Skip to content
Part 31 of 52 in the Series Alkalamin Kaddara by Lubna Sufyan

Asibiti suka wuce su dukan su, yanayin jikin Altaaf ɗin yasa likita ya ce sai ya riƙe shi kwana ɗaya. Ruwa aka ɗaura mishi, kasancewar su dukansu basu ci komai ba yasa Wadata fita don ya siyo musu wani abu da za su ɗan ci. Ammi ma fita ta yi zata siyo katin waya. Daga shi sai Barrah aka bari a ɗakin, don sai da suna hanyar zuwa asibiti ne ma ya tuna ya ganta tun da suka fito ofishin ‘yan sanda a Kinkiba. Bata dai ce mishi komai bane ba. Yanzun ma wani irin kallo take mishi da yasa shi tsarguwa. 

“Barrah…”

Ya faɗi muryarshi can ƙasa, numfashi ta sauke kamar ta jima tana riƙe da shi, kafin ta gyara zamanta. 

“Na san ka yi Yaya, ko menene aka ce ka yi ni nasan ka yi, a ƙasan zuciyar Ammi nasan tasan ka yi. Kuma baka kyauta ba…” 

“Barrah…”

Altaaf ya sake kiran sunanta, yana jin wani irin yanayi da bai taɓa ji ba a rayuwarshi, ga kunya da ya ji ta lulluɓe shi haɗe da dana sani marar amfani. Hannu ta ɗaga mishi dake nuna alamar bata son ji. 

“Bana son magana da kai…har mu bar asibitin nan ka yi kamar bana nan, karka min magana don Allah, Yaa Aslam ba zai so ya kalleka ba shima.” 

Wani abu Altaaf yai ƙoƙarin haɗiyewa da yai mishi tsaye a wuyanshi. Barrah na kallon shi yana kokawa da koma menene yake ji, ba matsalarta bane ba, ya gama ɓata mata rai sosai, barta da rashin kunyarta in ka shiga gonarta, amma bata son rashin adalci, bata son zalunci ko kaɗan, Aslam yasa ta ƙyamatar abin sosai, kuma ko me akai ma ‘yan ƙauyen nan tasan ba’a kyauta musu ba. Ta kuma san su ne da gaskiya, shi yasa tai zamanta a mota don kar ranta ya ɓaci fiye da yadda ya gama ɓaci da rashin kyautawar Altaaf ɗin. 

Sai da ta kira Aslam tukunna ya faɗo ma Altaaf ɗin a rai, ko hutun ƙarshen sati ya je gida sai Aslam ya tunatar dashi kan nisanta da ayyuka marassa kyau, bai taɓa sa nasihar a ranshi ba, sai yanzun, baya jin zai iya ɗaga ido ya kalli Aslam in ya ji maganar nan. 

“Karki faɗa mishi… Barrah kar Aslam ya ji.”

Ɗan ɗaga mishi kafaɗa ta yi. 

“Na ɗauka na ce karka sake min magana.”

Ta tambaya tana ware mishi idanuwa, damuwar da yake ciki ta sa bai kula rashin kunyar Barrah ba, bayajin karfie a jikinshi ma ballantana ya iya hayaniya. So yake bacci ya ɗauke shi ko zai farka ya samu abinda ya faru mafarki ne. Kallon shi Barrah ta sake yi da yadda fuskarshi take a kumbure. 

“Kuma ka ƙara muni, ka ga fuskarka? Kamar alkubus…” 

Murmushin ƙarfin hali yayi mata kawai. Lokacin ne Ammi ta turo ƙofar tana faɗin, 

“Wanne irin asibiti ne wannan? Ban samo katin ba fa sai da na fita wajen asibitin tukunna.” 

Kujera Barrah ta tura mata, ta karɓa tana juyata tukunna ta zauna. 

“Yaushe zamu wuce Ammi?”

Barrah ta buƙata a shagwaɓe. 

“Baki ga Altaaf ba lafiya ba? Sai gobe in Allah ya kaimu.” 

