Gidan Wadata ya kwana ranar, yadda ya ga rana haka ya ga dare, bacci ko ɓarawo bai sace shi ba. Duk soyayyar da ke tsakanin shi da abinci sai da sukai faɗa da Wadata da zai tafi kafin ya rufe ido ya sha ruwan tea, tukunna yai musu sallama yana kama hanyar Kano. Lokaci-lokaci Wadata yake kiranshi ya ji ya hanya don ya ga hankalin Altaaf ɗin baya jikin shi, ya jima bai kai Kano ba saboda yanayin tuƙin da yake kamar an mishi dole. Gidan shi ya fara wucewa ya watsa ruwa, wandon jeans ya saka sai riga marar nauyi, baya son duk wani abu da zai takura shi fiye da yadda yake jinshi.
Tun a hanya Altaaf da yai ta kiran Ashfaq bai ɗaga ba ya kira Yasir ya roƙe shi da ya faɗa mishi inda Ashfaq ɗin yake, da kamar ba zai faɗa mishi ba, don har ya bashi haƙuri ya kashe wayar, sai kuma ga text yayi mishi. Bai ɗauki mota ba, bai yarda da nutsuwar shi ba, da ƙafarshi ya taka zuwa titi yana tare mashin ya hau har Aminu Kano. Ba wai yasan kan asibitin ba ne, don sai da yayi tambaya kafin a nuna mishi ɓangaren da Ashfaq ɗin yake, sai da ya hango lambar ɗakin ya ji zuciyarshi na wani irin dokawa. Rabon da ya saka Ashfaq a idanuwan shi har ya manta.
Baisan hannun shi yayi zufar da da ke cike da fargaba ba sai da ya ɗora shi kan hannun ƙofar da nufin buɗewa, ya haɗiye wani irin yawu, ƙishin ruwan da baisan daga inda ya fito ba yana kama shi. Tsaye yayi tare da jingina goshin shi a jikin ƙofar yana kasa buɗewa, baisan ta inda zai fara ba. Idanuwan shi ya lumshe yana karanto duk wata addu’a da ta zo bakin shi, tunani yana soma fizgarshi zuwa shekarun da ya zaɓi ya manta da wanzuwar su.
*****
Kamar ko da yaushe, yau ma yana shiga gida abinci kawai ya ci, ko ruwa bai tsaya watsawa ba ya ɗauki mota yana wucewa gidan su Ashfaq, don baya jin daɗin yadda ya dinga kiran wayarshi a kashe. Ƙofar gidan yayi packing yana fitowa daga motar zuwa ciki. Da sallama ya shiga, yanayin yadda ya ga Ashfaq ɗin a tsaye yasan babu lafiya tun kafin ya tambaya.
“Altaaf…”
Ashfaq ya faɗi muryarshi na zuwa kunnuwan Altaaf ɗin da wani irin yanayi, kallon shi Altaaf yake, dauɗar kayan jikin Ashfaq ɗin ita ta fi komai tsaya mishi, Ashfaq da ko ƙura baya so ya gani a jikin kayan shi, me rayuwa ta mayar da su, da ƙyar ya iya mayar da hankalin shi kan Tariq da ke zaune, Arfa na kwance luf a jikin shi, kallo ɗaya yai ma idanuwan Tariq yasan a buge yake da kayan maye, don yasan yanayin tunda ya taɓa shaye-shayen a baya, har yanzun in ta kaɗa mishi yana kora syrup.
“Don Allah in ba inda za ka je ka zauna da su in dawo…”
Ashfaq ɗin ya faɗi cikin sigar roƙo. Kai Altaaf ya jinjina mishi.
“Ina za ka je?”
Numfashi Ashfaq ya ja yana fitarwa kamar yana ƙoƙarin danne ciwon da yake ji a zuciyarshi kafin ya amsa Altaaf ɗin da,
“Yasir ne… Tun jiya da ya fita bai dawo ba har yanzun…”
Ware idanuwa Altaaf ɗin ya yi.
“Innalillahi wa inna ilaihir raji’un.”
Ɗan murmushi Ashfaq yayi da ba shi da alaƙa da nishaɗi.
“Ka zauna da su in dawo.”
