Skip to content
Part 26 of 52 in the Series Alkalamin Kaddara by Lubna Sufyan

Tura ƙofar ɗakin ya yi yana shiga, numfashi ya sauke a gajiye ya cilla wayarshi kan gado, bangon da ke gefenshi ya dafa yana zare takalman ƙafarshi. Ya sha yawo, da gidansu Ashfaq ya je ƙarshe zai yi kwanciyarshi ne don ya gaji sosai. Washe garin ranar zai tafi makaranta, duk da an kawo mishi motarshi tun jiya, amma bada ita ya fita ba yau, yadda yake ɗokin mota kafin ya yi tashi, har mamaki yake yi yanzun da ya ji ta fitar mishi akai kuma. Sai yanzun ya gane duk ɗokin motar da yake yi don ba shi da ita ne.

Kwanciya yayi kan bayanshi yana jan ƙafafuwa ya haɗe su da jikinshi yadda zai iya kai hannuwanshi yana murza tafukan ƙafafun da yatsun shi da suke mishi ciwo, ya yini da takalma, tunawa ya yi bai yi sallali ba, ranshi a ɓace ya tashi zaune yana shiga banɗaki ya ɗauro alwala tukunna ya dawo ya fara jero salloli, yana jin Aslam ya shigo ɗakin da sallama, ya samu waje gefen gado ya zauna. Sai da ya idar da sallolinshi kaf tukunna ya gyara zamanshi kan dardumar yana juyawa ya kalli Aslam ɗin da faɗin,

“Ya akayi?”

A nutse Aslam yake kallon Altaaf ɗin, yadda ya ɗauki rayuwa na bashi mamaki, ba yau ya fara ganin yana haɗa salloli ba, don ya sha suna zaune a kira Sallah ya tafi masallaci ya bar Altaaf ɗin, Asuba ma kashedi yai mishi kar ya ƙara katse mishi bacci ya dinga ƙyale shi sa’adda ya tashi yayi abinshi. Yana tsoron faɗan Altaaf shi yasa bai mishi magana kan Sallah ba tuntuni, amma yanzun kam lokaci ya yi da zai mishi, ko da kuwa zai ɓata mishi rai ne.

“Gobe in Allah ya kaimu za ka tafi ko?”

Aslam ya tambaya cikin sanyin murya. Kai Altaaf ya ɗaga mishi da wani yanayi a fuskarshi na rashin fahimtar dalilin tambayar Aslam ɗin tunda ya riga ya sani. Numfashi Aslam ya ja yana fitarwa a hankali.

“Bansan ta ina zan fara ba…”

Ɗan ɗaga mishi kafaɗa Altaaf ya yi.

“Ka fara ko ta ina…bacci nake son yi, jikina na min ciwo.”

Kai Aslam ya ɗaga, kafin ya soma magana a nutse.

“Sallah na daga cikin muhimman abubuwa a rayuwar musulmi Yaya… Ba tun yanzun ba na kula kana wasa da ita sosai, abin yana damuna amma ina tsoron yi maka magana, yanzun ma da ƙyar na zo saboda sakamakon lahirarka na da muhimmanci a wajena… Kuma in ban faɗa maka ba bansan waye zai faɗa maka ba…”

Sosai Aslam yake kallon yadda Altaaf ɗin ya nutsu yana sauraren shi.

“Na san ba Sallah kaɗai bace matsalarka, don Allah ka gyara Yaya…ka ga za ka tafi wajen da babu wanda ya san ka, babu wanda zai maka faɗa ko ya gaya maka gaskiya, don Allah addininka ya zama farko a duk al’amuranka, ban isa in maka faɗa ba na sani, amma na isa in faɗa maka gaskiya ko da baka son jin ta.”

Wannan karon Altaaf ne ya sauke numfashi, yasan dai wa’azi ne Aslam ɗin yake mishi, tunda daga wajen Sallah na daga cikin muhimman abubuwa, ya daina gane komai, asalima sigari yake son busawa, yana kuma tunanin yadda zai shata a cikin ɗakin ba sai ya fita waje ba don a gajiye yake sosai.

“Yayaa… Kana jina ma kuwa?”

Aslam ya faɗi yana kallon Altaaf ɗin, kai Altaaf ya ɗaga mishi yana yin wata doguwar hamma.

“Yeah na ji ka. Na gode sosai, Allah ya ƙara malunta.”

“Ba Allah ya ƙara malunta ba, don Allah ka gyara.”

Aslam ya ƙarashe maganar da sanyin murya, don Altaaf ko kaɗan bai nuna alamun nasihar ta shige shi ba. Tashi ma yayi daga kan dardumar yana kama kafaɗar Aslam ɗin.

“Tashi ka je sai da safe, bacci nake ji.”

“Yaya…”

Aslam ya fara, Altaaf ya katse shi da,

“Sai na zagi ƙanwar uwarka ne za ka ƙyale ni Aslam?”

Murmushi Aslam ya yi yana miƙewa, Altaaf ɗin na tura mishi baya.

“Fita zan yi Yaya.”

“Baka sauri ne ai na gani.”

