Skip to content
Part 37 of 52 in the Series Alkalamin Kaddara by Lubna Sufyan

Da motar Altaaf ɗin suka fita, don Wadata ya ce ba zai yi asarar manshi akan Altaaf ɗin ba, kuma shi zai yi tuƙi, da murmushi a fuskar Altaaf ɗin yake bin duk wata magana da Wadatan zai yi, ba don baya samun farin ciki da Majida ba, amma ya manta rabon da ya tsinci kanshi cikin nishaɗi irin na yau, duk da damuwar abinda zasu tarar a Kinkiba. Kwance Altaaf yake cikin kujerar motar yana kallon hanya, don Wadata bai ce mishi uffan ba tunda suka fito. Kafin ya juyar da kanshi yana kallom Wadata da ke tuƙi yana bin waƙar da ya kunna a cikin motar a hankali, hannu Altaaf ya kai ya rage ƙarar kiɗan. 

“Ina su Yaks?”

Ya tambayi Wadatan da maimakon ya amsa mishi sai hannu da yakai yana ƙara sautin kiɗan da yake ji, sake ragewa Altaaf ya yi. 

“Ya suke? Shi da Jamal?”

Altaaf ya sake tambaya, kiɗan dai Wadata ya ƙaro, bai gaji ba shi ma ya sake kai hannu ya rage. 

“Ranka zai yi mugun ɓaci Altaaf.”

“Ba zai ɓaci ba tunda kana min magana…”

Ɗan kallon shi Wadata yayi na ‘yan daƙiƙu kafin ya mayar da hankalin shi kan tuƙin. 

“Ka ji, baka amsani ba.”

Cewar Altaaf.

“Ban sani ba, lokacin da ka daina musu magana na sani ne? Me yasa za ka dame ni yanzun?” 

Wadata ya faɗi a ƙufule, don bai ga dalilin da zai sa Altaaf ɗin ya dame shi ba, tambayar da yake mishi na tuna mishi da yadda bai gama yafe ma Altaaf ɗin ba, baya kuma so ranshi ya sake ɓaci. Hannu Wadata ya kai zai ƙara sautin yana faɗin, 

“Motar nan za tai mana kaɗan idan ka sake rage min.” 

Tukunna ya ƙara, duk yadda Altaaf yake son ya rage sautin yana tsoron ƙure haƙurin Wadatan, don haka ya sake gyara zama cikin kujerar kawai yana yin shiru, sai dai ya rasa tunanin da ya kamata yayi, shi yasa ya so jan Wadata da hira, shi kuma ya ƙi biye mishi. 

“Matar Yaks ta haihu?”

Altaaf yai maganar da ƙarfi kamar zai fasa ma Wadata dodon kunne, yana saka shi kashe kiɗan gaba ɗaya. 

“Za ka fasa min kunne ne don ubanka? Altaaf me yasa baka da hankali ne wai?” 

Wadata yake tambaya yana watsa ma Altaaf ɗin harara kafin ya mayar da idanuwanshi kan tuƙin da yake yi. Dariya Altaaf yayi. 

“Yi hakuri, ka ce kar in rage maka kiɗan, amma baka ce kar in yi magana ba.” 

“Shi ne za ka fasa min kunne? Sai na ce bana son magana da kai ne za ka fahimta?” 

Ɗan ɗaga kafaɗa Altaaf yayi. 

“Ni ina son magana da kai, ban ce dole sai ka amsani ba.” 

Numfashi Wadata ya sauke, ya manta yadda Altaaf kaɗai yake saka shi jin kaman zai yi hauka, yaran shi biyu, amma basa saka shi jin kamar ya fasa wani abu kamar yadda Altaaf ɗin yake saka shi ji, saboda su in yai musu hargowa suna jin tsoro su nutsu, amma Altaaf baya tsoron faɗan shi. 

“Kasan ina iya ajiye auren da kake da shi a gefe in maka duka ba wani abu bane ko?” 

