Skip to content
Part 10 of 52 in the Series Alkalamin Kaddara by Lubna Sufyan

Tuna Baya (Rayuwar Rafiq Mustafa Shettima) 

Alhaji Mustafa Shettima shi ne babban ɗa ga Justice Shettima da kuma Hajiya Hajara. Daga Mahaifiyar Alh. Mustafa har mahaifinshi yaren Kanuri ne ‘yan asalin garin Maiduguri. Zama ne ya mayar da shi garin Kano. Su takwas ne ‘ya’ya ga Justice Shettima. Mustafa, Abida, Nazir, Sadiya, Amina, Jabir, Kabir sai Autarsu Khadija. 

Asalin kakanninsu masu hali ne, hakan yasa bawai da aikin shi kawai Justice Shettima ya dogara ba, har ma da rassa na kasuwanci da kamfanoni har huɗu da ya gada daga wajen mahaifinshi kasancewarshi dmɗa ɗaya namiji. Su Alhaji Mustafa sun taso cikin wadata. Inda a cikin yaran Justice Shettima, Alhaji Mustafa ne kawai ya yi sha’awar karantar fannin da babanshi yayi wato ɓangaren shari’a. 

Yana shekararshi ta farko Allah ya yi wa Justice Shettima rasuwa. Hakan bai girgiza karatunshi ba tunda akwai wadata. Bayan kammalawarshi ne ya samu aiki a garin Abuja. Dama tun lokacin da yake makaranta soyayya mai ƙarfi ta ƙullu tsakanin su da matarshi Hafsatu wadda itama yaren Kanuri ce. Don haka da auren shi zama ya mayar da shi garin Abuja. 

Allah ya azurtasu da yara biyar. Rafiq, Fawzan, Zafira, Aroob, da Nadir. A zuciyar Alhaji Mustafa Shettima bayan zama cikakken Alƙali yana da sha’awar siyasa, don haka duk wani taku nashi da hangen abinda gobe zata haifar mishi a cikar burinshi yake yinshi.

Bayan ƙalubale da dama da ya fuskanta a lokacin da ya faɗa harkar siyasa za’a iya cewa ya shiga da ƙafar dama, inda ya yi kwamishinan ilimi a lokacin mulkin Fashola. Daga nan ne ya tsaya takarar gwamna inda tun a zaɓen primary aka kayar da shi, da yake shugaban ƙasar lokacin nasu ne aka sake bashi kujerar kwamishina ya riƙe. Yanzun kuma yana kan neman tsayawa kujerar mataimakin shugaban ƙasa. 

Ta ko ina ana damawa da Alh. Mustafa, ta fannin kasuwanci inda yake da hannun jari da manyan ‘yan kasuwa, yake kuma da gidajen mai sama da guda goma. Da wahala ka shiga gari a cikin Najeriya ka kira Mustafa Shettima ba’a samu wanda yasan shi ba. 

*****

A ko ina Rafiq ya samu kanshi zai iya cewa baisan menene rashi ba, kalmar bata taɓa ƙarasowa taku hamsin kusa da inda yake tsaye ba ma. Idan akwai abinda gaba ɗaya rayuwar shi da ta ƙannenshi ta ta’allaƙa akai bai wuce ƙin yin kuskure ba, a cikin rayuwarsu ta makaranta, da ta yau da kullum. Ko da yaushe cikin yin abinda Alhaji Mustafa zai yaba suke yi. Komai ya fara ne bayan Rafiq ya cika shekaru Ashirin da takwas a duniya.

A lokacin banda ‘yan uwanshi da suke ciki ɗaya, mutane shida ne suke da kusanci da shi. Abdallah, Faruk, Zaid, Muneeb, Arfan sannan Samira. Ita kaɗai ce macen da take cikin rayuwarshi take kuma da kusanci da shi wanda babu alaƙa ta jini. Ita ma dalilin babanta, Alhaji Habibu da ya kasance babban aminin Alhaji Mustafa ne, kuma abokinshi a kasuwanci da siyasa. 

Zai iya cewa abokantakar shi da Samira ba zaɓi bane ba. Babu yadda zai yi ne kawai. 

*****

Sauri take tana nufar hanyar kitchen ta ci karo da Zafira da ke shirin fitowa, hannunta ɗaya riƙe da plate ɗin da ke ɗauke da plantain da soyayayyen dankali, ɗayan kuma lemo. 

“Wai me yasa hankali ya kasa samun waje tare da ke?”

Zafira ta faɗi rai a ɓace tana yin sama da abubuwan da ke hannunta da kaɗan ya rage ta yi ɓari. Dariya Aroob ta yi. 

“Na ɗauka kun daina ɗaga burin ku akan maganar hankali na?”

Hararar ta Zafira ta yi tana shirin wucewa, da sauri Aroob ta riƙo hannunta. 

“Don Allah zo ki taimaka ki haɗa min coffee, yadda Ya Rafiq yake so.”

Gira zafira ta ɗaga mata duka biyun tana mata kallon da ke fassara ‘Rashin hankalin ki ya kai har haka?’

“Please, tun ɗazun ya sani da zai shiga wanka, ni ban ma ji ya yace in haɗo ba, hankali na yana kan Jhalak da akeyi a bollywood… Please please.”

Kallonta kawai Zafira take har lokacin. 

“Ya Rafiq zai kashe ni, pleaseee…”

“Har fatalwarki ba zai bari ba in ya fito daga wankan nan babu coffee ɗinshi.”

Zafira ta ƙarasa tana dariya, sake ware idanuwa Aroob ta yi. 

“Inalillahi…ki taimaka don Allah. Duk aiken da kike so zan je, ko me kike so in miki na kwana biyu.”

Girgiza kai ta yi tana shirin wucewa, da sauri Aroob ta sha gabanta. 

“Come on, kwana uku.”

“Kalli fuskata sosai… Kin ga alamar na damu? Matsa ki ban waje, abincina na yin sanyi.”

“Sati ɗaya… I promise ko me kike so.”

Wani murmushi Zafira ta yi tare da miƙa mata c

Kofi da plate ɗin da ke hannunta. 

“Kai min falo, ki shiga ɗakina ki mayar min kayan da na fito da su kan gado.”

“Da na bari Ya Rafiq ya kashe ni zaifi sauƙi.”

Aroob ta faɗi ƙasa-ƙasa. 

“Magana kike?”

Hannu tasa ta karɓi plate ɗin tana ficewa ta bar Zafira a kitchen ɗin. Bata ɗauki wani lokaci ba ta gama haɗawa ta ɗauko mug ɗin tana fitowa falo. 

“Aroob!”

Ta kira, da sauri Aroob ta fito tana mata murmushi, karɓar mug ɗin ta yi. 

“Thank you. Kin san ina son ki ko?”

Ta faɗi tana wucewa da sauri, kai kawai Zafira ta girgiza tana samun waje ta zauna. Saman benen gidan Aroob ta nufa tana hawa, tare da yin hanyar da zai kaita ɓangaren Rafiq. 