Altaaf ya faɗi yana ci gaba da tura Aslam ɗin har ƙofa ya mayar ya kulle yana murza mukullin, kar Barrah ta shigo mishi, yadda yake jin gajiya a jikinshi bai da ƙarfin ko zaginta balle kuma duka da yasan ƙa’ida ne don rikicinta ya yi yawa. Ko wanka bai yi ba ya kwanta, bacci mai nauyi ya ɗauke shi.

*****

Bai tashi ba sai ƙarfe goma na safe, lokacin da ya yi wanka ya gama shiryawa sha ɗaya ta yi, falo ya fito yana ganin Ammi a zaune

“Altaaf ɗan Ammin shi, haka maƙiya za su ganka su bar min kai.”

Murmushi Altaaf ya yi.

“Ammi na, ina kwana.”

“Ammin mu dai…”

Ya ji muryar Barrah a bayanshi, bata ma bari Ammi ta amsa gaisuwar da yai mata ba. Ammi ya kalla yana daƙuna fuska.

“Kinga Barrah ko?”

Ya faɗi, dariya Ammi ta yi.

“Jeka karya ƙyale Barrah.”

Takawa ya yi yana samun waje ya zauna a tsakiyar falon kan kafet daga gefen Ammi.

“Nan ya fi daɗin zama…”

Ya faɗi yana kallon Ammi da ta miƙe tana nufar dining table ɗin ta ɗauko mishi kayan karin, Barrah ta ƙarasa ita ma ta zauna tana ɗora kanta a gefen hannunshi, tureta ya yi.

“Ɗagani dalla can.”

Sake komawa ta yi.

“Me yasa za ka tafi?”

Ta tambaya a hankali, yana jinta ba shi da amsar da zai bata ne don haka ya yi shiru kawai yana ɗaukar soyayyar doya ya saka a bakinshi.

“Yaya me yasa zaka tafi? Kana jina fa.”

Ta ƙarasa a taɓare.

“Don Allah ki barni kafin doya ta biyo min ta hanci.”

Ammi na jinsu bata ce komai ba, ita ma tambayar da ke ƙasan ranta kenan, me yasa Altaaf ɗin zai tafi, me yasa zai yi nisa da gida har haka. Tana jinjija wa mutanen da ke kai yaransu wata ƙasar karatu, jiya ko baccin kirki bata yi ba saboda tunanin tafiyar Altaaf ɗin, kewarshi na danne ta tun yanzun. Anam ne ya fito da riga a hannun shi, murmushi Altaaf ya yi, yaron ba shi da hayaniya, zai iya yini a ɗaki in ba makaranta.

“Anam…”

Ya kira, kallonshi Anam ya yi yana saka riga a jikinshi tukunna ya mayar da hankalinshi kan Ammi.

“Ina jin yunwa.”

Yaron ya faɗi kamar Altaaf bai mishi magana ba.

“Kaifa shegen miskilanci ne matsalata da kai. Zo mu ci a nan.”

Altaaf ya sake faɗi, takawa Anam ɗin ya yi kamar zai je wajenshi ya fasa yana wucewa wajen Ammi ya zauna.

“Ammi kina ganin yaronki ya shareni ko?”

Altaaf ya faɗi.

“Allah ya ƙara, nima ba ka shareni ba.”

Barrah ta ƙarasa maganar tana dariya, tureta Altaaf ya yi yana harararta, bata damu ba ta sake mayar da kanta a jikinshi. A hankali ya gama karyawa ya miƙe yana komawa ɗaki ya sakko da takalman shi ya ɗauko jakarshi ta goyo da ya haɗa ‘yan ƙananan abubuwan da yake buƙata a ciki ya fito da mukullin motarshi a hannunshi.

“Ammi na shirya.”

Yace don tun jiya da yamma komai yana mota an saka mishi. Miƙewa ta yi tana kallonshi fuskarta ɗauke da yadda za ta yi kewarshi, ƙarasawa ya yi inda take tsaye yana shagwaɓe fuska

“In kina nuna yanayin nan kuka zan yi Ammi.”

Murmushi ta yi, yana mayar mata da shi shima.

“Don Allah ka kula, banda zama da yunwa, in kana son wani abu ka kirani, kuma banda daɗewa ba’a zo gida ba.”

“Kewarki ba za ta barni in daɗe ban zo ba Ammi.”

Ɗan hararar shi ta yi.

“Kamar da gaske…”

Ɗaga mata kai yake yi yana faɗin,

“Da gaske, ke ce fa favorite woman ɗina a duka duniyar nan.”

Wannan karon ‘yar dariya Ammi ta yi, za ta yi kewar ɗan nata sosai. Har bakin mota suka raka shi ita da Barrah da ta kama mishi riga ta riƙe dam idanuwanta na cikowa da hawaye. Fuskarta Altaaf ya tallafa cikin hannuwanshi.

“Barrah ba zan daɗe ba zan dawo ai.”

“Ni zan bika.”

Ta faɗi hawaye na zubo mata, numfashi ya sauke yana riƙe ta a jikinshi. Kuka take yi tana sashi jin wani iri, Ammi ya kalla yana roƙonta da idanuwanshi da ta taimaka mishi, zuwa ta yi ta kama Barrah tana riƙeta. Altaaf ɗin ya zagaya ya buɗe mota, yana jin Barrah na faɗin,

“Ammi me yasa zai tafi?”

