Lumshe idanuwa ya yi ya buɗe su akanta cike da yadda ya ke jin sonta.

“Amin Ya Allah. Na gode Jana. Allah yai miki albarka.”

Yatsanta ta saka ta rufe bakinshi.

“Amin. Ka manta babu godiya a tsakaninmu?”

Hannun ya kama yana cizon yatsan a hankali. Ƙwacewa ta yi tana yarfe yatsu.

“Haba mana. Da zafi fa.”

Ɗaga mata gira ya yi kawai da ke nuna ya san da zafin ai. Naushin kafaɗarshi ta ɗan yi a hankali.

Kafin muryarta da fuskarta babu alamar wasa ta ce,

“Idan kana da hali mu je gobe in raka ka ka ƙarasa siyayyar nan.”

Girgiza kai yayi.

“Me yasa? A bari zuwa next week ni kam na gaji. Ko ki je ke kaɗai.”

Jan numfashi ta yi ta fitar.

“Saboda ina so ka gama komai ya bar gidan nan. Ina son jin zuciyata free kaɗan. Bansan ko kagane me nake nufi ba. Inajin kishinka sosai. Ba zan iya ɗauka inajin maganar auren nan ba kullum. Na san yana nan. Believe me na sani kuma bana jayayya da shi. Sai dai bana so ana miƙo min shi gaban idona kullum.”

Saurin dumtse hannuwanta ya yi cikin nashi da faɗin,

“Don Allah ki yi haƙuri. Ban sani ba wallahi. Za mu je gobe mu ƙarasa in sha Allah.”

‘Yar dariya ta yi ganin yadda duk ya nuna bai ji daɗi ba da tunanin kamar yana hurting feelings ɗinta.

Sumba mai taushi ta manna mishi.

“Na gode da fahimta.”

Janta ya yi jikinshi.

“Yanzun nan kika ce babu godiya ko. Zo nan to.”

Dariya take tana ture shi. Kafin ya kashe mata jiki da wata irin soyayyarshi mai wahalar mantawa.

*****

Sallah ta idar. Wani irin kaɗaici ke damunta wanda ta kasa fahimtar daga inda ya ke fitowa.

Lumshe idanuwanta ta yi tana tuna fuskar Nawaf da murmushin shi. Cikin kunnuwanta take jin muryarshi yadda ya ke faɗin,

“Ina sonki Nur.”

Murmushi ta yi ta buɗe idanuwanta kafin lokaci ɗaya gaskiyar ba zai taɓa dawowa ba ta sake zauna mata.

“Allah ya haskaka kabarinka Nawaf. Ka tafi ka barni da kewarka mai yawa.”

Ta faɗi a sanyaye don zuwa yanzun lokuta irin hakan neman hawaye take ta rasa.

Sai ta wuni ita kaɗai a ɗaki abinta. In ba Mumyn Nawaf ɗin ta zo ta ce mata ta fito su ci abinci ba. Ko da can ita ba mai yawan magana bace. Balle kuma yanzun.

Jinta take duniyar ita kaɗai kamar bata da kowa. Bata da wanda za ta duba ta kira shi da nata. Sai yanzun ta ji hawayen na taruwa.

Gara da tana da Anty. Duk da ɗacin gaskiyar hakan in ta juya duniya za ta ce ga jininta komin ɓakinshi. Amma yanzun bata san daga ina ta fito ba. Yaya Farhan ya ce Anty tsintarta ta yi. A ina? Ta yaya? Shi ne bata tsaya tambaya ba, don ta san shi ma da wuya idan ya sani.
Ya akai ta ɓata? Su waye asalin iyayenta. Su waye danginta? Suna da rai? Basu da shi duk bata sani ba. Wani abu ne take jin ya ƙulle a cikinta. Sai yau da ta ɗan nutsu ta san tashin hankalin rasa Nawaf daban da na sanin bata da asali.