Buɗe baki Barrah ta yi tana kallon Ammi cike da mamaki. 

“Gobe fa? Me za mu yi in mun zauna. Ba ga Ya Imran nan ba, zai kwana da shi.” 

Hararar Barrah Ammi ta yi, ba don ta san Imran ɗin ba zai kula da Altaaf kamar tana wajen ba, sai don hidimar da yake ta yi da su ta yi yawa, kuma hankalinta zai fi kwanciya in tana ganin ya jikin Altaaf ɗin yake. 

“Ni bazan kwana ba gaskiya. Faɗa nake da Yaya.” 

Cewar Barrah da ta ƙarashe maganar tana hararar Altaaf. Bai ce komai ba, saboda baya jin yin wata magana. Kai kawai Ammi ta girgiza, indai faɗa ne tsakanin Barrah da Altaaf sun saba, ta san ba don bashi da lafiya ba da yanzun an ji kansu a asibitin, bakin Barrah ba zai yi shiru ba. Altaaf kuma hannunshi ba zai gaji da dukanta ba. Wadata kam daya dawo abinci ne lafiyayye ya siyo musu, don har da ice cream ya haɗo ma Barrah da shi. 

“Yaa Imran ka dawo gidan mu kawai. Don Allah Hajiya ta min musaya ta ɗauki Yaya.” 

Dariya Wadata ya yi tare da faɗin, 

“An gama ƙanwata.”

Kamar yadda yake kiran Barrah ɗin. 

“Ina jinku.”

Altaaf ya ce, saboda Wadata ya koma da ƙin ko kallon inda yake tun daga police station. Yanzun ɗin ma daga shi har Barrah basu ko kalle shi ba, hira suka ci gaba da yi kamar baya wajen. Ammi ce kaɗai takan mishi sannu, lokaci zuwa lokaci, babu yadda batai ba da ya ci abinci ko yaya ne ya ƙi, ƙamshin abincin ma amai yake neman saka shi yi. Har la’asar suna asibitin, da Wadata yai sallah ya dawo ne yake ce ma Ammi yamma na yi kar su yi dare a hanya. 

“Ai ba tafiya za mu yi ba. Za mu kwana.”

Ammi ta bashi amsa, girgiza mata kai ya yi. 

“Haba dai, kamar bai da kowa a Zaria. Don Allah Ammi kar ki min haka. Dama ko ba ki zo ba zamu dawo gida ne don mu zo asibiti.” 

Murmushi Ammi ta yi, tana jin nauyin Wadata sosai. Duk yadda ta so ta kwana dole suka juya bayan Altaaf ya ƙara tabbatar mata cewa ya ma fara jin sauƙin zazzaɓin, kawai sai rashin ƙarfin jiki. Har bakin mota Wadata ya raka su tukunna ya koma wajen Altaaf ɗin, zaune suke ɗakin ya yi wani irin shiru na ban mamaki, kafin Wadata ya ciro wayarshi daga aljihunshi yana kiran matarshi. Hira sukai ta yi abinsu, Altaaf kuma yasan saboda shi Wadata yai hakan, magana ce baya so yai mishi, zai ƙyale shi har sai sa’adda ya so su yi maganar, hakan yai ma kanshi alƙawari. 

***** 

Bacci ya samu yayi, don bai farka ba sai cikin dare da aka cire mishi ruwan da ya ƙare, dama shi ne na ƙarshe. Banɗaki ya shiga ya watsa ruwa, ba zai yi ƙarya ba banda damuwa babu abinda yake tattare da shi, zazzaɓin ma yasan tashin hankali ne dama ba wani abu ba. Jikinshi dai babu ƙarfi don babu abinda ya ci, baya kuma jin cin wani abu. Alwala yayi yazo ya gabatar da sallolin da ake binshi don Wadata ya kawo darduma. Gyara zamanshi yayi yana jingina bayanshi da bango, ya gaji da kwanciyar. 