Bakin ƙofa ta tsaya tana ƙwanƙwasawa. Ta kusan mintina biyu kafin ta ji muryarshi ya amsa da ‘Yes’. Turawa ta yi tare da yin sallama. Yana tsaye jikinshi sanye da kaftan, ɗinkin da samarin zamani ke ya yi. 

Gajeran hannu ne, yadin dark blue ya kamashi kadan, yana daura agogon shi.

“Gashi… A ina zan ajiye maka?”

Sai lokacin ya ɗago idanuwanshi cike da yanayin da ke nuna gajiyar da yake ji har cikin ƙasusuwan shi. 

“Saman kaina.”

Ya amsa yana tsare ta da idanuwa, fuskar shi babu alamar fara’a. Dariya ke son ƙwace mata, ko kaɗan Aroob bata raina abin dariya.

“Yi haƙuri… In ajiye a nan?”

Ta buƙata tana nuna mishi kan mirror ɗin ɗakin, hannun shi ya miƙa mata, ta taka tana sa hannuwanta biyun ta bashi mug ɗin. Karba yayi yakai zuwa fuskarshi yana ɗan busa iska a ciki kafin ya kurɓa. 

Kai kawai ya jinjina mata alamar yayi mishi, ta juya abinta tana ficewa daga ɗakin. 

“Aroob…”

Da gudu ta dawo tana raba mishi manyan idanuwanta. 

“Haka kika samu ƙofar?”

Ɗan dukan goshinta ta yi tana ja mishi ƙofar. Kafin ya samu damar tunanin ko yaushe Aroob zata yi hankali an sake turo ƙofar tare da yin sallama, takalmanshi ya cire yana ƙarasowa ya wuce Rafiq ɗin da ke tsaye ya faɗa kan gadon da yake a gyare tsaf. 

“Oh my God…”

Fawzan ya faɗi yana kai hannu ya lalubo pillow ya ɗaga kanshi ya ɗora yana wani maida numfashi. Sai da Rafiq ya sake kurɓarr coffee ɗin, ya samu waje ya ajiye mug ɗin tukunna ya kai hannu yana janyo ƙafar Fawzan daga kan gadon. 

“Don Allah Ya Rafiq ka ƙyale ni… Kasan daga inda nake? Ba ka ji yadda jikina ke min ciwo ba.”

“Na aike ka? Sakko ka gyara min gadona yadda ka ganshi, ka fice min daga ɗaki kuma…”

Ya ƙarasa maganar yana janyo ƙafafuwan Fawzan duka biyun daga kan gadon yana shirin janyo shi gaba ɗaya ne ya miƙe babu shiri yana ture hannuwan Rafiq ɗin, sakkowa ya yi daga kan gadon, fuskar shi a shagwaɓe yake faɗin, 

“Fine! Na tafi ɗaki na…”

Ɗaga mishi gira Rafiq ya yi yana nuna mishi gadon daya ya mutsa da baki. 

“Gyara shi tsaf.”

Tsaye ya yi sai da Fawzan ya gyara gadon tsaf tukunna. 

“Zo ka sauke ni gidan su Abdallah.”

Rafiq ya faɗi cike da umarni yana saka takalmanshi da ke ajiye, ya ɗauki wayoyin shi duka biyun, sai mug ɗinshi ya fice daga ɗakin yasan Fawzan ɗin zai biyo bayan shi. 

Sauka ya yi falon ƙasa inda ya samu zafira na danne-danne a wayarta tana cin plantain. 

“Ya Rafiq…”

Ta faɗi da fara’a a fuskarta. 

“Zaf… Ya school ɗin?”

“Ga ta nan babu daɗi… Sannu da dawowa.”

“Exams ko? “

Kai ta ɗaga mishi. Tana shekararta ta ƙarshe a Nile University da ke nan garin Abuja. 

“Allah ya taimaka, focus akan abinda ya kaiki ok?”

“In sha Allah. Yaa Faq…. Anty Samira fa?”

Zafira ta tambaya tana kallon fuskar shi. 

“Gata nan cikin mug ɗina.”

Dariya take sosai. Ta san da wahalar gaske ya amsa mata dama. Indai zaka tambayi Rafiq wani abu zaka sha baƙar magana. In baka ci sa’a ba zai yi banza ya ƙyale ka ne. 

“Kwana biyu ban jita bane ba, kuma bata leƙo mu ba. Ko don baka nan ne shi yasa…”

Ɗan ɗaga mata kafaɗa ya yi, in Samira take son gani ko magana da tana da lambarta, zata iya zuwa gidan su, bai ga dalilin da zai sa ta dame shi ba. 

“Fawzan!”

Ya kira a ƙagauce. 

“Yaya gani nan fa a bayan ka.”

Fawzan ya faɗi yana daƙuna fuska. Saida ya ɗan ƙara shan coffee din tukunna, da kanshi ya taka har kitchen ya ƙarasa, cika mug ɗin da ruwa yayi ya zubar a wajen wanke-wanke, ɗauraye wa yayi ya mayar wajen zamanshi, ya ɗauki ƙaramin towel ɗin da ke ajiye ya tsane hannun shi tukunna ya fito. 

Gaba ɗaya fuskarshi ta sauya, farin ciki bayyane har a idanuwan shi. 

“Nuri…”

Ya faɗi muryarshi ɗauke da daɗin da yake ji a zuciyarshi. Shi kam in dai a gaban mahaifiyar shi ne jinshi yake kamar yaro ɗan shekara biyu. Ita ma murmushi take yi, jikinta sanye da lifaya da kallo ɗaya za ka yi mishi kasan yana da tsada sosai. 

“Tun ɗazun na dawo bakya nan.”

Ya ƙarasa maganar yana sauke muryarshi kamar zai mata kuka. 

“Na leƙa ma Haj. Ruƙayya wani suna ne, ya gajiyar tafiya?”

Rausayar dakai yayi. Don ganin Nuri ya tafiyar mishi da gajiyar.

Yasan akwai shaƙuwa mai ƙarfi tsakanin mahaifiya da yaranta. Amman baya jin akwai irin ƙaunar dake tsakanin shi da tashi mahaifiyar, don ko ‘yan uwanshi sukan ce Nuri ta fi sonshi akan su, ba suna faɗa bane don suna kishin hakan, don ƙaunarsu a gareshi mai girma ce, suna faɗa ne don shi kanshi yasan hakan ne. 

“Alhamdulillah…”

Ya faɗi yana ƙarasawa ya karɓi jakar da ke hannun Nuri. 

“Ban ma ƙarasa ba, Daddy ne ya sani dawowa, wai za mu yi magana…”

Kafin Nuri ta bashi amsa Fawzan ya ce, 

“Yaya kaifa nake jira…”

“Na fasa…”

Daƙuna mishi fuska Nuri ta yi. 

“Ba fita za kai ba Rafiq?”

Girgiza kai ya yi. 

