Skip to content
Part 25 of 52 in the Series Alkalamin Kaddara by Lubna Sufyan

Da yake ɗalibai da yawa kan samu sa’a akan jarabawar share fagen shiga jami’a, Altaaf na ɗaya daga cikin ɗaliban da suka samu wannan sa’ar, don kuwa marking shi har ya haura wanda ake buƙata a gurbin karatun nashi. Jarabawar ita ta fara kawo rabuwarshi da abokanshi na sakandire dama daga shi sai Rumah ne suka samu sa’arta, sai dai inda Altaaf ya nemi gurbin karatu a Ahmadu Bello, shi kuma Rumah ya nema ne a Bayero da ke nan Kano ɗin.

Akwai ƙanin Ammi da ke aikin koyarwa a nan Zaria ɗin, don can ma yake zaune da iyalanshi. Shi ta yi wa maganar Altaaf ɗin don komai ya fi zuwar musu da sauƙi. Cikin ikon Allah kuwa Altaaf ya samu gurbin karatu. Ƙanin nata Ammi ta ɗora wa wahalar registration ɗin Altaaf. Shi yai mishi komai ya gama, yake kuma sanar da ita zai kira ya faɗi lokacin da Altaaf ɗin yakamata ya je. Lokacin ne Ammi ta ce ya kamata ya fara koyon tuƙi kafin a fara karatu. Murmushi ya yi.

“Na iya Ammi.”

Ya faɗi yana sa Ammi da ke zaune tana hararar shi.

“Bana son shiririta Altaaf.”

“Wallahi da gaske, na daɗe da iyawa. Sau nawa nake cewa ki kawo in kaiki unguwa kina ƙi?”

Girgiza kai Ammi ta yi.

“Yaushe ka koya ban sani ba?”

Ta buƙata, don sam hankalinta ya ƙi nutsuwa da cewar Altaaf ɗin ya iya tuƙi. Asalima tana tsoron bashi mota kar ya je ya ji wa kanshi ciwo. Ganin yayi shiru yana mata murmushi yasa ta sauke numfashi.

“Ni dai na fi son ka je ƙwararru su koya maka indai kana son in baka mota.”

Hannuwanshi Altaaf ya haɗe waje ɗaya yana lumshe mata idanuwanshi sannan ya buɗe su da faɗin,

“Duk yadda kike so haka za’a yi.”

Yanayin da yai maganar na sa Ammi yin ‘yar siririyar dariya. Shikam nishaɗi yake ji marar misaltuwa, kamar ya janyo ranar tafiyarshi makaranta haka yake ji. Ammi da kanta ta kula da hakan shi yasa ta ce mishi,

“Kawunka yace ai maka magana ko za ka zauna a wajen shi a Zaria.”

Tun kafin Ammi ta ƙarasa maganar Altaaf yake girgiza mata kai. Inda ya so zaman gida ne zai nemi gurbin karatu a Bayero, yana son walwalawa ne, yana son yin rayuwa ta wani lokaci ba tare da idanuwan kowa daya sani akan shi ba. Zai iya ƙirga ganin da yai wa Kawu Murtala ƙanin Ammi ɗin, kuma mutumin bai mishi ba kwata-kwata, don ya yi kalar ‘yan takura.

“Ammi karki fara maganar nan, ba zan zauna a gidan shi ba…”

Ita ma da Murtala yai maganar sai da ta jinjina ta, shi yasa ta ce mishi zata duba ta gani. Bata son abinda zai takura Altaaf ɗin ko kaɗan, dama saboda abinci ne take tunanin ya zauna a gidan Murtala ɗin, in tasan yana can hankalinta zai kwanta ta ɓangaren tunanin ko ya ci abinci ko bai ci ba.

“Dama saboda abinci da…”

Altaaf bai bari ta ƙarasa ba ya katse ta.

“Zan iya siyan duk abincin da nake son ci. Ammi bazan zauna a gidan kowa bafa, za ki kama min gidane a wajen makaranta.”

Ya ƙarasa yana jin ranshi na shirin ɓaci.

“Shikenan…meye na ɓacin ran? Sai in shirya in je Zarian da kaina in duba maka waje.”

Kai ya girgiza mata.

“Zan je da kaina ko kwana biyu sai in yi in duba wajen da nake so.”

Kai ta jinjina mishi kafin ya miƙe.

“Ina kuma zaka je muna hira?”

Shagwaɓe mata fuska Altaaf ya yi.

“Kaina na min ciwo zan kwanta ne.”