Kai kawai Altaaf ya iya jinjina mishi don baisan abinda ya kamata ya ce ba. Wucewa Ashfaq ɗin yayi, har ya kusan ƙofa ya juyo.
“Karka barsu su kaɗai Altaaf… Don Allah.”
Sai da Altaaf ɗin ya tabbatar mishi da babu inda za shi zai zauna da su har ya dawo tukunna ya fita. Kujera Altaaf ya hango ya janyota yana zama gefen Tariq. Baisan me ya kamata ya ce ma Tariq ɗin ba, don haka yayi shiru kawai yana ci gaba da danne-danne a wayar shi. Ya kusan awa ɗaya a zaune kafin kiran Ruma ya shigo wayar tashi. Ɗagawa yayi da faɗin,
“Ruma…”
Cikin sigar gaisuwa.
“Maza kana ina haka? Ga su Reena fa…”
Kallon Tariq yayi kafin ya amsa Ruma.
“Ina ɗan wani abu ne, amma dana zama free zan shigo. Kuna ina?”
Yana jin dariyar su ta cikin wayar Ruma ɗin.
“Muna ta wajen small chops, ba za ka iya zuwa ku gaisa ba. Gobe zata wuce school, don Allah ka zo minti nawa ne ba saika koma ba.”
Ɗan jim Altaaf yayi, Reena ƙawar su ce, tun suna Secondary yarinyar tai mishi, bai taɓa ta bane saboda ajin su ɗaya, baya son matsala, yaune kawai damar da yake da ita, tunda a Sudan take karatu, in ya je ɗin sukai magana ko da dare ne sai su sake haɗuwa.
“Za ka shigo ɗin mu jiraka? Ko mu yi gaba abin mu?”
Ɗan ƙaramin tsaki Altaaf ya ja yana sauke numfashi, minti ashirin ba zai canza komai ba, tunda Arfa ɗin ma bacci take, kuma Tariq na nan.
“Ina zuwa…”
Ya amsa Ruma yana miƙewa, ‘yan ɗari biyar guda biyu ya zaro yana miƙa ma Tariq da faɗin,
“Ka siya muku wani abu. Bazan daɗe ba yanzun zan dawo ka ji ko?”
Kai kawai Tariq ya ɗaga ma Altaaf ɗin, shi kuma ya juya yana kama hanyar da zata fitar da shi daga gidan.
*****
“Idan ba zaka shiga ba ka tashi daga jikin ƙofar.”
Muryar Yasir ta katse mishi tunanin da yake yi, raba kanshi yayi da ƙofar yana ɗagowa a hankali ya sauke idanuwan shi kan na Yasir ɗin.
“Ban san me zan ce mishi ba.”
Ɗan ɗaga mishi kafaɗa Yasir yayi.
“In zaka shiga ne ka faɗa min, ko me za ka yi bana son in kalla. In kuma ba zaka iya shiga ba ka matsa min.”
Kai Altaaf yake ɗaga ma Yasir ɗin yana tattaro duk wani ƙarfin gwiwa da yai saura a tare da shi ya murza ƙofar yana turawa da sallama ko zata rage mishi bugun da zuciyar shi take yi. Yana sakin ƙofar ta rufe a bayanshi, kamar mai tafiya kan ɓawon ƙwai yana tsoron fashewar shi, haka yake takawa yana shiga cikin ɗakin, Ashfaq da ke kwance ya ja jikinshi yana kishingiɗa don ya ga mai shigowa, idanuwan Altaaf kan fuskar Ashfaq ɗin suka fara sauka. A nan ya fara ganin yadda rayuwa tai mishi ado da tabbai da suka samu wajajen zama har ƙarshen rayuwar shi. Sosai yake kallon Ashfaq ɗin yana neman sanayya ko ya take a tare da shi amma ya rasa, wanda yake gani akan gadon nan ba Ashfaq ɗin da ya sani ba ne ba.
