Skip to content
Part 19 of 52 in the Series Alkalamin Kaddara by Lubna Sufyan

India

Kwanansu na huɗu kenan a ƙasar, kallo ɗaya zakai ma kowa a cikinsu ka ga ramar da ke tattare da fuskarshi da rashin kwanciyar hankali. Aiki uku aka yi ma Rafiq saboda kumburin da ƙwaƙwalwar shi take yi ta ciki. Likitocin na faɗa musu cewar akwai alamun samun nasara, maganar farkawarshi kuwa zai iya faruwa kowanne lokaci, Nuri ce ma da tambayarsu ko zai iya kai yaushe, Fawzan ya ce su ci gaba da mishi addu’a don shi kaɗai ne ya fahimci girman raunukan da Rafiq ɗin ya samu. 

Robar ruwa Aroob ta miƙa wa Naadir da ke zaune kan ɗaya daga cikin kujerun asibitin. Washegarin ranar da suka isa India ya je shima. Zafira ce kawai bata zo ba, kullum ta kira waya sai ta yi kuka, Daddy yaso ta zo ko hankalinta zai kwanta, Omeed yace bata da lafiya. Naadir kam tunda ya zo ya kasa shiga ɗakin da Rafiq ɗin yake sai dai ta window yake hango shi, wuni yake yi kuka, babu wanda yai ƙoƙarin lallashin shi, idanuwa kawai suke saka mishi. Ruwan ya bi da kallo, kafin ya karɓa ya saka ɗayan hannunshi ya ja hancin shi da ke mishi zafi. Kusa da shi ta zauna tana ɗan dukan kafaɗarshi da tata. 

“Ya isa haka Naadir…”

Ta faɗi muryarta a sanyaye, hannunshi yasa da sauri yana goge hawayen da suka zubo mishi. Baisan yadda zai fara daina kuka ba, a tsorace yake sosai tunda aka kira aka faɗa mishi haɗarin, daga farko ya ɗauka ɓoye mishi suke yi Rafiq ɗin ma ya rasu, da ya zo ɗin ma a yanayin da ya ga Rafiq ɗin banbancin shi da gawa kaɗan ne. 

“Ki ce min zai tashi, ki ce min babu abinda zai same shi…” 

Shiru Aroob ta yi, ba zata iya faɗa wa Naadir abinda bata da iko akai ba, ita kanta inda zata samu wannan tabbacin da yake nema hankalinta zai kwanta, zata yi bacci zuciyarta babu nauyin da take tare da shi yanzun. Su hotel Daddy ya kama musu, Nuri kam ta ƙi barin wajen Rafiq, ko ɗakin bata fitowa, likitocin ma in sun shigo basa cewa ta fita. In ta bar kusa da gadonshi sallah zata yi ko banɗaki zata shiga wani uzurin. 

Fawzan ne ya ƙaraso inda suke shima, hannunshi da chocolate ɗin Dairy milk babbar yana ci ya samu waje ta ɗayan gefen Naadir ya zauna, kallon shi Naadir ya yi a kasalance ya ce, 

“Saika lalata haƙoran ka, tunda na zo kake shan zaƙi.” 

“Likita ne Naadir, ya fika sanin zai lalata haƙoranshi.” 

Aroob ta faɗi, don ita bama haƙoran Fawzan ɗin take ji ba, cikin shi, ciye-ciyen da yakeyi ya wuce misali. 

“Da gaske ya kamata ka rage zaƙin nan kafin yai maka illa…” 

Sai da ya sake gutsurar chocolate ɗinshi ya tauna tukunna ya kalle su yana faɗin, 

“Ku ƙyaleni…”

Baisan yadda zai rage damuwarshi ba, sun sha kukan su, shi ya kasa, ba wani aiki yake yi ba tunda suka zo banda shiga ya ga Rafiq da baya ganin alamar ci gaba a tattare da yanayin shi. Ciye-ciyen da yake yi na rage mishi damuwa, ƙwaƙwalwar shi na tunanin wani abu banda halin da Rafiq yake ciki, yana tattara wani ɓangare cikin hankalinshi akan abinda yake ci, baya zaton in yai musu bayani za su fahimta don shima bai gama fahimta ba. 