“Zai dawo ai…”

Ammi ta ce, murfin motar ya ja ya rufe ya sauke glass yana faɗin,

“Ammi na tafi. Ki kula da kanki, sai mun yi waya.”

Kai kawai ta iya ɗaga mishi, tana binshi da addu’ar Allah ya tsare hanya har ya fita daga gidan, sun ɗan jima a tsaye ita da Barrah kafin ta kama hannunta data fisge tana rugawa cikin gida, a nutse Ammi take takawa zuwa cikin gidan, tana jin yadda yai mata shiru da tafiyar Altaaf ɗin.

* * ***

Da nishaɗi ya ƙarasa gidansu na Zaria. Jamal da Wadata ya samu a ƙofar gidan a tsaye. Ya buɗe motar yana fitowa, tunda aka kawo motar bai ji daɗinta irin yanzun ba, saboda yana kallon yadda ta siya mishi mutunci a idanuwan Jamal.

“Maza…”

Wadata ya faɗi, murmushi Altaaf ya yi yana miƙa mishi hannu suka gaisa, tukunna ya ba wa Jamal hannu shi ma.

“Barka da dawowa.”

“Na gode. Yaks fa?”

“Ya je tutorial na math.”

Jamal ya faɗi yana sa Altaaf ɗin daƙuna fuska. Me Yaks zai yi da tutorial, ko kaɗan bai mishi kalar marassa galihu ba, iya sanin shi su ne suke buƙatar karatu. Bai ce komai ba, taya shi shigar da kayayyakin shi suka yi cikin gidan. Wadata na faɗin,

“Me za ka yi da duk kayan nan?”

Kafaɗa Altaaf ya ɗan ɗaga mishi.

“Ammi ce fa.”

Girgiza kai Wadata ya yi yana gane inda sangartar Altaaf ɗin ta fara, takalma Altaaf ya cire yana kwanciya kan katifar da ke ɗakin. Kallon shi Wadata ya yi

“Me kakeyi haka?”

“Bacci nake ji.”

Altaaf ɗin ya amsa yana lumshe idanuwanshi. Kai Wadata ya girgiza.

“Tashi, wannan kayan waye zai shirya maka su?”

“Baku da mai aiki?”

Altaaf ya ce yana gyara kwanciyarshi, wata dariya Wadata yayi da ke fassara ‘Baka da hankali ko?’Ba kuɗin kawo ‘yar aiki bane basu da shi, Wadata na yin komai da taka tsan-tsan ne. Baya son ko kaɗan, baya son abinda yake yi ya kai kunnen babanshi. Yana kuma da tabbacin’ yar aiki ta zo gidan nan da sunan ta yi musu aiki ta tafi koda na mintina talatin ne, in bata zubar da cikin Yaks ba to zata zubar da na Jamal. In kuma suka ɗauko tsohuwa akwai damuwa, bakinsu baya shiru, sa’idon tsofin mutane na bashi tsoro. Don haka suke raba aikin gida wasu lokuttan ko ‘yan matansu su yi musu.

“Ka tashi mu shirya kayan, ɗakin zai fi maka daɗi inka kimtsa komai, ina so in fita ne, ka ga akwai makaranta gobe da safe.”

Maƙale kafaɗa Altaaf ya yi, bacci yake ji, kayan za su iya jira har ya tashi.

“Kaje abinka ni bacci zan yi.”

Ƙyaleshin Wadata ya yi, asalima ja mishi ƙofar yai bayan ya fita, shi kuma ya gyara kwanciyarshi, akwai amana tsakanin shi da bacci, musamman da rana yammaci haka, tunda ba samun wadatacce yake yi da dare ba. Baccin shi ya sha har bayan Magriba tukunna ya tashi ya shiga banɗaki ya watsa ruwa ko jikinshi da yai nauyi zai sake mishi, har ya fito ya koma yayi alwala ya dawo, kan katifa ya zauna yana janyo ɗaya daga cikin akwatinan shi ya buɗe yana soma fiffito da kayayyakin ciki, har sai da ya zaɓi wani jeans blue sai jar riga ya ajiye kan gado, sai dai me? Ya kasa mayar da kayan.

Mamakin yadda Ammi ta shirya tulin kayan cikin akwatin yake yi, ba yadda bai yi ba, har tashi yayi ya sa hannuwa ya danna kayan amman sun ƙi, ƙyale su yayi ya tashi ya sake kayan jikinshi, wanda ya cire ɗin yana barinsu nan, ya riga ya saba, inda ya cire kaya nan yake bari bai taɓa tunanin yin wani abu bayan haka ba, ko gado bai iya gyarawa ba, duk sa’adda zai fita ya bar ɗaki a hargitse in ya dawo an gyara an tattara kayan da ya cire kuma, sai dai ya gansu da gugarsu a wardrobe ɗinshi.