Numfashi Ammi ta ja.

“Bana ce maganar ya wuce ba?’

“Na sani kawai zan kwanta ne Ammi.”

Altaaf ɗin ya ƙarasa yana murza goshin shi. Ta baya yaji ana ja mishi riga da ƙarfin tsiya, ya kuma san babu me wannan aikin sai Barrah, fisge rigarshi yayi yana juyawa tare da ranƙwashinta akai.

“Ban ce karki sake ja min riga haka ba.”

Wajen ta dafe idanuwanta na cika da hawaye.

“Allah sai Ya saka min, mugu.”

Bakinta Altaaf ya kaima duka tana kaucewa.

“Me nai maka?”

Ta tambaya tana fashewa da kuka. Runtsa idanuwanshi yayi yana buɗewa sannan ya juya ya kalli Ammi.

“Don Allah Ammi ki ce yarinyar nan ta ƙyale ni in huta.”

Dariya Ammi ta yi don sun saba in dai shi da Barrah ne.

“Barrah zo nan ƙyale shi.”

Maƙale kafaɗa Barrah ta yi tana kama gefen rigar Altaaf ɗin ta riƙe dam tana ci gaba da kukanta.

“Sake ni.”

Ya faɗi yana ƙoƙarin ɓanɓare hannunta, ƙarfin yarinyar na bashi mamaki.

“Wallahi zan kwaɗa miki mari idan baki sake min riga ba.”

Kafaɗa ta sake maƙalewa, ya kuma san taurin kanta.

“Menene? Me zan miki?”

“Ai baka tsaya na faɗa maka ba ka ranƙwashe ni.”

Barrah tai maganar cikin kuka. Numfashi yake fitarwa a hankali, ciwon kan da yai wa Ammi ƙaryar yana yi ya fara saukar mishi. Ɗayan hannun Barrah ya kamo yana faɗin

“Yi hakuri ‘yar ƙanwata, faɗa min menene?”

Sake shagwaɓe fuska ta yi, kukan ma yanzun babu hawaye don rikici ne kawai take ji ya sani.

“Zamu ɓata fa idan baki faɗa min menene ba.”

Altaaf ya ƙarasa yana sa hannu ya goge mata fuskarta.

“Barrah mana… Menene?”

Jan hanci tayi tana kallon shi

“Yaya ne yace min wai za ka tafi makaranta, shi ne fa zan tambaye ka.”

Kai ya ɗaga mata.

“Me yasa za ka tafi? Kuma wai ba a nan garin ba?”

“Zan dinga zuwa gida ai in na tafi.”

Daga yanayin kallon da take mishi yasan bata fahimce shi ba.

“Mu je in baki wafers.”

Murmushi ta yi mishi.

“Da gaske?”

Kai ya ɗaga mata, shima yana da ciye-ciye sosai, amma lokutta da dama yakan ajiye ne saboda yana raba shi da rigimar Barrah. Bin shin ta yi kuwa ya bata tukunna ta tafi, mukulli yasa daga ciki yana kulle ɗakin shi. Rigarshi ya kama yana kallon inda Barrah ta cukwikuye mishi ita, ba zata taɓa riƙo hannunshi tai mishi magana ba sai dai ta kama mishi riga tana ja, ya dake ta kan haka har ya fara gajiya. Kwanciya yayi, yana da bashin baccin da bai yi ba jiya sun kwana club shi da Kaigama.

*****

Da yake kuɗi kan yi abubuwa da yawa a ƙasar Nigeria, yi ma Altaaf takardun da zai bashi damar yin tuƙi bai yi wata wahala ba, cikin ‘yan satika komai ya kammala, hatta da lambar mota an yi mishi, motar ce kawai bata ƙaraso ba. Duk da ya iya tuƙi bai hana Ammi sama mishi makarantar koyon tuƙi ba ya je don hankalinta ya kwanta kawai. A satin ne kuma yai shiri tsaf da cewar zai je Zaria don ya duba gidan da yake son zama, tunda karatu zai kankama satin gaba. Kaya kala huɗu ya ɗauka duk da yasan ba zai wuce kwana biyu ba. Suttura da shiga me kyau na da muhimmanci a wajen Altaaf sosai, don shine mutuncin gayu.

