Skip to content
Part 47 of 52 in the Series Alkalamin Kaddara by Lubna Sufyan

Kano

“Allah na gaji da asibitin nan, ina ji kamar an kulle ni a waje ɗaya ne…”

Cewar Ashfaq yana gyara zaman shi, ji yake da gaske kamar an kulle rayuwar shi waje ɗaya. Dariya Tariq da yake zaune kan kujera ya yi.

“Ka saba da yawo ne, ba ka nan ba ka can, ba dole ka ji kamar an kulleka waje ɗaya ba.”

Haɗe fuska Ashfaq yayi, duk da akwai ƙamshin gaskiya a zancen Tariq ɗin.

“Ni ka fita ka siyo min nama da surutun nan da kake min.”

Da mamaki Tariq yake kallon shi, kafin ya danna wayar shi da take kan cinyar shi yana ganin ƙarfe huɗu da kwata.

“Ina masu nama suka fara gasawa yanzun? Ka bari sai da dare Yaya…”

Miƙewa daga kwanciyar da yake yayi, yana gyara zaman pillow ɗin ya jingina.

“In ba za ka je ba ka faɗa min…”

Ya ce yana tsare Tariq ɗin da idanuwa, hakan yasa shi miƙewa yana nufar ƙofa, har ya buɗeta ya juyo da faɗin,

“Wane iri?”

Ɗan ɗaga mishi kafaɗa Ashfaq yayi da alamar da ke fassara koma wane iri tukunna ya fita daga ɗakin yana jan ƙofar. Numfashi Ashfaq ya ja yana fitarwa da nauyin gaske. Yana jin yanayin da yai ma Tariq ɗin magana na danne shi. Ba kuma laifin Tariq ɗin ba ne, Altaaf ne, shi ya ja mishi wannan ɓacin ran da yake fama da shi kwana biyu. Ya manta ranar ƙarshe da control ɗin shi ya ƙwace daga hannun shi akan abinda yake ji sai a kwanakin nan, kowa ya samu dama masifa yake mishi. Jiya Nurse ɗin da zata canza mishi ruwa yai ma ihun da har yau bata sake dawowa ɗakin ba, wani namiji ne yake shigowa sai likitan shi.

Lumshe idanuwanshi yayi yana jin kamar kanshi zai yi ciwo, baisan me yasa a duk shekarun nan sai yanzun ne Altaaf zai zaɓi ya zo mishi don ya taso mishi abubuwan da suka ɗauke shi lokaci yana binnewa ba, da mutuwar Arfa ya rufe komai, ko ita bai bari ta taɓa shi yadda ya kamata ba, saboda yana jin yadda komai zai tarwatse mishi in ya bar hakan ya faru, da sukai ma Yasir sadakar mutuwa ma bayajin ya ji wani abu, ya riga ya zagaye zuciyarshi da wasu irin katangun da Altaaf ya zo ya ƙwanƙwasa mishi.

Ƙwanƙwasa ƙofar ya ji an yi da wani irin ƙarfin gaske kamar ana shirin karyata. Tsaki ya ja yana ɗorawa da,

“Shigo…”

Ya tattara gaba ɗaya nutsuwar shi ya mayar kan ƙofar yana son ganin kowanne marar hankalin ne yake buga mishi ƙofa haka, ya ji an sake bugawa.

“Na ce kowaye ya shigo ko?!”

Ashfaq yace yana sauko da ƙafafuwanshi daga kan gadon da shirin zuwa ya buɗe ƙofar ya ga an turo, muryar Tariq na dira kunnuwan shi da faɗin,

“Nasan ƙila na maka kama da mahaukaci, wallahi da hankalina, zan dai iya samun matsalar haukan idan na ce musu na ganka suka ce cikin kaina abin ya faru…”

Daquna fuska Ashfaq yayi, don fitar Tariq ɗin da dawowar shi duka basu shige mintina sha biyar ba ko ƙasa da hakan.