Fuskar wancan ɗauke take da yanayi na kamala da wani sanyi da ba zai iya fassarawa ba, akwai fara’a a cikin idanuwan shi, akwai burika shimfiɗe a cikin su, wannan Ashfaq ɗin babu ko ɗaya daga cikin abubuwan da wancan yake da su, Altaaf zai iya rantsewa ba shi kaɗai Ashfaq ɗin nan ya tsorata a kallo na farko kaɗai ba, ga wani irin girma da ya ga ya yi mishi sosai. Shekarun da yayi bai ganshi ba sun nuna sosai. Har gefen gadon da Ashfaq yake Altaaf ya taka yana jin ƙafafuwanshi sun mishi nauyi sosai, hakan yasa shi jan kujerar da take a wajen ya zauna.
Da Ashfaq ya ji an turo ƙofar ma ya ɗauka Yasir ne, ko da wasa bai taɓa tunanin zai ga Altaaf ɗin ba, gashin da ke fuskar Altaaf ɗin ne kawai banbancin da ke tsakanin shi da fuskarshi da Ashfaq ya sani, sai tsayi da ya ƙara, bayan hakan yana nan yadda yake, haƙoran shi Ashfaq yake haɗewa waje ɗaya cikin bakin shi yana jin abinda ganin Altaaf ɗin yake mishi, yana jin yadda tunani ke son ƙwace mishi da ganin Altaaf, yadda abubuwan da ya zaɓi da ya danne suke son tasowa. Sosai yake kokawa da su, yake son maida tunanin da ya yunƙuro mishi.
*****
Duk inda yake tunanin zai iya ganin Yasir ya duba, har inda ma baya tunani ko zai ganshi, in ka ga yadda yake tafiya yana surutai shi kaɗai ba za ka taɓa tunanin akwai wadataccen hankali a tattare da shi ba. Ba haka sukai da Yasir ba.
‘Ka zauna da su in samo mana abinda za mu ci.’
Haka Yasir ya ce bawai zai tafi ya ƙi dawowa har yanzun ba.
“Yasir don Allah kar kai min haka, ni ya kamata in kasance ko ina ne kake yanzun, ni ya kamata in fita nemo abinda za mu ci ba kai ba.”
Ashfaq yake faɗi yana dafe kanshi tare da juyawa ko zai ga ɓullowar Yasir ɗin, dana sanin barin shi fita tun jiya yake ji da wani yanayi mai nauyin gaske. Tun jiyan yadda suka ga rana haka suka ga dare shi da Tariq, yadda Tariq yake kallon shi kamar shi ne sanadin ƙin dawowar Yasir na taɓa wani abu a zuciyar shi.
‘Komai baya tafiya dai-dai tare da mu, kana kallo kuma, ka dawo da shi, ka dawo da Ya Yasir.’
Tariq ya ce mishi da safe bayan sun idar da sallar Asuba, bai ce mishi komai ba saboda baisan abinda zai ce mishi ɗin ba, yana kallon yadda yake riƙe Arfa yana ƙin barinta ko kusa da Ashfaq ɗin ta zo kamar itama zai barta ta fita wani abu ya same ta. Duk yadda yaso ya ji haushin Tariq da laifukan da yake ɗora mishi ya kasa, saboda yana jin akwai gaskiya a tattare da hakan. Zazzaɓi yake ji a jikin shi tun safe, yanzun ɗin kuwa har cikin idanuwan shi a duk buɗewa da rufesun da zai yi yake jin zafin zazzaɓin.
“Ta ina kake so in fara? Yasir ta ina kake so in fara neman ka?”
Ashfaq yake tambaya yana juye-juye, hanyar gida yake nufa, ƙafafuwan shi har raɗaɗi suke saboda tafiya, ɗari biyu ce a jikin shi da ƙyar ya samu dakon da yayi a cikin kasuwa, in ya ɗauki Naira hamsin ya ce ya hau mashin da ita za su yi wani abin da ya fi hakan muhimmanci, ba tafiyar da yake yi bace damuwar shi, abinda zai faɗa ma Tariq, yadda zai fara sanar da shi bai ga Yasir ba, bai kuma san abinda zai yi ba shi ne damuwar shi. Tafiya kawai yake yi, ba zai ce ga daga inda yake samo ƙarfin da yake ɗaga ƙafafuwan shi da su ba. Baya son tunanin yanayin da yake ganin Tariq ɗin tun daren jiya da ya dawo, baya so ya alaƙanta Tariq da inda ƙwaƙwalwar shi take neman kaishi, hakan ba zai taɓa faruwa da Tariq ba.
