Abuja
Gida Muneeb ya mayar da shi. Sai dai ya kasa shiga, hannunshi na kan handle ɗin ƙofar, ya jingina kanshi a jiki ya kasa turawa, yana son samun nutsuwa ko ya take kafin ya shiga cikin gidan, kashedin likita na cewar ya kwantar wa da Tasneem hankali yake tunawa, baisan yadda zai fara kwantar mata da hankali in nashi yana tashe haka ba, yasan komai ya canza a rayuwarshi. Dalilin hakan yake son sani saboda ya gaji da jira.
Abinda su Nuri ke ɓoye mishi yake son sani, abinda yasan ya faru tare da haɗarin da ya yi ya kasa tunawa yake son sani yanzun. Numfashi yake saukewa a hankali, kafin ya samu ƙarfin tura ƙofar. A hankali ya shiga cikin falon ya ma manta da takalma a ƙafafuwanshi sai da ya nufi ɗakin Zafira ya je bakin ƙofar tukunna ya zame su yana ƙwanƙwasawa. Jin shiru yasa ya tura kawai ya shiga. A kwance ya hangota kan gadon ta lulluɓe har kanta.
Ƙarasawa ya yi yana zama tare da kama bargon ya buɗe mata fuska, in ba rashin hankali ba ya zata yi numfashi ta rufe duk wata ƙofar da zata shaƙi iska. Kallonta yake tana bacci, wani irin tuƙuƙin kishinta na ɗawainiya da shi kamar zuciyarshi zata fito. Ko ina ya kalla a jikinta sai yake ganin kamar shatin hannuwan mazan duk da suka taɓa ta ne yake gani.
‘Tana ɗauke da ciki sati huɗu.’
Maganar likitan ta dawo mishi. Cikinshi ne a jikinta, jikin da wasu mazan suka gama taɓawa, fuskarta yake kallo, ranar farko da ya fara ganinta na dawo mishi.
*****
Bayajin daɗin komai ne ranar, shi yasa ya fito don ya miƙe ƙafafuwanshi. Tunda ya dawo Kano yakan yi hakan in ya dawo daga aiki ba shi da abinyi a gida. Ba abokai yake da su a garin Kano ba, Muneeb ne kawai shi kuma fiye da rabin rayuwarshi tana garin Abuja yanzun, mutanen da yake mu’amala da su a Kano daga wajen aikin shi ne sai kuma unguwarsu yaran da yakan aika da duk ƙannai ne ba sa’annin shi ba.
Don haka in ya ji kaɗaici ya ishe shi sai ya fito ya yi yawo abinshi. Tafiya yake kanshi na ƙasa, kamar an ce ya ɗago ya hangota, ba sosai yake ganin fuskarta daga inda yake tsaye ba, amma yanayin tafiyarta yasa shi kallon takalman da ke ƙafarta, baisan sa’adda murmushi ya ƙwace mishi ba, abinda ya kwana biyu bai yi ba in har ba waya suke da ƙannenshi ba.
“Me ya kaiki?”
Yai maganar shi kaɗai, don daga yanayin tafiyarta za ka ga yadda takalman ke bata wahala, ƙoƙarin mata baya gajiya da bashi mamaki, ta saka takalma marasa tsayi mana in ba zata iya tafiya da wannan ba, amma wannan wahalar da me ta yi kama, yana kallonta yana ci gaba da tafiya abinshi, ya ɗan ƙara sauri don haka kawai ya tsinci kanshi da son ganin fuskarta sosai. Wata irin gurdewa ta yi da yasa zuciyarshi dokawa da ƙarfin gaske yana ƙarasawa inda take a durƙushe da faɗin,
“SubhanAllah.”
Ɗago kai ta yi idanuwanta na sauka cikin nashi, yana jin yadda zuciyarshi ta daina tsallen da take yi tana wata irin nutsuwa waje ɗaya, kamar tana ɗaukar hoton fuskarta tana samun wajaje daban-daban a zuciyarshi ta manna mishi su, a haka kowa zaice idanuwanta basu da banbanci dana ‘yan Nigeria, baƙaƙe ne da yankansu dai-dai misali, ya ga mata da idanuwansu suka fi nata girma, fari da kyau da komai.
Amma akwai abinda yake cikin nata da yasa yake jin kamar zuciyarshi ta yi developing fikafikai ne tana ƙoƙarin tashi daga ƙarƙashin shi. Tsintar kanshi yai da faɗin,
“Baki ji ciwo ba?”