“Tariq…”

Ashfaq ya kira yana leƙ kan shi cikin son hango wanda Tariq ɗin yake magana da shi, motsin da yayi na sa ƙirjin shi amsawa cikin raɗaɗin da ya ji har tsakiyar ƙwaƙwalwar shi. Hakan yasa ya runtsa idanuwan shi yana kiran,

“Yaa Rabb…”

Maganar da Tariq ya sake yi na saka shi buɗe idanuwan shi babu shiri, numfashin shi yana wahalar fitarwa saboda azabar da yake ciki.

“Tariq!”

Ya kira a ƙagauce.

“Yaya don Allah ka fito ka ganshi, ya ƙi shigowa…”

Tariq ya amsa muryar shi a karye, tashi Ashfaq ɗin yake son yi, amma ƙirjin shi kamar zai buɗe yake ji. Dafa gadon yayi da hannuwan shi duka biyun da nufin miƙewa, yana ɗago da kai ya sauke idanuwan shi kan Yasir da yanayin rayuwa bai hanashi gane shi ba, kayan jikin shi yake fara bi da kallo, wandon jeans ne iya ƙwaurin shi sai wata riga Yellow. Idanuwan shi Ashfaq ya ƙifta, yana sake ƙifta su cike da rashin yarda, kafin wata ‘yar dariya ta kubce mishi. Akwai dalilin da yasa duk yadda akaita mishi ta yi kayan maye bai taɓa karɓa ba, saboda yana son zama cikin hankalin shi ko da yaushe, ko yanzun ya kai kwana uku rabon da ya sha magungunan da za su rage mishi raɗaɗin ciwon shi, saboda suna saka shi bacci, in ya tashi yana jin kanshi yayi nauyi.

Yasir ɗin da yake tsaye ya sake kallo, da murmushin rashin yarda a fuskar shi ya ɗaga hannun shi yana ma Yasir ɗin alama da ya ƙaraso inda yake, ga mamakin Tariq, a hankali ya ga Yasir ɗin ya motsa yana takawa ya ƙarasa har bakin gadon Ashfaq ɗin, kujerar da ya tashi a kai ita Ashfaq ya janyo ma Yasir da ya kama yana zama, idanuwan shi na kan Ashfaq ɗin kamar yana so ya gane inda yasan shi ko makamancin hakan.

“Yayaa ka ga…”

Tariq ya fara magana, Ashfaq na katse shi ta hanyar faɗin,

“Shhhh…”

Shirun kuwa yayi yana jin yadda yake buƙatar wani abu da zai taimaka mishi a yanayin nan.

 Ashfaq kuwa hankalin shi gaba ɗaya yana kan Yasir, hannu ya kai yana ɗan taɓa kafaɗar shi a tsorace, a zaton shi Yasir ɗin zai wargaje ya ɓace ma ganin shi saboda yana da tabbacin a tunanin shi yake. Sai dai kuashi da tsoka a haɗe ya ji ya taɓa, alamar jikin mutum na gaske, hannun shi ya janye yana share zufar da yake ji a goshin shi, kafin ya girgiza kai cikin rashin yarda. Wani irin numfashi yake shaƙa yana fitarwa a wahalce.

“Me yasa nake jin kamar na san ku?”

Yasir da yake zaune ya tambaya, yana jin kanshi yana sarawa kamar zai rabe biyu. Muryar shi na dira kunnuwan Ashfaq ɗin da wani irin yanayi da ya saka shi saukowa daga kan gadon ya zauna a ƙasa yana dafe kafaɗarshi da yake jin kamar ba a jikin shi take ba saboda azabar zogin da take da yake neman fin ƙarfin ƙwaƙwalwar shi. Da kuyar ya iya faɗin,

“Ya… Ya… Yasir…”

Yana miƙa mishi hannun shi da ya kama da sauri saboda wani irin yanayi da yake ji da ya kasa fahimtar daga inda yake fitowa, a bakin gate ɗin asibitin yake tsayawa wani lokaci shi da yawan masu harkar Achaɓa irin shi don gudanar da sana’arsu, a nan Tariq ya ganshi ya same shi yana mishi maganar ya taimaka ya zo ya ga wani ɗan uwan shi, in ya ce musu ya ganshi ba za su yarda ba, ya zo suma su ganshi. Kayan jikin Tariq ɗin ya sanar da shi cikin hankalin shi yake, sai kuma wani irin kusanci da yake ji da yaron, da fuskar shi da take mishi kamanni da wadda ya sani amma ya kasa tuna ko a ina ne.