Kayan jikinka za su fara sai maka mutunci in ka shiga cikin mutane, kuɗi wadatattu Ammi ta bashi a hannunshi, don ta ce mishi in ya ga bazai iya zama a gidan Kawu Murtala ba ya kama hotel na kwanakin da zai yi. Ya kuma ji daɗin hakan sosai. Ammi taso ta sauke shi har Zaria ne ya ce mata zai bi motar haya, duk da wannan ne karo na farko da zai bar garin Kano. Mashin ya hau har tasha, samun motar Zaria bai mishi wahala ba da taimakon ‘yan union ɗin kasuwar, ƙaramar mota ce ƙirar golf, gidan gaba Altaaf ya shiga aka ce mishi mutum biyu ake sakawa, ya biya kuɗin wajen duka. Don ba zai zauna ya takura ba.

Altaaf bashi da ƙauyancin nan na in ka je waje ka ƙi tambaya bai samu wata matsala ba yana sauka Zaria. Yana fitowa daga tasha wani shago ya shiga ya musu sallama ya tambaye su inda zai samu hotel me kyau cewar ya zo hidimar makaranta ne. Aikam faɗa mishi suka yi, ya samu mai mashin zuwa Abu Hotel. Tun kafin ya ƙarasa ciki ya ga haɗuwar hotel ɗin. Ciki ya shiga har reception ɗin wajen, kwana ɗaya ya biya, tukunna ya faɗa a wajen yana son abinci tukunna ya karɓi mukullin shi yayi hanyar da suka nuna mishi.

Sai da yai wanka ya fito tukunna ma aka kawo mishi abincin, ci yayi ya ƙoshi ya sake kaya da sukai matuƙar karɓar shi, ya ɗauki baƙar face cap ɗin shi ya saka a kanshi tukunna ya fito. Mashin ya sake hawa zuwa jami’ar Ahmadu Bello, duk da yamma ta yi liƙis, yanayin ya mishi daɗi, musamman daya sauka ya shiga cikin makarantar ya fara cin karo da manyan gayu kala-kala. Ga ‘yan mata ko ta ina, wani murmushin nishaɗi ya ji ya ƙwace mishi. Tafiya yake cikin makarantar za ka rantse ya san inda ƙafafuwanshi suke takawa.

Wani shago ya gani da maza da mata a wajen da alama kowa siyayya yake, ƙarasawa ya yi shima, idanuwanshi suka sauka cikin na wata yarinya da tai mishi wani irin kyau duk da jikinta na sanye da hijab ne har ƙasa, murmushi ta yi a kunyace tana sauke nata idanuwan. Da alama tana son siyan wani abu ne amma yawan mazan da ke wajen ba zata iya kurtsowa ciki ba. Cikin ƙasaita Altaaf ya ƙarasa inda take yana faɗin,

“Sannun ki. Za ki siya wani abune?”

Kai ta ɗan ɗaga mishi a hankali.

“Me za ki siya in amso miki.”

Cikin ‘yar siririyar murya ta ce,

“Ruwa da Fanta.”

Kai Altaaf ya ɗaga mata yana komawa shagon, ruwan roba ya karɓo mata ɗan matsakaici sai Fanta na gwangwani ya dawo ya miƙa mata, hannuwa duk biyun tasa ta karɓa tana miƙa mishi ɗari biyar. Daƙuna mata fuska ya yi.

“Don Allah ka karɓa.”

Ta faɗi a kunyace.

Kai Altaaf ya girgiza mata alamar a’a, yana tsareta da idanuwanshi, kafin ta ce,

“Na gode.”

“Karki damu. Altaaf Isma’il Tafida”

Ya ƙarasa da faɗa mata sunanshi.

“Ruƙayya Hassan.”

“Ruƙayya…”

Altaaf ya maimaita sunan yana ɗanɗana yanayin shi akan harshen shi. Kallonta yake, hijab ɗin jikinta ya hana mishi kallon asalin abinda yake son dubawa a jikinta, don fuska kawai ba ita bace mace a wajen shi.

“Na gode… Sai Anjima.”

Ta faɗi tana juyawa ta soma tafiya, binta Altaaf ya yi suka jera.

“In dan taka miki mana.”

Kallon shi ta ɗan yi tana girgiza kanta.

“Yayana nake jira, zai zo ya kaini gida…”

Altaaf ya buɗe baki zai yi magana suka ji an kira sunanta, a tare suka juya, Altaaf na sauke idanuwanshi kan saurayin da duk alamu suka nuna zai ba Altaaf ɗin wajen shekaru uku da ‘yan kai.

“Ruƙayya.”

Ya sake kira a karo na biyu cike da alamomin tambaya, idanuwanshi na kan Altaaf yana ƙare mishi kallo.