Dariya Altaaf yayi. 

“Yaya Imran, ka kalleni, bana tsoron ka.”

Sauka daga titin Wadata yake yi yana ƙoƙarin taka birki. 

“Yi haƙuri…wasa nake fa.”

Altaaf ya faɗi yana ware idanuwan shi, ganin da gaske Wadata parking ɗin motar yake shirin yi yasa shi ci gaba da faɗin. 

“Wallahi wasa nake, kai ba’a wasa da kai ne to, ya za ayi ka daki mijin aure? Kuma a dokar Nigeria an hana ta’addanci, wallahi a Musulunci ma babu kyau cin zali…” 

Dariya ke son kuɓuce ma Wadata, amma ya danne, fuskarshi babu walwala ya kalli Altaaf ɗin da ke zare idanuwa ya ce, 

“Ka zauna kamar baka motar nan.”

“Ba zan yi motsi ba to?”

Wani kallo Wadata yai mishi da ya shi faɗin, 

“Na ji, mu je.”

Kai Wadata ya jinjina yana jan motar ya koma kan titi da ita sosai, bai kunna kiɗan ba, Altaaf kuma bai sake magana ba har suka ƙarasa Kinkiba, yayi mamaki da ya ga Wadata yana bin lunguna har kusan ƙofar gidan su Nuwaira, bai manta hanyar ba ko ɗaya. Waje ya samu yayi parking. 

“Ka yi zaune, ba za ka fita ba ne?”

Wadata ya tambaya, ware mishi idanuwa Altaaf yayi yana jin zuciyar shi ta yi wata irin dokawa. 

“In fita ina?”

Hararshi Wadata yayi

“Me na rakoka yi?”

Kai Altaaf yake girgiza ma Wadata yana roƙon shi da idanuwanshi, saboda ba haka ya ɗauka rakiyar zata kasance ba. Ko da wasa bai hango hakan ba, yace yana so ya karbo yaran shi, amma baya nufin zai yi hakan shi kaɗai da Wadata zaune cikin mota yana jiran shi, ya ɗauka in suka zo Wadata zai fita ne yana gaba shi kuma yana binshi a baya su je ya karɓo mishi yaran ya bashi su tafi, kamar yadda ya saba yi mishi abubuwa a baya. 

“Yaya Imran.”

Altaaf ya kira muryarshi na karyewa, gyara zama Wadata yayi yana fuskantar Altaaf ɗin. 

“Kana son karɓo yaranka ka ce, ko ba haka ka ce min ba?” 

Kai Altaaf ya ɗaga mishi a hankali. 

“Ka je ka karɓo su ina jiran ka.”

Wadata ya ƙarasa yana tsare Altaaf ɗin da idanuwa, yana ganin har lokacin hankali bai gama saukar ma Altaaf ɗin ba, idan ya ce yai mishi bayani da baki ba zai taɓa fahimtar shi ba, hakan ne kawai zai yi Altaaf ya gane wannan ƙaddarar tashi ba mai sauƙi bace ba. Don haka ya miƙa hannu ya buɗe murfin motar ya fita, zagayawa yayi yana buɗe ɓangaren da Altaaf ɗin yake zaune tare da janyo shi ya fito da shi waje. Kallon shi Altaaf yake idanuwa a ware, sosai yake ganin yadda canjin da Wadata yayi ba a waje bane kawai, Wadatan daya sani ba zai mishi haka ba, ba zai barshi ya fuskanci wannan abin shi kaɗai ba. 

“Ka wuce ka karɓo su, ina da hidimar da zan yi na biyoka…” 

“Me yasa?”

Altaaf ya tambaya yana gyara muryarshi don ya ji ta fito can ƙasa. 

“Me yasa za kai min haka? Na san zai ɗauki lokaci kafin ka yafe min gaba ɗaya, amma me yasa za kai min haka?” 