Ba zai ce ga dalilin da ya sa ya bi Tariq ɗin ba, kamar yadda yanzun ya kama hannun Ashfaq, da kamar hakan kanshi yake jira yai wata irin sarawa da ta sa shi runtsa idanuwan shi yana sa ɗayan hannun shi ya dafa kan nashi, hoton kwantar da wani da wasu mutane da suke sanye da jajayen kaya suka yi, ɗaya daga cikinsu na ɗaga wata irin wuƙa da ƙyallinta yake ƙara mishi ciwon kan da yake na dawo mishi, so yake ya buɗe idanuwan shi don ya kauce ma dawowar hotunan amma kamar an manne su da wani abu mai danƙo haka yake ji. Yana kallo mutumin ya tsugunna yana ɗora wuƙar a wuyan mutumin yana yanka shi kamar rago, jini na ci gaba da kwaranya, mutumin na wani irin mutsu-mutsu duk da riƙon da sauran mutanen sukai mishi, amma bai daina yanka wuƙar a jikin wuyan nashi ba, har sai da ya ga ya daina motsin da yake, bai ɗaga ba sai da ya raba gangar jikin shi da kan yana janye shi gefe.

Da wani irin gunji Yasir ya buɗe idanuwan shi yana sauke numfashi a wahalce, kanshi na ci gaba da mishi lugude, ya kama hannun Ashfaq ya riƙe gam kamar duka rayuwar shi ta ta’allaqa akan hakan.

“Yasir…”

Ashfaq ya kira cike da shakku a muryar shi, ware idanuwa Yasir ɗin yake a kanshi yana jin sunan na dira kunnuwan shi da wani irin yanayi don Muhammad yake amsawa tun lokacin da ya buɗe idanuwa ya tsinci kanshi yana tangaririya a titi, ƙwaƙwalwar shi kamar an kwashe komai da yake cikinta, banda irin hotunan nan da yakan gani lokaci zuwa lokaci, sai kuma mugayen mafarkan da yake fama da su duk ana yanka mutane a gaban idanuwan shi, ana kuma sassara su, a rarraba sassan jikin su baya tuna komai. Cikin kasuwa yake shiga duk kalar aikin ƙarfin da ya samu yayi, ya gama kuma ya kwana a tasha. Babu kalar sana’ar da baiyi ba, kafin ya tara ‘yan kudin da ya kama hayar shago a unguwar kurna Naira da kwabo, nan kan layin mai wuya, kasancewar akwai almajirai manya-manya, ga kuma shaguna nan da sukan kama suma.

Da kuɗin ya fara mishi tsada haɗawa suka yi shi da wani ƙolo nan suke zaune, a haka har Allah ya taimake shi wani Alhaji da ke kan layin da yake raba Achaɓa domin haya ya yaba da hankalin shi ya bashi ɗaya shima, kuma zai gode ma Allah tunda aka bashi mashin ɗin da za ka dinga kawo balas har shekara biyu ya zama naka yake cikin rufin asiri har mashin ɗin ya zama mallakin shi. Amma lokaci zuwa lokaci yakan ji wani irin fili a rayuwar shi da ya rasa na menene, yakan kuma so tuna daga yadda farkon rayuwar shi ya fara, amma saiya kasa.

Mugayen mafarkan da yake fama da su, malamin makarantar allon kusa da su ya faɗa ma yake mishi rubutu yana bashi har Allah ya taimake shi suka yi mishi sauƙi sosai. Yanzun kam yana jin su Ashfaq ɗin na neman dawo mishi da ciwon kan da yai fama da shi kamar zai mutu sabo da su.

“Yasir!!”