Wadata na zaune kan kujera, ya ja ɗaya ya miƙa da ƙafafuwanshi akai, sai wayarshi a hannunshi da earpiece a kunnenshi ɗaya, da alama kallo yake yi. Ba bacci ya samu ba, ko alamar shi baya ji, kanshi dai na ciwo sama-sama. Shi ya kira wata Nurse ta kwance ma Altaaf ɗin ruwa, yana kuma jinshi ya shiga wanka ya fito yayi sallolin shi, ko kaɗan baya son fara zancen abinda Altaaf ɗin yayi, sai sun bar asibiti, sai ya warke garau tukunna. 

Altaaf kam ya ɗauka zai iya jure sharewar da Wadatan yake mishi. Ko sannu baice mishi ba, ya ma ƙi kallon shi ballantana ya ga halin da yake ciki. 

“Yunwa nake ji…”

Ya faɗi, sai da Wadata yayi kamar bai ji shi ba tukunna ya sauke ƙafafuwanshi yana miƙewa, wata leda ya ɗauka yana ƙarasawa ya ajiye gaban Altaaf ɗin ba tare ya kalle shi ba, ya koma inda yake ya zauna. Yana ci gaba da kallon film ɗinshi. Yoghurt ɗin da ke cikin ledar kaɗai Altaaf ya ɗauka ya buɗe yana soma kurɓa a hankali. 

“Wanne film kake kallo?”

Altaaf ya tambaya kawai don Wadata yai mishi magana. Shi kallo ba damunshi yayi ba, da kanshi dai ba zai zauna yayi ba, gara yai bacci, in ya ga ana yi dai zai zauna ayi da shi. Ko in ya je gida sukan kalla shi da Barrah, da wahala ma su ƙarasa za su yi faɗa ko ita ta bar mishi wajen ko shi ya bar mata. Shirun dai Wadata ya yi, Altaaf yasan halin shi sarai, yana da taurin kai in yasa kanshi yin abu. 

“Don Allah ka min magana Yaya Imran…Ka ce wani abu, ka min faɗa nikam, koma mene ne banda shiru, bazan iya jurewa ba.” 

Altaaf ya ƙarashe maganar yana kallon Wadata da ko motsawa bai yi ba ballantana ya nuna alamun ya jishi, yoghurt ɗin rufe yana miƙewa ya ƙarasa inda Wadata yake, kujerar da ya ɗora ƙafafuwanshi akai ya janye yana zama, zuciyarshi wani irin zafi yake ji tana mishi. Zuwa yanzun ranshi ya soma ɓaci, yayi laifi ya sani, a karo na farko ya karɓi laifinshi, bai san me yasa Wadata zai zaɓi ya hora shi ta wannan fannin ba. 

“Na yi laifi, ban taɓa jin na yi laifin da ya kamata a hukuntani ba sai yanzun. Na ce kai min faɗa, ka zage ni yadda ka saba, amma karka share ni, bazan iya ɗauka ba, wallahi bazan iya ba.” 

Altaaf ya faɗi muryarshi da wani irin yanayi, idanuwa Wadata ya lumshe yana ƙirga ɗaya zuwa talatin cikin kanshi, saboda bayason tunanin komai, sosai ya jingina bayanshi yana ci gaba da ƙirgarshi, dare yayi sosai, ba zai yi maganar nan a asibiti ba kuma, yana jin idanuwan Altaaf na yawo kan fuskarshi. Bai ɗago ba ballantana ma ya buɗe nashi idanun har Altaaf yasa ran zai kalle shi ko ya kula shi. Baisan lokacin da suka ɗauka a haka ba, sai da ya ji Altaaf ya miƙe tukunna ya ɗago yana miƙewa, kafet ɗin da Altaaf ya sauke akai ya koma yana gyarawa ya kwanta. Altaaf ɗin ma kan gadon asibitin ya koma yana kwanciya. 