Yake tambaya da wani yanayi a muryarshi, da yasan ba zai taimaka mishi ba da bai ɗaga mishi buri ba, da bai sa ya ji kamar sun raba damuwarshi tare ba. Yana jin yadda Wadatan yake kallon shi cike da yanayin da ya kasa fassarawa. 

“Altaaf…Altaaf…. Altaaaaf… Ba za ka taɓa yin hankali ba, bansan me zai faru da kai kafin ka yi hankali ba…” 

Cewar Wadata, kallon shi Altaaf yake yana daƙuna mishi fuska cike da rashin fahimta. 

“Me haukan ka ya ɗauka? Za mu zo, in je in karɓo yaran in taho mu tafi gida ko? To daga nan kuma sai me?” 

Ɗan ɗaga kafaɗunshi Altaaf ya yi, shi ma bai sani ba, tunanin shi ya tsaya da shi, Wadata ya fara karɓo mishi yaran, sauran sun zo daga baya. ‘Yar dariya Wadata yayi. 

“Sai ka tafi da su gida, ka ce ina ka samo su? Wa za ka kaima yaran? Ammi ko Majida?” 

Wani irin numfashi Altaaf ya ja da maganganun Wadatan yana jin kamar yasa hannu ne a ƙirjinshi dai-dai inda zuciyarshi take yana ƙoƙarin ciro mishi ita waje, kwata-kwata bai yi tunanin ko me zai faru in ya karɓi yaran ba, in ya kai ma Ammi su me zai ce mata, ta yaya zai fara yi ma Majida bayani, kai yake girgizawa, yana jin ya mishi wani irin nauyi. Muryarshi can ƙasan maƙoshi. 

“Mu tafi gida….mu je kawai.”

Ya ƙarasa yana ƙoƙarin buɗe murfin motar da Wadata yai saurin mayarwa ya rufe yana ture shi gefe. Ya ga alamar Altaaf ɗin na son guduwa ne kamar yadda ya saba idan ba zai iya fuskantar abu ba, sai dai wannan karon ba zai barshi yayi wannan kuskuren ba. Ba don Altaaf ɗin ba, sai don yaran da yaima laifi tun kafin zuwan su duniya. 

“Me kake nufi?”

Ya tambaya.

“Ban sani ba! Bansan me nake nufi ba! Ban san me zan yi ba, na zo wajenka ne saboda bansan me zan yi ba, amma babu abinda ka yi sai ƙara hargitsa min komai, ka bar yaran, na haƙura… Ka bar ni kawai! Yaya Imran ka ƙyale ni don Allah.” 

Altaaf yake faɗi cikin hargowa, har ya gama Wadata na kallon shi, kafin ya lumshe idanuwa yana buɗe su a hankali  

“Ka kalleni…”

Kai Altaaf ya girgiza. 

“Ka kalleni Altaaf!”

Wadata ya faɗi muryarshi a dake wannan karon, hakan yasa Altaaf ɗin kallon shi. 

“Me yasa kake zaton zan iya karɓo maka yaranka? Me yasa ba za kai hankali ba Altaaf? Don Allah me yasa ba za kai hankali ba ne, me zan ce musu? Kun tunani? Yayan Altaaf Tafida da ya taimaka mishi aka ƙi bi muku haƙƙin ku? Ya ce mun akwai yaran shi a nan shi ne na zo in karɓe su…” 

Tunda ya fara magana Altaaf yake ganin rashin hankalin da ke cikin ta, da rashin yiwuwar abinda yake misaltawan, ba zai yiwu kawai Wadata ya je ya ce a bashi yaran ba, sosai yake jin ciwon kai na saukar mishi saboda tunanin da yake yi. 

“Me zan yi? Don Allah ka taimaka min.”