“Yaya kai nake jira dama.”

Ruƙayya ta faɗi a muryarta na rawa da alamun tsoro. Ƙarasawa saurayin ya yi inda suke ya miƙa wa Ruƙayya mukullin mota tare da faɗin,

“Ki je mota.”

Karɓar mukullin ta yi, ta kalli Altaaf idanuwanta cike da ban haƙuri tukunna ta wuce. Yadda saurayin yake bin Altaaf da kallo haka shi ma Altaaf ɗin yake binshi da kallo.

“Karka fara sauke hayaƙin da ka shigo da shi akan ƙanwata…”

Shine abinda ya fada, yana sa Altaaf ya kwashe da dariya, don yasan ma’anar kalmomin, yana kuma da tabbacin yayan Ruƙayya ma duka layinsu ɗaya. Hannu Altaaf ya miƙa mishi.

“Altaaf Isma’il Tafida. A-Tafida…”

Hannun ya karɓa suna gaisawa.

“Imran Hassan. Wadata…”

“Wadata.”

Altaaf ya maimaita, kai Wadata ya jinjina mishi.

“Karka zo kusa da ƙanwata”

Kafaɗun shi Altaaf ya ɗan ɗaga.

“Da gaske nake.”

Wadata ya faɗi cike da kashedi.

“Na ji amma da sharaɗi ɗaya.”

Cewar Altaaf ɗin fuskarshi babu alamun wasa.

“Meye sharaɗin?”

Wadata ya buƙata yana wa Altaaf ɗin kallon da ke fassara ‘Da wasa kake yi ko?’

“Za ka taimaka min in samu gida. Ina neman inda zan zauna ne.”

Murmushi Wadata ya yi.

“Kana da kuɗi ?”

Ɗan daƙuna fuska Altaaf ya yi.

“Ina nufin gidan kamar na nawa?”

Kafaɗun Altaaf ya sake ɗaga mishi.

“Ko nawa, inda babu takura, ba a jikina kuɗin za su fita ba.”

“Yayi kyau… Bani wayarka.”

Wadata ya faɗi yana miƙ ma Altaaf ɗin hannu, wayarshi Altaaf ya zaro ya bashi, ya daddana da alama ya saka mishi lambarshi ne a ciki.

“Mu hadu wajen ƙarfe takwas. Kana ina ne yanzun?”

“Abu Hotel.”

Altaaf ya bashi amsa a taƙaice.

“Zan zo in ɗauke ka lokacin.”

Kai Altaaf ya jinjina yana ƙoƙarin saving ɗin lambar Wadata ɗin. Shikuma ya juya ya tafi. Sai da ya sake zazzagayawa cikin makarantar har ya ji ya gaji tukunna ya juya yana nufar gate. Mashin ya samu ya mayar da shi Hotel ɗin, sai daya zauna tukunna ya ji gajiyar da yayi, da ƙyar ya kwance takalminshi yana kwanciya duk da yasan gab da magriba ne, kuma ko Azahar bai yi ba. Yasa a ranshi in ya tashi bacci ya haɗa su duka da isha’i yayi kafin Wadata ya zo ɗaukar shi.

*****

Kiran Ammi ne ya tashe shi daga baccin da yake yi, da ƙyar suka gaisa ta katse kiran don ta ji bacci yake, kanshi ya yi mugun nauyi, banɗaki ya shiga ya watsa ruwa ya fito, ya fara sa kaya ne ya tuna bai yi salloli ba ya koma ya ɗauro Alwala, da ba’a wajabta sallah ba zai haƙura da ita ne yau, don dai duk rashin yin sallar shi akan lokaci baya bari ranar ta wuce bai yi ba. Samu yayi ya jero su yana idarwa ko addu’a bai yi ba, sabon shi ne da ya idar da Sallah ya miƙe tunda ita ce aka wajabta mishi.

In ya zauna addu’a tabbas ranar ya ji labarin mutuwa ne. Hular shi ya saka ta baya wannan karon yana fesa turare a jikinshi, kan gado ya zauna ya saka safa a ƙafafunshi tukunna ya zira takalma yana ɗaurawa, cikin shi ya ji ya ƙulle waje ɗaya da alamar yunwa yake ji. Kuɗin da ya cire daga aljihun ɗayan wandon ya ɗiba yana mayarwa a na jikinshi, ya ɗauki agogonshi kenan ya ga kiran Wadata ya shigo, ɗagawa ya yi.