Tunda ya karya kwanar unguwar su zuciyar shi ta sake salon bugawar da take yi tare da ƙara gudu, sosai gudun ta yake ƙaruwa da duk takun da yake kusanta shi da gida, a ƙasan cikin shi da wani abu ya ƙulle ya fara sanin wani abu ya faru da su, wani abu ya sake faruwa da su, yanayin ba baƙo ba ne a wajen shi, yanzun ne ya fara fahimtar shi, duk idan wani abu mai girma zai taɓa rayuwar shi yakan ji yanayin, sai da ya samu waje ya tsaya yana dafa bango tare da maida numfashi, ya tuna cewar ya bar Altaaf tare da su, Altaaf yana nan ko menene ya faru, zai taya shi kula da su, shi yasa ya roƙe shi ɗin da ya zauna don yana jin in ya bar su Tariq su kaɗai wani abu zai iya samun su.
Da ƙyar ya samu ya ci gaba da tafiya, yamma ta yi sosai, dandazon mutane yake hangowa a gaban gidan su, amma zuciyarshi na gaya mishi baida alaƙa da taruwar su, ko kaɗan, don taron mutane a wajen shi ba abu ba ne me kyau, taruwar mutane a wajen shi tabbaci ne na wani mummunan abu ya faru da su. Takawa yake har ya ƙarasa inda mutanen suke, ture su yake yana wucewa da nufin shiga gida, cikin kunnuwanshi ya ji saukar muryar Tariq da wani yanayi yana faɗin,
“Arfa! Arfaaa!!”
Baisan yadda akai ya juyo ba, ko yadda ya samu ƙarfin ture mutanen da ke wajen ya ratsa tsakiyar su, Tariq ya gani zaune a ƙasa ya riƙo Arfa jikin shi yana wani irin numfashi kamar wanda aka shaƙe, jijjigata yake yi amma ko motsi bata yi, binta da kallo Ashfaq yayi, jinin da ke jikin doguwar rigar da take jikin ta na zaunar mishi da wani yanayi a zuciyar shi da yake da tabbacin ba zai barshi ba har abada.
“Tariq…”
Ya kira muryarshi can ƙasa don bai ma ɗauka Tariq ɗin ya ji shi ba sai da ya juyo. Yana ganin shi yana sakin wani irin gunjin kuka da Ashfaq ya ji sautin a cikin zuciyar shi. Numfashin Tariq ɗin yana tsai-tsaiyawa ya ce,
“Ya… Ya… Yaya… Bansan me ya sameta ba… Yaya don Allah.”
Tsaye Ashfaq yake kamar an dasa shi yana kallon Arfa, yana kuma jin yadda Tariq yake roƙon shi da ya yi wani abu, amma bai san me zai yi ba, duk idan ya runtsa idanuwan shi baya ganin komai sai jinin da ke jikin Arfa da yake son tabbatar mishi da abinda yake kokawar yarda da shi.
“Ashfaq”
Ya ji an kira ana dafa shi, juyawa yayi yana kallon Altaaf da yanayin razanar da ke bayyane a fuskar shi, cikin muryar da Ashfaq bai gane tashi bace ya ce,
“Na roƙe ka, sai da na roƙe ka karka barsu…”
“Ashfaq”
Altaaf ya sake kiran sunan shi wannan karin cike da roko, yana mayar da hankalin shi kan Tariq din
“Ka ɗauko ta mu tafi asibiti”
Tariq bai yi musu ba ya miƙe da Arfa da ke jikin shi yana ratsa mutanen da ke basu hanya.
“Muje Ashfaq”
Altaaf ya faɗi, bai yi musu ba ya bi bayan su Tariq saboda baya son ganin mutanen da ke kallon su, mutanen da taron su baida wani amfani, mutanen da yake da tabbaci in rai aka zare musu babu wanda zai taimaka musu da ko da ruwa, yana jin yadda soyayyar shi da mutane take yin wani irin nisa da mamaki saboda shi ɗin da kanshi ma mutum ne, ba zai yiwu ace baya son mutane ba. Asibitin kuwa suka nufa, suna zuwa da gudu Tariq ya shiga da Arfa ciki, yanayin ta yasa wata Nurse zuwa da sauri ta karɓeta, Ashfaq bai tsaya duba sunan asibitin ba, ya dai san na kuɗi ne daga yanayin kulawar da akai musu.