Gara Wadata bacci ya ɗauke shi, amma Altaaf kan kunnenshi aka kira Sallar Asuba, tashi yayi ya shiga banɗaki ya ɗauro alwala ya fito, lokacin Wadata ma ya tashi, don haka ya ja dardumar yana gyara tsayuwa don Kabbara sallah, kamar wanda aka doka ma guduma a kai haka addu’ar Nuwaira ta faɗo mishi, zuciyarshi tai wata irin mummunar dokawa, kafin tsoro ya kawo mishi ziyara lokaci ɗaya. A rayuwarshi zai iya ƙirga lokutan da yai Sallar Asuba akan lokacinta ballantan kuma cikin jam’i. In ka ga ƙafafuwanshi a masallaci ranakun juma’a ne. 

Tunanin Nuwaira na kan darduma tana haɗa shi da Allah a wannan lokacin yasa ƙafafuwan shi yin wani irin sanyi. Da ƙyar ya samu ya fara sallar, yana idarwa ya ɗaga hannunshi, sai dai me baisan abinda ya kamata ya roƙa ba, da ya idar da sallah miƙewa yake yi, hannuwanshi sun daɗe a tsaye kafin cikin zuciyarshi ya fara faɗin, 

‘Bansan ta inda zan fara ba. Ina jin kunya sosai, Allah ka yafe min, Allah karka amsa addu’ar Nuwaira, ka yafe mun, bazan sake ba.’ 

Lokacin Wadata ya fito daga banɗaki, shi kanshi ganin hannuwan Altaaf ɗin a sama ya bashi mamaki, baisan lokacin da wani murmushi mai sauti ya ƙwace mishi ba, yana ƙarasawa da ƙaramin tsaki tare da girgiza kanshi kawai. Shi ma mai laifi ne ya sani, laifuka da yawan gaske ma, amma bai cire rai da Rahmar Allah ba, musamman yanzun da yake rayuwar kowacce rana wajen ganin yayi aikin alkhairi fiye da ranar da ta wuce mishi. Sallah yayi ya koma ya kwanta din bacci yake ji. 

Ba’a sallame su ba sai ƙarfe sha ɗaya na rana, don saida suka tabbatar zazzaɓin da Altaaf ɗin yake yi bai dawo mishi ba tukunna. Tun a mota Altaaf yake jin dattin kayan jikinshi, a rayuwarshi ko yini ɗaya baya iyawa da kaya, amma yau kwanan kayan jikinshi biyu bai ma kula ba sai yanzun. Har suka ƙarasa gidan Altaaf ɗin babu mai magana, asalima waƙa Wadata ya kunna a motar. Yana yin parking ƙofar gida Altaaf ya buɗe murfin motar yana ficewa shi ma, sai da ya kai ƙofar gida ya tuna babu mukulli a jikinshi, tsaye yayi har Wadata ya ƙaraso ya buɗe gidan. 

Don har wayoyinshi da magungunan suna wajen Wadata, tare suka shiga falon, Altaaf ya wuce ɗaki don ya sake kayan jikinshi, Wadata kuma ya zauna a nan falon yana danna wayarshi. Altaaf ya daɗe tukunna ya fito sanye da wata riga ja da gajeren wando. Kan kujerar da Wadata yake yaje ya zauna kusa da shi, yana zama Wadata na miƙewa. 

“Yaya Imran…”

Altaaf ya kira, muryarshi ɗauke da wani irin yanayi. Wayar da ke hannunshi Wadata ya jefa kan kujera, tukunna ya kalli Altaaf ɗin, sosai yake kallon shi cikin fuska. 

“Ka warke?”

Ya tambaya muryarshi a kausashe, cike da rashin fahimta Altaaf din yake kallon shi. 

“In nufin babu abinda ke maka ciwo? Ka warke gaba ɗaya?” 

Wadata ya sake maimaita tambayar. A hankali Altaaf ya ɗaga mishi kai, yanayin shi ya dan tsorata shi, bai taɓa ganin kalar ɓacin ran da yake gani a fuskar Wadata ba tun haɗuwarsu. Jinjina kai Wadata yayi yana faɗin, 

“Good…tashi.”