Altaaf ya roƙe shi yana jin ƙirjinshi kamar zai faɗo saboda nauyin da yai mishi 

“Sai ka koma baya, sai ka gyara komai Altaaf…” 

Wadata ya faɗi muryarshi a tausashe ganin yadda Altaaf ɗin ya rikice gaba ɗaya, zuciyarshi na mishi nauyi da hakan, sai dai wannan abu ne da ba zai iya ɗauke mishi ba, abu ne dole shi kaɗai zai fuskanta, sai dai ya tsaya a gefe kawai in ya ga zai faɗi ya taimaka mishi ya miƙe tsaye. Motar Altaaf ya dafa yana wani irin maida numfashi, sai yanzun ya fahimci abinda yasa Wadata ya biyo shi suka zo Kinkiba. Yana so ya fahimtar da shi yadda su biyun kaɗai ba za su iya ba, yadda lokaci yayi da su Ammi za su san abinda ya aikata don su kaɗai ne za su iya tunkarar iyayen Nuwaira, lokaci yayi da har Majida zata san abinda ya aikata. 

Laifukan shi ne suke dawo mishi suna nuna mishi yadda bai isa ya hana rubutun da alƙalamin ƙaddara yayi mishi tabbatuwa ba. In har zai fuskan ci wannan shafin, zai yi shi da dukkan ƙarfin shi ne, runtsa idanuwan shi yayi na wasu daƙiƙa, kafin ya buɗe su yana gyara tsayuwar shi sosai, ya kalli Wadata. 

“Mu je gida…”

Murmushin da Wadata yai mishi na ƙara mishi wani irin ƙarfin gwiwa na ban mamaki, hannu yasa yana buɗe murfin motar ya shiga ciki, Wadata ma shigowar yayi, hakan yasa Altaaf ya kalle shi yana faɗin, 

“Ka ban Address ɗin su Jamal…”

Jinjina mishi kai Wadata yayi, gyara zama Altaaf yayi cikin kujerar da yake zaune kafin Wadata ya ja motar, yana jin yadda lokacin canja komai yayi, zai fara gyara alaƙar shi da mutanen da suke da kusanci da shi, yana buƙatar su don bai da tabbas akan alaƙar shi da ɗayan bangaren, ba zai zama shi kaɗai ba, yana da tabbas cewar ko me ya aikata Ammi ba zata guje shi ba, amma Majida da Aslam baida wannan tabbacin, yana buƙatar su Jamal, yana buƙatar Ashfaq, in hakan ya faru.

Abuja

Marmarin taliya take ji tun fitar Rafiq, hakan yasa ta shiga kitchen ta dudduba, saida ta gano store ɗin gidan da bata san da shi ba, ta ɗauko ta dawo kitchen ɗin ta dafa. Kwaɗayi ne da bata san daga inda ya fito ba, don da mai da maggi ta ci taliyar a cikin kitchen ɗin, ta wanke plate ɗin tukunna ta fito falon, ruwa ta ɗauka tana sha, kusan ƙwarewa ta yi jin motsi a bayanta da ya sa ta juyawa babu shiri tana tari tare da maida numfashi ganin Rafiq ɗin a tsaye, frames ɗin da ke rungume a ƙirjinshi ta fara kallo tukunna ta mayar da idanuwanta kan fuskarshi da babu alamun nutsuwa a tattare da ita. 

Kallon ta yayi yana wucewa ya nufi hanyar ɗakin shi, bata san me yasa ta bishi ba, yana turo ƙofar ta sa hannu ta riƙe tana shiga ɗakin. 

“Sugar”

Ta kira sunan shi cike da kulawa, frames ɗin da ke hannun shi ya ajiye a tsakiyar ɗakin yana zama a ƙasa kamar wanda baya cikin hayyacin shi, hotunan Tasneem ta bi da kallo, tana sauke idanuwanta kan wata kyakkyawar matashiyar mata, ba sai an faɗa maka cewa ta fito daga gidan hutu ba, daga fatar ta zuwa kwalliyarta da kayan da ke jikinta kawai sun wadatar, wata irin dokawa zuciyar Tasneem ta yi, tana ƙara gudu lokacin da idanuwanta ya sauka kan hoton Imaan. Tasan Rafiq bashi da ƙanwa ‘yar ƙarama, kuma shi ne babba a gidansu balle ta ce Imaan ɗin na kama da shi ne saboda yarinyar ɗaya daga cikin su ce. 