Saida ta girgiza mishi kai tukunna ta sauke idanuwanta daga cikin nashi. Tana saka yana jin kamar ta dawo dasu ya ƙara kallon cikin su ko na daƙiƙa ɗaya ne.
“Na gode.”
Ta faɗi muryarta na dirar mishi a kunnuwa da wani sauti mai nutsuwa. Gani ya yi ta gyara takalminta tana miƙewa kamar zata tafi.
“Baki faɗa min sunanki ba.”
Ya tambaya, mamaki na rufe shi, yana son sanin sunan nata, amma a tare da hakan yana son ta ɗan ƙara tsayawa karta tafi, ya jima bai ji nutsuwa irin wadda yake ji ba a yanzun. Zai iya cewa tun kafin haɗarin shi da ya canja komai. Baya son ta tafi haka kawai.
“In kana mamaki ne me yasa ka tambaya?”
Ta faɗi yanayin muryarta na canjawa ba kamar ɗazun ba, daƙuna fuska yake cikin rashin fahimta.
“Excuse me?”
Ya ce saboda bai gane me take nufi ba, wani irin kallo take mishi.
“Sunana nake nufi… me yasa ka tambaya?”
Kallonta yake wannan karon ba da mamakin maganarta ba, sai mamakin ƙarfin halinta, mata da yawa basa iya kallonshi haka su faɗa mishi magana ba tare da kunya ko alamar girmamawa ba. Wani abu yake ji yana faruwa a zuciyarshi, tana kuma sanar da shi da yarinyar da ya haƙura da tunanin zai samu ce tsaye a gabanshi yau.
“Saboda ina son sani. “
Ya buƙata yana tsare ta da idanuwa, yana kallon jarumtarta na narkewa da kallon da yake mata.
“Tasneem.”
Ta faɗi, sunan na zama a tare da shi.
“A nan unguwar kike?”
Ya sake tambaya don yasan ko yaushe tafiyarta zata yi, yana ganin yadda take mamakin tambayoyin da yake mata, kafin a hankali ta ɗaga mishi kai, muryarta yake son sake ji.
“Ki min magana da bakin ki.”
Sai da ta ɗan yi jim tukunna ta ce,
“Eh a nan unguwar nake, inka miƙe layin nan kwanar farko.”
Tana ƙarasa maganar ta wuce da sauri yana kallonta ta tare mota ta shiga, yana jin yadda motar ta wuce da ita a ciki tare da wani ɓangare na zuciyarshi.
*****
Motsin da ta yi ya yanke mishi tunanin da yake yi,yana kallonta, buɗe idanuwa ta yi tana sauke su a kanshi.
“Ya jikinki?”
Ya tambaya.
“Na ji sauƙi. Sannu da zuwa.”
Ta faɗi da sanyin murya, don kam ta ji sauƙin kamar yadda ta faɗa, har a jikinta take jin canji, magungunan da ta sha da baccin da ta ɗan samu har ƙwari ta ji, ta cikin bargon tasa hannu tana shafar cikinta, bai taso ba yana nan yadda yake, amma sanin akwai ɗa a ciki kawai yasa murmushi ƙwace mata. Da mamaki Rafiq yake kallonta, akwai dai-daito a rayuwarta da har take da ƙarfin halin yin murmushi. Yadda yake jin komai ya kwance mishi sai murmushin ya ƙara ɓata mishi rai.
Miƙewa ya yi daga gefen gadon yana nufar hanyar ƙofa, da idanuwa Tasneem ta bishi har ya fice daga ɗakin kafin ta mayar da su tana rufewa. Zata ɗauki duk wani hukunci da zai yi mata, ba zata dinga saka shi a zuciyarta ba balle ya ƙara mata ciwo, ba sai ya kula da ita ba, ta samu dalilin da zata kula da kanta yanzun. Zata yi komai don abinda ke cikinta.
Rafiq kuwa sai da ya ɗauko ruwa tukunna ya dawo falon ya kwanta, robar ruwan na riƙe a hannunshi ko buɗewa bai yi ba, jikinshi ya yi wani irin sanyi, a yanzun inda za’a tambayeshi ba zai ce ga asalin abinda yake damunshi ba. Saboda komai ma ji yake, gajiya, ɓacin rai, ƙunci, hargitsi, firgici duka sun haɗe mishi waje ɗaya. Yana jin wayarshi tai ƙara alamar shigowar saƙo. Bai bi ta kanta ba, saboda baya son motsa ko da hannunshi ne.