Kallon shi Altaaf yake, ya ji daɗi yana mishi magana ko ba komai, amma ya kasa fahimtarshi, da hannu Wadata yake ma Altaaf ɗin nuni da ya tashi, miƙewar ya yi kuwa. 

“Ya…”

Bai ƙarasa ba saboda wani irin mari da Wadata ya ɗauke shi da shi, ance ana mari ta ɓangaren haggu ne ko dama, ya ji kamar mutane sun ce ɓangare ɗaya ake iya mari a lokaci ɗaya, bai sani ba saboda wannan ne karo na farko da aka taɓa marin shi. Kuma jin hannun Wadata yake yi a ko ina na fuskarshi, gaba ɗaya ta ɗauki ɗumi. 

“Yaushe lissafi ya fara ƙwace maka? Yaushe hankalin da kake da shi ya gudu ya barka Altaaf?” 

Wadata ya tambaya, bai damu da cewar Altaaf ɗin a gigice yake da marin da yai mishi ba, wani marin ya sake ɗauke shi da shi, yanzun komai yake dawo mishi, fuskar Nuwaira da kallon da take mishi lokacin da yace yana tare da Altaaf ɗin duk tsayin dare. Kafaɗar Altaaf ɗin ya janyo yana sake wanka mishi mari, wannan karon yana ganin yadda bakin shi ya fashe. 

“Abinda kai bai isheka ba sai da ka sani na yi ƙarya…Altaaf sai da kasa na yi ƙarya… Kasan yadda nake ji akan fyaɗe, ka fi kowa sanin yadda girman laifin fyaɗe yake a wajena…kai… Kaine kake da bushewar zuciyar wulaƙanta mace har haka.”

Wadata ya faɗi yana kaima Altaaf ɗin wani irin duka, yasan yadda hannunshi yake shi yasa yake ƙoƙarin danne zuciyar shi, yake ƙoƙarin sanyaya zafin da take mishi, yana jin in aka bashi bindiga da damar kashe mutane masu manyan laifuka daga masu fyaɗe sai masu dukan matansu zai fara harbewa, sai ya tabbatar masu laifi irin na Altaaf sun daina numfashi saboda basu da wani amfani. So yake ya daki Altaaf sai ya gane kuskuren da yayi, so yake ya dake shi sai ya cire mishi sha’awar wulaƙanta kowacce mace. 

“Ba ƙani kawai na ɗauke ka ba, ina jinka kamar ƙanin da Hajiya bata bani ba…!” 

Wadata ya faɗi yana sake kaima Altaaf ɗin dukan da saida ya tsugunna, kamo shi Wadata yayi yana ɗago shi. 

“Kana da ƙarfin zuciyar wulaƙanta mace, baka da ƙarfin zuciyar jure dukana? Wanne irin namiji ne kai?!” 

Wadata ya tambaya yana ɗauke Altaaf da wani irin mari. 

“Altaaf mata nawa suke kawo kansu wajenka? Mata nawa ne kuɗi kaɗan za su siya maka? Sai ita? Sai ka wulakantata haka?” 

Altaaf baya gane me Wadata yake faɗi, saboda maganar shi na biyo bayan dukan da yake mishi, ko ina raɗaɗi yake mishi, fuskarshi jinta yake kamar ba’a jikinshi take ba, sau ɗaya ya taɓa ganin Wadata yayi faɗa da kanshi, lokacin yake ce ma Yaks ba zai taɓa yarda yayi ma Wadata abinda zai sa mishi hannu ba, zazzaɓi yake ji sabo yana rufe shi. 

“So nake in dake ka saika daina motsi, so nake in dake ka saika ji abinda kasa ta ji Altaaf, amma kashe ka zan yi in na ce in maka dukan nan.” 

Wadata ya ƙarasa yana hankaɗe Altaaf ɗin ya faɗi, saboda in yana ganin shi a tsaye zai ci gaba da dukanshi ne . Numfashi yake saukewa zuciyarshi na ƙuna. 