“Yaya… Da gaskiyar Naadir ka…”

Aroob ta fara, a tsawace Fawzan ɗin ya katse ta,

“Na ce ku ƙyale ni! Me yasa ba za ku barni bane ba?” 

Su duka kallonshi suke cike da mamaki, don lokacin ne karo na farko da suka ga ya yi hargowa irin haka. Abin na musu wani iri. 

“Mun damu ne kawai, ka yi haƙuri.”

Naadir ya ƙarasa, idanuwanshi cike taf da hawaye, robar ruwan da Aroob ta bashi ya ajiye yana miƙewa ya bar musu wajen. Idanuwa Fawzan ya lumshe ya miƙe yana bin bayanshi. 

“Naadir…Naadir…”

Yake kira yana ƙara sauri ya riƙo hannun Naadir ɗin daya juyo. 

“Menene?”

Ya tambaya. 

“Naadir mana, damuwa ce tai min yawa.”

“Damuwa ta yi wa kowa yawa Yaa Fawzan. Amma babu wanda ya zaɓi ya kashe kanshi saboda haka…” 

Hannun Naadir ɗin ya saki

“Ba kashe kaina nake ba.”

Wani kallo Naadir ɗin yake mishi da ke fassara ‘Da gaske?’ 

“Ba kashe kaina nake ba.”

Fawzan ɗin ya sake maimaitawa

“Wannan chocolate ɗin guda nawa ka sha daga safe zuwa yanzun? Iya na yau kawai banda na jiya, banda ranar da na zo… Kaci wani abu banda shi duk yau? In ba kashe kanka kake yi ba me kake yi?” 

Naadir yake tambaya ranshi a ɓace. Numfashi Fawzan ya sauke 

“Yana rage min damuwa.”

Kai kawai Naadir ya ɗaga mishi yana shirin juyawa. 

“Ina zaka je?”

“Ba nisa zan yi ba.”

Shi ne abinda Naadir ɗin ya faɗi yana wucewa. Numfashi mai nauyi Fawzan ya saki a karo na ba adadi yana juyawa shima ya koma inda ya baro, yana zama ya buɗe baki kenan zai yi magana Aroob ta rigashi da faɗin, 

“Karka damu na fahimta. Nima neman wanda zan ma ihu nake yi.” 

“Zuciyata ta min nauyi Aroob, kamar in cire in ajiyeta gefe nake ji.” 

Murmushin ƙarfin hali ta yi. 

“Ɗazun wasu nata hira suna dariya…”

Shima murmushin ya yi da bashi da alaƙa da nishaɗi ko kaɗan. 

“Rayuwar kenan, baƙin cikin wasu baya hana farin cikin wasu, duniyar wasu ba zata tsaya don ta wani ta samu matsala ba..” 

“Hakan na tsoratani, sosai hakan yake tsorata ni.” 

Ɗan ɗaga kafaɗa Fawzan ya yi. 

“Yan uwan Samira binne ta suka yi, suka dawo gida kuma suka haƙura, muna ganin shi har yanzun…” 

Kai Aroob ta jinjina, har lokacin mutuwar Samira na mata wani iri, kamar mafarki. Jikinta ya yi sanyi sosai, sanin cewa ganin da suke ma Rafiq ɗin ba shi bane zai hanashi mutuwa ba a kowanne lokaci Allah yaso hakan. 

“Zai iya tafiya a kowanne lokaci shima, Yaya zai iya mutuwa shima…” 

Aroob ta ƙarasa maganar muryarta na karyewa, hakan yasa Fawzan sauke numfashi yana faɗin, 

“Muma haka, za mu iya mutuwa kowanne lokaci, zamu iya riganshi duk da lafiyar mu ƙalau… Baki ga Imaan ba?” 

Kai ta jinjina mishi tana saka hannu ta goge hawayen da suka tarar mata a idanuwa. Babu wani abu na rayuwa da yake da tabbas, mutuwa bata jiran wani yanayi kafin ta kawo maka ziyara, zata iya ɗaukarka kana zaune, tsaye, kwance, zata iya ɗaukar yaro ko babba ko tsoho, mai lafiya ko akasin hakan, bata jiran dalilin da ya wuce cikar lokaci. Hakan Aroob ta fahimta yanzun nan. 

“Mu koma gida Yaya… Daga ko’ina addu’ar mu zata same shi.” 