“Hello…”

Ya faɗi a kasalance, yana jin duk jikinshi na mishi ciwo.

“Ina bakin hotel ɗin ka fito.”

Sauke wayar Altaaf ya yi daga kunnenshi yana saka ta cikin aljihun wando tukunna ya ɗauki agogon shi yana ficewa, aikam Wadata ya gani a cikin motarshi a zaune. Murfin ya buɗe yana shiga ya zame ƙafafuwanshi yana jingina jikinshi da kujerar motar sosai tukunna ya ja murfin ya rufe. Agogon shi ya ƙarasa ɗaurawa tukunna ya juyar da kanshi yana kallon Wadata da faɗin,

“Yunwa nake ji.”

Yanayin Altaaf ɗin Wadata yake kallo, daga ganin da yai mishi ɗazun yasan yaro ne, ya kuma san hayaƙin rashin ji yanzun yake ɗibar Altaaf ɗin, amma yanzun yadda ya shagwaɓe fuska har cikin idanuwanshi ya ƙara nuna mishi asalin yarintar Altaaf da kuma yadda ya fito cikin gata da taɓara.

“Me yasa baka ci wani abu ba kafin ka fito?”

Wadata ya ce yana kunna motar. Daƙuna fuska Altaaf yayi yana dafe cikinshi da ya ji ya yi ƙara.

“Bacci na yi. Kuma zan nema abu ne ka kirani…”

Numfashi Wadata ya sauke yana jin yanda Altaaf zai zame mishi aiki, don ya ga ba ƙaramin sangartacce ba ne, saidai ya makara, akwai wani abu mai shiga rai tattare da Altaaf ɗin. Duka ganin da yai mishi na yau kawai, yaron ya tsaya mishi a rai. Don haka ya kashe motar yana faɗin,

“Je ka yi take away…karka dade”

Ƙanƙance idanuwa Altaaf ya yi yana sauke murya cikin yanayin da ke samar mishi lambar duk yarinyar daya so kafin ya ce,

“Ba za ka siyo min ba.”

Tissue ɗin da ke gaban motar Wadata ya ɗauka yana jifan Altaaf da ita.

“Fitar min daga mota don Ubanka, ni za kai wa wannan fuskar.”

Kare fuskarshi Altaaf yayi yana dariya sosai.

“Karka ce min kyauna bai yi aiki ba yau, zuciyata zata karye…”

Altaaf ya faɗi yana dariya. Dube-dube Wadata yake yi yana neman abinda zai sake jifan Altaaf ɗin da shi, duk da dariyar da ke shirin ƙwace mishi, ganin babu ne yasa shi kallon Altaaf ɗin da yake ƙara ƙanƙance mishi idanuwa.

“Yanzun fa?”

Altaaf ya faɗi yana turo laɓɓanshi

Mukullin motar Wadata ya murza yana kunnata. Da sauri Altaaf ya buɗe murfin motar yana dariya

“Yi haƙuri.”

Harara Wadata ya watsa mishi, ya fita yana dariya. Take away yayo na dankali da ƙwai sai naman kaza, ledoji biyu ya yi daban-daban, sai da ya buɗe motar ya shiga ya zauna ya rufe tukunna ya miƙa wa Wadata leda ɗaya.

“Na ce maka ina jin yunwa ne?”

Wadata ya faɗi, ɗan taɓe baki Altaaf ya yi.

“Tarbiyata ba zata barni siyo wa kaina ni kaɗai ba.”

Girgiza kai Wadata yayi yana karɓar ledar ya ajiye tukunna ya ja motar suka tafi. Dankalin shi Altaaf yake ci hankalin shi a kwance. Duk da yana yi yana ma Wadata tsegumin ya rage gudu, saboda yana zazzage mishi abincin da yake ci. Shiru yayi ya ƙyale Altaaf ɗin , shi ne namiji ƙarami a gidansu, sai ƙannen shi mata gudu biyu, ya ga alama ƙaddara ta bashi wani ƙanin daga sama. A haka har suka ƙarasa, Altaaf ne ya fara fitowa daga motar yana jin kiɗa daban-daban na tashi a cikin wajen.

“Wow…”

Altaaf ya faɗi ba tare da ya sani ba, kallon yanayin yadda wajen yai mishi Wadata yake kallo, gidajen wajen Ɗanraka haka suke da kyau, gashi babu nisa da makaranta, ko yaushe cikin sababbin gine-gine suke.