“Ba mai muhimmanci bane, na ɗauka za ki daɗe ne shi yasa…”

“A’a na san za ka dawo shi yasa na fita da wuri…”

Takawa suke shi da Nuri za su nufi sashinta. Sai lokacin Zafira ta ce, 

“Sannu da zuwa…”

“Yauwa Zafira…”

Nuri ta faɗi suna wucewa ita da Rafiq ɗin, a falonta ta barshi tana shiga ciki, kan kujera ya zauna. Kayan jikinta ta sake zuwa doguwar riga mai kama da malun-malun ta less ruwan hoda sannan ta fito. Tun kafin ta ƙaraso ya ji kusancinta, zai iya rantsewa a zuciyarshi yake ji idan Nuri na waje ko da idanuwanshi basu ganta ba. 

“Yunwa nake ji sosai… Ban ci komai ba tun safe.”

“Rafiq ban hanaka zama da yunwa ba? Na ce ka dinga samun wani abu kana ci ko?”

Buɗe baki ya yi zai yi magana ta dakatar da shi tana ci gaba da faɗan zaman da yake da yunwa sai ulcer ta kamashi. 

“Nuri mana…ki yi haƙuri….kafin in ce zan nemi wani abu Daddy ya kirani, kuma dole sai na ƙarasa wasu abubuwan kafun in taho shi yasa…”

Bata kula shi ba ta wuce zuwa ɓangaren da suka baro. Da kanta ta shiga kitchen ta zubo masa dambun shinkafar da suka yi ita da Aroob, don bata taɓa yarda yaranta sun ci abincin ‘yan aiki ba, da kanta take kula da komai ta wannan ɓangaren. Sai kunun Aya da ta zuba mishi. Bata san yana bayanta ba, ba ƙaramin tsoro ya bata ba.

“Ya Salam!”

Ta faɗi da ƙarfi, da da akwai kaya a hannunta saita ɓarar da su, dariya Rafiq yake sosai. 

“Nuri tsoro…”

Yake faɗi yana ci gaba da dariya. Hararar shi ta yi. 

“Inda zuciyata ta buga da ba kai dariya ba…”

Plate ɗin yasa hannu ya ɗauka da kofin kunun ayan ya bi bayan Nuri suka koma falonta. Kan kujera ta zauna, shi kuma ya zauna kan kafet yana ajiye plate ɗin a gaban shi. Abincin ya nutsu yana ci, kallon shi Nuri take tana tunanin ta inda zata fara faɗa mishi dalilin daya sa Daddy ya kira shi ya dawo. 

“Ki faɗa min kawai Nuri, na san Daddy ba zai kira ni haka kawai ba…”

Rafiq ya faɗi yana ture plate ɗin abincin da ya ci rabi, ya ɗauki kofin kunun ayar da sanyin shi yake ratsa shi, sai dai sikari ya mishi yawa, don ba ma’abocin abubuwa masu zaƙi bane, in dan ta bakinshi ne kar a saka mishi sikari a ciki ma zai sha. 

“Menene kuma wannan karon? Babu wanda ya yi wani kuskure da Fawzan ya faɗa min…”

Girgiza mishi kai Nuri ta yi, tana haɗiye wani abu daya tsaya mata a maƙoshi. Miƙewa Rafiq ya yi yana komawa kan doguwar kujerar da take zaune, fuskarta yake nazari, kawai sai ya ji zuciyarshi ta soma dokawa, don yasan wani abu ne babba tunda ta yi shiru, tana tunanin ta yadda zata fara gaya mishi ne. 

Tana so ya fara ji daga bakinta ne, kafin Daddy ya dawo zuciyarshi ta ɗan nutsu, don bata son abinda zai biyo baya. 

“Ki min magana don Allah Nuri… Aikina yake so in bari ko?”

Kai Nuri ta sake girgiza mishi. 

“Don Allah karki cemun akan Fawzan ne, wallahi Nuri yana son asibitin nan, na ɗauka ya haƙura…”

Rafiq ya ƙarasa yana jin wani ɗaci akan harshen shi, Daddy ba zai taɓa barinsu su huta ba, da rana ɗaya ace sun so yin wani abu da yake zaɓinsu ne ya amince kai tsaye, bai taɓa ba. Abinda yake so dole shi za’a yi indai ana son zaman lafiya. Tunda ƙarancin shekaru Rafiq ya san cewa yana da banbanci da sauran yaran da ke ajinsu. 

Daddy yake gaya mishi cewar dole ne yafi kowa ƙoƙari a ajin, abokanshi ma dole su zama masu ƙoƙari, har ya fara hankali hakan bai canza ba, haka ya ga ya faru da duka ƙannen shi, babu wanda yasha wahala kamar Fawzan, don ƙwaƙwalwar shi bata ja yadda Daddy yake so. A littafin Daddy babu wani abu mai kama da rashin nasara. 

Baya fahimtar meye kuskure ko da ya ratso ta cikin ƙaddararka ne, ba zai ji uzurinka ba, indai nasara ce a littafin Daddy zaɓin samuwarta na hannun ka ne. 

“Duk ba wannan bane ba…”

Nuri ta faɗi tana katse wa Rafiq tunanin da yake yi. Duka hankalin shi ya mayar kanta yana jiran ya ji ko menene.

“Ya samar wa Zafira miji ne dama…”

Dariya ta kubce wa Rafiq da baisan daga inda ta fito ba, da alamun rashin yarda yake kallon Nuri, itama kallon shi take, bai daina dariya ba har lokacin da ya ce, 

“Miji? Zafira?”

Wata sabuwar dariyar na kubce mishi saboda abinda yasan ba zai yiwu bane ba. Duk da yana sane da haƙƙin Daddy ne ya samar mata mijin da zata aura, sanin halin Daddy yasa shi ƙin yarda da hakan.

“Rafiq…”

Nuri ta kira cike da damuwa. Miƙewa tsaye ya yi yana kai kawo cikin ɗakin, kafin ya yi tsaye yana watsa hannayen shi tare da girgiza wa a Nuri kai, lokaci ɗaya girman maganar da ta faɗa na danne shi. 

“Ki ce min Daddy bai yi amfani da rayuwar Zafira wajen siyasar shi ba, Nuri ki ce min baki barshi ba wannan karon, ki ce min kin zaɓi rayuwarta akan son Daddy wannan karon…”

Rafiq yake faɗi yana ƙarasawa ya tsugunna gaban Nuri ya riƙo hannuwanta, da duk wani abu da yake da shi yake roƙonta da ta ce mishi bata amince da wannan rashin adalcin ba. 

“Nuri don Allah… Wannan karon kawai…”

Ɗauke idanuwanta da take jin sun ciko da hawaye Nuri tayi daga kan Rafiq. Bata san yadda zata yi musu da Daddy ba ko kaɗan, don duk wani abu da zai yi yana mata bayani yadda zai gamsar da ita. Taso musa mishi maganar auren Zafira ɗin, ya zo mata da hujjojin da suka gamsar da ita. Ta kuma san koma waye gidan da zata huta ne. Kuma bawai tana soyayya da wani bane ba, don haka abu ne mai sauƙi. 