Bata da wani da zata duba ta kira nata. Wannan tashin hankalin daban ya ke. Ta tuno yadda ‘yan uwan Nawaf suke zagaye dashie cike da ƙauna kamar su yi karo-karo na ranakunsu na duniya su ƙara mishi. Yadda suke kuka na rashin shi. Yadda a kullum daga kanta har su mamanshi suke wuni yimishi addu’a.

Hawayen da suka taru idonta suka zubo da wani ɗumi. Wa zai nuna mata wannan ƙaunar? Wa zai mata irin addu’ar nan idan ta mutu.

Da ace suna da yaro ne ita da Nawaf ko ba komai in dangin Nawaf suka kalli yaron in bata za su iya tunata su yi mata addu’a.

Kira ta ji ya shigo wayarta. Ta ɗauko wayar da ke kan gado tana zama. Yaya Farhan ta gani rubuce a jiki. Ta ɗan yi murmushin takaici. Kamar wani zai kirata banda shi ɗin. Ta faɗi cikin ranta. Ɗaga kiran ta yi ta kara a kunnenta. Ya yi mata sallama da ta amsa da wani yanayi.

“Nuriyya menene? Kukan ne ba ki daina ba har yanzun ko? Sau nawa zan faɗa miki addu’ar ki ya ke so?”

Ai kamar maganganunshi sun buɗe mata sabon shafi ne. Cikin kuka ta ce,

“Ba shi bane yaya Farhan. Kawai ina tunani ne.”

Tana jin yadda ya ja numfashi tare da faɗin,

“Tunanin me? Sai kin sama kanki ciwo ko?”

Ta girgiza kai kamar yana ganinta.

“Bani da kowa a duniya da zan kira nawa yaya Farhan. Dana gama takaba ban san menene makomata ba. Ban san ina zani ba daga nan. Ban san wacece ni ba. Bansan asalina ba ban…”

“Shhhhhh please Nuriyya. Bana son wannan tunanin da kike yi. Ki daina faɗin haka.

Kina da inda za ki je. Kina da ni. Kina jina, kina da ni . Ba za ki taɓa rasa yadda za ki yi ba in ina nan.

Ina so za mu yi magana amma da sauran lokaci sai kin gama takaba kina jina. Bana son irin tunanin nan.”

Cikin sanyin murya har lokacin hawayen ba su daina zubo mata ba ta ce,

“Na daina. Yaya Farhan don Allah ka tayani duba wacece ni. Ka tayani dubawa ko zan samu dangina. Ko nima zan ga wani nawa.”

“Ki bari Nuriyya. Zan taya ki. Zan dubo miki, na miki wannan alƙawarin please ki daina damuwa har haka kin ji.”

Kai ta ɗaga ta sa hannu tana goge fuskarta.

“Na daina in sha Allah.”

“Uhum. Ko ke fa. Zan fita yanzun. In kina son wani abu ki kirani.”

“A dawo lafiya.”

Ya amsata yana kashe wayar. Ajiyeta ta yi gefe ta zame ta kwanta tana lumshe idanuwanta cike da tunani kala daban-daban.

*****

Yau kwananshi biyu da dawowa. Duka kwana biyun wajen su Safiyya ya yisu. Kusan komai nashi na gidan. Hakan ba ƙaramin daɗi i ya ke mishi ba. Sun gama magana da Abba kan zuwa ƙarshen satin da ya ƙara samun nutsuwa za su fara tafiya da shi don ya ga yadda harkar kasuwanci ya ke.

Tunda ya dawo Safiyya ta koma aiki abinta sai ta bar mishi Nana. Haka zai wuni biye wa shiriritarta. Ko su yi ta yawo abinsu.

Yanzun hakan ma ice cream suka fita suka sha. Fu’ad ɗin ya siyi kaji gasassu suka biya da Nana ya gaishe da su Inna.

Sun kuwa ji daɗin ziyarar duk da ba daɗewa suka yi ba. Da gida za su koma Nana ta ce a je wajen Momma.

*****

Suna shiga gidan ya ga Momma da Anty Fatima. Da alama Anty Fatima fita za ta yi. Gaisawa suka yi da Fu’ad ɗin.