“Muje…”

Wadata ya faɗi yana kama hanya, Altaaf ɗin na biye da shi har suka ƙarasa bakin wani gida, kiɗa ne kawai yake fitowa ta wajen, don Altaaf yana jin yadda dukan speakers ɗin yake amsawa har a ƙasar wajen ta cikin takalman shi, ƙofar Wadata ya murza yana buɗewa, wani irin hayaƙi ya fito, yana saka Altaaf ɗin yin baya, zama da Kaigama yasa ko daga nesa yaji wiwi yana ganewa. Turnuƙe ɗakin yake da hayaƙi, ganin Wadata ya shiga shi yasa yabi bayan shi, amman yakai mintina biyu kafin ya fara ganin mutanen da ke cikin falon, maza da mata sun fi su sha biyu.

“Ka ƙaraso…”

Wadata ya faɗi da ƙarfi saboda kiɗan da ke gauraye da ɗakin. Sosai Altaaf ya shiga cikin ɗakin, yana miƙa wa wanda duk ya gani hannu suna gaisawa, ciki har da matan kuwa. Kafin wani irin shiru ya ziyarci ɗakin sanadin kashe kiɗan da Wadata yayi.

“Haba Maza… Meye haka?”

Wani saurayi da zai yi sa’an Wadata ɗin ya faɗi.

“Sorry. Ga A-Tafida, cikon roommate ɗin mu.”

Ɗan daƙuna fuska saurayin ya yi.

“Na ɗauka kai kace mu uku kawai babu ƙari.”

Jinjina kai Wadata ya yi.

“Yanzun kuma na ce mun cika mu huɗu. A-Tafida ga Yaks da Jamal su kaɗai ya kamata ka sani yanzun, don su ne muke zaune tare da su.”

Wadata ya faɗi yana nuna mishi Yaks ɗin da Jamal, duk sun riga sun gaisa, sunayensu ne ya sani. Kai Yaks ya ɗan jinjina mishi, Jamal ne bai nuna alamun komai a fuskarshi ba, ya juya kan yarinyar da take rike a jikinshi yana sauraren maganar da take faɗa.

“Welcome to the gang…”

Wadata yace da murmushi, hannunshi Altaaf yakai goshin shi yana yi wa Wadata alamar saluting, kafin Wadata ya maida hankalin shi kan kayan kiɗan da ya kashe yana canja waƙar da ke kai tukunna ya kunna, kai Altaaf ya jinjina saboda waƙar tana bashi chargy yadda ya kamata, tuni ya manta da cewar baƙo ne shi a wajen, yaune ranar shi ta farko balle wani tunanin ya kamata ya fara sanin nasu halayyar kafin ya bayyana nashi, rawa ya soma takawa cikin ƙwarewa, don zaka rantse da iyawarshi aka haife shi.

Wata yarinya ce ta taso tana miƙa wa Altaaf ɗin hannu, kamawa ya yi ya ja ta suka soma rawar tare, ihu ‘yan cikin ɗakin suke musu, don da alama itama ba’a barta a baya ba wajen ƙwarewa a fannin. Saida ya ja ta jikinshi sosai tukunna cikin kunnen shi ta ce,

“Anisa…”

Kai Altaaf ya jinjina mata tunda yasan ta riga ta san sunanshi. Altaaf yaso komawa Hotel ɗin, Wadata yace ya kwana nan kawai, bai yi musu ba tunda in ya koma ɗin ma babu abinda zai yi da ya wuce zama shi kaɗai, ga yanayin wajen ya mishi ba kaɗan ba, har wajen ƙarfe biyu suna cashewa, bai kuma yi wahalar sabawa da duk mutanen wajen ba. Ko da kowa ya tafi aka barsu su huɗu a ɗakin, shi, Yaks, Jamal da Wadata ba baccin sukayi ba, hira suka tisa har da Altaaf ɗin za ka rantse sun shekara da sanin juna, kafin bacci ya kwashe su a nan falon.

* * ***

Bai bar gidan su Wadata ba sai wajen sha biyu, har hotel ɗin da yake Wadata ya sauke shi sukai sallama akan cewa in ya koma gida Ammi zata tura kuɗin hayar Altaaf ɗin a account ɗin Wadata, shi ma ya shirya ya taho. Don ji yake yi kamar ya zauna. Kayan shi ya shirya ya mayar musu da mukullin su ya fito ya hau mashin zuwa tasha. Gidan gaba ya sake kamawa shi kaɗai zuwa garin Kano. Baccin da bai samu ba a daren jiya ya rama a cikin motar, don haka ya ga saurin tafiyar sosai, ko mintina sha biyar bai yi ba da farkawa suka isa tashar Kuka da ke nan ƙofar ruwa.