“Bata soyayya da kowa Rafiq, abin zai zo…”

A karo na farko a rayuwarshi da ya ɗaga hannuwanshi duka biyun yana haɗe su waje ɗaya alamar roƙon Nuri da ta yi shiru, bai taɓa jin baya son abinda zai fito daga bakinta ba sai yau. Kallon shi take, tana ganin yadda ranshi yake a ɓace ta cikin idanuwanshi da suka ƙanƙance. Miƙewa ya yi. 

“Ta sani?”

Ya tambaya, Nuri ta girgiza mishi kai. Dariyar takaici mai sauti ta kubce mishi. 

“Ni Daddy yake so in fara gaya mata… Shi yasa ya kirani… Ni yake so in faɗa mata…”

Ya ƙarasa yana dafe kanshi da yake jin ya fara ciwo. Ya kai mintina biyu a tsaye dafe da kai, kafin ya juya yana ficewa daga ɗakin ba tare da ya ce wa Nuri komai ba. Jingina kanta ta yi da kujera tana lumshe idanuwanta, yaranta ne komai nata, farin cikinsu na da muhimmanci a wajenta musamman Rafiq, sai dai farin cikin Daddy da shi zuciyarta ta buɗe ido. Bata tunanin ko ƙaunarsu zata fi hakan girma.

*****

Murmushi ta yi ganin Aroob ta mayar da duka kayan da ta fito da su kan gado, buɗe wardrobe ɗin ta yi, komai a shirye yake tsafe, ta sake shirya mata komai, atamfa ta haɗa su complete waje ɗaya. In tanan ɓangaren ne kuma Aroob bata da ha’inci, saboda babu wanda ya kaisu tsafta ita da Rafiq duk gidan. Basa son ƙazanta, kuma ɗakunansu ne ko takalmi ba zaka gani inda bai kamata ba, gado a gyare tsaf-tsaf. 

Remotes ta ɗauka duka biyun tana zama kan gado. Ta kunna kayan kallon kafin ta ja ƙafafuwanta kan gadon ta kwanta, ganin bata samu wani abin kirki a duk tasoshin da take kallo ba yasa ta miƙewa tana zuwa ta canza zuwa DVD. Sannan ta dawo ta kwanta, Merlin take kallo seoson 1, film ɗin yana burgeta. Sai dai yana farawa tasa pause. Tun Shekaranjiya rabonta da kallo, a ƙagauce take kuma da ta ga ya za’a ƙare. 

Karatun jarabawar yau ya hanata kallo jiya, sai dai tana da tsallaken sati ɗaya kafin wata jarabawar. Matsalar Muneeb ne, tare suke kallo, ko me take zai jirata sai ta gama su kalla tare, wani lokacin ma tana kallo suna waya suna tattauna abinda yake faruwa. Wayarta ta soma ruri, ɗauka ta yi murmushi na ƙwace mata, ta ɗaga da karawa a kunne, bayan ta amsa sallamar shi tana ɗorawa da, 

“Kamar kasan kai ne a raina…”

“Na ji a jikina ne shi yasa na kira.”

Tana jin murmushin da yake yi a muryarshi, gyara kwanciyarta ta yi, zata iya rantsewa tun bata san menene so ba Muneeb yake matuƙar burgeta, in ya zo gidansu wajen Rafiq, yadda komai nashi yake a nutse. 

“Ya exams ɗin?”

Ya buƙata ta ɗayan ɓangaren…”

“Alhamdulillah… Saura biyu amma na gaji, dama su mana ita a kwana biyu mu huta.”

Zafira tai maganar cikin sigar tsegumi. Dariya ya yi. 

“Kamar gobe ne in sha Allah, za ki ga kun gama lafiya ƙalau…”

Kai ta ɗan ɗaga cikin yarda da abinda ya faɗa. 

“Allah ya nuna mana. Ya aikin ka?”

“Gashi nan sai gajiya…”

“Sannu…”

Sai da ya sauke numfashin da ta ji cikin kunnenta, zuciyarta na nutsuwa waje ɗaya tukunna ya amsa da, 

“Yawwa.”

Shiru ta yi tana rasa abinda zata ce saboda yadda son shi ke mata yawo, ko ƙwarin kirki bata ji. 

“Zafira…”

Yadda yake kiran sunanta da muryarshi mai sanyi na sakata jin daɗin sunan fiye da yadda zata iya misaltawa. 

“Ya kamata su sani, na gaji da ɓoye wa kowa abinda ke tsakanin mu… Kallon Rafiq cikin ido koda yaushe da sanin ina sonki ba tare da goyon bayanshi ba yana min wani iri.”

Wannan karon ita ta sauke numfashi mai nauyi. Ta fi shi son bayyana abinda yake tsakanin su, sai dai tana jin tsoro, duk da ita ce mace babba a gidansu, har ƙasan zuciyarta tana da tabbacin ba za’a barta soyayya da kowa ba tare data gama makaranta ba. Shi yasa ta roƙi Muneeb da su bar komai sirri a tsakanin su har lokacin da zata gama makaranta. Ba shi kaɗai bane yake jin wani iri, ba zai gane babu sirri a tsakanin ta da yayanta ba sai wannan karon. 

Tana kuma jin nauyin abin na danneta da duk rana. Ji take kamar ta gaya mishi kawai ta sauke nauyin, amma duk lokacin da ta samu ɗan ƙarfin gaya mishi, sai ya yi dai-dai da lokacin da zai sake jaddada mata karatu kaɗai ya kaita makaranta, shi kaɗai ne dalilin da yasa ta je makaranta, abokan da zata zagaye kanta da su a makaranta ya zamana harkar makaranta kawai take hada su. Ba sai ya furta mata kai tsaye cewar cikin kashedin shi har da soyayya ba, shi yasa take tsoron faɗa mishin. 

“Kinyi shiru…”

Muneeb ya faɗi da alamun damuwa a muryarshi. 

“Na kusa, sauran sati biyu…”

“Shekaru biyu Zafira…a da muna ganin muna da dukkan lokacin da muke buƙata, yanzun kullum da tsoron kar lokaci ya ƙure mana nake bacci…ko Rafiq ne ya sani hankalina zai kwanta ta wani fannin….ba zamu taɓa wuce saurayi da budurwa ba in dai ba su sani ba…”

Kai take ɗagawa kamar yana ganinta. 

“Na sani…”

“Bazan iya ƙara jira ba… Zan faɗa mishi da kaina…”

Tashi zaune Zafira ta yi babu shiri, zuciyarta na dokawa. 

“Love…”

Ta faɗi. 

“Bazai yi aiki ba wannan karon Zafira, na gaji sosai, na baki dukkan lokacin da kike buƙata, ki nuna min soyayyar mu na da muhimmanci a wajenki…”

Da sauri ta ce, 

“Ina sonka… Ina sonka sosai ka sani kuma.”