Agogon wayarshi ya duba ya ga bakwai da mintina biyar, kwanciya yayi yana jiran a kira isha’i ya haɗa ya yi su gaba ɗaya, don baya son rarraba sallah. Hakan yayi yana idarwa ya miƙe ya fita zuwa falon, babu kowa sai Yaks a zaune kan kafet ya baza takardu da alama nazari yake yi, sai da Altaaf ya ga takeway ɗin dake gefenshi ne tukunna ya ji yunwar da yake ji ta saukar mishi gaba ɗaya har cikinshi yana ƙullewa. Kan kujera ya zagaya ya zauna yana kwantar da kanshi a jikin hannun kujerar.

“Kana ciki ashe.”

Yaks ya faɗi yana ɗorawa da,

“Na ɗauka kun fita da su Wadata ne.”

Kai Altaaf ya girgiza ma Yaks, muryarshi can ƙasa ya ce,

“A’a, Jamal ya ce min ka je tutorial.”

“Wallahi kuwa. Math ɗin nan yana neman bani matsala… Wane course aka baka?”

“English fa”

Altaaf ya amsa, jin Yaks yayi shiru yasa shi cewa,

“Kaifa?”

“Quantity Survey.”

Maimaitawa Altaaf yayi don bai taɓa jin course ɗin ba a rayuwarshi.

“Har su Wadata? Course ɗaya kuke karanta?”

“A’a shi da Jamal suna Civil Engineering ne.”

Ware idanuwan Altaaf ya yi, don yasan Engineering ba ɓangare bane me sauƙi, yanayin shi ya ba Yaks dariya, ƙarar yunwa cikin Altaaf ɗin ya yi.

“Cikinka ne yake ƙara haka?”

Yaks ya tambaya, ‘yar dariya Altaaf ya yi.

“Ka ɗauko abincinka a kitchen, na siyo mana da zan dawo.”

Miƙewa Altaaf yayi da sauri yana faɗin,

“Karka gayama Wadata, na fi sonka a yanzun nan.”

Yana jin dariyar Yaks ɗin, aikam takeaway ne guda shida, bibbiyu a haɗe, kitchen ɗin tsaf-tsaf komai a jere kamar na Ammi. Ɗaukowa ya yi ya fito ya zo ya zauna, yana ci suna ɗan hira da Yaks ɗin , a wajenshi yake jin shi da su Wadata duka suna shekararsu ta ukku kenan a makaranta, ma’ana sun wuce Altaaf ɗin da aji biyu, bai yi mamaki ba duk da tsayinshi zaizo ɗaya dana Yaks da Jamal, Wadata ne dogo sosai yasan sun girmeshi.

Ranar ma basu kwanta ba sai sha biyun dare don abokan su Wadata sun zo musu, ranar kuma hankalin Altaaf kwance ya bushi sigari, don ya ga Yaks ma yana shan sigarin, bai da tabbas kan Wadata da Jamal.

*****

Bacci yake me nauyi ya ji ana bubbugashi.

“Barrah ranki zai ɓaci.”

Altaaf ya faɗi muryarshi cike da bacci, yana jan pillow ya gyara kwanciyarshi, ya manta cewar ba’a gida yake ba. Bubbugashi ya ji an sake yi.

“A-Tafida ka tashi lokaci na tafiya fa.”

Sai da ya ji an ce A-Tafida tukunna yasan ba’a gida yake ba, a hankali ya buɗe idanuwanshi yana ware su kan bangon ɗakin, kafin komai ya soma dawo mishi, juyowa ya yi da sauri yana kallon Wadata.

“Baccinka yayi yawa… Ka tashi ka shirya.”

Kai kawai Altaaf ya iya ɗaga mishi, duk da akwai haske a ɗakin bai hana shi janyo waya ya duba agogo ba, ƙarfe shida da rabi na safe, shi yasa yake jin kamar bai yi wani bacci ba. Da ƙyar ya ja ƙafafuwa zuwa banɗaki ya yi wanka ya ɗauro alwala, har ya idar da sallah bai daina hamma ba, kaya ya sake hargitsowa ya ɗauko wanda zai saka, wanda ya cire ma nan ƙasa ya bar su yana fita falo. Muryar Wadata da Yaks ya jiyo ta hanyar kitchen ɗin ya nufi can. Wainar ƙwai ce Wadata yake soyawa, Yaks kuma ya haɗa tea yasa cokali a ciki ya buɗe fridge ɗin da sai lokacin Altaaf ya kula yana nan ya ɗibi cake yana ɗan ɗaga ma Altaaf kai tukunna ya wuce.

“Me za ka ci?”

Ɗan daƙuna fuska Altaaf ya yi, shi ba son shan shayi yake yi da safe ba.

“In munje makaranta na ci wani abu.”

“Karka fita cikinka babu komai, ko ruwan Tea ka sha ga wainar ƙwai.”

Kai Altaaf ya ɗaga mishi yana zuwa ya ɗauki cup da cokali, gwangwanin madara dana Milo ya ɗauka yana buɗewa ya zuba, ya ce ma Wadata,

“Ya isa haka?”

Kallon shi Wadata yake da mamaki a fuskarshi.

“Ka daina kallo na haka…Ya isa ko sai na ƙara?”

“Me kake yi da rayuwarka?”

Wadata ya tambaya yana ma Altaaf ɗin wani irin kallo.

“Barshi tunda ba zaka faɗa min ba.”