Batasan ƙafafuwanta sun kasa ɗaukarta ba sai da ta ganta zaune kusa da Rafiq ɗin, hannu ta kai tana shafa fuskar Imaan a jikin hoton, muryarta can ƙasan maƙoshi ta ce, 

“Sugar”

Sauran maganganun na maƙale mata saboda bata san me ya kamata ta ce mishi ba, ko wace tambaya ya kamata ta yi duk ta rasa. 

“‘Yata ce…”

Rafiq ya faɗi, yana jin maganar ta koma mishi cikin kunnuwan shi, yana kuma jin yadda zuciyarshi ta matse waje ɗaya,’yar shi ce da gaske, da ya kasa tuna riƙe ta a cikin hannayen shi. Idanuwan shi ya sauke cikin na Tasneem da take kallon shi cike da shakku da alamun tambaya, saboda ya ɗaure mata kai, in har yana da yarinya ba zai taɓa ɓoye mata kafin auren su ba, ko soyayya ya ce mata bai taɓa yi ba, kuma ta yarda da shi saboda bai taɓa mata ƙarya ba ko da a tuntuɓen harshe ne kuwa. 

“Kina mamaki kema ko? Nima shi nake yi, mamaki nake Neem, yarinyata ce, wannan kuma Matata ce, su duka na kasa tuna yin rayuwa dasu…” 

Runtsa idanuwa Tasneem ta yi tana buɗe su da faɗin, 

“Innalillahi wa inna ilaihir raji’un…”

A hankali tana sake maimaitawa, bata taɓa sanin tana da kishi ba sai yau da take jin numfashinta na barazanar ɗaukewa, musamman da ta sake kallon Samira ta ga yadda ta ko ina ta fita komai. 

“Tana… Suna ina yanzun?”

Ta tsinci kanta da tambayar Rafiq ɗin cikin rawar murya, bata san matsayin auren ta da shi ba, yanzun da wannan ɓoyayyen sirrin ya fito bata san me zai faru ba, amma za tai ƙarya in ta ce zuciyarta bata mata rawa da wani irin yanayi mai nauyin gaske. 

“Sun rasu… Hatsari mukai wai, shi yasa bana iya tuƙi… Sun rasu Neem, amma na kasa tuna su, wane irin miji ne ni a wajen ta, wanne irin uba ne ni…” 

Rafiq ya ƙarasa maganar yana wani irin jan numfashi, hannu Tasneem ta miƙa mishi idanuwan ta cike taf da hawaye, nashi da ke kyarma ya ɗago yana sakawa cikin natan, matsawa ta yi sosai tana riƙo shi jikinta, rungume shi ta yi tana matse shi a jikinta sosai, wasu hawaye masu ɗumi suka zubo mata, ƙirjinta take ji yana zafi da ciwon da Rafiq ɗin yake ji. Bata san me zata ce mishi ba ko me ya kamata ta yi mishi don ya ji sauƙi, saboda har ranta ta kasa saka ƙafafuwanta cikin takalman shi. 

Sai yanzun ta fahimci nisantaccen yanayin da takan gani a idanuwan shi lokuta da dama, yanayin da ke nuna kama ya rasa wani abu mai muhimmanci a rayuwar shi da shi kanshi baisan menene ba. Yanzun tasan ya rasa matar shi da yarinyar shi da wani ɓangare na tunanin shi, tana jin yadda yake maida numfashi kamar wanda yayi gudu, ƙara rike shi ta yi tana zame hannunta ɗaya ta dafa cikinta. Tunanin wani abu zai same shi kawai na barazana da duk wani sauran haske da take gani a rayuwarta. Saboda haka bata san yadda Rafiq ɗin yake ji ba, wasu sabbin hawayen ta ji sun sake zubo mata. 

