Skip to content
Part 52 of 52 in the Series Alkalamin Kaddara by Lubna Sufyan

Har wajen Nudra ɗin ya leƙa, ya manta ranar Islamiyya ce, bai sameta ba ma. Amma ba don ita kawai ya fito ba, yai ma Altaaf text yana so su haɗu, ya kuma tura mishi address ɗin gidan shi da su haɗu a can. Yanzun daya ƙaraso ya kira shi, ba yadda bai yi da ya shiga ba ya ƙi, yana jingine jikin motar shi a ƙofar gida har Altaaf ɗin ya fito. Zuwa yanzun ya fahimci abinda ya faru da Arfa na cikin ƙaddarar su gaba ɗaya, amma Altaaf ne sanadin faruwar komai. Har yanzun yana jin wani iri a zuciyar shi idan ya ganshi. Yafe mishi abu ne da yake jin zai faru wata rana, amma zai ɗauki lokacin da baisan iyakacin shi ba. 

“Ashfaq me yasa ba zaka shigo ba?”

Altaaf ya tambaya yana miƙa mishi hannu suka gaisa. 

“Mu yi magana a nan ɗin ma yayi…”

Ya amsa, jingina da jikin motar Altaaf ɗin yayi shima yana faɗin, 

“Ya su Tariq?”

“Suna gida. Ya iyali?”

Murmushi ne ya ƙwace ma Altaaf ɗin, watanni uku sun zo ma rayuwar shi da wani irin sauyi na ban mamaki, mutane kance yayi ƙiba, kuma yasan ba komai bane sai kwanciyar hankalin da ya samu, sam baya kwana da fargabar fitowar abinda ya binne, ga su Hussain da sukai wani irin shaƙuwa da su yanzun, yadda Majida take kula da yaran kawai ya ishe shi kwanciyar hankali. 

“Alhamdulillah…”

Ya amsa, godiyar na fitowa daga ƙasan zuciyar shi. Wayar shi Ashfaq ya zaro daga aljihun shi yana shiga manhajar bankin shi tukunna ya miƙa ma Altaaf ɗin da ya karɓa yana dubawa cike da rashin fahimta 

“Kuɗin da suka rage min kenan, ina son yin wani abu da su, bansan me zan yi ba, bansan wajen wa zanje ba shi yasa na zo wajen ka…” 

Ashfaq ya faɗi, sai yau tunanin ya zo wajen Altaaf ɗin ya shiga kanshi. Kallon wayar Altaaf yayi yana ɗagowa ya kalli Ashfaq ɗin, wani abu na mishi tsaye a zuciya 

“Ashfaq…”

Ya kira a hankali yana ɗorawa da, 

“Abinda ya kamata in maka kenan, tuntuni…abinda zan maka kenan, ko acan baya zan iya ba tare da taimakon Ammi ba…” 

Ɗan murmushi Ashfaq ɗin yayi mishi, shi kanshi yau da tunanin ya zo wajen Altaaf ɗin ya faɗo mishi sai da ya tuna baya, lokacin da duniyar ta haɗe mishi waje ɗaya, da yazo wajen Altaaf ɗin da neman taimako da abubuwa da yawa ba su faru ba. 

“Nima da na zo wajen ka, ƙila da na kauce ma faruwar abubuwa da dama…” 

Kai Altaaf ya girgiza mishi. 

“Nima ya kamata in yi wannan tunanin, me yasa ban yi tunanin nan ba?” 

Altaaf yake faɗi yana jin wani iri. 

“Alƙalamin Ƙaddara Altaaf. Komai a rubuce yake. Ba za mu canza abinda ya faru ba. Na zo yanzun, shi ne abu mai muhimmanci…” 

Kai Altaaf ya jinjina. 

“Babu matsala. Za kai abubuwa da dama da kuɗin nan. Ka zo gobe in Allah ya kai mu, zamu fara zuwa kasuwa tare…” 

Kai Ashfaq ya jinjina yana faɗin, 

“Bani kaɗai bane ba, su Yasir, sun yi girman da ya kamata suna da abinyi na kansu.” 

Numfashi Altaaf ya sauke.