“Ka zo ka ɗauke min motarka daga gidana. Ko don zan sa a kawo maka… Kar ƙafarka ta tako min cikin gida sai ka gyara halayenka, bana son ganinka wallahi. Bana son ganinka ko kaɗan Altaaf…karka sake nuna min fuskarka sai ka gyara halayenka…” 

Wadata ya ƙarasa maganar yana juyawa ya fita daga gidan. Don in yana ganin Altaaf ɗin baisan ko zai iya daina dukan shi ba. Altaaf kuwa yana jin wayarshi na ƙara , alamar kira amma ba zai iya tashi daga inda yake ba ma ballantana har ya ɗauka. Ko ina jikinshi ciwo yake, bai taɓa sanin ciwo kalar wannan ba, waje da cikin jikin shi ciwo yake sosai, musamman zuciyarshi da maganganun Wadata suka taɓa. Wadata ya tsane shi, bai taɓa hango rana irin wannan ba, ko bai ji a muryarshi ba ya gani a dukan da yai mishi. 

In bai tsane shi ba, ba zai dake shi kamar baya son shi ba. Yayi laifi, amma bai taɓa tunanin Wadata zai mishi wannan dukan ba, da bakinshi ya faɗi baya son ganin fuskar shi, abin ya tsaya mishi a rai fiye da tunani, ya samu waje sosai ya zauna a zuciyarshi. Inda zai iya kuka zai yi ko zai samu sauƙin abinda yake ji. Baisan lokacin daya ɗauka a haka ba, bai tashi ba saida ya ji ana ƙwanƙwasa gidan, da ƙyar ya iya kai kanshi bakin ƙofa, motarshi ce Wadata ya aiko mishi da ita kamar yadda ya ce. Mukullin ya karɓa yana mayar da gidan ya kulle ya koma ɗaki ya kwanta kawai. 

***** 

Satin shi ɗaya bai leƙa ko ƙofar gida ba, abinci ma sai dai yasa cikin abokanshi wani ya siyo ya kawo mishi, duk kiran da zai shigo wayarshi zai ɗauka Wadata ne, ko in ya ji an ƙwanƙwasa ma zai ɗauka shi ne ya zo duba shi. Amma shiru, ya ɗauki waya ya fi sau a kirga da nufin ya kirashi amma ya rasa ƙarfin gwiwa. Duk in ya zo kira maganganun Wadatan ne suke dawo mishi, baya son ko ganin shi ballantana kuma muryarshi. 

A kwanaki bakwai ɗin daga Yaks har Jamal sun kira shi, amma bai ɗaga wayar ba haka take gama ringing ta yanke. Baisan ko sun kira bane su faɗa mishi yadda suka tsane shi suma. Jin shi yake shi kaɗai, duniyar ta mishi wani irin fili, gaba ɗaya Zaria ta fita daga kanshi, ya soma ƙirga watannin da ya rage mishi ya gama ya tafi. A yanayin da yake ji ma komai ya fita daga ranshi, haka ya koma makaranta, su kansu abokanshi sai da sukai mamakin canjin shi, in yaje aji ba zai fita ba sai lokacin sallah yayi tukunna. Sosai suke mamaki, Altaaf na kula da su , suna tsoron tambayarshi. 

Duk wani party ya daina yi a gidanshi, ya daina zuwa, kowanne abu ake a makaranta ba zaka ganshi a wajen ba, gaba ɗaya hankalin shi ya koma kan karatu. Bashi da ƙarfin yin wani abu daya wuce hakan. Ganin ana yawan matsa mishi da kira yasa shi sake layi gaba ɗaya, lambobin da suke da amfani a wajenshi kawai ya ɗauka yana adana su, ya kira su Ammi da sabon layin nashi. Bai nemi Wadata ba, in ya kira ya ji a kashe wataƙila ya zo ya ganshi. Hakan yasa ma ranshi, amma shiru kake ji. 