Sai da ya ɗan yi jim tukunna ya ce 

“Nasani, ki nuna min na kai matsayin da Rafiq zai iya sani…”

Runtsa idanuwanta ta yi tana buɗe su a hankali, ta san dole Rafiq ya sani dama, amma kullum tana ganin akwai sauran lokaci, kafin nan ta shirya. Sai dai yanzun take da tabbacin ba zata taɓa shiryawa faɗa mishi tana soyayya da babban abokin shi ba, ta ina zata fara, tunanin hakan kawai yasa kamar ta shige ƙarƙashin gadonta saboda kunya, ga kuma tsoro bayyananne da take ji. 

“Bari in baki lokaci ki yi tunanin da kyau…”

“Kwana nawa nake dashi?”

Ta buƙata. 

“Daga nan zuwa sa’adda zan haɗu da shi…”

“Love ko yaushe za ka iya haɗuwa da shi fa.. Ina nufin ko yau ma za ku iya haɗuwa. “

Zafira take faɗi a tsorace. 

“Zaɓin naki ne Princess…”

Muneeb ya ce yana katse wayar kafin ta samu damar bashi amsa.

“Innalillahi…”

Ta faɗi tana ajiye wayar akan gado. Ta san halin Muneeb kaf, ya gajin kamar yadda ya faɗa, a muryarshi kawai ta fahimci hakan, kuma baya faɗa mata abinda ba zai yi ba, suna haɗuwa da Rafiq ɗin zai faɗa mishi. Tana son ya fara ji daga wajenta, bata so Muneeb ya fara faɗa mishi, ko ba komai Yayanta ne, kuma yana faɗa musu ko yaushe suke buƙatar abokin shawara a tare da shi za su samu. 

Bata taɓa wani buƙatar ƙawa ba, tana da su barkatai a makaranta, amma wadda zata kira ƙawaye sosai duk sun haɗa jini, yaran ‘yan uwan Nuri ne ko na Daddy. Suma ba wanda zai ce wata hira banda ta duniya ta taɓa haɗa su. In tana son shawara ko wani abu ‘yan uwanta suna nan. Saukowa ta yi daga kan gadon ta fita daga ɗakinta zuwa na Aroob da yake jere da natan. 

Sai da ta ƙwanƙwasa Aroob ɗin ta ce ta shiga tukunna ta tura ta shiga, kan hannun kujerar Aroob ɗin ta zauna, gaba ɗaya komai na ɗakin kalar pink ne mai haske da mai duhu. Haka kuma yake tun yarintarta komai na ɗakinta har zanin gado. 

“Na kasa sabawa, kullum na shigo ɗakinki sai inga kamar na shiga duniyar Cartoon…”

Dariya Aroob take yi. 

“Da yake ma duk sa’adda kike shigowa ban gayyace ki ba…”

Juya idanuwanta Zafira ta yi tana taɓe baki. 

“Na ji… Ni ba abinda ya kawoni kenan ba. Kisa kanki a matsayina…. Ke ce kike ɓoye wa Ya Rafiq wani abu babba, sai lokaci ya zo da dole ya sani, za ki so ya ji a wajenki ne ko a wani waje…”

Ɗan ɗaga gira Aroob ta yi tana kallon Zafira, kafin ta ce, 

“Wani abu babba kamar son Muneeb?”

Ware idanuwa Zafira ta yi tana miƙewa da sauri ta ƙarasa inda Aroob take tana rufe mata baki, tureta Aroob ta yi tana dariya. 

“Wallahi ina mamakin yafda akai Ya Rafiq bai gane ba, kalli yadda kuke kallon juna in ya zo gidan nan…”

Sake ƙoƙarin rufe mata baki Zafira take yi tana jin fuskarta na yin wani ja saboda kunya. Bata taɓa tunanin Aroob ta sani ba, ko da wasa kuwa. 

“Wai ba za ki yi shiru ba sai wani ya ji ki Aroob…”

Zafira ta ce tana murmushi cike da kunya. Matsawa Aroob ta yi tana jingina bayanta da abin gadon, wannan karon babu alamar wasa a muryarta take kallon Zafira. 

“Ki faɗa mishi… Bansan me yasa kika ɓoye ba tun da farko, in Yaya yasaniy komai zai miki sauƙi a wajen Daddy…”

Ciza leɓenta na ƙasa ta yi. 

“Tsoro nake ji wallahi… In ya yi min faɗa kuma fa?”

Daƙuna fuska Aroob ta yi. 

“Ki ce abokin shawararki ki ke son magana da shi ba Ya Rafiq ba… Kafin ki faɗa mishi, yana mana faɗa ne kawai in yana Yayanmu.”

Ɗan shiru Zafira ta yi tana juya maganar Aroob ɗin. 

“Ki tashi… Ki je ki faɗa mishi kawai…”

“Yanzun?”

Zafira ta tambaya tana ware idanuwa. Kai Aroob ta ɗaga mata

“Me kike jira…”

Miƙewa Zafira ta yi, gudun zuciyarta na ƙaruwa, tana jin shi a ko ina na jikinta. Har ta kai ƙofa Aroob ta ce, 

“Zaf…”

Juyawa ta yi. 

“Ya haɗu…”

Girgiza kai ta yi tana ficewa, dariyar Aroob ɗin kafin ta rufe mata ƙofa na saka ta murmushi. Ƙafafuwanta har kyarma suke yi lokacin da take ƙarasawa ɓangaren Rafiq ɗin. Sama-sama take jinta lokacin da ta ƙwanƙwasa mishi ƙofa, ta kusa mintina biyar a tsaye tukunna ta sake ƙwanƙwasawa, shiru, zata juya ta koma ne don ta ɗauka ko ya fita ta ji ya ce, 

“Shigo…”

Zata rantse zuciyarta cikin hannunta da ta buɗe ƙofar da shi ta koma saboda zufar da yake yi, tana jin ya ɗauki sanyi, murza shi take da ɗayan hannunta lokacin da ta shiga ɗakin, sai take ganin kamar ya ƙara mata girma yau. Falon da wajen bacci, har da ƙaramin wajen cin abinci za ka iya ganinsu daga nan inda kake tsaye. Hawan bene biyu ya rarraba ko wanne ɓangare da ɗan uwanshi. 

Yanzun zata iya cewa a falonshi take a tsaye. Yana zaune kan kujera ta mutum ɗaya. Fuskarshi babu walwala, yanayin shi na ƙara mata tsoron da take ji. 

“Zan iya dawowa wani lokacin…”

Ta faɗa tana shirin juyawa. 

“Menene?”

Ya buƙata a taƙaice. Maƙoshin ta tajii ya bushe, wani yawu ta haɗiye tana fuskantar shi, wasa take da hannuwanta. 

“Na ga kamar a gajiye kake…”

Sai lokacin ya ɗago yana sauke mata idanuwanshi. 

“Yaushe na taɓa gajiyar da bazan saurare ku ba?”

Duk da maganar ta fito da sigar tambaya, tasan ba amsa yake buƙata ba. 