Shiru Fawzan ya yi, abinda yake tunani kenan da safiyar ranar, babu wanda yasan ranar tashin Rafiq. Nuri tana tare da shi, zamansu ba zai ƙara mata komai ba sai damuwa. 

“Rayuwar zata yi mana wani iri Babu Yaya Rafiq, bansan ta ina zamu fara ba.” 

Aroob ta sake faɗi, wannan karon tana barin hawayenta suna zubowa. Hannunta Fawzan ya kama yana dumtsewa cikin nashi. 

“Za mu iya, kafin ya tashi ne kawai. Komai zai dai-dai ta.” 

“In sha Allah, komai zai dai-dai ta.”

Aroob ta ce tana sauke numfashi. Naadir suka hango da lemon gwangwani a hannunshi yana ƙarasowa inda suke zaune tare da buɗe lemon yana saka abin zuƙa a ciki, ko zama bai yi ba Aroob ta fisge lemon. 

“Aroob mana…”

Naadir ya faɗi yana zama, zuƙar lemon ta yi tana haɗiye shi da ƙyar, duba gwangwanin take yi tana ƙoƙarin karantawa Fawzan ya karɓe, sakar mishi ta yi tana kallon shi, yana zuƙa ya furzo shi, hakan yasa Aroob matsawa kar ya ɓata ta, da sauri ya miƙa wa Naadir da ke dariya, karɓa ya yi ya ci gaba da sha hankali a kwance. Kallon shi Aroob ɗin da Fawzan suke, kafin Fawzan ya ce, 

“Wannan yaron akwai harshe a bakin shi kuwa?” 

Girgiza kai Aroob ta yi. 

“In akwai ma baya aiki.”

Dariya Naadir ya yi. 

“Babu Sugar a ciki ne shi yasa.”

“Bansan me yake damunku kai da Yaya Rafiq ba, me Sugar yai muku?” 

Fawzan ya tambaya, shi ba marar lafiya ba, bai ga dalilin da zai sha abu babu sugar ba, har addu’a yake Allah kar ya ɗora mishi lalurar da za’a hana shi shan Sugar. 

“Kawai damuna yake ne shi yasa.”

Girgiza kai Aroob ta yi cike da tausayawa rayuwar Naadir ɗin da take ganin baisan daɗi ba. 

“Tsaya, kaima ba ka son sanyi ko?”

Murmushi yai mata yana ɗan daƙuna fuska. 

“Waye yake son sanyi?”

Kai Fawzan ya zuro don ya ga fuskar Naadir ɗin sosai yana faɗin, 

“Abin sanyi take nufi Dumb-Dumb, lemon hannunka ma babu sanyi.” 

Sai da ya ƙarasa shanye lemon shi tukunna ya ce, 

“Ba sosai ba.”

Dafe kai Aroob ta yi da hannu, Fawzan kuma yana taɓe baki yake girgiza ma Naadir din kai. 

“Ko ni da nake da asthma ina rayuwa mai daɗi.” 

Dariyar da ke cike da rashin yarda da abinda suke faɗi Naadir ya yi. 

“Na kasa yarda da ku biyun nan, akwai abubuwa masu daɗi banda kayan sanyi da zaƙi.” 

“Faɗi guda uku.”

Aroob ta ce da sauri. 

“Kayan marmari, nama…”

“Naadir… Naadir karka fara saka nama, baka son maiƙo.” 

Fawzan ya faɗi a gajiye. 

“Bana son maiƙo saboda kasala yake samin.”

Nuna shi da hannu Aroob ta yi tana cewa, 

“Yaron nan ba mutum bane ba Yaa Fawzan… At all ba mutum bane ba.” 

Fawzan baisan lokacin da ya yi dariya ba, suma dariyar suke, mamaki yake yi don jin dariyar daga zuciyarshi ta fito, tabbas a tare da kowanne tsanani akwai sauƙi, mantuwa na cikin ni’imomi da Allah ya yi ma bayin shi, ko da ba dauwamamiya ba kuwa, don yanzun nan ‘yan daƙiƙu Allah ya mantar da su damuwar da suke ciki sun yi dariya, numfashi ya sauke suka ci gaba da hira a hankali. 