Amman me, a hankali kwanaki suke yin satika, satikan na ja zuwa watanni, ko a hanya bai ga Wadata ba, duk da ba fita yake ba sosai sai dole, yanzun ma abokanshi sun fi shi hawa motarshi, in kazo ya ara maka tunda can ma baya hanawa. Tun abin na mishi wani iri har ya zame mishi jiki, Wadata ya barshi kamar yadda Ashfaq ya barshi, su duka ya musu laifin da suke jin ba za su iya yafe mishi ba. Karatu ne kaɗai abinda yake rage mishi damuwa, sosai yai mamakin yadda har kayan maye sun fita daga ranshi, ya sha wasa da kwalbar syrup in ya kasa bacci, amma ya ɗaga ya sha na mishi wahala. Akwai abubuwa da suka girmi shaye-shaye, sai yanzun ya tabbatar. 

Yana cikin jarabawarshi ta ƙarshe ne Ammi tai mishi magana tana son ya je ya ga wata yarinya a katsina in ya samu dama, bata san ko zatai mishi ba. Dama tun bayan abinda ya faru da su Nuwaira tana yawan mishi maganar aure duk idan yaje weekend. Kamar yadda Barrah ta faɗa mishi ne, Ammi tasan ya yi wani abu ba daidai ba, soyayyarshi ba zata barta ta furta ba. Bata san tun faruwar abin mata sun fitar mishi daga rai ba, don haka ya ce mata in yarinyar ta mata yasan shima za tai mishi, saboda tasan kalarshi. Hakan ba ƙaramin daɗi yai ma Ammi ba. 

Har aka saka ranar shi mamaki yake yi, saboda abune da bai taɓa kawowa a kusa-kusa ba. Da Ammi ta tura mishi lambar yarinyar ma sunan kawai ya duba ‘Majida’. Bai kira ba, baisan me zaice mata ba. Haka ya ci gaba da ware ido ko zai ga Wadata tunda yana da tabbacin Ammi ta faɗa mishi maganar sa ranarshi, shiru bai zo ya neme shi ba. Bai sake saka Wadata a idanuwanshi ba sai ranar daya gama jarabawar ƙarshe. Yana fitowa da farar riga a jikinshi, mutane nata son su mishi rubutu a jiki kamar yadda ya zama al’ada ta ‘yan makaranta. Amma ya ƙi tsayawa, gida kawai yake son zuwa ya haɗa sauran kayanshi ya bar Zaria ko zai samu nutsuwar daya daɗe da rasawa. 

Kamar an ce ya ɗaga ido ya ga Wadata tsaye jikin motarshi, sai da zuciyarshi tai wata irin dokawa, da sauri ya ƙarasa inda Wadata yake tsaye. 

“Yaya Imran…”

Altaaf ya faɗi muryarshi cike da shakku da tsoron ko idanuwanshi ne suke mishi wasa, kamar maganar zata iya sakawa Wadata ya ɓace, amma yana nan tsaye bai dai kalle shi ba ne kawai, zuwa Altaaf ɗin yai da niyyar hugging ɗin Wadata ɗin, amma sai yasa hannu a tsakaninsu yana ture Altaaf ɗin baya. Ɗayan hannunshi da ke riƙe da marker ta rubutu ya ɗago yana sa ɗayan hannun ya buɗeta , Altaaf da ke tsaye yana kallon shi ya kama yana juyawa, rubutu yai a bayan rigar Altaaf ɗin yana faɗin, 

“Congrats. Allah yasa alkhairi.”

Tukunna ya mayar da marker ɗin ya rufe yana saka ma Altaaf a aljihunshi, bai bari ya ce komai ba ya buɗe mota ya shiga yana janta ya tafi abinshi. Altaaf na tsaye a wajen, mutanen da ke son mishi rubutu jikin riga haka suka zo wajen suka same shi, bata su yake ba, idanuwanshi na kafe kan shatin tayar motar Wadata, zuciyarshi ta gama karɓar cewar ya rasa Wadata, ya zo mishi murna ne saboda abune da Wadata zai yi, ba don ya yafe mishi ba don ko ido bai bari sun haɗa ba. 

