21 February 2017
Har ya gama bubbuga ƙofar ya tafi ba ta buɗe ba. Kuka kawai take yi. Sai da ta yi mai isarta sannan ta tashi ta shiga toilet. Ruwan ɗumi ta haɗa ta shiga ciki, saboda jikinta ko'ina ciwo yake yi. Yadda Nawaf ya janyota daga kan kujera ya jefar ƙasa. Ba ƙaramar buguwa ta yi ba. Za ta iya rantsewa wani lokaci Nawaf ba shi da hankali. Zaman lafiyarsu na wata biyu ne a shekara ɗaya da rabi da aurensu. In har sunan Farhan ya gifta cikin gidan sai an samu matsala. . .