“Yasir ya koma makaranta… Yasir ɗinka ku zo kasuwa da shi. Tariq shi dama yana zuwa makaranta ko?” 

Kai Ashfaq ya ɗan ɗaga ma Altaaf ɗin 

“Ya kusan gamawa ma, Yasir ne bansan ko zai so ya koma ba…ba mu yi maganar ba.” 

Ashfaq ya ce muryar shi na sauka ƙasa sosai. 

“Idan ba zai koma ba shikenan, amma kai mishi maganar dai. Tariq In sha Allah baida matsalar aiki idan ya gama. Da zarar na yi ma Ammi bayani shikenan. Amma ku ukun dai ku zo kasuwa gobe in shaa Allah…” 

Ajiyar zuciya Ashfaq ya sauke yana kallon Altaaf ɗin 

“Na gode… Na gode fiye da yadda zan iya faɗa maka.” 

Don ji yake komai zaiyi dai-dai, ba zai rasa kula da su Tariq ba, amma hakan zai yiwu ne da taimakon Altaaf ɗin. 

“Don Allah ka daina. Ni ba godiya nake so ba, abinda ya kamata mu yi ne mu duka tuntuni. Ka yafe min shi na fi buƙata, ka ce ka yafe min Ashfaq don Allah… Ka ji.” 

Altaaf ya ƙarasa muryar shi a karye. Ashfaq ya daɗe shiru kamar ba zai amsa ba kafin ya miƙa hannu ya karbi wayar shi daga hannun Altaaf ɗin yana faɗin, 

“Zan faɗa, ka yi haƙuri ba yanzun ba, a hankali Altaaf… Bazan iya ba yanzun, bana so in maka ƙarya.” 

Kai Altaaf ɗin ya jinjina, ya ji abinda yake so zuwa yanzun. Akwai yaƙinin Ashfaq ɗin zai yafe mishi, ya tabbatar mishi da hakan, zai jira duk lokacin da zai ɗauka in dai ya samu aron rayuwar yin hakan. Hannu kawai Ashfaq ya miƙa mishi suka sake gaisawa tukunna ya buɗe motar shi ya shiga, yana barin Altaaf tsaye a wajen da tunanin lokacin da rayuwa ta kawo su nan, amma waje ne da yake fatan tsayawa na lokaci mai yawa kafin ya canza.

******** 

Kasancewar Asabar ce, duk da ba aikin da ya shafi hutun mako Altaaf yake ba, bawai yana fita ko ina ba ne duk ranar Asabar da Lahadi, sai dole idan akwai wani abu da sai yana wajen zai yiwu. In ba haka ba zai ce shi yana hutun ƙarshen mako ne. Su Hussain na makarantar Islamiyya, shi ya kaisu da kanshi, kasancewar wuni za su yi sai yamma, Majida kuma ta tafi saloon itama, yasa shi fitowar shi. Gidan su ya fara biyawa, tunda ya shiga yai sallama yake jin gidan ya mishi shiru, waje ya samu ya zauna kan kujera yana faɗin, 

“Ammi!”

Shiru ya ziyarce shi, kafin ya ji takun tafiya, ɗan juyawa yayi yana ganin Barrah da fuskarta ta kumbura da alamun bacci ta tashi, muryarta a dakushe ta ce, 

“Haba mana Yaya, ka zo kana ta ihu, bacci fa nake…” 

Baki a buɗe Altaaf yake kallon ta. 

“Da ka yi sallama, ba saika shiga ciki ka duba ka ga ko tana nan ba, ya zaka tsaya a falon mutane kana ƙwala musu kira kamar sabon makaho.” 

Har lokacin kallon ta Altaaf yake, yana tunanin ranar da zata daina rashin kunyar nan. 

“Don Ubanki ni ne sabon makaho? Ni kike ma rashin kunyar nan haka?” 

Waje ta samu nesa da shi tana zama tare da turo laɓɓanta 

“Ka daina zagina Yaya, na girma fa.”

“Zaki rama ne don Ubanki?”

Altaaf ya faɗi yana tsare ta da idanuwan shi, yana tabbatar da ta ga shekarunta ba za su taɓa hana shi dukanta ba. Dariya ta yi. 