“Ban san me zan ce maka ba, idan na ce ka yi haƙuri yayi kaɗan… Ban san me zan ce maka ba… Allah ya baka dukkan sauƙi.” 

Tasneem take faɗi tana sake riƙe shi gam, shiru ya yi, baya jin yin magana da yace mata ta yi shiru, baya buƙatar komai da ya wuce ta ci gaba da riƙe shi har ya samu nutsuwa ko ya take. Baisan lokacin da suka ɗauka a haka ba, har sai da ya ji numfashin shi ya dai-daita tukunna ya zame jikin shi daga nata a hankali yana dafa ƙasa ya miƙe tsaye. 

“Ina za ka je?”

Ta tambaya, baisan inda zashi ba shi ma, amma yana buƙatar shaƙar wata iskar daban da ta cikin gidan, kanshi yake ji a cunkushe. 

“Ban sani ba nima…”

Kai Tasneem ta ɗan ɗaga mishi, tana jin bata da wani amfani a wajen shi, hakan kawai yasa wani abu ya tokare mata ƙirji. 

“Ka kula da kanka…. Allah ya tsare…”

Ko amin bai ce ba ya wuce, tana kallon shi har ya fice daga ɗakin, tukunna ta mayar da hankalin ta kan hotunan su Imaan da ke ajiye, tana jin wani iri da yadda kishin Samira yake ƙara yawaita a zuciyarta duk da ta rasu, tunanin kowacce irin rayuwa ta yi da Rafiq na mata wani irin tsaye. 

***** 

Fita yayi daga gidan ba tare da yasan inda zashi ɗin ba da gaske. Bai kuma nemi Isah ba duk da yasan yana kusa, takawa yake da ƙafafuwan shi, so yake sai ya ji ba zai iya ɗaga ƙafarshi ba tukunna ya tsaya, ƙila idan ya gajiyar da jikin shi ƙwaƙwalwar shi ma zata gaji ta barshi ya ɗan sarara, tunani ne cunkushe a cikinta, amman ko ɗaya babu wanda zai ce ga daga inda yake ko ga asalin ma’anar shi, tafiya kawai yake gefen titi. Ya jima sosai yana tafiya kafin ƙishin ruwa ya addabe shi. Ji yake kamar yayi kwanaki rabon shi da ruwa. Hannu yasa cikin aljihun wandon shi yana laluba kowanne daga cikinsu, kafin ya ji wallet ɗinshi, ɗaukowa yayi ya buɗe, yana sauke numfashi ganin akwai kuɗi a ciki. 

Wani store ya hango, don haka ya ci gaba da takawa har ya shiga, bai tsaya wani ɓata lokaci ba ya ce ma ma’aikacin wajen ruwa yake so roba ɗaya, ɗauko mishi kuwa yayi, ɗari biyar Rafiq ya bashi, zai juya ya ɗauko mishi canji ya ce ya bar shi kawai, ya wuce yana fita daga store ɗin, a ƙofar wajen ya kwance robar ruwan yana kafa baki ya soma sha, wata irin dokawa zuciyar shi tayi da ta sa shi ƙwarewa, tari yake babu ƙaƙƙautawa yana kokawa da numfashin shi, kafin komai ya tsaya mishi cak. Zai rantse duka duniyar ta yi tsaye ne a lokacin. Don ko bugun zuciyar shi baya ji balle yasan ko yana numfashi ko baya yi. 