***** 

Tsaye suke a bakin ƙofar ɗakin, Fawzan rataye da jakarsu shi da Aroob a kafaɗarshi. Nuri suke son yima sallama tunda ranar za su wuce, Naadir kuma sai da yamma. Shi suke ta fama da shi don ya shiga ɗakin ya yi tsaye bakin ƙofa. 

“Naadir in muka shiga tare mu duka zai fi maka sauƙi.” 

Aroob ta faɗi a tausashe. Girgiza mata kai ya yi yana goge hawayen da sunƙi daina zubar mishi. 

“Idan na shiga zan ganshi, komai zai tabbata ya faru…” 

A ƙufule Fawzan ya ce, 

“Glass ɗin da ke tsakanin ku ba zai canja komai ba, ba zai canja cewar yana kwance a gadon asibitin can ba, ba zai canja yiwuwar samun matsala ba inya tashi kenan… Babu abinda zai canja.” 

Kallon Fawzan ɗin Aroob ta yi, 

“Yayaa…”

Ta kira cikin son ya bi Naadir ɗin a hankali, hannun ƙofar Fawzan ya kama yana murzawa ya shiga yabarsu nan tsaye. 

“In ba zaka iya shiga ba, ka yi zamanka anan. Ko daga ina kake addu’ar ka zata isar mishi.” 

Aroob ta ƙarasa tana shiga ɗakin itama. Ƙofar Naadir yake kallo, tsoron shiga yake yi, tsoron ganin Rafiq a yanayin da yake ciki yake. Har ranshi yana jin wahalar da rayuwa zata yi mishi in babu Rafiq, kasancewar shi yasa Naadir bai taɓa jin kewar Nuri ba ko Daddy. Baima san yadda zai fara nufarsu da matsalolinshi ba. Idanuwanshi ya lumshe yana maida numfashi tukunna ya tura ƙofar yana shiga. 

Yana buɗe idanuwanshi ya sauke su kan fuskar Aroob da ke mishi murmushi tana ɗan ɗaga mishi kai cikin son bashi ƙarfin gwiwar cewa komai zai yi dai-dai. Takawa yayi yana ƙarasawa inda Rafiq ɗin yake kwance jikinshi duk wasu wayoyi, sai abin abinci ta hancin shi, yayi wani irin fari kamar babu jini a jikinshi, hannu Naadir yakai dai-dai hancin Rafiq din ya ji ko yana numfashi don bai ga alamar hakan ba. 

Daga Aroob, Fawzan har Nuri kallon shi suke, da alama ya ji abinda yake son ji ɗin, don hannunshi ya sauke yana kallon Rafiq ɗin, muryarshi da wani yanayi yake faɗin, 

“Yaya karka barni yanzun don Allah, wa zan faɗa wa matsalata? Ka warke, za ka warke, babu abinda zai sameka saboda ban san yadda zan yi ba ni, Daddy ba zai taɓa sauraran matsalata ba…Nuri zata yi abinda Daddy yake so ko da yaushe…” 

“Naadir…”

Fawzan ya kira cike da kashedi, Nuri ta ɗaga wa Fawzan ɗin hannu alamar ya ƙyale shi, ta saka hannu ta goge hawayenta, ba tun yanzun ta san basa buƙatar kulawarta ba, basa zuwa mata da matsalarsu ko kaɗan, gara ma sauran akan Naadir. Rafiq ne komai na yaron, don ko rainon shi bata wahala ta yi ba, Rafiq ya sha tafiya da Naadir garuruwa su yi kwanaki saboda ba zai zauna a gida in baya nan ba, zaita kuka. 

Ko ciwon maganganun da ya faɗa bata yi ba, Rafiq na buƙatar ta, hakan kawai ya isheta. Shi yasa take addu’ar ya tashi, ya samu sauƙi bata san ya filin duniyar zai zamar mata in babu ɗanta a ciki ba. Ci gaba da maganarshi Naadir ya yi. 

“Ko don ni kawai ka tashi don Allah, don ni kawai, su Yaya Fawzan sun girma su… Nikam ina buƙatar ka wallahi.” 

“Duka muna buƙatar shi Naadir ba kai kaɗai ba.” 

Aroob ta ƙarasa tana goge hawayenta. 

“Me yasa za ku tafi?”