Wani likita ne ya ƙaraso shi ma da gudun shi suna shimfiɗe Arfa a nan ƙasa don ganin kamar tana buƙatar taimakon gaggawa da ba zai iya jira a shiga wani waje da ita ba, sosai likitan yake dubata, kafinya ɗagata yana wucewa da ita, binsu Tariq zai yi Nurse ɗin ta hana shi, dole sukai tsaye bakin ƙofar ɗakin da aka shiga da Arfa ɗin, likitan ya fi mintina ashirin kafin ya fito daga ɗakin yana kallon su da wani yanayi a fuskar shi da Ashfaq baya so.
“Ina iyayen ta?”
Likitan ya tambaya, hakan kuma ba zai rasa ganin da yayi Ashfaq kanshi ba zai ƙarasa shekara ashirin ba, kuma ya girmi Altaaf da kusan shekara ɗaya, balle kuma Tariq
“Ka fada mana ko menene, iyayen ta sun rasu dukkan su”
Wani irin numfashi likitan ya ja.
“Kuna buƙatar ‘yan sanda…”
“Yan sanda kuma?”
Tariq ya tambaya da mamaki ƙarara a muryarshi, su duka suna zubama likitan idanuwa.
“Saboda…”
Kokawa likitan yake da maganganun da zai faɗa musu, hakan kawai na ƙara tabbatar ma Ashfaq da ba alkhairi ba ne ba.
“Ka ga, ƙanwar ku ce?”
Likitan ya tambaye su, kai suka ɗaga mishi su duka ukun.
“Na ce kuna buƙatar ɗan sanda ne saboda fyaɗen da akai mata.”
Likitan ya ƙarasa maganar da wani irin yanayi a fuskar shi.
“Me? Fya… Fyaɗe?”
Tariq yake tambaya cikin ɗaga murya, Ashfaq kam wani irin duhu yake ji cikin kanshi na mamaye ɓangarorin da haske yai ragowa.
“Tana ina?”
Ashfaq ya tambaya.
“Ku yi haƙuri… Ku yi hakuri…”
Kai Tariq yake girgiza ma likitan don ba zai yiwu ba.
“Karka faɗi ko me kake son ka faɗa, don Allah karka faɗa…”
Haƙurin dai likitan yake ci gaba da basu yana ƙarawa da
“Ta rasu!”
Durƙushewa Tariq yayi yana wani irin gunjin kuka da ke fitowa wani iri saboda kokawar da yake yi da numfashin shi, wuce shi Ashfaq yayi zuwa ɗakin da Arfa take ya ɗaukota a kafaɗarshi yana fitowa da ita, tsugunnawa yayi ya kamo Tariq da ke wani irin kuka yana miƙar da shi tsaye, baisan me likitan yake faɗi ba saboda baya gabanshi, jan Tariq yake suna nufar hanyar da ta shigo da su Asibitin, zuwa motar Altaaf ɗin da ya rugo yana buɗe musu suka shiga. Banda kukan Tariq baka jin tashin komai a cikin motar har suka karasa gida. Fitowa Ashfaq yayi har lokacin gawar Arfa na kafaɗarshi.
Binsu ciki Altaaf yake shirin yi Ashfaq ɗin ya dakatar da shi tare da sa ɗayan hannun shi ya tura shi baya.
“Ashfaq”
Altaaf ya faɗi cike da shakku da alamun tsoro. Kai Ashfaq yake girgiza mishi.
“Ka tafi Altaaf…”
“Don Allah… Ashfaq…”
Kai yake girgiza ma Altaaf ɗin,
“Sai da na roƙe ka, karka bar su, ka zauna da su har in dawo na ce, ban ɗauka zai maka wahala ba.”
“Ashfaq”
Altaaf ya ce, amma ko nuna alamun ya ji ya kirashi bai yi ba ya ci gaba da maganar da yake yi.
“Bazan taɓa yafe maka ba Altaaf…ka tafi…don Allah ka tafi bana son ganin ka.”
Ashfaq ya ƙarasa yana juyawa ya kama hannun Tariq da yake kuka har lokacin suna shigewa cikin gida.