Cewar Altaaf yana rufe gwangwanin madarar ya ɗibi Sugar cokali ɗaya ya zuba, sake ɗiba zai yi Wadata ya ce,

“Baka da hankali? Yayi yawa.”

“In na tambayeka za ka tsaya min kallon banda wani amfani.”

Zuwa Wadata ya yi ya karɓi Cup ɗin daga hannun Altaaf yana ture shi.

“Matsa mon, kana da amfanin ne?”

Dariya Altaaf ya yi, Wadata ya haɗa mishi shayin yana miƙa mishi. Karɓa yayi ya kurɓa, da zafi sosai, furzo da shi yayi yana ajiye cup ɗin.

“Kashe ni za ka yi ne Wadata?”

Wannan karon Wadata ne yake dariya, tea ɗin ya haɗa shima yana ɗaukar plate ɗin wainar ƙwan shi.

“Ba za ka fifita min ba?”

Altaaf ya ce yana ɗaukar nashi Cup ɗin zai bi bayan Wadata.

“In ka biyo ni saina watsa maka Tea ɗin nan.”

Ya ce yana harar Altaaf ɗin da ke mishi murmushi da haƙoranshi duka a waje. Girgiza kai Wadata ya yi, babu yadda za’ai Altaaf ba zai shiga ranka ba, akwai abubuwa a tattare da shi da za su baka mamaki, takaici da dariya a lokaci ɗaya, yana cikin irin mutanen da za ka haɗu da su sau ɗaya su tsaya maka a rai na tsayin lokaci. Suna gama karyawa suka fita, mukullin gidan Wadata ya ba Altaaf shima, ko da zai dawo babu kowa yana da nashi.

Su duka kowa na da mota, duk da gasu ga makaranta ba wata tafiya bace ba. Altaaf barin tashi motar yayi ya shiga ta Wadata

“Me kake min a mota?”

“Bansan inda zan yi ba. Sai ka nuna min ajina fa.”

Shiru Wadata yai mishi yana jan motar suka wuce. Har bakin ajinsu Altaaf ya ƙarasa da shi, babu inda Wadata bai sani ba a cikin makarantar.

“Ni yau sai ƙarfe huɗu zan tashi…”

“Ba zaka fito ka rakani ba?”

Altaaf ya faɗi yana wani ware mishi idanuwa.

“Fita kafin in watsa maka mari.”

Dariya ya yi yana buɗe murfin motar ya fita, sosai halayen Wadata ya banbanta da na Ashfaq, amma yana mishi kewa yana yi da shi ta fanni da dama. Hular shi ya ja sosai yana shiga ajin, daga tsakiya ya samu wuri ya zauna. Lectures biyu suka yi da safiyar kafin su fita sai kuma ƙarfe biyu, har ya yi abokai guda huɗu don tare suka tafi suka ci abinci, Altaaf ɗin ya siya musu lemuka, yawo suka shiga yi a cikin makaranta, yau dai ya yi Sallah a masallaci ba ranar juma’a ba, kuma yayita kan lokaci saboda abokan sun jashi masallaci.

*****

Ba zai yi ƙarya ba yana jin daɗin makaranta sosai, abinda yake so shi yake yi. Mata ne gasu nan birjik suna kawo kansu kullum, musamman da suka ga yana tare da Wadata, don a zamanshi yanzun ya gane Wadata na cikin manyan gayun da aka sani a jami’ar. Kuma ɗan tsohon ministan kuɗi ne, sannan Yaks da Jamal ma iyayensu masu farcen susa ne suma. Shi yasa tafiyar ta zo musu ɗaya, duk wata yake zuwa gida ya yi kwana biyu, yanzun gashi watanshi na biyar kenan a makaranta har sun fara test jarabawa na gabatowa.

Kwance yake a ɗakin shi, yasa abin jin Kiɗa a kunnuwanshi, don haka bai ji shigowar Wadata ba sai da ya ga giccin shi, abin kunnen ya zare yana bin Wadata da ke tattara kayayyakin Altaaf ɗin da suke ko ina a ɗakin.

“Bansan me yake damunka ba wallahi. Ya zan iya bacci a ɗakin nan haka, kai ba ka jin kunya wani ya shigo?”

Da ido Altaaf yake binshi, dama yayi niyya in Anisa ta shigo da dare ranar yace ta gyara mishi kafin Wadata ya zo ya gani.

“Har kwando na kawo maka, ba zai kasheka ba in ka cire kayanka ka saka a ciki. In mai wanki yazo zai ɗauka, amma son jiki ba zai barka ba…”

Daƙuna fuska Altaaf ya yi yana faɗin,

“Zan gyara dama ai.”

Hararar shi Wadata ya yi yana ƙarasa tattara sauran kayan ya zuba a kwandon, ledojin biscuit ne da alewowi ko’ina a cikin ɗakin. Baisan ya zai yi da Altaaf ba, inda ya ci komai nan yake bari, sai dai in shi ya shigo ɗakin ya ga dattin na shigar mishi ido ya gyara. Don bai son ƙazanta ne da ya ƙyale Altaaf ɗin, to bola zai mayar da ɗakin, babu abinda ya iya, asalin sangartacce ne. Idanuwan shi ne suka sauka kan wata takarda, har zai wuce ya koma yana ɗaukowa. Dubawa ya yi ya ga takardar test ce, cikin sha biyar, ɗaya da rabi Altaaf ya ci, ware idanuwa Wadata ya yi. Ya nemi waje ya zauna.