Nuri ta tambaya muryarta can ƙasa. 

“Duniya ba zata jira mu komai ya dai-dai ta ba Nuri, ina da aiki da yake buƙatar zuwana, Aroob na da makaranta nan da jibi, Naadir ma haka…” 

Maganganun da Fawzan ɗin ya faɗi gaskiya ne, sai dai tana ganin Rafiq ya fi komai muhimmanci a yanzun. Don haka ta ce, 

“Komai zai iya jiran ku, aikin ka babu matsala in Daddy ya yi magana, haka makarantar Aroob. Naadir ne kawai…” 

Kai Aroob ta girgiza. 

“Yaya baya so muna amfani da sanayyar Daddy ko kuɗin da yake da shi. Ya ce mu dinga yin abinmu kamar kowa… Akwai abubuwa da yawa da kuɗi da sanayya basa aiki akai.” 

“Kamar lafiyar Yaya yanzun… Kuɗi ba za su iya siyar mishi ita ba.” 

Fawzan ya ƙarashe ma Aroob yana ɗorawa da, 

“Zaman mu bazai canza yanayin shi ba, tafiyar mu ma haka. Da kanshi zai so mu yi wani abu da rayuwar mu bamu tattaru anan ba Nuri, daga ko ina addu’ar mu zata iso mishi.” 

Fawzan ne yake magana amma idanuwan Nuri na kan Rafiq ɗin, don tana jin maganganun shi ne a cikin muryar Fawzan, tarbiyar su tashi ce, ta bashi dukkan kulawa shi kuma yana basu fiye da yadda ita ɗin zata iya, girmansu da hankalinsu na bata mamaki, sai yake mata kamar yanzun ne suke ‘yan yara, ta kauda kanta tana juyowa ta ga sun girma bata san ya aka yi rayuwa ta kawosu wajen ba. 

“Zai yi alfahari da ku a ko’ina.”

Ta faɗi da hawaye a idanuwanta. 

“Muma muna alfahari da shi a ko’ ina.”

Naadir ya faɗi. Aroob ce ta matsa kusa da Rafiq ɗin. 

“Allah ya baka lafiya Yaya… Zamu dawo in sha Allah, zamu dawo mu tafi da kai gida.” 

Ɗan jim ta yi tukunna ta koma baya tana bama Fawzan damar matsowa shima. 

“Zamu tafi saboda lokaci ya yi tsaye anan Yaya, zaman jiran ka tashi zai zamar mana matsala, lokacin baya tafiya in muka jira…zamu tafi ne don mu ga saurin shi. Allah ya baka lafiya, in sha Allah za mu dawo kamar yadda Aroob ta faɗi… Za mu dawo.” 

Fawzan ya ƙarasa yana jin wani abu mai nauyi ya tokare mishi zuciya. Aroob ya ɗan kalla, ta ɗaga mishi kai alamar su tafi. Nuri ya kalla yana fadin, 

“Ki kula da kanki Nuri. Yaya na buƙatar ki fiye da ko yaushe yanzun. Muna sonki mu duka kin sani ko?”

Kai kawai Nuri ta iya ɗaga mishi, Aroob ce ta ƙarasa tana rungume Nurin sosai, ta cikin hakan take son faɗa mata duk maganganun da bata san yadda zata ɗora su kan kalamai ba. Tana ɗagowa Daddy na shigowa don tare za su wuce da su Fawzan ɗin. Nuri kawai za su bari tare da Rafiq. 

“Kun gama ko?”

Daddy ya tambaya, 

“Eh mun gama.”

Aroob ta amsa musu, tana ƙarasowa ta rungume Naadir. 

“Ka kula da kanka. Za mu yi waya.”

Kai kawai ya iya ɗaga mata saboda kukan da yake yi. Fawzan kuwa da ya ƙaraso hannunshi yasa cikin sumar Naadir ɗin yana hargitsawa, hakan nasa Naadir ture hannun Fawzan ɗin yana zagaya nashi ya rungume Fawzan. 

“In kana da matsala ka kirani. Nasan bazan iya zama kamar Yaya ba, amma zan kwatanta…” 

Fawzan ya faɗi a hankali. 