Ashfaq ya kira wannan karon yana jijjigashi, din ya ga alama da gaske Yasir ɗin ne a gaban shi bawai a tunanin shi yake ba, amma yana kallon shi kamar bai gane shi ba, abinda baya jin zai iya ɗauka a halin yanzun.

“Da gaske ina ji kamar na san ku.”

Yasir ya sake faɗi yana sa Ashfaq gyarawa ya durƙusa kan gwiwoyin shi yana kama ɗayan hannun Yasir ɗin ya riƙe tare da dumtse su duka biyun.

“Ba kana ji bane ba, ka sanmu, wallahi ka sanmu. Yasir kai ne…Tariq bai yi ƙarya ba da ya ce min ya ganka, da gaske ya ganka ɗin. Oh Allah na…”

Cewar Ashfaq kamar wanda ya samu taɓin hankali yana ɗorawa da,

“Ka kalleni, ko me ya sameka ya riga ya sameka, amma ba zai yi sanadin da za ka manta mu ba, ka kalleni da kyau Yasir, kallona za ka yi , ni ne…”

Kallon shi Yasir ɗin yake yi kuwa, zuciyarshi na wani irin tsalle a cikin ƙirjin shi, yanayin na sa shi jin kamar tare da wani abu a cikin ƙwaƙwalwar shi hakan ta faru.

‘Yasir ka tashi mana, kana ji har an tashi sallah, ni na tafi ka yi sauri kai alwala ka fito.’

Ya ji wata murya a wata irin duniya da yake jinta da nisan gaske ta faɗin. Ganin da gaske Yasir yake bai gane shi ba ya sa Ashfaq kallon Tariq da yake tsaye ya zuba musu idanuwa yana faɗin,

“Tariq ka zo, in ya kasa gane ni babu abinda zai samu rayuwar shi da zai manta ka…”

Ƙarasowar kuwa Tariq yayi yana samun waje gefen gadon ya zauna. Hargitsi ba sabon abu bane a wajen shi, shi yasa yake a nutse daga wajen shi, ba za ka taɓa cewa wani abu mai girma na faruwa da shi ba. Inda ma zai samu ko da syrup ne kwalba biyu, komai zai fi tafiyar mishi yadda ya kamata.

“Kai mishi magana mana Tariq…”

Ashfaq yake roƙon shi cikin wani irin yanayi, har lokacin yana durƙushe kan gwiwoyin shi, kallo ɗaya za kai mishi kasan ba cikin hankalin shi yake ba.

“Me zan ce mishi?”

Ɗan ɗaga kafaɗa Ashfaq yayim

“Komai ma…ban san meya same shi ba, komai ka faɗa mishi.”

Numfashi Tariq ya sauke.

“Bansan ta ina zan fara ba. Yaya Yasir ka kalle ni, ban san me zan gaya maka ka tuna ba, ban san ya zan fara faɗa maka jini iri ɗaya ne yake yawo a jikin mu ba, wallahi bansan ta inda zan fara ba, ko me ya kamata in ce maka…”

Sosai Yasir yake kallon shi, maganganun shi na mishi kamar dirar wani abu cikin kan shi.

“Yadda mukai rayuwa tare zan fara zayyana maka Yaya? Ko yadda muka rasa su Ummi? Ko sunana zan faɗa maka?”

Ko motsi Yasir bai yi ba, idanuwan shi da sukan kifta lokaci zuwa lokaci kawai suka nuna alamar cewar yana jin Tariq ɗin. Murmushi kawai Tariq yai mishi yana dafa katifar da dukkan hannuwan shi, sosai yake buƙatar shan wani abu, ko ya yake, yana jin yadda jikin shi ya soma ɓari daga ciki, idanuwan shi ya lumshe, farkon da Ashfaq ya zo da Yasir abokin shi da ya ji yayi waƙa ba zai manta kalaman daya faɗa mishi ba.