Yakan ji takun tafiyar Nuri in ta shigo waje, yakan ji yanayin ta ko da takun ta bai yi sauti ba, zai rantse lokuta da dama a zuciyarshi yake fara jin kusancin Nuri kafin ma idanuwan shi su tabbatar mishi ta zo wajen, ko ranshi ne yake a ɓace in ta yi murmushi sai nashi ya bayyana, Nuri ce komai nashi, amma a duniya bai taɓa jin kusanci makamancin na yanzun ba da matar da ke wucewa ta gaban shi. Har ta ɗan gitta shi ya ga ta yi tsaye cik kama an dasa ta, kafin a hankali ta juyo, sai lokacin Rafiq ya ji numfashin shi ya dawo, saboda yadda yake kokawa da iskar da yake shaƙ da tai mishi kaɗan. 

Runtsa idanuwan shi yayi yana sake buɗe su, yayi hakan yafi sau biyar dan ya tabbatar ba mafarki yake yi ba, kafin dariya ta kubce mishi, har lokacin idanuwan matar na kafe kan fuskar shi, robar da ke hannun shi ya ɗaga yana kwara ruwan a fuskar shi tare da maida numfashi saboda sanyin da ruwan yake da shi. Sosai ya sake ware idanuwan shi akan matar yana jin zuciyarshi na shiga wani irin yanayi da yau ne karo na biyu da ya taɓa jin shi, ita ce matar da ta wuce shi a KFC. Fuskarta Rafiq yake kallo, baisan lokacin da yake takawa ba sai da ya ganshi tsaye gab da ita tukunna. 

Hannu ya ɗago kamar wanda ikon jikin shi ya ƙwace daga hannun shi, don ba zai ce ga abinda yake faruwa ba, abu ɗaya ya sani, yana son tabbatar da cewar ba mafarki yake yi ba, kan fuskar matar ya kai hannun shi yana taɓa kuncin ta, bata ɓace ba, sake taɓawa yayi wannan karon bugun zuciyar shi yake ji har cikin kunnuwan shi, bata ɓace ba tana nan tsaye tana kallon shi, idanuwanta cike taf da hawayen da ke neman hanyar zubowa. Hawayen bai hana Rafiq karantar tsoron da ke shimfiɗe cikin su ba. Dariyar ya sake yi yana girgiza ma zuciyar shi kai, saboda tunanin da take ɗarsa mishi abu ne da ba zai yiwu ba. 

Kafin ya ƙarasa haukacewa ya ɗaga ƙafar shi yana matsawa daga kusa da matar, zuciyar shi na mishi ihu da yadda bata son hakan, amma bai biye mata ba, zuwa yanzun ya daina yarda da zaɓin da take mishi. Sai da ya tattaro duk wani ƙarfi da yake da shi tukunna ya iya juyawa da niyyar tafiya. 

“Rafeek…”

Matar ta kira sunan shi cikin yanayin muryarta da yasa duk wani gashi na jikin shi miƙewa. Juyawa yayi, iya abinda ya faru da shi yau kawai yasa bai yi mamakin jin sunanshi a bakinta ba, hawayen da ya gani cikin idanuwanta ne suka zubo, wasu na bin su, baisan me yasa yake son ƙarasawa ya goge mata su ba, baisan me yasa yake jin kamar a zuciyarshi hawayenta suke zuba ba, bai ma san me yasa yake jin kusancin da yake ji da ita bayan bai taɓa ganin ta ba. Sosai yake kallon fuskarta, kafin a hankali ya kai hannuwanshi duka biyun yana taɓa tashi fuskar. 

Kai yake sake girgizawa, hauka yake yi tabbas, da ya sani bai fito daga gida ba, da ya zauna a gida kar wani abu ya same shi, juyawa ya sake yi, wannan karon ji yayi ta riƙo shi tana zagayawa tare da fuskantar shi, kuka take yi yanzun, kuka sosai da yake nuna daga zuciyarta yake fitowa, tana riƙe da hannun shi har lokacin, hannun ya bi da kallo, a zuciyar shi yake jin yaune idanuwan shi suka taɓa ganin ta, amma ba baƙuwa bace a zuciyarshi, runtsa idanuwan shi Rafiq yayi, ko tana cikin ɓangaren da tunanin shi ya manta ita ma. 