“Kafinu Yaya ya tashi…”

Kai Fawzan ya ɗaga ma Naadir ɗin yana maimaita, 

“Kamun Yaya ya tashi…”

Tukunna ya zame jikinshi daga na Naadir ɗin yana bin bayan Aroob suka fice daga ɗakin. Naadir ma binsu ya yi suna ba wa Daddy da Nuri waje don su yi magana. Ya kai mintina goma kafin ya fito, har bakin ƙofar asibitin Naadir ya raka su suka hau taxi ɗin da zata kaisu airport tukunna ya koma ciki. 

Bayan Wata Uku 

India

Zaune take kan darduma tana karatun Qur’an. Tunda ta yi sallar asuba take nan zaune, don karatun kan ɗebe mata kewa, duk sati biyu Daddy yake zuwa ya kwana ya koma. Su Fawzan kuma sai su yi waya sau nawa a rana, wata rana zata saka a speaker ne su yi ma Rafiq magana tunda likitoci sun ce duk da bai tashi ba akwai yiwuwar yana jin duk abinda ake yi kuma hakan zai taimaka mishi sosai. 

Zata iya cewa ana samun ci gaba don ciwukan da ke jikinshi su ne take ganin suna warkewa. Wata irin ƙara take ji kamar shigowar saƙon waya, kafin ta gama gane daga ina ne, likitoci wajen guda shidda sun shigo ɗakin sun yi kan Rafiq cikin yanayin da yasa Nuri miƙewa daga kan dardumar don ta ga me yake faruwa, ga zuciyarta da ke wata irin dokawa kamar zata fito daga ƙirjinta. 

Wayarta ke ƙara akan kujerar da take tsaye a gefe, cikin likitocin wani ya juyo yana kallonta, kafin ya mayar da hankalin shi kan Rafiq ɗin. Dubawa ta yi ta ga Fawzan ne, hakan yasa ta fita daga ɗakin sannan ta ɗaga wayar. 

“Nuri, kun tashi lafiya?”

Fawzan ya faɗi. Muryarta na rawa ta amsa shi da, 

“Bansani ba dai….Rafiq ne…”

“Me ya same shi? Me suka ce ya sami Yaya Rafiq ɗin?” 

Yake tambaya hankalinshi a tashe. Ta window ɗin Nuri ta leƙa, har lokacin suna kan Rafiq. 

“Bansani ba Fawzan, wallahi bansani ba ga likitocin can suna duba shi.” 

“Innalillahi wa inna ilaihir raji’un…”

Fawzan yake faɗi cikin tashin hankali yana ɗorawa da, 

“Bari in kira Daddy….mu ga ko zai yiwu mu taho tsakanin yau da gobe.” 

Kai Nuri take iya ɗaga mishi duk da ba ganinta yake ba, wani abu ya tokare mata maƙoshi ya hanata magana. Shi ya katse kiran daga ɗayan ɓangaren. Batasan iya lokacin da ta ɗauka a waje tana kai-kawo ba. Sai da ta fara ganin fitowar likitocin daga ɗakin tukunna ta zuba musu ido, ɗaya daga cikinsu ne ya ƙaraso inda take fuskarshi ɗauke da murmushi yake mata magana cikin harshen turanci, 

“Ina taya ki murna, yaronki ya tashi, daga dukkan alamu babu wata matsala. Amma yana buƙatar wadataccen bacci don ƙwaƙwalwar shi ta samu dai-daita, mun mishi allura. In ya farka karkiyi mishi magana ko ya zai jima bai ce komai ba, ki ƙyaleshi sai ya fara magana da kanshi tukunna…” 

Wani irin numfashi Nuri ta sauke hawayen farin ciki na zubo mata. 

“Alhamdulillah…”

Take jerawa babu adadi, tana dafa bangon wajen ta tsugunna saboda ƙafafuwan ta sun yi sanyi sosai. Rahmar Allah ce da ta gani a lokacin da bata taɓa zato ba, zata yi ƙarya in ta ce bata tsorata da ciwon Rafiq ba, musamman da ta ga ya jima bai ko motsa ba. Da ƙyar ta samu ta miƙe tana kiran lambar Daddy. Bugun farko ya ɗaga yana faɗin, 

“Hafsatu…”

Kamar yadda yake kiran ta. 

“Rafiq ya farka… Yanzun nan… Yana bacci amma ya farka.” 

