Abuja
Gida Muneeb ya mayar da shi. Sai dai ya kasa shiga, hannunshi na kan handle ɗin ƙofar, ya jingina kanshi a jiki ya kasa turawa, yana son samun nutsuwa ko ya take kafin ya shiga cikin gidan, kashedin likita na cewar ya kwantar wa da Tasneem hankali yake tunawa, baisan yadda zai fara kwantar mata da hankali in nashi yana tashe haka ba, yasan komai ya canza a rayuwarshi. Dalilin hakan yake son sani saboda ya gaji da jira.
Abinda su Nuri ke ɓoye mishi yake son sani, abinda yasan ya faru tare da haɗarin da. . .
Dakyau.