Ya jima a haka, kafin daga kwancen ya soma kwance robar ruwan, gudun kar ya sha a kwance ya biyo mishi ta hanci ne yasa shi tashi zaune, ruwan ya sha sosai tukunna ya rufe robar ya ajiye a ƙasa. Wayarshi ya zaro daga aljihu tukunna ya koma ya kwanta. Cire mukullin jiki yayi yana buɗe saƙon, ganin sunan Zafira yasa shi saurin dannawa don ya karanta saƙon:
‘Karka kira in ka ga saƙon nan Yaya. Amma ka zo ka ɗauke ni. Don Allah ka zo da sauri.’
Wata irin miƙewa yayi babu shiri yana sake karanta saƙon zuciyarshi na wata irin dokawa. Kiran wayarta yake shirin yi ya tuna ta ce in ya ga saƙon kar ya kira.
“Me yake faruwa ne haka Zafira? Baki min bayani yadda zan gane ba.”
Rafiq ɗin yake faɗi yana wucewa ya zira takalmanshi, zuciyarshi ta jima bata nutsu da auren Zafira ba, tunda ta yi auren a shekara biyu sau uku ya ganta, yanayin sanyinta ya ƙaru, a zatonshi aure ne ya ƙara nutsar da ita, sai yanzun da saƙon nan nata yake jin kamar ya yi babban kuskuren ƙin tambayarta sosai ko akwai wata matsala. Lambar Isah ya lalubo yana kiranshi, yana cikin gidan ma ashe wajen maigadi suna labari. Rafiq ɗin asibiti yace ya wuce da shi.
Suna hanya yana sake karanta saƙon Zafirar. Ta ce ya zo da sauri, yasan in ba babbar matsala bace ba zata ce haka ba, a cikin ƙannenshi ta fi kowa rashin buƙatar kulawa ko da tana yarinya, bata iya buɗe baki ta ce abu na damunta ba sai ya kai maƙura, ko rashin lafiya in ba kwanciya tai ba bata faɗa, ya manta akwai damuwa a tare da shi.
“Don Allah kar wani abu ya same ki Zaf, karki bari wani abu ya same ki, gani nan zuwa yanzun…”
Shi ne abinda Rafiq yake faɗi yana kiran wayar Nuri da ta ɗaga da faɗin,
“Rafiq…”
“Kuna asibitin ko Nuri?”
Ya tambaya.
“Eh muna nan. Lafiya dai ko?”
Kai ya girgiza kamar tana ganin shi
“Jikin Tasneem ɗin ne? Me ya faru?”
Nuri take tambaya cike da kulawa.
“Gani nan ma, yanzun zamu ƙaraso asibitin.”
Ya faɗi yana sauke wayar daga kunnen shi, ko mintina goma basu yi da gama wayar ba da Nuri suka shiga cikin asibitin, bai jira Isah ya gama parking ba ya buɗe ya fita, da sauri-sauri yake takawa yana shiga cikin asibitin, har ya ƙarasa ɓangaren da Fawzan ɗin yake yana kaiwa ɗakin ya tura, sai da ya shiga tukunna ya yi sallama. Su duka ukun a zaune ya same su.
“Rafiq me ya faru ne wai? Ka ɗaga min hankali.”
Nuri ta faɗi tana nazarin shi.
“Zafira ce.”
“Me ya sami Zafirar?”
Fawzan ya faɗi a razane. Aroob na ɗorawa da,
“Me ya sameta Yaya?”
Ta miƙe zata ɗauko wayarta. Hakan Rafiq ya gani yasa shi faɗin,
“Karki kirata Aroob, ta ce kar a kira. In zo in taho da ita gida kawai, in yi sauri…Nuri kar wani abu ya same ta.”
Rafiq ya ƙarasa maganar yana jin komai ya kwance mishi. Ruwan da ke jikin hannun Fawzan ya cire yana sakkowa daga kan gadon, tare da danne wajen da ya zare ruwan saboda jinin da yake fitowa.
“Muje Yaya…”
Fawzan ya faɗi, don bai ga amfanin tsayuwar da Rafiq ɗin yake yi ba, ta ce ayi sauri, Allah kaɗai yasan halin da take ciki.
“Fawzan…”
Nuri ta kira tana kallon shi, ta ma rasa abinda zata ce, a kwanakin nan tana yawan tunanin Zafirar haka kawai, ko da sun yi waya kuwa tana manne a ranta fiye da ko yaushe, sai dai take sakata a addu’a Allah yasa hakan alkhairi ne.
“Karki ce in zauna Nuri, don Allah karki ce in zauna. Hankalina ba zai kwanta ba wallahi.”