Har hotuna da sukai sai dai in wannan ya ja shi ta nan wancan ya ja shi, amma shi kam hankalinshi baya wajen, suna gamawa ya wuce gida ya tattara kayanshi, gidan da sauran kuɗin shi bai ƙare ba wajen wata shida, don wasu abokanshi da suke aji uku ya bar ma, kayan sawa kawai ya ɗauka suma ba duka ba, ya fito ya saka a mota yana yin sallama da mutane ya wuce. Baisan hanyar gidan Wadata ya nufa ba saida ya ganshi a ƙofar gidan, ya fi mintina sha biyar tsaye a ƙofar gidan da mota a kunne, bai kashe ba ballantana ya fito, idanuwanshi ya lumshe. 

‘Na gode Yaya Imran. Na gode fiye da yadda zaka fahimta. Ka yafe min, don Allah ko ba yanzun ba ka samu waje a zuciyarka ka yafe min. Na gode.’ 

Ya ƙarashe yana jin ƙirjinshi ya yi wani irin nauyi. Buɗe idanuwanshi yayi yana sauke wani irin numfashi mai nauyin gaske, kafin yayi baya da motar yana juyawa, da duk yadda yake nisa da Zaria da yadda yake ƙara zurfin ginin ramin da zai binne duk wani abu daya danganta shi da A-Tafida. Ko kiranshi akai da sunan sai ya ji wani abu ya kwance a zuciyarshi..! 

***** 

Wayarshi ya ji ta yi vibrating cikin aljihunshi tana tsorata shi sosai, numfashi yake saukewa kamar wanda yai gudu, ya ɗan haɗa kanshi da gaban motar kafin ya ɗago, rabon da ya bari tunanin shi yai yawo haka, ya tono mishi abubuwan da ya binne har ya manta. Wayar ya zaro har ta yanke. Majida ce, ganin sunanta kawai yasa jikinshi ƙara mutuwa. Wani sabon kiran ne ya sake shigowa, ɗagawa yai yana karawa a kunnen shi. 

“Mi nai maka?”

Ta tambaya a shagwaɓe. 

“Majee…”

“Bawani Majee, mi nai maka? Baka kirani ka ce man ka isa lahia ba, awa nawa da tahiyarka? Na bari in ga ko za ka kira ni baka kira ba.” 

Numfashi ya sauke, ya shiga tunani ne sam bai duba lokaci ba, shi ya saba mata ba sa daɗewa haka ba su yi waya ba, in kuma ya fita yakan kira ya ce mata ya sauka lafiya. Yasan Majida da saka abu a ranta. 

“Ba abinda kikai min, banda kati ne, inda nake kuma babu kati a kusa shi yasa.” 

Shiru ta ɗan yi kafin ta ce, 

“Lahiya dai ko? Muryarka tai man sanyi da yawa.” 

“Lafiya ƙalau, kawai gajiya nake ji.”

Ya amsa a taƙaice, yana buɗe wajajen da zai adana muryarta, a lokaci ɗaya kuma tsoro mai tsanani ya shige shi. Mutanen daya shaƙu da su, su yake ma laifi suna barin shi, Majida na ɗaya daga cikin mutanen da baya jin zai iya rasawa, zuciyarshi bata da wannan ƙarfin yanzun. 

“Sannu…”

“Majee zan kira ki. Ina zuwa.”

Altaaf ya faɗi yana kashe wayar kafin ta ce wani abu. Baisan ta inda zai fara ba, jin muryar Majida, tunanin zata iya barinshi in asirinshi ya tonu, tuna jerin mutanen da suka bar rayuwarshi, komai ya dawo mishi sabo sosai.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 4.8 / 5. Rating: 4

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Alkalamin Kaddara 30Alkalamin Kaddara 32   >>

1 thought on “Alkalamin Kaddara 31 ”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×