Tana jin numfashin da Daddy ya sauke ta cikin wayar. Ya ma kasa magana, muryarshi ɗauke da wani irin yanayi ya ce, 

“Oh Allah na…kinsan na haƙura? Kullum saina faɗa wa kaina Rafiq lokaci kawai yake jira… Wallahi komai zan yi yaron nan yana maƙale a zuciyata, sai ma na zo yin ƙaramin abu da shi ɗin kawai zan kira yai min duniyar ke min duhu.” 

Murmushi Nuri ta yi. 

“Duk duhun da take maka bai kai nawa ba, kafi kowa sani, ba don bana ƙaunar su Fawzan kamar raina ba, amma Rafiq shi ya fara wanke mon gorin juya a wajen danginka…” 

‘Yar dariya Daddy ya yi.

“Dangina ni kaɗai ko?”

Da murmushi a fuskar Nuri ta ce, 

“Karka ce ban maka kara ba, dangin mu.”

“Yawwa ko kefa, za mu taho in sha Allah zuwa gobe ko jibi da yaran gaba ɗaya.” 

Jinjina kai Nuri ta yi. 

“Fawzan ya ce zai kiraka dama.”

“Bai kira ba text ya min wai ko zai yiwu shi da Aroob su taho yau ko gobe.” 

Numfashi Nuri ta sauke a hankali, zuciyarta na mata wani sanyi da yanayin alaƙar yaran da Daddy, Rafiq ne kaɗai yake da ƙarfin halin kiran Daddy kai tsaye in dai wata buƙatar ce, ta tabbata da Rafiq ɗin na nan yanzun ko text ɗin da Fawzan bai yi ba tasan shi zai kira. 

“In ya sake tashi sai ki kirani mu gaisa da shi.” 

“In sha Allah, ka kula da kanka.”

Nuri ta fadi, ya amsa da,

“Ke ma ki kula da kanki da Rafiq ɗin. Allah ya ƙara lafiya.” 

Amsawa ta yi da amin tana katse kiran. Sai da ta koma ɗakin ta zauna tukunna taima Fawzan text cewar Rafiq ɗin ya farka. Bai kira ba hakan ya sanar da ita cewar ya ajiye wayar yana aiki ko wani abin dai. Zama ta yi ta saka Rafiq a gaba tana jero Hamdala da zata ci gaba da yin ta har ƙarshen rayuwarta na ƙarin aron lokaci da Allah ya ƙara basu tare da Rafiq ɗin. 

***** 

Idanuwanshi yake so ya buɗe da yake ji kamar an manne su da gam saboda nauyin da sukai mishi, ya ma fi jin nauyin kanshi sosai. Da ƙyar ya samu yana buɗe idanuwan, dishi-dishi yake gani kafin a hankali ya fara ganin fari-farin abu kamar bango, sake runtsa idanuwanshi ya yi kafin ya buɗe su sosai. Bango ne yake gani, wuyanshi da yake ji kamar baya haɗe da jikinshi ya juya a hankali yana kallon gefe. 

Nuri ya gani a zaune tana mishi murmushi, kallonta yake yana so ya yi magana amma harshen shi kamar an ɗaure da wani abu, sautin ma da zai samu ya fito da shi ya kasa, yana jin kamar lokacin ne zai fara koyan maganarshi ta farko. Cikin kanshi yana jin ya faɗi sunanta da yake son kira a fili amma abin ya gagara. Ji ya yi kamar ya yi amfani da duka ƙarfin shi saboda gajiyar da yake ji a duk wata gaɓa ta jikinshi. 

Runtsa idanuwanshi ya yi yana son tuna abinda ya faru ko yake faruwa amma baya ganin komai sai fili, sake buɗe su yayi akan Nuri da yake so ta ce wani abu amma kallon shi take yi, yana ganin hawayen da ke zubo mata duk da murmushin da ke fuskarta. Baisan daga inda wani ƙaramin sauti ya fito mishi ba. 

“Nuri…”

Ya kira, ba don gaba ɗaya nutsuwarta na kan Rafiq ba ba zata ga laɓɓanshi da suka motsa da sunanta ba, don sautin shi ko kaɗan bai fito ba, wani nauyi ta ji ya ɗaga mata daga zuciyarta, wasu hawaye masu ɗumi na zuba daga idanuwanta tare da hakan. 