Fawzan ya ce. Rafiq kuma ita yake kallo yana son jin me zata ce , Nurin yake kallo don ko da yardarta ko babu zai je ya taho da ‘yar uwarshi. Amma yana son a karo na farko ta zaɓe su kafin Daddy, ta yi abinda take ganin shi ne dai-dai ba sai Daddy ya tabbatar mata ba.
“Nuri…”
Rafiq ya kira cike da roƙonta, yana buƙatar ya ji tana tare da su, don ya tabbatar Daddy zai ce abi a hankali ne, a kirata a ji me yake faruwa kar su je su taho da ita, amma zuwan shi ne dai-dai tunda duka sun san halin Zafira. Nuri ta fi kowa don bai taɓa ganin Zafira ta je mata da buƙata ba, in har ta yi ɗin ma wajenshi take zuwa.
“Kuje ku taho da ita.”
Nuri ta faɗi muryarta na rawa, hannunta da ke riƙe da wayarta na mata ƙaiƙayi da son ta kira Daddy, amma yau kam yayi haƙuri, ko da abin nan da ta yi zai zama kuskure, hargitsin da rayuwar Rafiq take ciki tasa ta zaɓe su a farko yau, numfashin da Rafiq ɗin ya sauke na sata jin ba zata taɓa dana sanin zaɓinta ba.
“Na gode Nuri… Na gode…”
Rafiq yake faɗi, kafin ya kalli Fawzan
“Muje mu ga jirgin ƙarfe nawa zamu iya samu zuwa Lagos yanzun nan.”
Fawzan takalmanshi ya saka ya ma riga Rafiq ɗin kaiwa ƙofa.
“Yayaaa.”
Aroob ta kira, juyawa suka yi a tare shi da Fawzan ɗin, sai da Fawzan ya ga ta nutsar da hankalinta kan Rafiq tukunna ya gane da Rafiq take.
“Karku baro ta. Don Allah karku barota.”
Kai Rafiq yake jinjina mata, ya faɗa wa Zafira sa’adda duk take son dawowa kiranshi kawai zata yi zai je ya ɗaukota. Yanzun kuwa lokaci yayi da zai cika wannan alƙawarin. Tare da Fawzan suka taka suna fita daga asibitin zuwa motar Rafiq ɗin, Isah ya ɗauke su zuwa Airport. Sai da suna hanya tukunna ya tura wa Nuri saƙo:
‘Tasneem Nuri. Ki tura mata Aroob don Allah.’
Harya ajiye wayar, ya kasa haƙura, ko ba komai akwai igiyar aure tsakanin shi da Tasneem, akwai yaronshi da yake jikinta. Ba zai ɗauki ƙafafuwanshi ya bar gari bai sanar da ita ba. Saƙon ya tura mata itama:
‘Tafiyar gaggawa ta kamani zuwa Lagos yanzun Neem, ki kula da kanki, Aroob zata zo ta taya ki zama. Bazan wuce kwana ɗaya ba.’
Har a zuciyarshi ya ji wani sanyi da saƙon da ya tura. Ya sauke haƙƙinta da yake kanshi.
*****
Kaduna
Tunda yai Sallar Asuba yake jin idanuwanshi da suke a kumbure da alamun rashin baccin da bai samu ba jiya. Wannan ne karo na biyu a rayuwarshi da bacci ya ƙaurace mishi. Ko tashi bai yi daga kan dardumar ba, ya dai jingina bayanshi da bangon wajen ne. Ƙarar shigowar saƙo ya ji, hakan na saka shi miƙa hannu ya ɗauko wayar akan gado. Sai lokacin ya kula data ɗinshi ma a kunne take, don ma wayarshi na riƙe caji sosai. Sai da ya kashe data ɗin tukunna ya buɗe saƙon:
‘Aslm. Ina kwana, ka tashi lahia dai ko? Kana raina tun daren jiya, ya jikinka?’
Numfashi ya sauke, a tashin hankalin nan da yake shirin tunkaro shi ya fi jin Majida akan komai, da dukkan zuciyarta take sonshi, yasan ba don abin hannunshi ba, a tsawon auren su Majida bata taɓa buɗe baki ta tambayeshi kuɗi ba, shi yasa duk sati yake bata abinda duk Allah ya hore mishi, bai taɓa ganin mace marar damuwa irinta ba. Screen ɗin wayar yake shafawa dai-dai kan saƙon nata.