“Mun zo ke kuma har za ki tafi?”

Ɗan daƙuna fuska ta yi ta ce,

“Asibiti ma zan wuce Fu’ad”

Ware idanuwa ya yi.

“Ya Rabb. Waye ba lafiya?”

“Hamza ne yayo waya sun kai Hussaina tana naƙuda yanzun can zan tafi.”

Ji ya yi zuciyarshi na dokawa. Momma ya kalla.

“Is she okay?”

Dariya ta ɗan yi duk da damuwar da ke fuskarta. Anty Fatima ce ta ɗan daki goshinta.

“Fu’ad Allah ya shirya mana kai. Ance maka tana naƙuda kana tambaya if she is okay. Kasan she is not. Allah dai ya sauketa lafiya.

Momma bari in tafi kar ya zama ba ‘yan uwanta tare da ita. Ki kira Fa’iza inata kira ta ƙi shiga tunda na fito.”

“To shikenan. Allah ya sauke ta lafiya.”

Cewar Momma. Anty Fatima ta amsa da amin.

“Ko inzo mu je tare?”

Fu’ad ya buƙata. Kafin anty Fatima ta amsa Momma ta ce,

“Ba abinda za ka iya mata. Ko ita da wuya su barta ta shiga balle kai namiji. Kai mata addu’a kawai daga nan.”

Shiru ya yi yana daƙuna fuska har Anty Fatima ta fice. Yana kallon Momma da Nana suka wuce abinsu. Babban falo ya zauna shiru yana tunani. Anan Hassan ya shigo babu ko sallama.

“Bro ina Momma?”

Kallonshi Fu’ad ya yi.

“Lafiyarka kuwa?”

Hannu ya sa cikin gashin kanshi ya yamutsa kafin ya ce,

“Inata kiran Hussaina lambarta a kashe. Na mijinta kuma ba ya zuwa. I know she is not okay. Ina ji a jikina ne kawai.”

Murmushi Fu’ad ya yi. Jini daban ne. Bond ɗin da ke tsakanin Hassan da Hussaina yasa yana ji a jikinshi ɗin tana cikin matsala.

“Calm down. Tana asibiti za ta haihu ne.”

Sauke numfashi Hassan ya yi.

“Wanne asibiti?”

Fu’ad ya amsa shi da,

“Ban sani ba wallahi. Yanzun Anty Fatima ta tafi kuma. Buh’ Momma ta ce maza ba sa zuwa.

Ba za su barka ka shiga ka ganta ba.”

Wayarshi ya ke dannawa da alama Anty Fatima zai kira tare da faɗin,

“I don’t care zan tsaya a waje. Ina son zuwa…”

Wucewa ya yi yana ficewa daga ɗakin.

“Hassan!”

Fu’ad ya kira. Ai ko juyowa bai yi ba ya wuce abinshi. Fu’ad ya ja numfashi yana girgiza kai. Shi kanshi ya damu. Musamman da ya san mata har mutuwa suke yi wajen haihuwa.

Akwai teammate ɗinshi da matarshi ta mutu wajen haihuwa. Wani tsoro ya ke ji har ranshi. Ya ɗauko wayarshi da shirin kiran Anty Fatima sai ga momma ta fito tana faɗin,

“Hussaina ta haihu. Namiji.”

Sauke wani numfashi Fu’ad ya yi da bai san yana riƙe dashi ba.

“Alhamdulillah. Momma tana lafiya dai ko? Ita da babyn?”

Kai Momma ta ɗaga mishi tana murmushi. Kafin Nana da ta fito ta riƙe mata hannu da faɗin,

“Granny mu je mu ga baby ɗin. Ina son babies fa.”

Dariya Momma ta yi.

“Ke da ƙaninki. Za ku je ku ganshi ni kam ba yau ba.”

Shagwaɓe fuska Nana ta yi . Ta kalli Fu’ad.

“Dady Please.”

Murmushi ya yi.

“Za mu je har da mumynki anjima.”