Sake buɗe su yayi saboda kukan ta na ci mishi rai, ya buɗe bakin shi ya fi sau biyar yana kasa fito da sauti ko kaɗan, ɗayan hannun shi yasa yana ɓanɓare nata daga jikin nashi tukunna ya wuce. 

“Rafeek…”

Baya son yadda take jan sunan shi, baya so ana ƙarashe sunan shi da K, baya kuma son yanayin yafda tsikar jikinshi take tashi da kiran sunan shi da ta yi. Ƙoƙari yake da duk wani abu da yake da shi yana ƙara ɗaga ƙafarshi don yai mata nisa, yai ma wannan ɓangaren na haukan da ya same shi nisa, gida yake so ya je, da ya sani ma da bai fito ba. 

“Rafeek… Karka tafi don Allah… Ka tsaya in ƙara ganin fuskarka ko na minti ɗaya ne.” 

Ta faɗi tana wani irin wahaltaccen kuka, baisan ko yanayin muryarta bane, ko numfashin da take mayarwa ko kuma sautin kukan da take yasa shi tsayawa yana juyawa ba, a gajiye ya ce, 

“Wacece ke? Rayuwata a hargitse take a yanzun nan, bana son sabon hargitsi…” 

Kai take ɗaga mishi, tana saka hannu tana goge fuskarta, amma hawayen ta bai daina zuba ba. 

“Wacece ke? Zan rantse yau na fara ganin fuskarki, amma ina jin kamar na sanki duk tsawon rayuwata, don Allah wacece ke?” 

Ganin ta ci gaba da kuka yasa shi sauke numfashi, kan shi ya ɗan dafe yana runtsa idanuwa. 

“Yaa Allah, me yake damuna haka?”

Ya tambayi kan shi a hankali, juyawa yake shirin yi wannan karon da niyyar ko me zata ce ba zai juyo ba. Kafin ta buɗe bakinta da furta kalaman da harya bar duniya zasu ci gaba da firgitashi ta ce, 

“Ni mahaifiyarka ce!!! Maman ka ce ni Rafeek!” 

Kalamanta ne suke mishi yawo cikin kannuwan shi suna samun wajajen zama a ko ina na jikin shi, numfashin shi ya ji ya soma mishi wuyar fita, kafin ƙafafuwan shi su fara rawa, durƙusawa yayi yana dafe cikin shi da ke hautsinawa, kafin ya runtsa idanuwan shi cikin zuciyar shi yana furta, 

‘Innalillahi wa inna ilaihir raji’un.’

Ya maimaita babu adadi tukunna ya ɗago yana sauke numfashi. 

“Ina motar ki?”

Ya tambayeta cikin muryar da bai gane tashi bace ba, cike da rashin fahimta tai mishi nuni da motar, hannun ta Rafiq ya kama yana janta bai damu da mutanen da ke kallon su ba har wajen motar. 

“Bana iya tuƙi, amma ke za ki tuƙa mu har gidan mu, ina so wani ya tabbatar min bani kaɗai nake ganin ki ba, ba ni kaɗai na ji abinda kika faɗa ba…” 

Rafiq ya ƙarasa maganar har lokacin yana jin kukan ta, bata kuma yi mishi musu ba ta ciro jakar da ke rataye a hannun ta tana fito da mukullin motar, yana kallon yadda jikinta yake kyarma, shi kam zazzaɓi sabo ya ƙara rufe shi, murfin motar ta buɗe tana shiga, ya zagaya ya buɗe shima, address ɗin gidan ya faɗa mata yana gyara zaman shi ya jingina kanshi a jikin motar da lumshe idanuwan shi ko zai samu sauƙin juyawar da yake ji gaba ɗaya duniyar shi tana yi

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 3 / 5. Rating: 2

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Alkalamin Kaddara 36 Alkalamin Kaddara 38 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×