*****
“Ashfaq!”
Altaaf ya kira a karo na babu adadi kafin ya samu nasarar raba shi da tunanin da yake yi.
“Me ka zo yi? Na ɗauka na faɗa maka bana son ganin ka.”
Kai Altaaf ya jinjina, yasan me Ashfaq ɗin ya faɗa mishi, daga ranar kuma Ashfaq yayi ƙoƙarin ganin Altaaf bai sake nuna mishi fuskarshi ba, dan sa’adda ya koma gidan ma basa nan, sun bar gidan shi da Tariq, ya sha wahala kafin ya gano inda suka koma, ko da ya gano ɗin ma bai samu ya ga Ashfaq ba, sai dai Yasir yake haɗuwa da shi, shi ne ma ya bashi lambar wayar Ashfaq ɗin, kuma zuwan da yake yi akai akai neman Ashfaq ɗin yasan cewar Yasir abokinshi ne, bai dai san inda suka haɗu ko ya akai suka haɗu ba.
“Nasan me ka ce min, ban manta ba…”
Sosai Ashfaq ya tashi daga kan gadon, in bai manta me ya faɗa mishi ba, baisan me yasa ya zo ba, yana sa shi jin zuciyarshi kamar zata fito saboda abinda yasa shi yi yanzun, tunanin da ya dawo mishi da shi sabo yana fama mishi ciwukan da yake riritawa.
“Kar ka ce in yafe maka…”
Ashfaq ya faɗi cike da kashedi, yana sa Altaaf ɗin jin wani irin nauyi a ƙirjin shi.
“Me yasa?”
Numfashi Ashfaq ya ja yana fitar da shi ta bakin shi, ƙiris control ɗinshi yake jira ya ƙwace daga hannun shi, ganin Altaaf ya saka shi jin abubuwan da ya jima bai ji ba, daga Tariq, Yasir, kudi, sai kanshi ne abinda ya damu da su yanzun, baisan me yasa Altaaf zai dawo da kanshi rayuwarshi ya ƙara mishi wata sabuwar wahalar ba.
“Idan na roƙe ka ma ba zai yi aiki ba, na farko ma bai yi ba da na ce don Allah ka fita ka barni, karka ƙara dawowa, amma ba zai yi aiki ba, banda wannan darajar a wajen ka.”
Fuskarshi Altaaf yasa cikin hannuwanshi yana wani irin maida numfashi, maganganun Ashfaq ɗin sun mishi zafi sosai, fiye da yadda yake zaton za su yi mishi, duk da ya zo da shirin jin kowanne irin abu daga wajen Ashfaq ɗin, a hankali ya buɗe fuskar shi yana sauke idanuwan shi kan Ashfaq.
“Ka faɗi duk abinda zaka faɗa Ashfaq, ban zo wajen ka ba yau sai da na shirya zan ji duk wani abu da za ka faɗa min kuma zan jure…”
Murmushi Ashfaq ya yi.
“Banda abinda zan faɗa maka, ka kulle min ƙofar in ka fita.”
Ya ƙarasa maganar yana komawa ya kwanta kan bayanshi tare da lumshe idanuwan shi, sai dai abinda ya manta shi ne Altaaf yana da naci in har ya saka ma ranshi abu, ya kuma saka ma ranshi sai Ashfaq ɗin ya yafe mishi, ko ba yau bane sai ya fara mishi magana a hankali a hankali, ko da kuwa in ya zo kullum zai kore shi ne.
“Babu abinda yake tafiya dai-dai a rayuwata Ashfaq…komai zai ƙara jagule min, son kaina na da yawa ban nace kan ganin na gyara dangantakarmu ba tun tuni sai yanzun da nake buƙatar duk wani wanda zan iya samu a ɓangarena. Amma bai dameni ba wallahi, abinda ya dameni shi ne ina buƙatarka a rayuwa ta, ka yi haƙuri, ka yafe min, na maka laifi, ban cika maka alƙawarin da na ɗaukar maka ba. In da zan koma baya zan sake komai wallahi…. Don Allah ka yi haƙuri.”
Ba tare da Ashfaq ya buɗe idanuwan shi ba ya ce,
“Matsalar kenan, ba za ka iya komawa baya ba… Ba za ka iya canza komai ba. Amma zaka iya tafiya ka bar min ɗakin nan in sha iska.”
“Ashfaq mana.”
Altaaf ya faɗi yana ɗorawa da,
“Ka yi haƙuri… Don Allah ka yi haƙuri… Ka ji.”
Shiru Ashfaq yayi, amma surutun Altaaf ɗin ya fara hawar mishi kai, kuma komai zai iya faruwa in bai fita daga ɗakin ba. Surutun Altaaf ya ci gaba da yi mishi, a hankali ya miƙe yana juyo kuafafuwan shi ya sakko da su daga kan gadon suna taɓa ƙasa. Altaaf ya kalla cikin fuska.
“Ka tafi don Allah.”
Kai Altaaf ya girgiza mishi duk da yanayin Ashfaq ɗin ya tsorata shi ba kaɗan ba, zuciyar shi na faɗa mishi ƙaddararshi kenan shan duka a hannun mutanen da ya fi kusanci da su, don da alama gab Ashfaq yake da saka mishi hannu, ba kuma zai fita ba.
“Ka ce ka yafe min to, ko ka ce za ka yafe mun ko ba yau ba ne ba. Sai in tafi.”
Altaaf yai maganar yana wani irin sauke murya. Cikin hargowa Ashfaq ya ce,
“Me yasa baka ganewa ne? Bazan iya yafe maka ba Altaaf, bansan laifin wa zan gani ba idan na yafe maka! Kana jina…bazan iya yafe maka ba….don Allah ka tafi kafin in dake ka, bana so Tariq ya shigo ya ganka… Go, just go Altaaf don Allah.”
Kai Altaaf yake jinjina mishi yana miƙewa don ganin yanayin yadda zaman nashi ke hurting ɗin Ashfaq ɗin.
“Zan dawo… Ka yi haƙuri, amma zan dawo, zan kuma ci gaba da dawowa har sai ka yafe min.”
Altaaf ya ce cike da alƙawari kafin ya taka zuwa ƙofar yana ficewa daga ɗakin.
*****
Yana fita ƙofar asibitin wayarshi ya ɗauka yana kiran Ammi ta ce mishi sun dawo ita tana gida ma, don haka ya tari mai mashin yana nufar can kan shi tsaye. Bai sake jin shi kamar ana rabashi da wani ɓangare na jikin shi ba sai da ya shiga gida da sallama ya samu Ammi a falon tare da Aslam.
“Ammi…”
Ya kira muryarshi ɗauke da wani irin yanayi.
“Yaya ina wuni”
Aslam ya gaishe da shi, kai kawai ya iya ɗaga ma Aslam ɗin yana kasa ko kallon inda yake ballantana ya iya haɗa idanuwa da shi. Yanayin shi Ammi ta kalla yasa ta faɗin,
“Altaaf ɗin Ammin shi, lafiyarka dai ko?”
Kai ya girgiza ma Ammi, don ba lafiyar shi ƙalau ba, muryarshi can ƙasan maƙoshi ya ce,
“Aslam don Allah ka bamu waje mana.”
Ba tare da musu ba Aslam ya miƙe yana ficewa daga gidan ma gaba ɗaya. Numfashi Altaaf ya sauke ya ƙarasa kusa da Ammi ya zauna a ƙasa kan kafet yana matsawa ya ɗora goshin shi kan gwiwarta yana wani irin sauke numfashi da yasa Ammi dafa kanshi kamar wani ƙaramin yaro.
“Altaaf… Kasan za ka iya faɗa min komai ko? Menene? Waya taɓa ka? Wa yai maka wani abu?”
Murmushin ƙarfin hali Altaaf yayi, babu wanda ya taɓa shi wannan karon, shi ne ma yai laifin, bai kuma san ta inda zai fara faɗa mata ba.
“Ikon Allah, me nake gani haka?”
Barrah ta faɗi tana mayar da alewar da take sha ɗayan gefen bakinta tare da ware idanuwa. Ba tare da Altaaf ya ɗago da kanshi ba ya miƙ hannu yana ware shi saitin inda ya ji muryar Barrah
“Gata nan za ka karya mata ƙafa ai, don Allah ka tashi Yaya ni kunya nake ji.”