“Allah ya baka haƙuri, Ammin bata nan, ka bar mana gidan mu, inta dawo sai ka zo.” 

Hararar ta Altaaf yayi yana zaro wayar shi da ya ji alamun text ya shigo daga aljihu, kafin ya duba, Barrah ta tashi daga inda take ta koma kusa da shi. 

“Yaya banda kuɗi Allah… Ka ji.”

Tai maganar a shagwaɓe .

“Sai me ya faru?”

Sake shagwaɓe mishi fuska ta yi 

“Yaya mana…”

Harararta ya sake yi, baisan kalar kashe kuɗin da Barrah take ba, ko satin da ya wuce ya bata kuɗi, kuma ya tabbatar Ammi ma ta bata wasu. 

“Bazan bayar ba, bansan Uban me kike da kuɗi ba ma. Ki tambayi Aslam…” 

Ya ƙarasa yana buɗe saƙon da ya shigo wayarshi, ƙaramin tsaki na ƙwace mishi ganin ‘yan Glo ne sukai mishi text ɗin. 

“Haba mana, ya zan tambaye shi kuɗi yana hidimar aure saboda Allah? Ni tausayin shi nake ji wallahi.” 

Gira kawai Altaaf ya ɗaga sama yana kallon Barrah ɗin. 

“Ni dai in ba zaka bani ba ka faɗa min …”

“Tashi daga kusa da ni kafin in ci Uban ki wallahi…” 

Tsayawa ta yi tana kallon shi, ganin yana shirin motsawa yasa ta tashi da gudu, dai-dai shigowar Aslam da sallamar da kafin su amsa ya ɗora da, 

“Yaya mana, cin zali da ranar nan…ya zaka zo har cikin gidan su ka takura mata?” 

Kallon shi Altaaf yayi

“Ni ba gidan mu bane?”

Kai Aslam da Barrah suke girgiza mishi. 

“Kaima ka kusan barin gidan ai, kema don Ubanki auren za mu yi miki, ki tattara ki bar Ammi ta huta…” 

Turo mishi laɓɓa ta yi, tunda saurayin da yake zuwa wajenta ya je ya gaishe su sun ƙi barin ta huta da maganar auren nan, ita take so ta yi, amma ta ga kamar sun gaji da ita ne dama. Gefenta Aslam ya zauna, yana gaishe da Altaaf ɗin da ya amsa yana kallon Barrah da ko gaisuwar bai samu ba. Hakan yasa ta miƙewa. 

“Ni indomie zan dafa…”

Da sauri Altaaf ya ce, 

“Ina ci…in bai yi daɗi ba sai na ci Ubanki kuma.” 

Ƙarfin halin shi yasa ta yi dariya kawai tana wucewa ta nufi hanyar kitchen ɗin, hakan ya sa Altaaf mayar da gaba ɗaya hankalin shi akan Aslam, ba auren shi da yake matsowa bane damuwar Altaaf ko kuma yadda har a maganar auren babu shi a ciki, wata shida suka saka dama, yanzun kam abinda yai saura baima ƙarasa kai wata shidda ba. 

“Aslam me yasa za kai nisa har haka? Minna fa…” 

Altaaf ya faɗi da damuwa shimfiɗe a muryar shi, baya so Aslam ɗin yai nisa da gida haka, idan kuma yana buƙatar su fa? Ko wani abin da ba fata ake yi ba ya taso. In ma baya buƙatar su, su suna buƙatar shi a kusa. 

“Aikin da na nema can suka kaini Yaya.”

Aslam ya amsa da sanyin murya, wurare uku suka bashi zaɓi, Abuja, Katsina, sai Minna ɗin. Bai dai faɗa ma su Ammi an bashi zaɓi bane kawai, ya kuma zaɓi Minna, zai yi ƙarya idan ya ce ba zai yi kewar su ba, don ya ma fara yi tun yanzun. Ko Barrah da ya faɗa mata bata ce komai ba, shiru kawai ta yi, har yanzun kuma bata bari maganar ta sake haɗa su ba, Ammi ma banda 

‘Allah yasa alkhairi.’