Dariya tayi tare da faɗin,

“Mu kaɗai banda tsofi ko dady?”

Ware mata idanuwa ya yi kafin Momma ta kai hannu ta ja mata kunnuwa.

“Wayyooo!”

Nana ta faɗi tana rugawa wajen Fu’ad. Dariya kawai ya yi.

“Je ki ɗauko hijab ɗinki na san mumynki ta dawo daga aiki. Sai mu je mu ga babyn ko?”

Da gudu ta tashi ta nufi ɓangaren Momma ta ɗauko hijabinta. Sallama suka yi mata suka wuce abinsu.

*****

Indomie da dafaffen ƙwai suka samu Safiyya na zaune tana ci. Zama suka yi gefe. Nana ta ce,

“Mumy har ice cream muka je muka sha.”

Harararsu ta yi saboda bakinta a cike ya ke da abinci. Sai da ta haɗiye ta nuna su da fork ɗin da ke hannunta.

“Ku biyun nan ba ku da kirki.”

Dafe ƙirji suka yi a tare suna ware mata idanuwansu masu kala ɗaya.

“Yes ba ku da kirki. Kunsan ba zan ci abinci ba baku rage min ba ko?”

Langabe fuska Nana ta yi. Fu’ad ya yi saurin cewa,

“Nace Nana ta ajiye miki fa. Ta ce mu cinye kina ci a office.”

Kallonshi Nana ta yi harda gasping.

“Dady…”

Ware mata idanuwa Fu’ad ya yi da ke fassara ko ba a yi hakan ba?

Kallonta ta mayar kan Safiyya da ido ta ke roƙonta ta fahimta. Dariya Safiyya ta yi,

“Nasan Princess ba za ta ci bata tunani ba.”

Daƙuna fuska Fu’ad ya yi.

“Me kike nufi?”

Ɗaga mishi kafaɗa ta yi alamar duk abinda ya ɗauka hakan ta ke nufi.

“Mumy wajen baby za mu je. Babyn Anty Hussaina.”

Sosai fara’a ta bayyana kan fuskar Safiyya.

“Hussaina ta haihu ne?”

Ta tambayi Fu’ad, ya ɗaga mata kai.

“Ke muka zo mu tafi tare da muga baby ɗin a tare suna asibiti ma.”

“Kai Alhamdulillah. Na ƙoshi ma, bari in yi wanka sai mu tafi.”

Nana ta sakko ƙasa ta ɗauki plate ɗin tana komawa kan kujera da shi.

“Dawo ki ajiye min abuna in na dawo zan cinye. Ku da kuka ci delicious.”

Dariya Nana ta yi tana ɗibowa da fork ɗin.

“Dady buɗe bakinka mu ci.”

Ture hannunta ya yi.

“Um um ke na ƙoshi fa.”

“Please…. Pretty please.”

Ta faɗi tana mishi wani puppy eyes da ya kasa ce ma a’a. Buɗe baki ya yi ta saka mishi.

Bakinshi a cike ya ke faɗin,

“Nana na ƙoshi wallahi ki ci.”

Cokali ɗaya tasa a bakinta ta daƙuna fuska tana haɗiye shi ba tare da ta tauna ba ta ajiye plate ɗin saboda yadda taste ɗin shi ya yi mata wani iri a baki.

“Ki ci mana.”

Cikin sanyin murya ta ce,

“Ba yunwa nake ji ba dama.”

Kai ya ɗaga mata ba tare da tunanin komai ba. Haka suka zauna suka jira Safiyya ta fito suka kama hanya. Suna hanya ne ya kira Anty Fatima ta ce musu suna Aminu kano. Safiyya ta ce ma Fu’ad,

“Mun je hannunmu na dukan cinya?”

Dariya ta ba shi.

“Tunanin da nake kenan fa. Ko mu biya baby dream mu siya abu?”