Hakan na sa Altaaf ɗin tashi zaune ya fisge takardar ya duba. Ɗan ƙaramin tsaki ya ja don ya ɗauka wani abin ne daban.

“Meye wannan A-Tafida?”

Wadata ya tambaya, ɗan taɓe mishi baki Altaaf ya yi yana wani ƙanƙance ido alamun abin bai dame shi ba. Jakarshi da ke ajiye a gefe Wadata ya kai hannu zai ɗauka, Altaaf ɗin ya janye gefe, hakan yasa Wadata tashi tsaye ya riƙo jakar, amma Altaaf ya ƙi saki, don duk test da assignment score ɗinshi na ciki kuma babu wanda ya wuce uku da rabi, bai taɓa damuwa da rashin ƙoƙarin shi ba, yanzun ɗin ma bai damu ba, baya so dai Wadata ya gani ne kawai. Hannunshi Wadata ya kama yana murɗewa.

“Wadata zaka karya ni ne?”

Altaaf ya faɗi cikin ƙara ji don ya ji riƙon da Wadata ya mishi ba kaɗan ba.

“Saki don Ubanka.”

Babu shiri ya sakarma Wadata jakar, ɗauka ya yi yana fita da ita falo, Altaaf ɗin ya sauko ya bi bayanshi yana murza hannu. A tsakiyar falon ya zazzage jakar Altaaf ɗin yana fito da duk takardun da ke ciki. Dubawa yake yana ajiye su gefe, su Yaks sun dawo da hankalinsu kan Wadata ɗin, sai da ya gama tukunna ya miƙa musu yana faɗin,

“Ku kalli abinda yaron nan yake yi.”

Jamal ne ya fara dubawa yana ware ido da faɗin,

“Innalillahi….A-Tafida…”

Don shi bai san yana da ƙoƙari ba sai da ya zo ABU ya kuma haɗu da Wadata, daga shi har Yaks ɗin Wadata yasa suka soma karatu, don bai yarda da faɗuwa ba a rayuwarshi, yakan ce musu ku yi iskanci mai aji, iskancin da za’a girmamaku saboda ku ba daƙiƙai bane ba, labarin iskancinku ko ya kai gida ba zai yi tasiri ba saboda sakamakon makarantarku me kyau ne. Sun kuma ga ranar hakan, din shi kanshi yana jin daɗin kasancewa cikin masu ƙoƙarin ajin dan shi ne na biyu a ajinsu. Wadata kam tun daga aji na ɗaya shi ne yake wuce kowa a komai.

Juyawa Wadata ya yi yana kallon Altaaf ɗin, saboda yaune rana ta farko da ya ɓata mishi rai, ji yayi kamar takardun Ruƙayya ne ya gani, don har ranshi yana jin Altaaf kamar ƙanin shi.

“Baka karatu ko?”

Yaks ya tambaya. Kan hannun kujerar da Wadata yake Altaaf ya zauna.

“Marasa galihu sune suke karatu, ni ba abinda zan yi da shi.”

Wata irin dariya Jamal yayi, Yaks na faɗin,

“Tashi daga nan…”

Da rashin fahimta yake Altaaf yake kallon shi.

“Ka tashi na ce.”

Tashin yayi kuwa yana sake waje, tukunna ya kula da kallon da Wadata yake mishi, ya gane dalilin da yasa Yaks yace ya tashi daga kusa da shi don gab yake da kwaɗa mishi mari. Bai san rashin hankalin Altaaf ya kai haka ba.

“In za ka yi iskanci ka yi me aji mana, ta yaya za ka yi iskanci da daƙiƙanci? Wa za ka burge? Ko baka tunanin barin wannan rayuwar ne nan gaba? A ɗan iska za ka dawwama?”

Ware mishi idanuwa Altaaf ya yi.

“Ammi na da kuɗi…”

“Idan baka rufe min baki ba ranka zai ɓaci Altaaf, wallahi baka da hankali, Za’a kore ka, ba zaka zauna a makarantar nan ba.”

Cikinshi Altaaf ya ji ya ƙulle, don yana bala’in son makarantar. Jinjina mishi kai Wadata yake yi.

“Ba secondary ba ne nan da za ka dinga zuwa na ƙarshe babu wanda ya damu da kai, nan za su kore ka ne.”

Fuskar Altaaf ɗauke da damuwa yake kallon Wadata

‘Bana so a kore ni.”

“Sai ka fara karatu kenan.”

Jamal ya faɗi yana dariya. Hankalin Altaaf kuma na kan Wadata don ya ga ya ɓata mishi rai sosai, a lokacin ne kuma yasan Wadata ya shiga layin mutanen da ra’ayinsu akanshi yake da muhimmanci.

“Wadata…”

Ya kira da wani yanayi a muryarshi

“Zaka fara karatu, ko ka fara karatu ko mu raba hanya… Bana son rashin aji, daƙiƙanci na cikin wannan layin.”

Ya ƙarasa maganar yana miƙewa ya bar falon. Su Yaks ya kalla.