Bata ce wani abu ba. 

“Idan saboda Ammi ne za kai nisa haka, ta karɓi auren ka da Nuwaira Wallahi, tuntuni ta karɓi auren, ba zata baku wata matsala ba.” 

Kai Aslam yake girgiza mishi da wani nauyi a ƙirjin shi. 

“Ba saboda Ammi bane…”

Ya furta a hankali. 

“To menene?”

Altaaf din ya faɗi. 

“Me zaisa kai nisa damu da yawa haka?”

Kallon shi Aslam yake, bazai iya faɗa mishi cewar shi ne dalilin da zai sa shi yin nisa da gida ba, Nuwaira ta roƙe shi da in zai iya ya ajiyeta inda ba zata dinga ganin Altaaf ba, shi ne kawai roƙon da tai mishi tunda ta amince ma auren shi, idan Altaaf ɗin barazana ne da kwanciyar hankalinta bai ga me yasa ba zai yi nesa da ita ba, kacokan auren ta da zai yi don ya sama mata nutsuwar da ta rasa ne. Amma hakan baya nufin baya jin ɗan uwan shi har ƙasan zuciyar shi. Ƙaddarar su shi da Nuwaira ba mai sauƙi ba ce, su dukkan su suna da muhimmanci a rayuwar shi, ba zai yi ƙarya ba Altaaf ɗin ya fita muhimmanci, don ita zai iya rabuwa da ita, amma ko zai sake jinin jikin shi gaba ɗaya ba zai taɓa canza cewar Altaaf ɗan uwan shi bane. 

“Yaya…”

Kawai ya iya faɗi, yana ganin Altaaf na kallon shi, kafin ya ɗan ware idanuwa, wani yanayi da Aslam baya so na dira kan fuskar Altaaf ɗin da yake sauke numfashi a hankali, ya fahimta yanzun, baisan ya aka yi ya kasa fahimta ba sai yanzun, yana dai mamakin ciwon da yake ji zuciyar shi na mishi da zai zama dalilin da Aslam ɗin zai yi nisa. Ko da ya zauna kusa da su ya ma kanshi alƙawarin zai yi duk iya ƙoƙarin shi na ganin bai nuna ma Nuwaira fuskar shi ba. Bai ma da ƙarfin gwiwar ko da neman gafararta ne, duk da zunuban laifin da yake mata da suke danne shi duk idan ya ga giccin su Hussain. 

“Ba zan so barazana da kwanciyar hankalin ku ba. Ka yi haƙuri za kai nisa da ‘yan uwanka saboda ni… Ka yi haƙuri Aslam…” 

Altaaf ya faɗi muryarshi na karyewa. Kai Aslam yake girgiza mishi yana kasa cewa komai saboda nauyin da ƙirjin shi yai mishi. Murmushin ƙarfin hali Altaaf ya ɗora kan fuskar shi. 

“Allah ya sa alkhairi, ya kuma nuna mana lokacin. Ango an sha ƙamshi…” 

Dariya Aslam yayi a kunyace, Barrah da ta shigo ɗakin da plate a hannun ta tana faɗin, 

“Dariyar me ake yi banda ni?”

“Gulmammiya… Ba’a sani ba.”

Altaaf ya faɗi, kan table ɗin ɗakin ta ajiye plate ɗin indomie ɗin da ƙamshin ta duk ya cika ɗakin, ta sha kayan haɗi ga ƙwai da ta soya kuma. Cokalin da ke ciki Altaaf ya miƙa hannu ya ɗauka, ba don yana jin cin indomie ɗin ba, ta fita ranshi da maganar da suka yi da Aslam, amma ba zai sa Aslam ya ji kamar bai kyauta mishi ba, bayan ba shi da laifin komai a duk abinda yake faruwa. Saboda haka zai danne tashi damuwar har sai ya fita daga gidan. 

“Yaya jira ake yi sai an ce ma mutum ga abinci, haka ne tarbiya me kyau.” 

Duka Altaaf ya kai mata a baya, yana sata matsawa babu shiri. 

“Kina so ki ce banda tarbiya me kyau kenan ko?”