“Majee…”
Ya kira sunanta da wani irin yanayi. Ya jima yana ganin bata dace da shi ba, ba namiji irinshi ya kamata ta aura ba, amman
da tafiyar lokaci da yadda yake ƙoƙarin gyara halayenshi sai yake jin tamkar duk zunubanshi suna ragewa ne, kamar zuwa yanzun ya cancanci zama mijinta. Lumshe idanuwan shi yayi fuskokin yaran nan tana dawo mishi. Yana jin wani irin kusanci da su da har tsikar jikinshi tashi take yi. Ashfaq ya ce mishi ya fara tabbatar da yaranshi ne tukunna sai yai tunanin abinda zai faru.
‘Na jima da daina tunanin abinda gobe zata haifar min saboda banda tabbacin zan ganta, yau nake da, tunanina ya tsaya akan yaune kawai, in na ji na buɗe idanuwa goben na yi tunani akanta.’
Maganganun Ashfaq na wani lokaci suka dawo mishi, sosai yake buƙatar ɗan uwanshi, abubuwa da yawa za su zo mishi da sauƙi idan Ashfaq ɗin na tare da shi. Zai yi abinda ya ce yanayi a kullum, zai tsaida tunanin shi a yau kawai, cikin hakan ya haɗa da tabbatar da yaran nan nashi ne. Shi ne kaɗai abinda zai faru yau, haka ya ci gaba da faɗa wa kanshi yana rubuta wa Majida amsar saƙon da ta turo mishi:
‘Wslm. Lafiya ƙalau, kema kin tashi lafiya? Inata kewarki da yawa.’
Sai ma da ya ga alamar an karanta saƙon tukunna yake jin jikinshi na mishi ƙaiƙayi da son riƙeta, ya ji ɗuminta a tare da shi, yasan damuwarshi zata rage inda tana riƙe a jikinshi, Majida alkhairi ce a rayuwarshi da bai taɓa mafarkin samu ba. Wayar ya ajiye ya tashi ya shiga wanka, sai da ya fito ne ya tuna komai na wajen Majida. Zama yayi gefen gadon yana ɗaukar waya ya kirata.
“Majee.”
Yace tana ɗagawa.
“Ina kwana.”
Ta gaishe da shi. Numfashi ya sauke.
“Ba mun gaisa ba yanzun?”
Yana jin dariyarta.
“Yoo ba’a ƙara gaisawa?”
Girgiza kai kawai yayi.
“Wanka nayi, ki kawo min kayan da zan sake, da komai da kike tunanin ina buƙata.”
“Yanzun zan zo, in taho ma da abin kari?”
Bayason dogon surutu a yanayin da yake ciki.
“Komai ma ki taho min da shi.”
Ya faɗi yana sauke wayar daga kunnenshi tukunna ya katse kiran. Baisan me Majida take tattarowa ba dan ta kai mintina goma koma fiye da haka, wayarshi ya ɗauka ya sake kiranta, ta ɗaga da faɗin,
“Gani nan kohwa wajen, ka hito ka ansa.”
“Ki tura ki shigo mana Majee, na ce miki wanka na fito fa.”
Altaaf din ya fadi a gajiye.
“Ni kunya nike ji, mutane na ta wucewa suna ganina, don Allah ka hito.”
Baisan kalar kunyar Majida ba, har mamaki take bashi wasu lokutan.
“In ba za ki shigo ba ki koma.”
Ya faɗi yana katse kiran, in ba gani tai ranshi ya ɓaci ba ba zata shigo ɗakin ba, sai da yai tunanin da gaske ta koma tukunna ya ji an buɗe ƙofar falon. Jira yake ta shigo ɗakin baccin ya ji shiru, kafin wayarshi ta fara ƙara, dubawa ya yi ya ga ita ce, miƙewa yayi yana buɗe ƙofar ɗakin da yake ciki ya hangota a falon tana tallabe da hijabinta da alama wani abinne a ciki. Sai da ya tabbatar sun haɗa idanuwa tukunna ya koma ciki abinshi.
“Don Allah ka hito ka ansa.”
Ta faɗi da ƙarfi, yana jinta yai shiru, ta kusan mintina uku ko fiye da hakan, tukunna ya ji takun tafiyarta ta shigo ɗakin , hararar ta yayi daga inda yake zaune, ta turo mishi laɓɓanta tana tsugunnawa. Wasu robobi masu murfi guda uku ta fara ajiyewa da cokali, tukunna ta miƙe tana juye sauran abinda ke cikin hijabinta akan gadon, kayanshi ne na sakawa, riga da wando na wani yadi purple mai haske, sai hula da alama takalma ne a baƙar leda, brush ɗinshi, man shafawa da turaruka kala biyu, sai comb ɗin taje kai.