“Bana son tsayuwar nan Zafira. Ki samu wajen zama…”

Ya sake faɗi yana binta da kallo har ta zauna. Zuciyarshi na matsewa waje ɗaya da abinda Daddy yake so ya yi mata. Da abinda ba zai taɓa amincewa da shi ba, idan Nuri ba zata nuna wa Daddy rashin kyautuwar hakan ba shi zai yi. 

“Yaya…”

Ta kira tana yin shiru kuma. Dafe kai yayi da hannuwanshi biyun yana sauke numfashi kafin ya ɗago ya kalleta. Daga yadda take wasa da hannuwanta zuwa yanayinta gaba ɗaya ya nuna a tsorace take da ta faɗa mishi ko menene. 

“Me kike buƙata?”

“Aboki…”

Ta faɗi da sauri. Jinjina kai ya yi, shi ya faɗa musu cewar duk sa’adda suke son faɗa mishi wata magana da suke tsoron zai musu faɗa, ko wata tambaya da suke ganin Yayansu ba zai amsa ba, zai zama abokinsu, su faɗa mishi hakan suke buƙata, sai su yi maganarsu lafiya ƙalau. Yana ganin yadda suke yawan amfani da hakan fiye da yadda ya kamata. 

Musamman Fawzan da zai shigo ya ɗaukar mishi abu, in ya zo magana sai ya ce ɗakin abokinshi ne ya shigo, in ka ɗauki abin abokinka baya faɗa, haka abokai suke yi, dole yake ƙyaleshi. Zafira ce bata fiye mishi haka ba, to ko meye yanzun yasan yana da muhimmanci a wajenta. 

“Ina jin ki. “

“Ya Rafiq daman…”

Katse ta ya yi da girgiza mata kai, yana ɗora murmushin da yakan yi wa ‘yan waje, wanda baiday kusanci da zuciyarshi saboda baya jin nishaɗi ko kaɗan. 

“Rafiq kawai…”

Kai ta ɗaga duk da yasan ba zata iya kiran sunan shi kai tsaye ba. Hannuwa tasa tana goge fuskarta da take jin alamun zufa. Wani numfashi ta ja. 

“Ni da Ya Muneeb muna soyayya!”

Ta faɗi da sauri tana rufe fuskarta, tana kuma jin kamar wani nauyi ya sauka daga kanta. ‘Ya Muneeb muna soyayya’ kalamai huɗun da Rafiq ya ji sun dira cikin kunnenshi suna yawata ko’ina na jikinshi cike da neman inda ya kamata su zauna. Kafin su samu waje a cikin kanshi su yi daram suna aikama zuciyarshi saƙon girman da hakan yake nufi. 

“Tun yaushe?”

Ya tambaya muryarshi can ƙasan maƙoshi. Ba zai ɗaga murya ba, ba zai yi komai ba

“Shekara biyu.”

Ta amsa har lokacin fuskarta na rufe da hannuwanta, so yake ya girgiza ta, ya ji dalilin da yasa bata faɗa mishi tun farko ba, maimaita wa kanshi cewar aboki ta ce tana buƙata ba Yayanta ba. Amma ƙwaƙwalwar shi ta kasa tuna yadda aboki ya kamata ya yi a yanayi irin wannan. Muneeb, dole ya ji dalilin da zai sa ya ɓoye mishi in Zafira bata faɗa mishi ba. 

“Kina son shi?”

Ya sake tambaya yana ƙirga ɗaya zuwa goma cikin kanshi, kafin ta ɗaga kai a hankali. 

“Zafira…”

Ya kira. Ba sai ya ƙarasa ba, ya fi son ta yi magana da bakinta ta kuma san hakan. 

“Yaya kunya nake ji wallahi…”

Ta faɗi tana duƙunƙune fuskarta a jikinta. Runtsa idanuwanshi ya yi yana buɗe su a hankali. 

“Kina son shi?”

Ya sake maimaitawa. 

“Eh… Sosai…”

Zafira ta faɗi tana haɗe jikinta kan kujerar kamar zata shige ciki. 

“Yana kula da ke yadda ya kamata?”

“Yaya…”

Zafira ta ce tana jin kamar ƙasa ta buɗe ta haɗiyeta saboda kunya. 

“Abokin ki ne ni, na damu ne kawai, ƙawata nada saurayi shekaru biyu sai yanzun nake sani dole in ji duka details ɗin…”

Miƙewa Zafira ta yi da sauri tana rugawa da gudu ta bar mishi ɗakin. Duk da abinda yake ji sai da dariya ta kubce mishi. Kafin lokaci ɗaya ta ɗauke kamar yadda ta zo babu sanarwa, a wata duniyar, a wani gidan, banda duniyarsu, banda nasu gidan, zai yi farin ciki saboda Muneeb mutumin kirkine, kowanne Yaya zai yi alfahari da ƙanwarshi ta samu Muneeb a matsayin mijinta. 

Sai dai a tashi duniyar, abu ne da yasan ba zai yiwu ba, abune mai wahala, a maimakon farin ciki, zuciyarshi cike take da tsoron da bai taɓa sanin kalarshi ba, tsoron yadda duniyar Zafira take gab da birkicewa. Zai ɗora gaba ɗayan laifin akan Muneeb da bai faɗa mishi tun da wuri sa’adda zai iya tsayar da abin ba tare da su biyun sun shiga yanayi ba. 

Tashi ya yi yana ƙara shiga cikin ɗakin sosai zuwa ɓangaren baccin shi, mukullin motarshi ya ɗauka a gefen gado yana fita daga ɗakin zuwa hanyar da ta fitar da shi daga gidan gaba ɗaya. Yana tafiya yana tunanin yadda akai bai gane abinda yake faruwa tsakanin Muneeb da Zafira ba. Sai yanzun da ta faɗa ne yake ganin alamomi da yawa. Akwai ranar da motar Zafira ta samu matsala ta kirashi suka tafi da Muneeb ɗin don ya duba mata. 

*****

Bayan ya dudduba ne ya ɗago ya kalli Rafiq ɗin da faɗin, 

“Dole sai na tafi da motar gareji…”

Shagwaɓe fuska Zafira ta yi 

“Ya Muneeb har yaushe? Za’a gama gyarawa yau?”

“Zaf…”

Rafiq ya kira cike da kashedi, da baya tare da Muneeb ɗin ma lokacin data kira da ba su taho tare ba, don sam baya yarda sukai mishi gyaran mota tunda ba kuɗin yake karɓa ba, Rafiq na jin wani iri, ya fi yarda da duk kusancin da ke tsakaninku in hidima ta shigo ta cikin sana’arka a baka haƙƙinka yadda ya kamata.

“Yaya zan fita da motar ne fa…”

Ta faɗi tana turo laɓɓanta. Idanuwa kawai Rafiq ya tsareta da su. Dole ta ɗauke nata tana sadda kanta ƙasa don ta san baya musu faɗa a gaban wani, amma dole zata sha faɗa in suka je gida. 