“Maza sai ka yi karatu fa.”

Yaks ya ce yana tattara takardun Altaaf ɗin ya mayar da su cikin jakarshi da ke ajiye a wajen.

“Wadata ya ɗauke ka kamar ƙaninshi, ba zai so a koreka ba, don Allah ka gyara kafin a fara jarabawa.”

Tashi Altaaf ya yi yana nufar ɗakin Wadata, ƙofar a buɗe take don haka ya shiga, ɗakin tsaf da shi, har gadon a gyare yake, yana mishi yanayi da ɗakin Ashfaq wajen tsafta. Jikin bango ya jingina kafin ya ce,

“Babu abinda zanyi da takardun makaranta, ban taɓa ra’ayin aikin gwamnati ba, ina son yin kasuwanci kamar Ammi ne, na kuma san banda matsalar hakan. Makaranta bata da muhimmanci a wajena da ya wuce nishaɗi…”

Ba tare da Wadata ya kalle shi ba ya ce,

“Me yasa kake faɗa min?”

Ɗan ɗaga kafaɗa Altaaf ya yi.

“Saboda bana son a koreni, ba zai yiwu ba kuma sai na yi karatu.”

“Sai ka fara ai.”

Ɗan murmushi mai sauti Altaaf yayi, din ya ga alamar Wadata bai gane me yake nufi ba, fara karatu a wajenshi ba ƙaramin aiki bane ba, saboda bai iya ba. Yau da gobe ta sa ya ji turanci ya kuma iya rubutawa ya karanta, shi ma wasu kalaman da ya sani in zai rubuta su ba za su fito daidai ba.

“Sai ka taimaka min, bansan ta inda zan fara ba…wannan zai zama karo na farko da zan fara karatun makaranta…”

Sai lokacin Wadata ya kalleshi, ganin fuskarshi yayi babu alamun wasa, da gaske yake yi wannan ne karo na farko da zai yi karatu. Goshin shi Wadata ya dafe.

“A-Tafida fita, jeka kawai, kaina na min ciwo.”

“Karatun fa?”

Altaaf ya faɗi, pillow Wadata ya ɗauka yana jifanshi da shi, ganin bai tafi ba ya tsaya yana dariya yasa shi taku biyu da gudu Altaaf ɗin ya fice daga ɗakin. Numfashi Wadata ya sauke, yaron ya gama ɓata mishi rai yau ɗin nan, sam bai yarda akwai daƙiƙi ba, ya yarda wasu sun fi wasu saurin fahimta da wuri, inda za’a bi kowa a yanayin ƙwaƙwalwar shi babu wanda ba zai samu grade masu kyau ba.

*****

Sa Altaaf ya yi karatu ba ƙaramin aiki ya zame ma su duka ukun ba. Yaks ne ya je department ɗin su Altaaf ɗin tare da shi suka tattara duka wani handouts da suke amfani dashi. Suka kuma rarraba kowa ya ɗauki abinda yake tunanin zai iya taimaka ma Altaaf da shi. Amma yanayin ƙwaƙwalwar Altaaf ɗin na ba Wadata mamaki, kamar tunda aka halitta mishi ita bai taɓa amfani da ita ta wannan ɓangaren ba, yanzun kuma da buƙatar hakan ta taso bai san ta inda zai fara ba.

Saboda Altaaf ɗin ya hana su kawo mata, kaf abokansu ce musu yai su nemi wani wajen kafa dandalin sai bayan jarabawa, don ya maida hankalinshi duka kan karatun ammansai hamdala. Ga shiriritar Altaaf ta fi ƙarfinshi, don ma yana ganin girman Wadata. Yanzun ma ya saka shi a gaba ne ya ce ya yi karatu, su kuma suna hira da su Wadata.

“Abdul ya kirani ɗazun fa. Satin nan za’a fara game ɗin nan.”

Yaks ya faɗi, Jamal na faɗin,

“Nima Idris ya min magana…wai mutun 20 suka ce wannan karon ko?”

“Na ga kamar anyi yawa ma…”

Cewar Wadata. Kai Yaks ya girgiza mishi.

“Ba’a yi yawa ba, waccan shekarar fa mutum talatin suka ɗauka, aka ɗauki winners uku. Wadata ka kwafsa mana wallahi.”

Dariya Wadata ya yi.

“Me na kwafsa muku?”

Jamal ne ya harare shi yana faɗin,

“Baka ma san me ka yi ba? Ka fa kai stage ɗin ƙarshe kawai ka janye.”

Da murmushi a fuskar Wadata ya ce,

“Kun fi kowa sanin halina, bana haɗa shimfiɗa da yarinya ba da amincewarta ba, ba kuma na haɗa shimfiɗa da ita bata cikin hayyacin ta.”

“Saidai ka jata ta soka kamar ranta inka samu abinda kake so ka wurgar da ita ko?”

Yaks ya buƙata, dariya Wadata ya yi.

“Ya fi min sauƙi, ko me zai faru da amincewa ta.”

Kallon su Altaaf yake yi.

“Zan yi game ɗin.”

Ya faɗi yana saka su duka ukun girgiza mishi kai lokaci ɗaya. Wadata na ɗorawa da,

“Na ɗauka karatu kake yi?”