Har yai niyyar tare mashin daga nan cikin tashar ya fasa yana ɗan takowa, masu saida alewoyi da biscuits ya gani, ya siya masu yawa don ya kai ma Barrah da Anam, duk da ya siya ne don Barrah ɗin ita ce za ta fi damuwa da rashin tsarabarshi, tukunna yahau mashin zuwa gida, nan ma bakin hanya ya tsaya shagon da yake siyan taba, don jikinshi har wani ƙaiƙayi yake da ya busa hayaƙi, duk ranar bai sha ba. Kara huɗu ya zuƙe nan take yana jin daidaton da sigarin kan bashi, biyu ya ƙara ya siya cingam mai minti guda biyu ya jefa a bakinshi tukunna ya taka zuwa gida.

Yana ƙarasawa ya duba agogon shi ya ga biyar saura. Motar bata cika da wuri ba, sun ɓata lokaci sosai a tasha. Gida ya shiga da sallama yana ɗaga labulen, kafin ya gama saukewa Barrah ta ruƙunƙume shi tana ihun murna.

“Yayaaaa sannu da zuwa.”

Take faɗi, numfashi Altaaf ya sauke a gajiye.

“Bana ce ku daina ce mun Yayan nan ba?”

Altaaf ya faɗi yana ƙoƙarin gyara tsayuwar shi kar riƙon da Barrah tai mishi yasa su faɗi. Ammi ya gani zaune tana mishi murmushi

“Ammi.”

Ya faɗi yana mayar mata da murmushi.

“Altaaf sannu da dawowa, an sha hanya ko?”

Kai Altaaf ya ɗaga yana ɗan turo laɓɓanshi.

“Na gaji sosai, jikina na min ciwo. “

Ya faɗi ba wai don yana jin gajiyar ba, sai don yana gaban Ammi, sangartar ce ta motsa mishi kawai. Cike da kulawa Ammi ta ce,

“Sannu, Barrah ki sake shi yazo ya zauna…”

Sake maƙale shi ma Barrah ta yi, tana sashi yin yar dariya, zaiyi kewar ciwon kan da take saka shi kwana biyu, yanzun ne yake jin har a zuciyarshi yafi son Barrah duk a cikin ‘yan uwan nashi, bai gane hakan ba saboda ta fi kowa takura mishi, kuma da wahala a rana bai taɓa lafiyar jikinta ba. Lokacin da ya cike makarantar jiyai kamar ya janyo kwanakin tafiyar tashi dln ya yi gaba abinshi ya huta da fitinarta kwana biyu. Amma yanzun kam har a ƙasan zuciyarshi yake jin ‘yar ƙanwar tashi. Riƙeta yayi a jikinshi yana faɗin,

“Ƙyale ta Ammi…”

Ya jata suka ƙarasa kan kujera ya zauna, tana zama a jikinshi.

“Yaya me ka siyo min?”

Ta faɗi cikin muryarta da take a taɓare ko da yaushe.

“Ban siyo miki komai ba.”

Altaaf ya faɗi yana ɗorawa da,

“Ɗauko min ruwa mai sanyi.”

Hararar shi Barrah ta yi.

“Baka siyo min komai ba ne zan ɗauko maka ruwa? Za ka bushe ashe…”

Mintsinar mata hannu Altaaf ya yi, ta kuwa kaima hannunshi duka tana murza wajen, idanuwanta na cikowa da hawaye. Kai ya tallabe mata sosai yana haɗa mata da wani duka a bayanta.

“Ammi kin ganshi ko? Me nai maka? Wallahi sai Allah ya saka min.”

Barrah take faɗi cikin kuka.

“Ɗaga ni don Ubanki.”

Altaaf ya ce yana ture ta. Hawayenta ta goge tana sake zama a jikinshi tana kumbura fuska da faɗar,

“Wallahi ba zan tashi ba, saina zauna duka na.”

Girgiza kai ya yi, yanzun ya fara kewarta amma har ta ishe shi, sai da Ammi ta miƙa mishi robar ruwa tukunna ya lura da ta tashi ma, karɓa ya yi ya buɗe yana sha, Barrah ta sauka daga jikinshi tana ɗaukar jakarshi tare da rugawa da gudu, babu shiri ya ajiye robar ruwan yana binta ya riƙo dam, jakar yake ƙoƙarin ƙwacewa don akwai kwalin sigari a ciki. Da ƙyar ya samu ya karɓa yana ɗagata sama tare da buɗewa ya zaro ledar siyayyar da ya yi ya miƙa mata yana maida numfashi.