“Anjima zan kawo miki har gida in sha Allah…”

Muneeb ya faɗi yana murmushi. Kai kawai Zafira ta ɗaga mishi tana zuwa ta gaban su zata wuce. 

“Zafira…”

Rafiq ya faɗi a gajiye wannan karon. Juyowa ta yi ta kalli Muneeb ta ce, 

“Nagode…”

“Karki damu…”

Tana buɗe mota ta shiga, Rafiq ya matsa yana taka ƙafar Muneeb ɗin da ya ture shi da sauri yana durƙusawa ya murza yatsun ƙafarshi tukunna ya ɗago yana watsama Rafiq ɗin wani kallo. 

“Ka gaji da idanuwanka a jikinka ne ko?”

Rafiq ya faɗi shima yana hararar Muneeb ɗin 

“Ba tun yanzun nasan kana baƙin ciki da ƙafata da tafi taka kyau ba, sai dai ban ɗauka ya kai har haka ba…”

Dariya Rafiq ya yi. 

“Baka da hankali kai kam… Ƙanwata ce Muneeb.”

Fuskar da ke nuna alamun ‘me nayi’ Muneeb ɗin ya yi wa Rafiq. 

“Kana kallonta fiye da na Yaya da ƙanwa…”

Ɗan ɗaga kafaɗa Muneeb ya yi. 

“Tana da kyau…”

Duka Rafiq ɗin ya kai wa Muneeb ya kauce yana dariya. 

“Ka wuce ka kaita gida… Zan tafi da motar.”

Kai Rafiq ya ɗan ɗaga mishi. 

“Mun gode…”

Girgiza kai kawai Muneeb ɗin ya yi ba tare da ya ce komai ba. Wucewa Rafiq ya yi ya shiga tashi motar. Ɗan juyawa ya yi ya kalli Zafira, inda ta tattara hankalinta gaba ɗaya ya kalla, bai ga komai ba sai Muneeb da ke rufe gaban motarta. Ɗan daƙuna fuska ya yi saboda ya kasa gane yanayin da ke fuskarta, ƙarar tashin motar ne yasa ta juyowa ta ɗan kalli Rafiq ɗin. 

Sai da ya yi baya suka hau titi tukunna ya ce, 

“Ina tarbiyarki, ko kuɗi kika biya shi ya kamata ki mishi godiya ba saina tuna miki ba…”

“A gajiye nake shi yasa, hakan ba zai sake faruwa ba…”

Kai kawai ya ɗaga mata ba tare da ya sake cewa komai ba. 

*****

Sai yanzun abin ya faɗo mishi, bayan nan abubuwa da yawa sun faru, bai taɓa kawowa a ranshi ba, ba don soyayya na baka zaɓin wanda za ka so ba, sai dai ya ɗauka kawai Yaya da Ƙanwa Muneeb da Zafira suke yi. Bai taɓa zaton ya fi haka ba. Motarshi ya buɗe yana shiga. Sai da ya zauna tukunna ya yi wa Nuri gajeren text. 

‘Na je wajen Muneeb Nuri.’

Ya sa wayar a key ya mayar aljihu. Kanshi tsaye ma’aikatar su Muneeb ɗin ta gyaran motoci ya isa. Yana parking ɗin motarshi ya wuce ya shiga ciki har inda zai kaishi office ɗin Muneeb. Yaron da ke kula da shiga da fitar mutane a office ɗin Muneeb ɗin ma gaishe da shi ya yi yana ɗorawa da, 

“Shi kaɗai ne, yana ciki.”

Don haka ya ƙarasa, ko ƙwanƙwasawa bai yi ba ya buɗe ƙofar ya shiga. Muneeb na kwance kan kujerar hutawar da ke office ɗin. Ya ɗan ɗago da kanshi, kallo ɗaya ya yi wa Rafiq ya ce, 

“Ta gaya maka kenan!”

Ɗan kai kawo Rafiq yake yi a office ɗin Muneeb ɗin yana rasa kalar tunanin da ya kamata ya yi. Daddy ya riga da ya samo wa Zafira miji, da wahala matuƙa wani abu ya canza ra’ayinshi, in har ya saurari cewa Zafira na da wanda take so in ya ji Muneeb ne ba zai amince ba, Rafiq na da tabbacin ko da ace Daddy bashi da wanda zai ba auren Zafira da wahala ya yarda da Muneeb. 

Ganin har lokacin Rafiq bai ce komai ba yasa Muneeb tashi zaune. Damuwa bayyane a fuskarshi. 

“Na san ya kamata in faɗa maka, Zafira ce ta ce lokaci bai yi ba, ita ta roƙe ni da in bari ta gama makaranta tukunna…”

Girgiza mishi kai Rafiq yake tunda ya fara magana. 

“Me yasa zaka biye mata? Me yasa baka faɗa min ba Muneeb?”

Kallon shi Muneeb ya yi. 

“Ina son ta, tun da na fara ganin ta nake sonta, na san ta yi yarinta a lokacin amma bai hana zuciyata doka mata ba, ban faɗa mata ba sai da tana level 2 Rafiq…ya kamata in sanar dakai kafin in faɗa mata ɗin… Shi ne kuskurena…”

Dariyar takaici mai sauti Rafiq ya yi. Ƙin faɗa mishi shi ne kuskure na biyu da Muneeb ya yi, na farko son Zafira ne. Ganin kallon da Rafiq ɗin yake mishi yasa shi faɗin, 

“Baka amince ba? Baka sona da ƙanwarka…”

Ɗan dafe kai Rafiq ya yi, baisan ta inda zai fara wa Muneeb bayani ya fahimta ba. 

“Kafin ka faɗa mata ya kamata in sani…”

Ya sake maimaitawa kamar hakan kawai ya isa ya fahimtar da Muneeb ɗin abinda yake son fahimtar da shi. 

“Na ce maka na san ya kamata in faɗa maka, ban yi ba… Ka yi haƙuri ban faɗa maka ina son ƙanwarka ba kafin in faɗa mata…in so kake kullum in dinga rubuto maka text ɗin haƙuri har sai ka haƙura zan yi…amma ina sonta, ko yanzun kuka ce in turo manyana zan yi wallahi… A shirye nake in aure ta.”

Ƙarasawa Rafiq ya yi ya zauna kan kujerar da Muneeb ɗin yake, don yadda ya ƙarasa maganar kawai za ka iya jin yadda Zafira take da muhimmanci a wajen shi.

“Me nake dashi da baka sona da ƙanwarka? Kasan ko ƙawa mace banda ita Rafiq, kai ka sani, ita ce mace ta farko da zuciyata ta doka ma, kuma bata ƙara ba har yanzun…”

A rikice Muneeb ɗin yake, gani yake Rafiq baya son shi da Zafira. Shi kuma baisan ta inda zai fara mishi bayani ba, kafin ya kai kan Zafira kenan, daya sani tun daga farko zai mishi bayani, in har yana sonta Rafiq ɗin yake gani, zai haƙura, ba zai fara yarda ya janyota ta soshi har haka ba. Ba zai so su duka biyun su wahala ba.