‘Yaa Rabbi, Tariq kana da murya, sosai kana da murya, me yasa ba za ka fara waƙa ba? Ina nufin waƙa sosai a studio da komai da komai’

Ba zai manta yadda yai dariya ba kawai, don har Ummin shi kafin rasuwarta tana faɗa mishi yadda Allah ya bashi murya, ko da karatun Ƙur’ani yake yi, lokutan da suke zuwa Islamiyya har malamai kan yi magana kan muryar shi. Yasir ya fi kowa gaya mishi yadda nuryar shi jari ce, za su nemi kuɗi da ita sosai, duk dai bai taɓa ra’ayin hakan ba tun da farko, waƙa ba komai bace sai nishaɗi a wajen shi, lokuta da dama baisan yana yi ba sai ya ji sautin muryar shi cikin kunnuwan shi tukunna. Sai dai akwai sautin tsuntsun da ke nutsar da shi, tsuntsun kanari, yana da su da yawa a cikin wayar shi.

Yanzun ma cikin kanshi yake kwaikwayar sautin, bai san yadda akai ya ƙwace yana fitowa fili ba, asali ma baisan ya fito filin ba. Yana yi ne ko zai samu ‘yar nutsuwa. Idanuwan shi a lumshe yake, zai iya rantsewa har cikin kanshi yana ganin tsuntsun Kanarin da yake ƙoƙarin kwaikwayon sautin shi. Ba Ashfaq ba ne yake kallon shi, Yasir ne yake jin sautin har cikin ƙasusuwan jikin shi.

‘Banza kawai, wallahi na ɗauka tsuntsun gaske ne, ka sa ina neme-nemen inda nake jin kukan tsuntsu.’

Yasir ya ji maganganun sun dawo mishi.

‘Allah ya yafe maka halinka.’

Ya sake ji.

‘Tariq za mu ja kuɗi da muryarka ɗin nan.’

Maganar ta sake dawo mishi, yana runtsa idanuwan shi, wasu hotuna na gilma mishi, kafin ya buɗe su cikin tashin hankali ya ce,

“Tariq!”

Hakan yasa Tariq ɗin buɗe idanuwan shi yana kallon Yasir da yake zame hannuwan shi daga cikin na Ashfaq ɗin, hannun shi na rawa ya ɗaga shi zuwa fuskar Tariq ɗin, da sauri Tariq ya ɗora nashi hannun kan na Yasir yana faɗin,

“Yaya…”

Muryar shi a karye, ganin sanayya a idanuwan Yasir ɗin, ganin yanayin da mafarkin shi bai bari ya manta ba na buɗe wani abu a cikin zuciyar shi.

“Ka ce min ka nemi kuɗi da muryar ka.”

Yasir ya faɗi yana rasa yadda akai ya rasa shekaru masu yawa haka tare da Tariq ɗin, yadda yai girman da yayi yanzun ba’a gaban idanuwan shi ba. Wata irin dariya Tariq yayi tare da girgiza ma Yasir ɗin kai, hawayen da suke cike taf da idanuwan shi na zubowa, wasu na biyo su kamar an buɗe fanfo, ba zai ce ga asalin abinda yake ji ba a yanzun. Basu zo a ‘yan biyu ba shi da Yasir, amma shaƙuwar da take tsakanin su zai iya zama hakan, ko bacci akan katifa ɗaya suke yi, ba zai iya cewa ga kayan shi gana Yasir ba, don duk wanda suka zo gaban shi sakawa yake tunda kusan girman su ɗaya lokacin.

“Ina ka je ka bar ni Yaya Yasir? Don Allah ina ka je ka barni? Yaya ya yarda ka mutu, ko da minti ɗaya ban taɓa yarda ba, wallahi suna addu’ar sadakar mutuwarka inayin ta Allah ya bayyanaka, saboda na san da ka mutu zan ji a jikina… Ko ya ne zan ji a zuciyata ka barni kaima…”

Ɗayan hannun shi kawai Yasir ya kai yana tallaban ɗayan gefen fuskar Tariq ɗin, saboda baida amsar tambayar shi, baisan ina ya je ba, yanzun komai ma yake dawo mishi, yanzun fitar ƙarshe da yayi daga cikin gidansu da niyyar samo musu abinda za su ci take dawo mishi, haka su Ummi, Amjad da Arfa, komai dawo mishi yake, ciwon da ya fita da shi a zuciyar shi na buɗewa daga inda ya ɓoye ya fito tare da samun wajen shi ya koma kamar bai taɓa rabuwa da shi ba. Da sauri Yasir ya sauke hannuwan shi daga fuskar Tariq yana juyawa ya kalli Ashfaq da yake girgiza mishi kai tun kafin ya fara magana.