“Manyan kaya kika ɗauko min?”
Altaaf ya tambaya yana kallonta.
“Na ga wajen rasuwa ne shi ya sanya na ɗauko maka, baka so ne?”
“Idan bana so ya zan yi da ke tunda kin riga kin ɗauko?”
Ya ƙarasa maganar yana ɗaukar brush ɗin tare da miƙewa, gani yayi tana shirin juyawa yasa shi cewa,
“Ina zaki je?”
“Komawa zan yi, ina kama masu aiki ne.”
Kai Altaaf ya girgiza.
“Ki jira ni in fito.”
Ya shiga banɗakin, brush yayi tukunna ya fito, Majida ko zama bata yi ba tana tsaye.
“Ki samu wajen zama, babu inda zaki.”
Shagwaɓe fuska ta yi.
“Amman dai…”
Katse ta Altaaf yayi.
“Ni dai na ce babu inda za ki je, zaki iya yin abinda kike so.”
Ya ƙarasa yana ɗaukar man da ke a doguwar roba ya matsa a hannunshi ya ci gaba da shafawa, inda tasan yadda ranshi yake a jagule da bata so tafiya ta bar shi shi kaɗai ba, ganinta yasa ya ɗan ji sauƙin tunanin da ke neman danne shi. Majida kuwa kallon shi take yi, Ammi ta ganta sa’adda zata fito, kuma tana da tabbacin tasan wajen Altaaf ɗin zata taho, yanzun in ta ga ta jima zata ɗauka wani abun ne ya faru, dama ga kunyar Ammi da take ji zai ƙara mata wata. Yanayin shi take kallo yana shafa man, rikicin shi sai addu’a, waje ta samu ta zauna gefenshi.
Bai sake ce mata komai ba har lokacin, shirya kanshi yake yi, tasan hali ranshi ne ya soma ɓaci, da zai ce ta tayashi shiryawa, tsaf ya gama shiryawa, kayan daya cire ma shi ya linkesu yana ajiyewa kan gadon. Yayi wani kicin-kicin da fuska, robobin da ta shigo da su yake ja gabanshi, tasan yanayin cikinshi, shayi ba damunshi yayi ba, ko da safe ya fi son tai mishi wani abin. Buɗewa yayi, roba ɗaya wainar shinkafa ce da miyar a haɗe waje ɗaya ta ji naman rago sai ƙamshi take yi.
Cokalin ya ɗauka yasa ciki, sai da ya fara ci tukunna yasan yunwa na ɗawainiya da shi ba kaɗan ba, duka ya cinye wainar don guda huɗu ce ta saka mishi, bai ko taɓa sauran robobin ba don ya ji ya ƙoshi, robar ruwa kaɗai ya ɗauka da tun jiya ya sha rabi ya buɗe yana sake shan wani.
“Baka cin sauran?”
Majida ta tambaya muryarta a sanyaye, kallonta yayi yana ɗaga mata kai alamar eh. Yana kallon yadda take tunanin fushi yake mata, bai kuma yi ƙoƙarin gyara mata ba tunda ba zai iya mata bayanin asalin abinda yake damunshi ba, ledar takalman ya ɗauka yana fito da su ya ajiye ƙasa tukunna ya saka wa ƙafafunshi, ya ɗauki hular itama ya buɗe ta yana gyara karin tukunna ya saka.
“Zaki iya tafiya yanzun.”
Ya faɗi ba tare da ya kalleta ba, yana ɗaukar wayarshi ya saka a gaban aljihun shi, ya ɗauki mukullin mota.
“Hushi kake man ko?”
Majida ta ce, idanuwanshi ya sauke mata a kasalance.
“Fita zan yi.”
Ya faɗi a taƙaice yana miƙewa, ita ma miƙewa ta yi tana takawa inda yake, maɓallan rigar da bai ɓalle ba ta kama tana ɓalle mishi su, tukunna ta riƙe fuskarshi cikin hannuwanta.
“Allah ya tsare ya maidoka lahiya. In hushi kake yi kayi haƙuri ni dai.”
Murmushi yayi yana ranƙwafowa ya sumbace ta tukunna ya kama hanuwanta yana janyeta gefe ya wuce, ba sai ta ga damuwa da tsoron da yake ciki ba. Yasan zata tattara kayayyakin ne ta fice itama, gidan a cike yake, rumfunan da ke kafe duk mutane ne, sai da ya ƙarasa suka gaggaisa yana ƙara musu gaisuwa tukunna ya wuce ya shiga motarshi, zuciyarshi na wata irin dokawa yake nufar ƙauyen Kinkiba.