“Kai da ita… Ba zaku faru ba”

Miƙewa tsaye Muneeb ya yi yana kallon Rafiq da ke fassara ‘Ka ce min wasa kake’. Ganin shi ma Rafiq ɗin na kallon shi ba tare da ya sake cewa komai ba ya tabbatar mishi da gaske yake nufin abinda ya faɗa. 

“Me yasa? Banda duk wata halayya da aka shimfiɗa a musulunci na sharuɗɗan aure? Ina da ilimin addini, na fito daga gidan mutunci, ina da sana’a, ina da gidan kaina…me ya rage kuma?”

Shiru Rafiq yayi saboda baisan ta inda zai fara ba, saboda kanshi na mishi wani irin ciwo. 

“Saboda me Rafiq… Ka faɗa min ina jinka.”

Muneeb yake fadi ranshi a matuƙar ɓace. 

“Rafiq…”

“Saboda kuɗin ku bai kai ba! Saboda babanka ba kowa bane a Nigeria!”

Rafiq ya faɗi cikin ɗaga murya. Dana sani na lulluɓe shi saboda yanayin da yake gani a fuskar Muneeb ɗin. 

“Muneeb…”

Rafiq ya fara, hannu Muneeb ya ɗaga mishi alamar baya son ji. Muryarshi ɗauke da mamaki, ɓacin rai, da abubuwa fiye da wanda kalamai za su iya misaltawa ya ce, 

“Ko a mummunan mafarki ban taɓa tunanin za ka min gorin arziƙi ba Rafiq…ko baka faɗa min ba nasan ni kaɗai ne talaka a cikin ku, wallahi ba saika tuna min ba ina sane, ina sane da cewar karatuna dukkan shi kaine, rufin asirin dana samu har nake kula da ƙannaina da iyayena kaine… Ban taɓa zaton za ka goran ta min ba…”

Har a zuciyarshi Rafiq yake jin ciwon da Muneeb yake ji, ƙirjinshi har zafi yake mishi. Sai da Muneeb ɗin ya zagaya ya zauna kan kujerar office ɗin nashi tukunna ya sake kallon Rafiq da faɗin, 

“Za ka iya tafiya, ka faɗa min abinda ka zo yi…sai dai ikon bayar da aurenta ba a hannunka yake ba, zan yi trying wajen Daddy, bazan ji kamar ban mana wani ƙoƙari ba…”

Kallon shi Rafiq yake yi sannan ya ce, 

“Na ɗauka ka sanni kamar yadda kake tunanin na san ka, na ɗauka za ka iya faɗar abinda zan iya da wanda bazan iya ba…”

“Mutane na canzawa da duk rana, kuma zaka san abinda suka nuna maka ne kawai…”

Girgiza kai Rafiq ya yi. Shi ba mutum bane mai yawan surutu, duk cikin abokanshi Muneeb ya fi saninshi akan kowa. Amma ba kowanne maganganu suke haɗa shi da Muneeb ɗin ba. Yau ya zama dole yasan wani abu. Dole ya fahimtar da shi, bayan rasa Zafira, ba zai bari Muneeb ya sake rasa abokin shi ba. Ko ba komai yana buƙatar wanda zai taimaka mishi jinyar rashin Zafira. 

“Gori shi ne ƙarshen abinda zai haɗa ni da kai Muneeb, inda zan iya mantar da kai duk abinda ka lissafa na taɓa yi maka zan yi… Saboda bana maka bane don n ka dinga tunawa ko da yaushe, na yi ne saboda zumuncin da ke tsakanin mu…”

Ganin yayi shiru yasa Rafiq ci gaba da faɗin, 

“Matsayin babanka da ko waye shi a Nigeria ne abu na farko da Daddy zai fara dubawa, sai kai ɗin da kanka, me kake da shi? Waye kai? Wanne mataki ka kai a rayuwa? Wannan su ne abinda zai duba kafin addininka, kafin martabar gidan ku…”

“Rafiq…”

Muneeb ya soma muryarshi daban haƙuri saboda ya fara fahimtar Rafiq ɗin yanzun. 

“Ka bari in gama… Ko ca akai in zaɓar wa Zafira miji bazan iya zaɓo kamarka ba, Muneeb kana da halayen da ni dakaina nake son samu. Ina sonka da ƙanwata, wallahi ina son ka da auren Zafira… Na damu da me yasa baka faɗa min daga farko bane saboda in maka bayanin nan, saboda ka bar son da kake mata iya kai kaɗai ba saika janyota cikin abinda ba zai faru ba…”

Dafe kai Muneeb yayi da hannuwanshi duka biyun. 

“Innalillahi wa inna ilaihir raji’un…”

Shine abinda yake faɗi yana maimaitawa ko zai samu dai-daito a duniyar da yake jin ta birkice mishi lokaci ɗaya. 

“Ka yi haƙuri…”

Rafiq ya faɗi saboda bai da wasu kalaman da zai iya faɗa wa Muneeb ɗin don ya ji sauƙin abinda yake ji. 

“Rafiq… Ka taimaka mana.. Don Allah ka yi wani abu akai. Wallahi ina son ta…”

Muneeb yake roƙon Rafiq ɗin yana jin kamar zuciyarshi zata faɗo. Miƙewa Rafiq ya yi. 

“Ka yi haƙuri…”

Juyawa ya yi yana nufar ƙofa, da gudu Muneeb ya taso ya sha gabanshi kamar wanda ya samu taɓin hankali. 

“Ka ce min za kai wani abu… Ka ce min bazan rasata akan wannan dalilin ba…”

Rafiq kauda kan shi yayi saboda baya son ganin yanayin da Muneeb yake ciki ko kaɗan. Ya raɓa shi ya buɗe ƙofar ya fice daga office ɗin. Ya fi mintina goma zaune cikin mota ba tare da ya san asalin abinda yake tunani ba, tukunna ya samu ya tayar da motar yana nufar gida.

Yana zuwa ɓangaren shi ya wuce ya saka wa ɗakin mukulli. Ɗan ƙaramin littafin da yakan rubuta matsalolin da yake da su ya duba wanda ya kamata ya fara takai ya ɗauko. Ya rubuta Muneeb, yana sokewa don ya riga da ya mishi bayani, ya kuma san zai fahimta. Tukunna ya rubuta Zafira, matsala biyu ne a tare da ita, yadda zai faɗa mata auren su da Muneeb ba zai yiwu ba, sai kuma yadda zai samu ta koma dai-dai. 

Sannan ya rubuta Daddy, shima abu biyu, yanda zai haƙura da aurar da Zafira, da kuma yadda zai samu ya bari ta zaɓi wani mijin da kanta, wanda zai so, ɗan gidan wani babban ɗan siyasa ko hamshaƙin mai kuɗi. Littafin ya ajiye gefenshi ya kwanta yana rufe idonshi ko zai samu nutsuwar fuskantar Daddy anjima.

<< Alkalamin Kaddara 9 Alkalamin Kaddara 11 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×