Hakan bai sa Yasir fasa faɗin,

“Me kake a asibiti? Me ya sameka? Ina Arfa?”

Kai Ashfaq ya ci gaba da girgiza mishi, tambayar da baya so yai mishi kenan, duk lokacin da zai duba ƙofa a lokutan da yake tsammanin ganin dawowar Yasir ɗin, kalaman da zai yi amfani da su wajen mishi bayanin yadda akai ya bari abinda ya samu Arfa ya sameta yake nema.

“Yaya ina ƙanwata?”

Yasir yake faɗa duk da yana ganin amsar tambayar shi shimfiɗe a idanuwan Ashfaq ɗin, baisan hawaye sun tarar mishi ba saida ya ji zubar su kan kuncin shi, yana jin mutumin daya kira shi lokacin da yake gararambar neman ko da dako ne cikin kasuwa, yana kuma tuna yadda ya bi bayan mutumin har cikin motar shi ba tare da sanin me yasa yake binshi ba, da wata hoda da mutumin ya ɗauko yana fesa mishi da bai sake sanin inda kanshi yake ba.

“Sace ni a kai. Wani mutum na bi a motar shi, wallahi bansan ya akai na bishi ba. Dana dawo kuma ban tuna komai ba, bansan ya akai ban tuna ku ba. Ku yi haƙuri ban tuna ku ba… Ku yi haƙuri, ina take? Ku faɗa min inda take don Allah.”

Yasir yake roƙar su, bayan ya rasa Ummi a fuskar Arfa yake ganin giccinta lokaci zuwa lokaci, don daga ita sai Amjad ne suke kama da Ummi da har hakan, da suka rasa Amjad baya barin ta ɓace ma ganin shi, don tana ɗebe mishi kewar su, yana ganin in su duka ukunne kawai a duniyar shi komai zai dai-daita ko yaya ne, ko fitar da yayi saboda Arfa ne, in su za su jure yunwa don sun san rashi ita bata sani ba. Cikin wani sabon tashin hankalin yake kallon su.

“Shekara nawa na yi? Ta yi girma sosai ko? Don Allah ku ce min baku bari ta mantani ba. Tariq kai min magana… A fuskarta nake ganin Ummi, ka ce min bata mantani ba…”

Yasir ya ƙarasa yana daina tarbe hawayen da suke zubar mishi. Fuskar shi Tariq yasa cikin hannuwan shi wani gunjin kuka na ƙwace mishi da yake ji tun daga zuciyar shi, kafin ya ɗago a wahalce yana goge fuskar shi da faɗin,

“Abu mai muhimmanci yanzun shi ne ka dawo, kana nan kai, shi ne mai muhimmanci yanzun…”

Kai Yasir ya girgiza mishi, abu mai muhimmanci shi ne ya gansu, shi ne ya gane su, babban abu mai muhimmanci ya ga Arfa ita ma.

“Ta rasu… Kwana ɗaya da ɓatanka ta rasu.”

Ashfaq ya faɗi da wani irin nisantaccen yanayi a muryar shi, yana jin kamar Yasir ɗin da kuma kan shi yake faɗa ma mutuwar Arfa ɗin, don shima bai ji ta ba, yanzu ɗin ne yake jin wasu abubuwa na ɗagawa daga zuciyar shi. Kallon shi Yasir yake yana jin komai ya tsaya mishi cak. Idanuwan shi Ashfaq ya ɗago yana sauke su cikin na Yasir ɗin.