Hararar shi Barrah take don sosai ta ji zafin dukan da yai mata. 

“Me nayi maka kawai za ka ci zalina?”

Cokalin ya sa yana naɗo indomie ɗin da shi yasa a bakin shi tukunna ya ce, 

“Ɗauko plate in zuba miki taki, ba zan ci da ke ba tunda baki da kunya.” 

Buɗe baki Barrah tayie. 

“In dafa abu kana cewa za ka ɗibar min?”

Cokalin Altaaf ya ajiye yana miƙewa, da gudu Barrah ta tashi 

“Ɗaukowa zan yi fa!”

Ta faɗi idanuwanta cike da hawaye, yadda a shekarunta Altaaf yake sata kuka na bata mamaki, zata fita waje Babbar yarinya da komai, amma minti goma da Altaaf idanuwan ta sun fara cika da hawaye, cin zalinta ne bata san ranar da zai bari ba. Ko da ta kawo plate ɗin ma, sai da Aslam yasa baki, ɗan kaɗan ya zuba mata yana gutsurar mata rabin wainar ƙwan guda ɗaya. Kuma bai ma cinye duka ba ya tashi ya fice, magana ya so ta yi ta bashi dalilin da zai ci zalinta, kuma ba zai faru ba, ko don shi ma auren zata yi ta je gidanta ta yi duk abinda take so ba tare da sa idon Altaaf ba. 

* * *** 

Tsaye yake jikin motar shi da yai parking a harabar gidan, ƙananun kaya ne kamar ko da yaushe a jikin shi, da rigar sanyi da aka fi kira da Hoodie, face cap saman kanshi sai kuma ya ɗora hular rigar da take jikin shi a saman face cap ɗin. Da wahalar gaske ka kalle shi baka sake kallon shi ba. Yaks duk da ya ji kamar muryar Altaaf ɗin ta waya bai yarda shi ɗin bane, sai dai babu wanda yake mishi wulaƙancin kiran shi da Yaya Yakubu sai Altaaf ɗin, har ƙannen shi kuwa sunsan baya so. 

Ya fito ne kawai, duk da bai ga fuskar shi ba, daga yanayin shigar shi yasan cewar Altaaf ɗin ne, wani murmushi ya ƙwace mishi yana takawa da sauri ya ƙarasa tare da kaima Altaaf ɗin wani duka da yasa shi matsawa yana faɗin, 

“Ouuchhhh… Ku karya ni, ku karya ni kawai kuyi ma matata asara…” 

Dariya Yaks yayi yana kai hannu ya dafe goshin shi kaɗan kafin ya sauke ya mayar da shi kan ƙugun shi yana sake saukewa yayi wata dariyar. 

“Ɗan banzan yaro kawai…”

Ya faɗi bakin shi ya ƙi rufuwa. Kai Altaaf yake ɗagawa yana dariya. 

“Nima nayi kewar ka.”

Hararar shi Yaks yayi duk da ya kasa daina fara’a, ba kaɗan yai kewar Altaaf ɗin ba a tsawon shekarun nan. Da wani yanayi a fuskar Altaaf ɗin ya ce, 

“Kayi haƙuri ya ɗauke ni tsawon shekarun nan.” 

Kai Yaks ya jinjina.

“Sai ka ci ubanka ai, idan kuna samun matsala da Wadata kana haɗawa da mu. Jamaal zai kashe ka A-Tafida…” 

Daƙuna mishi fuska yayi. 

“Altaaf… Altaaf Isma’il Tafida. Ina da iyali Yaks.” 

Dariya Yaks ɗin yayi yana ganin wani irin canji na nutsuwa tare da Altaaf ɗin. Kafin Altaaf ɗin ya kalle shi yana faɗin, 

“Goodness me ya same ka haka? Ka tsufa Allah.” 

Wani dukan Yaks ya sake kai mishi yana kaucewa. 

“Ba zaka canza ba ko Altaaf?”

Ɗan ɗaga kafaɗa Altaaf ɗin yayi yana shagwaɓe fuska. 

“Ba laifina bane da nake da kyau har haka.”

Dariya kawai Yaks yayi suna ƙara gaisawa. