Skip to content
Part 43 of 52 in the Series Alkalamin Kaddara by Lubna Sufyan

Abuja

Ɗakinta ta wuce tana saka mukulli ta rufe shi daga ciki.Tana da tabbacin su Huda basu dawo daga makaranta ba. Hakan ba ƙaramin daɗi yayi mata ba, don tana da tabbacin zasu tsareta da tambayar me ya faru don yanayinta bai ɓoye tashin hankalin da take ciki ba. Bata jin ta shirya basu wannan amsar. Kan gado ta ƙarasa ta zauna, ɗan kunnayen da ke kunnuwanta ta cire, sannan ɗankwalinta da mayafi, komai nauyin shi take ji, kayan jikinta, jikin nata da kanshi da duk wani abu da ya ƙunsa. 

Bata san ta inda ya kamata ta fara tunani ba, ba wai don bata san rana irin ta yau zata iya zuwa mata ba, sai dai hakan baisa ta shirya hargitsin da zuwan yau zai taho mata da shi ba, asalima ko a tunanin da take yi bata ɗauka abin da wahala haka ba, sai yanzun da take jin kamar wani ya kama ƙafafuwanta ya wuntsula ta tana tsaye ne da kanta, ta kuma soma jin jiri saboda wahalar da hakan take dashi. 

***** 

Ba zata ce ta taso cikin wadata ba, suna da rufin asiri don sun fi ƙarfin abincin wata ɗaya ma, su huɗu ne kacal a wajen mahaifinta M. Kamala da mahaifiyarta Maryama. Bara’atu, Asiya, Fadila sai autansu Shamsu. Mahaifinta ɗan kasuwa ne da yakan siyar da yadika na maza da kuma na ‘yan makaranta Islamiyya da boko, yana da ɗan karamin shagon shi da yake haya a kasuwar Sabon Gari. Duk da daga shi har mahaifiyar ta basu yi karatun boko ba, gashi kuma Allah ya azurta su da samun yara mata har uku, hakan yasa M. Kamala tsayawa tsayin daka wajen ganin sun samu ilimin addini da na boko. 

Duk da surutun da yake sha daga dangin shi da na matarshi kan karatun yaran, don a ganinsu in yara mata sun samu karatun addini hakan ya wadatar, asalin shi da Maryama ‘yan ƙauyen Kurfi ne na jahar Katsina, kasuwanci ya kai iyayensu garin Kano har suka samu wajen zama. Don shi M. Kamala ƙauye ya koma ya auro Maryama. Amma duk da hakan ya toshe kunnuwanshi daga dukkan wani surutu da ake mishi, Bara’atu ce bayan ta gama aji uku a sakandire masoya sukai mata ca, hakan ya ba su Maryama tsoro suka aurar da ita, haka ma Asiya tana aji biyar aka rabata da makaranta aka aurar da ita. 

Duka wannan abin a idanuwan Fadila suka faru, lokacin tana aji biyu Sakandire, duk da makarantar gwamnati ce, Allah yai mata wata irin ƙwaƙwalwa, bata taɓa karanta abu sau biyu ba, in ta gani sau ɗaya ya wadatar, hakan yasa take shiri da malamansu na Islamiyya da kuma na boko. A Islamiyya ta yi ƙawa guda ɗaya da take makarantar kuɗi, Hannatu. Wata irin shaƙuwa ta ƙullu tsakanin su da Fadila na son ta ji ta koyi yaren turanci, don larabci kusan babu abinda bata ganewa, mayarwar ne ba komai ba, shi ma tana ƙoƙarin kamanta hakan. 

Lokacin da ta shiga aji huɗu a Sakandire tana jin turanci sosai, don har mamaki malamanta suke yi na kalar ƙoƙarin ta, in ta dawo makarantar boko da islamiyya ta kammala dukkan ayyukanta, kunnenta na manne da ƙaramar Radio tana sauraren labarai da duk wasu shirye-shirye da ake na turanci tana ƙoƙarin ganin ta gyara turancin ta. 

“Fadila Baturiya…”

Babanta kan faɗi in ya ganta da Rediyonta, abin na mata daɗi ba kaɗan ba. 

“Baba kamin addu’a kai dai, ina da burin yin karatu mai zurfi.” 

Shi ne amsar Fadila a koda yaushe. M. Kalama bai taɓa kashe mata burinta ba, don har gida wasu cikin malamanta na Islamiyya kan zo su faɗa mishi yadda take da matuƙar ƙoƙari. Don haka maganar shi bata wuce. 

“Allah ya bamu aron rayuwa ya taimake mu.”

Burin da Fadila take da shi yasa bata kula kowanne saurayi da zai zo mata da maganar soyayya. Ko a hanya ka tareta zata ce maka an mata miji ka yi haƙuri, mijinta Soja ne baya ƙasa, da kuma ya dawo za’ayi bikinsu, hatta ƙawayenta a lokacin banda Hannatu babu wanda baisan Sojan Fadila ba, ta yi hakanne don kar wani yayi ƙoƙarin cewa zai haɗa ta da saurayi ko yai mata maganar dalilin da yasa bata kula samari. Takan ji Mamanta na maganar ita har yanzun shiru, bata cewa komai don burin ta na karatu shi ne sama da komai a lokacin, bata kuma fatan komai yai mata katanga da hakan. 

A haka da ƙyar ta kai aji shida, don lokacin ba dangi kaɗai suke mata surutu ba, har mamanta a ƙagauce take da ta ga sun kawar da ita, maganarta a kullum Fadila kaɗai ce macen da ta rage a gabansu, sai autansu Shamsu, takan ce gara ta aurar da ita ko zata yi bacci babu fargabar komai. Amma Fadila ta ƙi yin tsayayyen saurayi ballantana ma har ta kai ga maganar aure. Maryama kan ce M. Kamala ne ya biyewa shirmen Fadila na cewar tana son ci gaba da karatunta bayan aji shida. 

Murmushi kawai yakan yi, yana ji a jikinshi ‘yar tashi zata zama wani abu wata rana. Duk da yasan dole ne zata yi aure, amma kyawun Fadila da ƙoƙarinta yana da tabbacin wanda duk zata aura wanda yasan muhimmancin karatu ne zai kuma barta ta cika burinta. Ko da ma babu surutun’ yan uwanshi na kawar da Fadila, akwai rashin wadatar da zai ɗauki nauyin karatunta. Ana haka ta zana jarabawar kammala Sakandire ta WAEC da kuma NECO. Zuwa lokacin matsin da ake mata kan aure yayi yawa, don dai rashin wani tsayayyen da za’a ce ya turo ne kawai yasa ba a aurar da ita ba. Fadila ba zata manta da wani yammaci da yazo mata da sauyi mai girma ba, watanni kaɗan bayan kammala jarabawarta ta aji shida. 

Don kuwa Principal ɗinsu ce ta zo da kanta, sosai zuciyar Fadila ke dokawa da son sanin abinda zuwan Principal ɗin tasu ya ƙunsa. Tasan gidan ne lokacin Fadila na aji huɗu da tai wata irin rashin lafiya kamar ba zata tashi ba, sun zo dubata saboda muhimmancin da take da shi wajen ba makaranta gudummuwa, don ko gasa za’a je Fadila kan zamo ɗaliba ta gaba-gaba wajen lashe musu gasar. Hakan ya ƙara sawa suke ji da ita sosai. Principal ɗin bata wani ɗauki lokaci wajen sanar da Maryama wajen babansu Fadila ta zo ba bayan sun gaisa. 

Hakan yasa Maryama sanar da ita cewar yana kasuwa, baya kuma dawowa sai bayan sallar Magriba, cewa ta yi zata jira saboda maganar na da matuƙar muhimmanci. Zaman kuwa ta yi suna ɗan taɓa hira har Magariba suka tashi suka yi sallah. Fadila na ɗaki daga bakin ƙofa ta laɓe don ta ji ko menene, gabanta kuwa faɗuwa kawai yake yi. Har M. Kamala ya shigo suka gaisa da Principal ya wuce ɗakinshi. Maryama ce ta bishi tai mishi bayanin abinda yake faruwa. 

Fitowa yayi, Maryama na saka mishi kujera ya zauna. Sake gaisawa suka yi da baƙuwar kafin ta soma mishi bayanin zuwanta. 

“Ba saina sake faɗa muku yadda Fadila take da matuƙar ƙoƙari ba, dukkan kun san da wannan. Jiya ne jarabawar su ta aji shidda ta fito. Da kaina na je na dubo ta Fadila, ta kuma yi nasarar cinye dukkan subjects ɗin.” 

Hamdala M. Kamala da Maryama suke yi, alfaharin da suke da Fadila fal a fuskarsu, magana ta ci gaba da yi da faɗin, 

“Akwai jarabawa da gwamnati kan yi duk shekara da take ba ɗalibai samun damar yin karatu a ƙasar waje, kuma gwamnati ce take ɗaukar ɗawainiyar komai. Na zo ne saboda sati na sama za’ayi jarabawar, ina son in roƙe ku da ku bar Fadila ta zana jarabawar nan, tana da ƙoƙarin da zata zama wani abu a rayuwar ta.” 

Tunda aka ambaci ƙasar waje, Zuciyar Maryama ta soma rawa, ta sha jin labaran yaran da kan je ƙasashen waje don yin karatu, rayuwarsu ta lalace, maza ma balle kuma ɗiya mace, ita kam wannan abin bai zauna mata ba. Hatta shi kanshi M. Kamala tunanin da yake yi kenan. Sosai Principal ke musu bayanin muhimmanci karatun da kuma ci gaban da ba Fadila kaɗai ce zata samu ba, har da su kansu da kuma al’umma gaba ɗaya. Sosai M. Kamala da Maryama suka jinjina maganar, surutun da za su sha a dangi kaɗai ma ya ishe su. Yanzun ma suna kan sha balle kuma an ji labarin za su bar Fadila ta yi wannan jarabawar. Ƙila ma ‘yan uwan M. Kamala da suke ƙauye su yanke alaƙa da shi gaba ɗaya. Yasan aƙidarsu ta rashin son makarantar boko. 

“Na san dole za ku yi tunani mai zurfi akai. Ku barta tayi jarabawar, komin ƙoƙarin da kake da shi sai kana da rabo ne zaka ci, idan ta ci sai ku fara tunanin me za ku yi da hakan.” 

Fadila kuwa tana daga ɗaki, jikinta ya ɗauki ɗumi da maganganun da take ji, da alwalarta dama, don haka sallolin nafila ta shiga jerowa tana roƙon Allah da ya sa iyayenta su amince da wannan damar da take shirin samunta. Damar da ko a mafarki bata taɓa hango zata samu ba, sosai take kuka a sujjadarta, don har ranta tana matuƙar son karatunta, tana kuma da buruka masu tarin yawa. 

***** 

Sai da aka kwana uku da zuwan principal tukunna iyayen Fadila suka amince da ta zana jarabawar, bayan dogon nazari da kuma tattaunawa da M. Kamala yayi shi da matarshi, sun kuma yanke hukuncin in har Fadila ta ci jarabawarta za su toshe kunnuwansu daga dukkan surutun mutane su barta ta tafi. Don M. Kamala yana ganin dama ce Allah ya bashi ta sanadin ‘yar tashi wataƙila yayi arziƙin da kaf danginsu babu maishi. Ya kuma san idan hakan ya faru su kansu zasu manta da yadda suka ta mishi surutu lokacin tafiyarta makarantar. 

Ba Fadila ba hatta’ yan uwanta sai da suka jinjina al’amarin ta hanya mai kyau. Don ci gaban ‘yar uwarsu nasu ne gaba ɗaya. Da wani irin ƙarfin gwiwa Fadila ta je ta zana jarabawarta ta dawo gida suka ci gaba da addu’ar neman zaɓin Allah akan jarabawar da tayi. Sai dai su kansu iyayen Fadila basu da masaniya akan abinda zata karanta, principal ɗinsu kanta ta yi mamaki da ta ji cewar ɓangaren engineering Fadila take so, maimakon likita kamar yadda ta hango mata. 

Kai Fadila ta girgiza mata tana murmushi, akwai likitoci da dama, ita ma tunanin zama likitan ya sha zuwar mata, sai da ta ji hira da wata Eng. Munnira a gidan radio na BBC Hausa, abin ya ƙayatar da ita sosai, musamman da ta ji nasarorin da ta samu da matakin da ta kai a rayuwa. Fadila na da burin zama wata, tana da burin yin kuɗi ba ‘yan kaɗan ba, ba al’umma zata yi wa karatu ba, ba zatai ƙarya ba, ba don ta taimaki kowa ba face sai don kanta da iyayenta take da burin karatu, ko da kuwa likitan ta zama. Kuɗin da zata samu ne farko kafin komai. 

Sannan acan ƙasan zuciyarta tana da burin auren mai kuɗi, kuma wayayye wanda boko ta ratsa, ba don komai ba sai don cikar burinta, ko da bata samu fita ƙasar waje ba. Ta kuɗiri niyyar soma kula samari sosai, a cikinsu ta fitar da wanda zata yi amfani da shi wajen cikar burinta, a ranta tana jin zata iya auren sa’an mahaifinta indai yana da kuɗi kuma hakan na nufin cikar burinta. Wannan shi ne tunanin Fadila a ko da yaushe, yadda zata zama wata, yadda sunanta zai shahara a ƙasarta. 

Har azumin nafila ta ci gaba da yi bayan yin jarabawarta, aikam sunaye na fitowa a gidan Radio ta fara ji sunanta ne na takwas cikin wanda aka ɗauka zuwa ƙasar Mexico, daga ita har Maryama sun kasa ɓoye murnarsu, don rungume juna sukayiy suna tsallen farin ciki. Koda M. Kamala ya dawo gida suka sanar da shi haka nashi farin cikin ya kasa ɓoyuwa. Sun yanke shawarar su ja bakinsu su yi shiru, ko ‘yan uwa sai bayan ta tafi za su ji, tunda su dukkansu Allah yayi ma iyayensu rasuwa ballanta a ce basu kyauta ba. Sai dai yayye da kuma kawunnai. 

A cikin watanni uku aka kammala shirin komai, nasiha babu kalar wadda Fadila bata sha ba, kuka kam sun ci shi ita da Maryama da ‘yan uwanta, hatta Shamsu sai da ya zubda ƙwalla don sanin cewar ba zasu sake ganinta ba sai bayan shekaru huɗu cur. Babu kuma wanda yake da tabbacin kaiwa lokacin a cikinsu, sai dai ɗan Adam baya rasa buri. Haka jirginsu Fadila ya ɗaga zuwa ƙasar Mexico tare da sabon shafin da alƙalamin ƙaddara ya rubuta mata. 

***** 

Yau ce ranar farko da zata fara zuwa aji, su biyu ne a ɗakin su, ita da Zainab Isah, itama ‘yar Nigeria ce, sai dai akasin Fadila da gwamnati ke ɗaukar ɗawainiyar karatunta, Zainab mahaifinta ƙusa ne a gwamnati, shi ne kuma yake ɗaukar nauyin karatunta a ƙasar ta Mexico kuma shekarta ta biyu kenan. Kallo ɗaya za kai mata daga yanayin shigarta da komai kasan ta waye ta fannin duk da zai fassara kalmar. 

Fadila ta ɗauka zata yi girman kai, sai ta sameta da sauƙin hali, don ta karɓe ta da hannu biyu kamar dama tana jiranta. Yanzun haka shiri suke na tafiya makaranta, Zainab na taje gashinta da babu laifi duk da ba tsayin kirki yana da cika sosai. Ta kalli Fadila da ke sanye da riga da zani ɗinkin simple. Girgiza mata kai Zainab ta yi. 

“Zani a ranar ki ta farko? Ki yarda da ni kina buƙatar kayan da za ki sake a cikin su…” 

Ɗan murmushi Fadila ta yi, atamfar ita ce mai kyau kuma sabuwa a cikin duka kayan da ta mallaka, don ta sallar da ta wuce ce. Kusan yanayin ta Zainab ta gani yasa ta faɗin. 

“Da kaɗan kika fi ni tsayi, ina zuwa…”

Wucewa ta yi ɓangarenta ta buɗe wajen ajiyar kaya ta ciro doguwar riga da Fadila ba zata ce ɗinka ta aka yi ko ta kanti bace tana cilla mata. 

“Wannan zai yi. Kiyi sauri ba kya so ki makara ajinki na farko ba.” 

Ɗauka Fadila ta yi tana jin laushin rigar cikin hannunta da baƙuntar komai, ji take kamar mafarki take har lokacin, ta kasa yarda rayuwa ta kawota inda take yanzun. Shi ne ƙarin abinda yasa ta karɓi rigar da Zainab ta bata, in mafarki ne ba zata yi wasa da duk wata dama da ta samu a cikin shi ba. Tana kallo Zainab ta girgiza kanta ganin ta wuce banɗaki don sake kayan. Ita kanta da ta fito saida ta yi mamakin yadda rigar ta zauna mata kamar an auna.

“Wow…Rigar nan bata taɓa min kyau kamar yadda ta yi miki ba.” 

Murmushi Fadila ta yi a kunyace. 

“Come on, kwanan mu biyu fa, kunyar nan ta tafi haka.” 

Zainab ta faɗi suna yin dariya su dukkansu. Ƙarasa shiryawa suka yi, Zainab ta bata wani farin mayafi ta kuma taimaka mata ta naɗa shi tasa mata wani ɗan ƙaramin abu ta matse shi yadda ba zai faɗi ba. Tare suka fita, Fadila na ƙoƙarin yin kalle-kalle, don ƙauyancin ta tasan ya bayyana shimfiɗe da yanayinta ba saita sake fito da shi ba. Amma duk da haka da suka shiga makarantar sai da ta sa hannunta ta shafi ginin ko zata ga ya ɓace. 

Zainab na ta gaisawa da mutane. Turawa, Larabawa da ‘yan ƙasashe kala-kala, baka sanin akwai al’umma sai ka bar duniyar da ka saba da ita zuwa wata tukunna. Gyara zaman jakar da ke kafaɗar ta da Zainab ce ta bata ta yi tana jin daɗin yadda babu wanda ya damu da kallon su, kowa harkar gabanshi yake yi, kafin ta ɗago da kanta tana sauke idanuwanta akan shi. Akwai wani tsohon littafin turanci da wata ƙawarta ta bata, cewarta yayanta ne yayi gyaran ɗaki duk ya zubdo su shi ne ta ɗauko mata. Tun bata gane komai a littafin take karantawa har ta fara ganewa. 

Zata rantse bata taɓa zaton da gaske wasu abubuwan da ta gani a cikin littafin suna faruwa ba, sai yanzun da ta tsinci kanta tsundum cikin wani shafin, iskar wajen ta yi tsaye na wasu ‘yan daƙiƙu, kafin ta ci gaba da kaɗawa cikin wani yanayi da ba shi da kalaman misaltawa, hannu ta kai kan ƙirjinta tana dafe zuciyarta da ta shiga wani hali da bata taɓa tunani ba. 

“Yaa Allah…”

Laɓɓanta suka furta, sai bayan wasu shekaru masu zuwa ne zata fahimci da gaske zuciya ke ganin kyau a yanayi na soyayya, idanuwa basa wani amfani a lokacin. Yanzun kam bata tunanin ta taɓa sauke idanuwanta akan wata halitta ta jinsin namiji me kyawun wanda idanuwanta suka sauka akai. Hakan bashi da alaƙa da farin fatar shi ko yanayin shi da ba na Bahaushe ba, don ya fi mata kama da Balarabe, don tana da nacin kallon fina-finan India duk idan ta samu damar yin hakan. Har gidan maƙwaftansu take shiga saboda fina-finan India. 

Bata tunanin ko a cikin duk wanda ta gani akwai me kyauwun shi. Tana tunanin in ya fi yadda yake kyau ba zai kasance cikin jinsin bil’adama ba. Ya ɗaga hannun shi yana tura yatsun shi cikin gashin kanshi kafin ya sauke hannun yana kallon agogon da ke ɗaure a hannun shi. Yanayin na ƙara mishi wani kyau da yasa numfashin ta ɗaukewa. Girgiza ta ta ji an yi. 

“Banza inata magana kin yi shiru…”

Zainab ta faɗi tana ƙarasa maganar da dariya sosai ganin inda hankalin Fadilan ya tattara. Ita kam Fadila jikinta ya gama mutuwa cikin wani irin yanayi, numfashin ta ma bata jin yana fita dai-dai, bata kuma jin zai sake komawa yadda yake da. 

“Nawfal Adyan Jawdan…”

Zainab ta furta a hankali, ba saita faɗa ba, Fadila tasan sunan nashi ne, na saurayin da ke tsaye nesa da ita ne, don ya dace da shi ta ko ina. 

“Har yanzun na rasa abinda yake da shi da mata suke gani haka. Ina nufin akwai wanda suka fishi kyau a ajinmu kawai sun fi goma, balle kuma duka makarantar nan…” 

Kai Fadila take girgiza ma Zainab ɗin tunda ta fara magana, bata yarda ba, a jinsin mutanen duniya na zamaninta bata tunanin akwai wanda ya fi Nawfal kyau, ballantana kuma a cikin makarantar nan. Bata gansu ba, da suka shigo, yanzun ma gasu nan suna wucewa, amma ko kusa basu kaishi kyau ba. Murya can ƙasa ta ce, 

“Ba za ki gane ba Zainab…”

Ɗan daga kafaɗa Zainab ta yi. 

“Well malamin mu ne…”

Cike da mamaki Fadila take kallon Zainab 

“Meye?”

“Gani nayi yayi yarinta da zama malami. Na ɗauka ɗalibi ne…” 

Kai Zainab ta girgiza. 

“Dole sai tsoho ne zai zama malamin makaranta? Kuma ai ba yaro bane ba, ya kai shekara talatin da wani abu… Kin ga muje…” 

Zainab ta ƙarasa tana jan hannun Fadilan don ta ga alama bata ƙi su wuni tsaye a nan ba in dai Nawfal na wurin. Juyawa Fadila ta sake yi don ta kalle shi, ta kusa sauke idanuwanta cikin nashi, kallon ta yake kamar yasanta, zata rantse da Allah kallonta yake kamar yana mamaki tare da kasa yarda cewa ita ɗince ya gani, kamar ya sha jiranta sai yau ya ganta. Kallon na sake jefata cikin wani irin yanayi, ba a tunaninta bane, Nawfal kai ya ɗan ɗaga mata cikin alamar gaisuwa kafin su sha kwana ya ɓace ma ganinta. 

Jininta da ya ɗauki ɗumi ya kamata ya zama kashedi a wajenta, da yadda wani irin zazzaɓi mai zafin gaske ya rufeta ga zuciyarta na dokawa har cikin kunnuwanta. Hakan duka ya kamata ya zamar mata kashedi na ta yi nisa da Nawfal. Sai dai burinta yayi dai-dai da shi, mafarkinta ne ya zama gaskiya a gaban idanuwanta. Lokaci ɗaya abinda ya kawota ƙasar Mexico ya ɓace mata da tunanin yadda zata samu Nawfal ta kowanne hali…” 

***** 

“Yafindo…”

Huda ta kira a karo na ba adadi, muryarta cike taf da tsoro ganin yanayin da mahaifiyar tata take ciki. Sai lokacin ta katse mata tunanin da take yi. Hannu Yafindo ta miƙa ma Huda da ta kama tana dumtsewa tare da zama a gefen gadon. 

“Yafindo… Lafiya dai Ko?”

Huda ta tambaya cikin harshen Fulatanci, kai Yafindo ta girgiza mata kuka mai sauti na ƙwace mata, da yasa Huda riƙo ta jikinta a rikice, idanuwanta na cika da hawaye itama don wannan ne karo na farko da ta ga hawayen Yafindon su na zuba cikin yanayin nan. Ba wai bata kuka ba, amma ba irin na yau ba. Ƙwanƙwasa ƙofar aka yi. 

“Waye?”

Huda ta buƙata muryarta a karye. 

“Ni ne…”

Numfashi ta sauke kafin ta ce mishi ya shigo. Yana turo ƙofar ganin shi yasa kukan da Huda ke dannewa ya ƙwace mata. 

“Hamma…”

Ta kira tana so yai wani abu kan halin da Yafindo take ciki don ita kam bata san me ya kamata ba. 

“Me ya faru?”

Zaid ya buƙata. Kai Huda ta girgiza mishi alamar itama bata sani ba. Ta ɗayan gefen ya ƙarasa yana zama kusa da Yafindo. Cikin sanyin murya ya kira sunanta, yana ƙara mata gudun kukan da take yi don bata san ta inda zata fara musu bayani ba, bata ma san me zata ce musu ba.  

Bata san me zata fara gaya musu ba. Hakan kawai na ƙara jefata cikin tashin hankali, kuka take yanzun kam sosai. Musamman da ta ji hannun Zaid kan kafaɗarta. Huda na sake dumtse hannunta da take riƙe da shi, lallashin ta suke ba tare da sun sake ce mata komai ba, a lokaci ɗaya kuma suna faɗa mata ba sai ta gaya musu abinda yake damun ta ba, nutsuwarta suka fi buƙata. 

***** 

Su dukkan su a gidan Muneeb suka kwana, da sassafe bayan sallar Subh suka koma gida. Tun lokacin kuma da Rafiq ya shiga ɗaki bai fito ba. Ya sa mukulli ya kulle daga ciki. Ba yadda Aroob bata yi ba don ya buɗe ta kawo mishi abinci, amma ya ƙi yana faɗa mata baya jin cin komai ta barshi kawai. Nuri tasa suka ƙyale shi dole, amma suna nan zaune a bakin ƙofar ɗakin shi. Abincin su ma nan suka ci, Nuri bata yi ƙoƙarin ce musu su tashi ba, don bata tunanin za su saurareta, ko son da suke mata ya fi na Rafiq, nisan babu wani yawa. Har goman dare suna nan zaune, sallah kawai ke tashin su. 

“Yaya don Allah ka buɗe mana mu shigo… Wallahi ba za mu yi surutu ba, zama kawai za mu yi.” 

Aroob ta faɗi tana ƙara ƙwanƙwasa ɗakin. 

“A nan za mu kwana in baka buɗe ba…”

Cewar Fawzan yana ɗora wa da, 

“Yaya mu ɗauko pillow ko za ka buɗe mana?”

Rafiq daga ɗayan ɓangaren yana jinsu, tun da aka idar da sallar isha’i ya ɗauka sun tafi, baya son magana, in zai iya tsayar da tunanin shi na ‘yan kwanaki zai yi l, hutawa kawai yake son yi daga komai. Shirun su ne yasa ya ɗauka sun tafi tun ƙarfe takwas, agogon da ke manne a bangon ɗakin ya duba yana ganin goma har ta wuce. Taurin kansu na bashi mamaki, sai dai me ƙannen shi ne, wannan a jinin su yake. 

Wani abu ya ji ya matse a ƙirjin shi, wani ɓangare tare da shi na tuna mishi cewar su ba jininshi ba ne ba duk da hakan bai canza yanayin ƙaunar su a zuciyar shi ba. 

“Fawzan don Allah ku tafi. Ina buƙatar zama ni kaɗai ne kawai.” 

Ya faɗi muryarshi babu ƙarfi. 

“Tam ka zauna. Muna nan dai in kana buƙatar mu.”  

Fawzan ɗin ya faɗi. Yana jin muryoyin su ƙasa-ƙasa alamar suna hira. Ba dai za su bar ƙofar ɗakin nashi ba. Tashi yayi daga kan kujerar falon yana nufar ƙofar ya sa hannu ya murza mukullin ƙofar yana buɗewa, suna zaune a bakin kofar ɗakin za ka rantse da Allah cikin ɗakunan su suke yadda suka barbaje. 

“Ban isa in yi magana ku ji ba ko? Zafira harda ke…” 

Kai ta girgiza mishi da sauri tana faɗin 

“Yaya…”

“Ba wani Yaya… Ban ce ku tafi ba tun ɗazun?”

Ya buƙata yana riƙe da ƙofar, Aroob ce ta miƙe tsaye, idanuwanta cike taf da hawaye da yasa shi kiran  

“Aroob…”

Don baya son kukan da take shirin yi, ko kaɗan baya son su sake yin kuka fiye da wanda suka yi jiya, kansu zai yi ciwo in bai fara ba kenan. Ya buɗe baki zai yi magana Aroob ta faɗa jikin shi ta zagaya hannuwanta a bayanshi ta rungume shi gam kamar zai ruga. 

“Aroob za ki karya min haƙarƙari…”

Sake matse shi ta yi, wannan karon da gaske yake jin kamar zata karya mishi haƙarƙari, ƙarfinta na bashi mamaki. 

“Na ji ku shigo…sake ni.”

Dariya ta yi duk da kukan da take yi tana ɗagowa daga jikin shi. Ɗakin ya juya zai shiga ya ji takun tafiyar Nuri kamar cikin zuciyarshi take yin shi, ya ji kusancin ta kamar yadda yakan ji ko da takunta bai yi sauti ba, ya rayuwa za tai mishi haka? Wannan kusancin, wannan ƙaunar a ce babu haɗuwar jini. 

“Nuri…”

Ya furta yana juyowa, murmushin ƙarfin hali ta yi mishi, yana ganin yadda idanuwanta sukai zuru-zuru. 