“Karatu nake, amma kunne na bai da wani zaɓi tunda kuka kira mace.”

Dokar mishi baya Wadata ya yi da ƙafa yana sashi matsawa tare da shagwaɓe fuska.

“Me nai maka?”

“Ka yi karatunka.”

Wadata ya faɗi cike da kashedi, turo laɓɓa Altaaf ya yi yana mayar da hankalinshi kan karatunshi. Yasan Abdul ɗin da suke magana ai, zai je da kanshi ya ji game ɗin menene ake yi, balle kuma jininsu ya haɗu, don har birthday party ɗinshi Sai da ya gayyaci Altaaf, don a makaranta yake jin shi kaɗai ne ɗan aji ɗaya da ya halarci partyn, wasu ma na ƙaryar cewar ɗan uwan Altaaf ɗin ne shi yasa ya gayyace shi. Bai bi takansu ba, hankalin shi rabi ne kan karatu, haka Wadata ya kula da shi shi yasa ya canza maganar da suke yi don Altaaf ɗin ya maida hankalin shi kan karatun.

Yana fita da yammaci gidansu Abdul ɗin ya wuce da yake basu da nisa, ya kuwa yi sa’a yana nan, su shida ne a nasu gidan, kuma aji huɗu suke su. Gaisawa ya yi da kowa ya koma gefen Abdul ya zauna.

“A-Tafida ya dai?”

Abdul ya tambaya yana dariya, yasan duk sun ɗauke shi ƙaninsu ne saboda Wadata.

“Dama zan tambayeka ne.”

Altaaf ya amsa.

“Wadata yasan za ka zo?”

Kai ya girgiza ma Abdul. Duk da yana ganin girman Wadata baya nufin yana buƙatar izinin shi kafin ya je inda yake so ko yayi abinda yake so.

“Wane irin game ne kuke yi?”

Ya tambaya. Ware idanuwa Abdul yayi, abokanshi na fara dariya.

“Game ɗin mu bana yara bane ba.”

Idris ya amsa Altaaf ɗin.

“Nima ba yaron bane ba ai…kuma da Abdul nake magana ba kai ba.”

Cewar Altaaf yana kallon Idris, don bai mishi ba dama can, ya kuma tsani a ce mishi yaro.

“Idris ƙyale shi.”

Abdul ya faɗi yana ɗorawa da,

“A-Tafida ba game ɗinka bane wannan.”

Magana Altaaf zai yi ya ji an tallafe mishi bayan kai, da sauri ya juya yana faɗin,

“Oucchhh….”

“Ai na san saika zo dama…”

Wadata ya faɗi yana zagayawa ya zauna. Dariya Abdul ya yi.

“Sai da na tambayeshi ko kasan ya zo ma.”

“Kana magana kamar mijina ne sai ya ban izini zan fita.”

Altaaf ya faɗi, ƙafa Wadata ya taka mishi yana faɗin,

“Marar kunya…”

Dariya su Abdul ke musu, a nutse Wadata ya kalli Altaaf don yasan ko bai faɗa mishi ba sai ya gano ko akan me suke game.

“Nasan baka da surutu shi yasa banda matsala ka sani…bansan ko tun yaushe game ɗin ya fara ko wa ya fara ba, mun zo mun samu ne muka ɗora muma, muna yin list ɗin mata da suka fi kowa nutsuwa a makarantar nan, tukunna mu saka kuɗi, wanda zai iya biya ya shiga… Yawan wanda ka haɗa shimfida da su yawan score ɗin da za ka samu, ana cire winners guda uku a ƙarshe, sai a raba kuɗin a ba wa kowa.”

Altaaf ya kai mintina biyu yana tauna maganar Wadata kafin ya ce,

“Wooo…”

Apple ɗin da ke ajiye cikin plate kan table Wadata ya ɗauka ya gutsura yana taunawa, kafin ya ce,

“Yep yanzun sai ka tashi ka tafi ko? Tunda ka ji.”

Ware idanuwa Altaaf ya yi.

“In tafi ina? Ina so in yi nima.”

Kai Wadata ya girgiza.

“Ina so inyi ni.”

Dariya Abdul ya yi.

“Safara Auwal. Level 200 computer science. Ko baku haɗa shimfida ba inta kulaka da sunan soyayya, za mu yi game ɗin shekarar nan da kai.”

Wani ƙayataccen murmushi Altaaf ya yi.

“An gama.”

Yana miƙewa.

“A-Tafida…”

Wadata ya kirashi cike da kashedi, kashe mishi ido ɗaya yayi yana ficewa.

“Altaaf!”

Wadata ya sake kira amma ya riga ya fice daga da gidan. Wani kallo Wadata ya watsa ma Abdul da yake dariya kafin ya tashi ya bi bayan Altaaf ɗin, wannan shirmen game ɗin zai hana shi karatu, ya aka ƙare da yadda Altaaf ke son nuna kanshi ta ɓangaren mata ballantana kuma an saka abin a matsayin gasa, bai damu da shiga ko ƙin shigar Altaaf game ɗin ba, amma ya damu da zamanshi a makaranta.

<< Alkalamin Kaddara 25Alkalamin Kaddara 27 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×