“Rafiq… Rafiq…”

Take kira muryarta ɗauke da wani yanayi mai wahalar fassarawa, hannunshi ta riƙo tana dumtsewa cikin nata, a karo na farko tunda suka zo asibitin da ta ji hannunshi ya dawo kamar nashi, da inta riƙe sanyin su kawai yakan karya mata zuciya. Tana jin kamar ba hannun mutum ta taɓa ba, ta kasa cewa komai saboda kukan da take yi sosai. Uwa ce kawai zata fahimci halin da take ciki a yanzun, farin cikin da zuciyarta take ciki ba zai misaltu ba. 

Maƙoshin shi Rafiq ya ji ya bushe kamar ya shekara bai sha ruwa ba, baya jin zai iya sake fito da wani sautin, hannun Nuri da ke riƙe da nashi ya girgiza, hakan yasa ta dawo da hankalinta duka kanshi, da hannunshi yai mata nuni cewar zaisha ruwa. Da sauri ta miƙe tana ɗaukar roba da kofi don ta zuba mishi ruwan ta bashi. Sai da ta taimaka mishi ya iya ɗan ɗagowa kaɗan yana shan ruwan kamar shayi saboda ji yake in yai sauri amai zai yi. 

Saida ya ishe shi tukunna ya janye kanshi, kofin ta ajiye tukunna ta taimaka mishi ya gyara kwanciyarshi. Idanuwanshi ya rufe saboda har lokacin suna mishi nauyi, bacci mai ƙarfi na sake ɗaukarshi. Tsaye Nuri take ta ji karar wayarta, ƙarasawa tayi ta dauka, murmushi ya kwace mata ganin Fawzan ne. Tana ɗagawa ya fara faɗin, 

“Nuri, ina Yayan? Yanzun na ga text ɗinki wallahi, ina shigowa gida na duba wayar… Yana ina? Aroob!” 

Ya ƙarasa maganar yana ƙwala wa Aroob kira kafin ya ci gaba da faɗin, 

“Ina yake wai? Kisa wayar a speaker mu yi magana da shi. Aroob! Kizo Yaya ya tashi…” 

Sai da Nuri ta ɗan janye wayar daga kunnenta. Ta mayar tana cewa, 

“Ya koma bacci yanzun”

“Nuri…. Yayan fa.”

Taji muryar Aroob.

“Malama ki ban wayata, muna magana ne.”

“Ka bari muna gaisawa… Nuri… Yaa Fawzan don Allah ka ƙyaleni mana, zan baka ka tsaya… Nuri ki mishi magana…” 

Girgiza kai Nuri ta yi. 

“Kusa wayar a speaker mana to.”

Ta faɗi a gajiye, don in suka fara babu ranar gamawa. 

“Nuri ta ce kabari a saka a speaker…”

Aroob ɗin take faɗa wa Fawzan. Da alama wayar suka saka a speaker. 

“Ina Yayan?”

Suka faɗa a tare. Numfashi ta sauke. 

“Bacci yake yi. In ya tashi zai iya magana zan kira ku. Ya makaranta Aroob? Fawzan ya aikin?” 

“Makaranta lafiya ƙalau.”

Aroob ta amsa, Fawzan na cewa

“Aiki gashi nan kamar kullum. Gidan babu daɗi wallahi, munata kewarku sosai.” 

“Sai mu kaɗai kamar mayu, ga Yaya Fawzan kamar kaza wajen…” 

Bata ƙarasa maganar ba da alama duka Fawzan ɗin ya kai mata. 

“Daga na faɗi gaskiya. Karfe takwas ka yi bacci…” 

“Kunga nima baccin zan yi. Anjima zan kira ku . Banda faɗa, ku kula da kanku.” 

Nuri ta faɗi bata jira amsarsu ba ta katse kiran tana sauke wayar daga kunnenta, fuskarta ɗauke da murmushi. Tashi ta yi itama tana zuwa ta kwanta saboda baccin da take ji, tana lumshe idanuwanta wani bacci mai cike da nutsuwa data manta rabon da ta yi irinshi ya ɗauketa.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 1 / 5. Rating: 1

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Alkalamin Kaddara 18Alkalamin Kaddara 20  >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×