“Tasneem…”

Nuri ta sake faɗi yana jin yadda ƙirjin shi yake ƙoƙarin buɗewa da kiran sunan Tasneem ɗin, don numfashin shi ya fara wahalar fita. 

“Ka barta ita kaɗai, ka ga ba cikakkiyar lafiya gare ta ba, tun jiya baka gida, hankalin ta ba zai kwanta ba. In ba za ka koma ba, Fawzan ya sauke Aroob ta taya ta kwana…” 

Kai Aroob take girgizawa, tana turo laɓɓanta, idanuwanta cike taf da hawaye. Bayan Rafiq ta laɓe tana maƙale kafaɗa. 

“Yaya ni ba inda zan je. Ka faɗa ma Nuri ina nan ka ji.” 

Ta ƙarasa maganar hawaye na zubo mata. Ga Zafira nan sai a ce ita zata je ta kwana, ba mai sata barin Rafiq a halin da yake ciki. Numfashi Nuri ta sauke. 

“Kuje ku ɗauko ta… Sai ta kwana a nan.”

Muryar Rafiq can ƙasan maƙoshi ya ce, 

“Tana gidan su…”

Cike da mamaki Nuri take kallon shi, kafin kalaman shi su zauna mata. 

“Rafiq!”

Ta kira cikin tashin hankali

“Rafiq me ka yi?”

Ta buƙata muryarta na karyewa. Idanuwan shi Rafiq ya ji suna raɗaɗi amma baya jin alamar hawaye ko kaɗan a cikin su, ga hanjin shi sun ƙulle tunda Nuri ta kira sunan Tasneem ɗin. Shi kanshi bai san me ya aikata ba, sai yanzun ma ya tuna bata da lafiya, ya kuma tuna sharuɗɗan likita akanta. Wannan karon jikin shi ba ɗumi ya ɗauka ba, jin shi yake kamar an watsa mishi ruwan ƙanƙara. 

“Yayaaa.”

Fawzan ya kira, Rafiq na jin muryarshi cike da tuhuma da rashin jin daɗin abinda ya aikata ɗin. 

“Yaa Rafiq da ciki a jikinta fa.”

Zafira ta ce muryarta na rawa da alamun kukan da ke son ƙwace mata, tun jiya ta sa ƙafafunta cikin takalman da ƙaddara ta miƙo ma Rafiq amma sun kasa zama, bata san asalin hargitsin da yake ji ba, amma hakan bai danne adalcin ta ba. Don shi ya koya musu hakan, ko shi yayi ba dai-dai ba su nuna mishi, kar ƙaunar da suke mishi ta taɓa hana su ganin laifin shi, ya koya musu ƙauna bata cika sai da ganin kuskuren juna. 

“Ka yi kuskure Yaya.”

Zafira ta furta a hankali, Nuri na jinjina kai don ita ba zata taɓa iya faɗa mishi hakan ba. 

“Ƙila yayi kuskure, ƙila bai yi ba. Idan ta yi mishi wani abu ne fa? Me yasa zaku dinga kallon shi kamar yayi wani abu bayan bakui san me ya faru ba?” 

Aroob take faɗi a hasale tana kama hannun Rafiq ɗin ta dumtse cikin yanayin da ke faɗa mishi ita ta fahimta, ita ba zatai judging ɗin shi ba ko me ya faru. Hakan yasa zafin da ƙirjin shi yake yi ya ragu, sai dai baya son kallon tuhumar da suke mishi. Bai ce komai ba ya juya yana riƙe da hannun Aroob suka wuce cikin ɗakin. Fawzan da Zafira na rufa musu baya, Nuri na kallon su, Fawzan ya rufo ƙofar don shi ne ƙarshen shiga, suna barinta tsaye a wajen kamar basa buƙatar ta tunda suna da junan su, kamar basa buƙatar kowa a duka rayuwarsu indai suna da juna, kamar ko da duniyar zata birkice indai suna tare da junan su za su sake miƙewa. Numfashi mai nauyi ta sauke, indai komai zai dai-dai ta bata damu da yadda suka nuna basa buƙatarta ba.

<< Alkalamin Kaddara 42Alkalamin Kaddara 44 >>

2 thoughts on “Alkalamin Kaddara 43”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.