“Ki ƙyale ni haka Barrah don Allah.”

Altaaf ya ce yana zage zip ɗin jakar tukunna ya dawo ya zauna.

“Kawo in ɗibar ma Autana.”

Ammi ta ce ma Barrah da ta tattara ledar gabanta tana maƙale kafaɗa.

“Ni kaɗai Yaya ya ba…Yaya wai har da Anam?”

Kai Altaaf ya girgiza yana faɗin,

“In kinga dama ki Sam mishi.”

Don ba zai ce da Anam ya siya ba ta zo ta fitine shi. Biscuit ɗaya da alewa biyu ta ba wa Ammi tana wucewa ɗaki abinta. Gefe Ammi ta ajiye ta mayar da hankalinta kan Altaaf.

“Ya Zaria? Ka samu gidan kuwa?”

Kai ya jinjina mata, yana amsawa da,

“Alhamdulillah, na samu fa Ammi.”

Kafin ya ci gaba da bata labarin yadda suka hadu da Ruƙayya da kuma yayanta Imran da yadda gidan tare da Imran ɗin ne ma zasu kama, shi ba zai biya duka ba, za su raba kuɗin ne, yana barin ɓangaren da bai kamata ta sani ba, ya ƙarashe labarin da faɗar karamcin Imran ɗin. Sosai Ammi ta ji daɗin jin har Altaaf ya samu abokai masu kirki haka. Hirarsu suka cigaba da yi da Altaaf ɗin a nutse.

* * ***

Washegari Ammi da wuri ta je banki ta tura ma Wadata kuɗin hayar Altaaf ɗin, don sa’adda ta fita ma Altaaf bai tashi daga bacci ba, har sai da ta dawo ta dafa farar shinkafa tunda tana da miya a fridge. Ta kwashe tukunna ta je ta tashe shi ya shirya su fita kasuwa su siyo abubuwan da zai buƙata.

“Ammi anjima, bacci nake ji.”

Altaaf ya faɗi kamar zai yi kuka yana jan pillow ya gyara kwanciyarshi, pillow ɗin Ammi ta zame don har an yi Azahar, in ta biye wa Altaaf ba fitar za su yi ba.

“Ka tashi fa Altaaf. Ka ga siyayyarmu da yawa, rana na yi.”

Tashi zaune ya yi yana murza fuska, kafin ya duba agogo, taɓare wa Ammi fuska ya yi.

“Cikin ranar nan Ammi?”

Kai ta ɗaga mishi.

“In sha Allahu, tashi ka yi wanka.”

Miƙewa ya yi yana wata tafiya a dole bacci yake ji, yanayin shi gaba daya yana saka zuciyarta nauyi da sanin kwanaki kaɗan ya rage ya tafi makaranta, Altaaf ne zai zauna shi kaɗai a wani waje bayan ko kula da kanshi bai iya ba. Ficewa ta yi daga ɗakin tana zuwa ta ɗauki kuɗi da jakarta, ta ɗauko mayafi tana fitowa falo ta zauna jiran Altaaf ɗin. Ya kai mintina sha biyar ko bayan nan, sannan ya fito ya saka wata riga fara ƙal mai dogon hannu da irin dogon wuyan nan, sai baƙin jeans, kyawunshi ya matuƙar fitowa.

“Allah ya kare min kai daga sharrin maƙiya.”

Ammi ta faɗi tana murmushi, shagwaɓe fuska kawai Altaaf ya yi don bacci ne a idonshi sosai. Haka suka fara zuwa super market don tai mishi siyayyar kayan ciye-ciye. Haka ya dinga binta a baya, inta tsaya duba abubuwa zai wani langaɓe a jikinta yana kwantar da kanshi a kafaɗarta a dole bacci yake ji, bai damu da mutanen da ke wajen suna kallon shi ba, don wannan matsalarsu ce, shi tashi matsalar baccin da yake ji ne kawai. Haka har kasuwa ma da suka je siyan kayan sawa, don ma suna da shagon da suke siyayyarsu, suna komawa gida kam a falo ya kwanta kan kujera yana ci gaba da baccin shi.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 3.3 / 5. Rating: 3

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Alkalamin Kaddara 24Alkalamin Kaddara 26 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×