Yana ƙarasawa ƙauyen tun kafin ya shiga unguwar yake jin zazzaɓin shi ya dawo sabo, ga wata irin zufa da yake ji har cikin tafukan hannunshi, saitin gidan daga ɗayan tsallaken yayi parking, sai da ya juya kanshi ya kalli gidan ma yasa hanjin cikin shi na hautsinawa, kanshi ya kwantar jikin abin tuƙin motar yana sauke numfashi, yana jin kamar ƙarshen duniyarshi ne yake shirin zuwa, kafin a hankali ya fara jin iska mai ƙarfin gaske na kwashe ƙasar ramin da ya yi ya binne rayuwarshi.
*****
Rayuwar Altaaf Isma’il Tafida
Kano
Tun bayan rasuwar iyayen su Isma’il, shi da yayyenshi duka kowa ya fara neman na kanshi, kasancewarshi ƙarami a cikinsu bai sa ya zama koma baya ba, don shige-shige duk ya fisu, yana tunanin hakan na da alaƙa da dogon burin shi, don ya ga su kamar zuciyoyin su sun wadata da zama inda suke a yanzun. Musamman babban Yayansu Hisham, tunda duk ya fisu wadata kuma yana taimaka musu dai-dai ƙarfinshi.
Ana hakane Isma’il ya samu aikin tuƙi a gidan Alhaji Ashiru wanda fitaccen ɗan canji ne a garin Kano, da yake Isma’il ya san hannunshi, gashi tsaf-tsaf, duk da rashin tsadar kayanshi babu budurwar da zata kalleshi bata sake kallonshi ba don cikin ‘yan uwanshi shi ne ya biyo kyawun mahaifiyarsu, aikin shi a gidan Alhaji Ashiru shi ne kai yaranshi matan makaranta ya kuma ɗauko su, sai sauran unguwa na matan nashi biyu in buƙatar hakan ta taso.
Akwai yarinyar Alhaji Ashiru wato Amina da baya ɓoyewa wajen nuna yadda ya fi sonta, don hakan ya jefa kishi tsakaninta da ‘yan uwanta da suke Uba ɗaya, duk da wasu lokutan in suna son abu wajen Alhaji Ashiru da ita suke kama ƙafa, ta fara nuna wa Isma’il alamun so, sam bai kawo ma ranshi ba, ganin kyawu da aji irin na Amina, tun tana mishi a ɓoye ta hanyar alkhairi har ta fito fili ‘yan gidansu babu wanda bai sani ba.
Ba ƙaramin rikici aka yi ba, don Alhaji Ashiru ya so Amina ta auri ɗan ƙaninshi ne gidan hutu, yaro mai ilimin boko kamar ta, amma sam ta rufe ido, da kuka da komai in ba Isma’il ba bata son kowa, shari’a har da manyan yayyen Alhaji Ashiru, don duk wani wanda tasan ya isa yai ma Alhaji Ashiru magana kan amince wa aurenta da Isma’il saida takai ƙararshi. Kan dole ba don yana so ba akai auren. Fushin da yayi ne yasa yace sai dai ta zauna duk inda Isma’il yake da halin kama musu ko da gidan haya ne kuwa.
Duk don ya nuna mata kuskuren da ta yi na auren Isma’il ɗin tun ba’ayi nisa ba, aikam gidanshi na gado da yake haɗe dana sauran ‘yan uwanshi ya tare da Amina, duk surutun da ‘yan uwanta suke mata bata damu ba, mahaifiyarta ce kaɗai take goyon bayan auren, don tace baka san arziƙin mutum ba, tunda ta yaba da hankalin Isma’il. Haka suka yi zamansu cikin ƙaunar juna har Allah ya fara azurta su da samun zuri’a. Halaccin da Isma’il yake ganin Amina ta mishi, tsoron rasata da kuma kwaɗayin abin duniya don yana da burin zama hamshaƙin mai kuɗi yasa shi sakar mata ragamar gidanshi gaba ɗaya.
Abinda duk take so shi ake yi, yasan ‘yan uwanshi, har ma da abokai na mishi kallon mijin hajiya, bai kuma damu ba. Yara huɗu Allah ya basu, Altaaf shi ne na farko, Aslam, Barrah sai kuma ƙaraminsu Anam. Sai dai me, son duniya Amina ta ɗauka ta ɗora wa Altaaf, uhm ya ce sai ta ji dalili. Tun yana da ƙarancin shekaru zaka gane sangartacce ne, babu kwaɓa balle zagi. A ƙasan ran Isma’il baya son hakan, don sangartar Altaaf na damunshi, amma ba zai iya tsawata wa Amina ba, ballanta ya ga kamar son shi neya koma kan Altaaf.