Kai Ammi ta girgiza.
“Ki ƙyale min yaro Barrah.”
Daƙuna fuska Barrah ta yi.
“Yanzun in wani ya ji sai ya ɗauka ɗan shekara biyu ne ba talatin da wani abu ba….Yayaaa ka ɗaga min Ammi.”
Barrah ta ƙarasa maganar tana zagayawa cikin falon tare da kamo hannun Altaaf ɗin tana janshi, ɗagowa yayi ya sauke mata gajiyayyun idanuwan shi, yanayin fuskarshi yasa ta sakin hannun shi tana kai nata hannun kan kuncin shi da ta ji wani irin zazzaɓi ne ruf a jikin shi.
“Yaya me ya same ka? Baka da lafiya ne? Me ya faru?”
Kai Altaaf ya girgiza mata, damuwar da ke fuskarta na taɓa mishi zuciya.
“To menene? Me ya sameka? Wani ne yai maka wani abu? Ammi me kikai mishi?”
Barrah ta ƙarasa maganar tana kallon Ammi cike da tuhuma.
“Don ubanki ni? Me zan mishi to?”
Ammi ta tambaya tana mamakin ƙarfin halin Barrah, kamar tana son nuna mata ta fita son Altaaf ɗin . Cike da sabuwar damuwa Barrah ta ce,
“To me akai mishi?”
Wannan karon Altaaf ne ya amsa ta da faɗin,
“Bakomai Barrah, babu wanda yai mun wani abu. Ki je ina son magana da Ammi.”
Kai ta girgiza mishi tana maƙale kafada, rigimarta tun yarinta babu abinda ya canza. Numfashi Altaaf ya sauke, yasan faɗa ba zai kaishi ko ina ba.
“Don Allah…”
Ya ce cike da roƙo.
“Za ka faɗa min ko menene? In kun gama magana da Ammi?”
Kai ya ɗaga mata, ko bai yi niyyar faɗa mata ba ma dole ta sani.
“Ba wai ina sonka bane ko wani abu, bana so wani abu ya same ka ne saboda babu wanda zan takura ma.”
Ta faɗi tana wucewa, sai da Altaaf yai ɗan murmushi duk yanayin da yake ji kuwa. Hankalin shi ya mayar kan Ammi, yana riƙo hannuwanta duka biyun tare da jan wani irin numfashi mai nauyi yana fitar da shi a hankali, idanuwan shi kafe kan hannun Ammi da yasan ko kowa ya barshi ba zata taɓa barin shi ba, tukunna cikin wani irin nisantaccen yanayi ya soma magana.
“Kin tuna Nuwaira? Ammi kin tuna ta?”
Wani irin dum Ammi ta ji cikin kunnuwanta kamar Altaaf ɗin ya doka mata wani abu, ta tuna Nuwaira, ta manta ta na tsawon shekarun nan, amma bawai ta ɓace mata gaba ɗaya ba ne ba. Kai ta jinjina mishi a hankali maƙoshin ta na bushewa, haka kawai take jin bata son jin ko menene Altaaf ɗin zai faɗa mata.
“Da gaske ne, wancan lokacin abinda ya faru ba ƙarya tai min ba…”
Altaaf ya faɗi yana jin wata irin kunya da bai taɓa sanin zai iya jinta ba, girman laifukan shi na danne shi, iya Ammi ce kawai yake buɗe ma wannan sirrin kaɗai cikin dubunnan da bata sani ba, baisan me zai faru a filin alƙiyama inda duka duniya zata ga sirrikan shi ba. A hankali tsoro mai tsanani yake maye gurbin kunyar da yake ji. Ammi kuwa kamar an dasata, numfashi ma a hankali take yinshi saboda tashin hankalin da take jinta a ciki, da ƙyar ta iya cewa,
“Shekarun da yawa Altaaf, kuma ya riga ya wuce, karka bari ya dame ka…kana jina?”
Kai Altaaf ya girgiza mata, bai wuce ba, matsalar kenan, shi ma ya ɗauka ya wuce, amma sam bai wuce ba.
“Ammi”
Ya kira a wahalce, bai bari ta amsa ba ya ɗora da faɗin,
“Ta haihu… Yara biyu… Mace da namiji… Yara na ne Ammi!”