“Ta rasu…”

Ya faɗi yana jin zuciyar shi kamar zata rabe gida biyu, don ƙirjin shi kamar ana hura mishi wuta yake ji. Wani abu ne kamar yana zuba a zuciyar shi, sosai ya zauna akan tiles ɗin ɗakin yana ɗora kanshi kan ƙafar Yasir da yake zaune, abinda yai tunanin sun raba hanya da shi ne yake ji yanzun, kasa yarda yayi saida ya sa hannunshi ya taɓo idanuwan shi ya ji hawaye ne.

Kamar tabbaci yake jira wani irin gunjin kuka ya ƙwace mishi da yasa Yasir kai hannu yana taɓa shi, don yi yake kamar zai shiɗe musu, ko da Amjad ya rasu Yasir ba zai ce ya ganshi yayi kuka ko ɗaya ba, har tsoro abin ya dinga bashi kar ya samu matsala, baya jin da ya ɓata ma yayi kuka, ba kuma ya jin da Arfan ta rasu yayi kuka.

“Yayaa…”

Yasir ya kira muryarshi a dakushe da kukan da yake yi shi ma, amma Ashfaq din ya ƙi ɗagowa, kuka yake har numfashin shi na tsaitsayawa. Cike da tsoro Yasir ya sa hannuwan shi duka biyun yana ɗago da Ashfaq da ya ƙwace yana sake mayar da kanshi jikin ƙafafuwan Yasir ɗin, ko ina jikin shi ɓari yake, shi kanshi bai san ya zai iya tsayar da kukan ba, don baisan tun lokacin da yake riƙe da shi ba, yaune yake jin kamar an sauke mishi laifin ɓatan Yasir ɗin daga kanshi komai da yake riƙewa ya dawo mishi lokaci ɗaya.

“Ta rasu Yasir. Arfa ta rasu…”

Ashfaq yake faɗi yana ci gaba da wani irin kuka da Yasir ɗin yake ji har ƙasan zuciyar shi, don yana ganin yadda Ashfaq ke ɗora laifin mutuwarta akan shi.

“Na ji ka ai, lokacinta ne yayi. Lokacinta ne yayi Yayaa…”

Ɗagowa Ashfaq yayi yana girgiza mishi kai.

“Ni ne na bar su, da ban tafi nemanka ba da bata rasu ba, amma ya zan yi? Tariq ya ce ni ya kamata in tafi duk inda kake…”

Riƙo shi Yasir yayi yana kallon Tariq ɗin da yake kallonsu cike da ban haƙuri, maganganu na da tarin abin mamaki. Na kowa mallakin shi ne kawai kafin su ƙwace daga bakin shi, ya faɗi abinda ya faɗa saboda baisan ta ina zai fara neman Yasir ba, ya faɗi abinda ya faɗa saboda yana jin Yasir ya tafi da ɓangaren rayuwarshi da babu abinda zai taɓa mayewa. Ya faɗi abinda ya faɗa ne saboda Ashfaq ne kawai, baida wanda zai ɗora ma alhakin laifin da yake jin an mishi. Ƙasa ya sauko yana kama Ashfaq ɗin da ya riƙo hannun shi.

“Ya dawo Tariq, ka yi haƙuri na kasa nemo maka shi, don Allah ka yi haƙuri…”

Kuka Tariq yake yana girgiza mishi kai, shi kanshi Yasir ɗin kujerar da yake kai ya zame yana zama ƙasan, Ashfaq suka riƙe da yake kuka kamar ranshi zai fita, nasu ciwukan suka manta da su na wannan lokacin don Ashfaq ya fi su buƙatar lallashi, amma baya ma nuna alamar yana jinsu, kuka yake na abinda ya samu rayuwar shi, kukan rasuwar Amjad yake yi yau, rashin shi yake ji a duk wani lungu na zuciyar shi, kuka yake na rashin Arfa, kuka yake na tashin hankalin ɓatan Yasir ɗin da kuma tunanin da yayi na bazai sake ganin shi ba, kuka yake na abinda rubutun Alƙalamin Ƙaddara yai ma tashi rayuwar.

<< Alkalamin Kaddara 46Alkalamin Kaddara 48 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×