Ko wasa suke da sauran yaran ‘yan uwanshi in sun shigo, irin faɗan yaran nan wani ya taɓa Altaaf sai Amina ta rama mishi ta kuma ƙwace kayan wasan ta kore su gida. Tun Altaaf na ƙaraminshi baya ganin kan kowa da gashi, ga rashin kunya, komin girmanka zai gaya maka son ranshi, kullum cikin kawo ƙararshi ake a unguwa ya jibgi yaran mutane, Amina kuma taita masifa don anga ɗanta ya fi na kowa gata a unguwar shi yasa aka saka mishi idanuwa. Daya fara zuwa makaranta ma ba maida hankali yake yi ba sai jibgar yaran mutane, har malaman makarantar bai ƙyale su ba, da yake ta kuɗi ce babu mai taɓa shi, duk laifin da zai yi in aka dake shi Amina zataje ta ɗaga hankalin duka malaman makarantar.
Haka rayuwa ta ci gaba da tafiyar musu, duk da sauran ‘yan uwanshi ma ba kwaɓarsun Amina take yi ba, amma rayuwar Altaaf ta fi tasu gurɓata, don kalar son da take mishi bata haɗa shi dana kowa ba, har Isma’il da kanshi kuwa. Ko cikin sauran gidajen yara masu tasowa kamar Altaaf, ba mai iya zama da shi da baƙin halinshi sai Ashfaq, watannin haihuwarsu babu nisa, duka wata shida Ashfaq ɗin ya bashi. Da shi kaɗai jinin Altaaf ya haɗu, shi ne kuma yake taka shi a zauna lafiya.
Kullum rayuwar Altaaf ƙara lalacewa take, duk wani taron marasa jin magana a makaranta shi ne jagoransu, da ya zo sakandire ma basu cika zama ba, katanga suke haurawa. Islamiya kuwa da ƙyar ya iya yadda zai yi Sallah da hukunce-hukuncenta, shima tun yarinta ne da ake fito da su ana koya musu kullum, duk Islamiyyar da za’a saka shi rashin ji baya bari ya zauna, tunda in an dake shi, Amina zata je tai rashin mutunci sai a bata ɗanta su tafi gida.
Tun yana aji biyu sakandire suka tashi daga gidan gadon Isma’il, saboda rasuwa da Allah ya yi wa Alhaji Ashiru, sun kuma gaji dukiya mai tarin yawa, tun daga gidaje zuwa filaye, don ɗaya daga cikin gidajen da Amina ta gada ne suka koma. Anan ne suka fara haɗakar kasuwanci da babban yayanta da suke uwa ɗaya uba ɗaya, ta kuma ɗora Isma’il akan wasu cikin kasuwancinta, dama abinda yake nema kenan ya samu.
Duk da haka Altaaf baya wuni gidan, in suka gudu daga makaranta suka gama yawonsu da abokanshi zai yi unguwar su ta da wajen Ashfaq. Bai ƙara lalacewa ba sai da ya gama aji uku, Amina ta sake mishi makaranta inda ya ci gaba daga aji uku, ya kuma haɗu da yaran da suka fito daga gidajen da ya fi nashi kuɗi, lokacin ne ya fara shan sigari suka kuma fara saka mishi ra’ayin bin mata. Lokacin ne yayi hankalin da ya fara ɓoye wannan halayyar tashi daga wajen Amina. Ko ‘yan bushe-bushen su suka yi zai bari sai ya daina warin hayaƙi tukunna ya shigo gida.
Kuɗi ba matsalarshi bane ba, ko nawa yake so Amina zata bashi, balle yanzun da aka daina kawo mata ƙararshi, wani irin so take ƙara nuna mishi. Takan ce ma Isma’il dama ta ce mishi yarinta ke damun Altaaf gashi yanzun ya nutsu. Komai ya kwaso Ammi kamar yadda suke kiranta. Nutsuwar da yayi ta daina faɗa da mutane bai wuce hankalinshi daya bar nan ya koma kan ‘yan bushe-bushe da kuma mata ba. Ashfaq kaɗai yasan wannan mugayen halayen daya fara, sosai kuma suke faɗa akan hakan.
Haka komai ya ci gaba da tafiya har Altaaf ya kai aji biyar a sakandire, daga nan ne asalin komai ya fara.
Dakyau.