Kai ta ɗaga mishi. Haka kuwa suka yi, baby dream suka fara biyawa suka siya kayan babies masu yawan gaske. Ba yadda bai yi ba su haɗa kayan Safiyya ta ce a’a. Kowa ya siya da nashi kuɗin ya kai. Itama ai ƙanwarta ce. Har Fa’iza can suka sameta.

Fu’ad ko ta kansu bai bi ba idanuwanshi na kan Hussaina da take ta murmushi. Ya ƙarasa ya zauna gefenta.

“Hey lil sis. Sannu.”

Dariya ta yi tana ƙasa da kanta a kunyace. Babyn na hannun Anty Fatima ta taso tana miƙo wa Fu’ad shi. Kallonshi ya ke a hannun Anty Fatima. Ya mishi kyau sosai. Sai bacci ya ke yi. Yatsan shi ya sa ya ɗan taɓa fuskar shi.

“He is so so cute…”

Ya faɗi da wani nisantaccen yanayi a muryarshi.

“Ka karɓe shi mana.”

Anty Fatima ta faɗi. Ya girgiza mata kai alamar a’a. Ganin shi yake ɗan ƙararrami.

Miƙa mishi shi ta yi. Ya ware idanuwa yana buɗe hannayenshi ya karɓe shi. Nana ta taso daga wajen Fa’iza tana  ƙoƙarin hango shi. Zama Fu’ad ya yi suna kallon yaron tare. Safiyya ta taso ta ƙaraso wajensu. Miƙa mata shi Fu’ad ya yi yana tashi daga wajen ta zauna. Rocking ɗinshi take a hankali. Tana murmushi. Fu’ad ya kalleta ya kalli Nana sai ya ji wani abu tun daga yatsan ƙafarshi ya taso ya zo dai dai zuciyarshi yayi tsaye.

Da sauri ya fice daga ɗakin yana doko ƙofar da ɗan ƙarfi. Kallon Safiyya su Anty Fatima suka yi sannan suka kalli ƙofar.

Tashi ta yi ta ba wa Anty Fatima babyn ta fita ta bi Fu’ad. Yana tsaye bakin ƙofa hannayenshi cikin aljihun wandonshi.

“Me hakan ya ke nufi?”

Safiyya ta buƙata. Ya juyo ya zuba mata idanuwanshi.

“Ba ki gani ba kenan? Sofi bazan iya baki wancan farin cikin ba. You loook so so…”

Kasa karasawa ya yi saboda ɗacin da ya ke ji har zuciyarshi. Sauke numfashi ta yi.

“Ka daina tunanin nan please. Na samu Nana ko da ba mai tsawon kwana bace a duniya na ji me ake ji. Na wuce gorin haihuwa har abada. Na san soyayyar ‘ya’ya wannan kawai kyauta ce mai girma.”

Yanayin yadda ta ƙarasa maganar ya mishi wani iri. Ƙarasawa ya yi ba tare da damuwa da cewa a asibiti suke ba ya rungumeta.

“I am so sorry Sofi. Ni ya kamata a ce ina biyan zunubin kuskuren da na yi ba wai mu raba tare ba.”

Sake matse shi ta yi.

“Ni da kai. Ko ka manta ne. Ka dinga hango me muka yi Akan so, za mu jure wannan in sha Allah.

Allah ya san damu.”

Kissing gefen fuskarta ya yi.

“I love you.”

“Nasani…”

Kawai ta amsa shi da. Hakan take amsawa duk idan ya faɗi i love you ɗin nan tun bayan maida auren su. Tana jin sonshi. Sake furta mishi zai ɗauki lokaci. Da alama ya fuskanci hakan.

*****

Shagali sosai aka yi bayan sunan Hussaina. Lokacin Fu’ad ya fara gane kan kasuwancinsu. Duk da Abba bai fara fita ƙasashe da shi shigo da kaya ba. Sai dai ya barshi nan shagunan su na cikin Kantin Kwari. Haka rayuwa ta ci gaba da tafiyar musu cike da ƙauna da zumunci mai ban mamaki har bayan Wata biyu.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 2.5 / 5. Rating: 2

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Akan So 42Akan So 44 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×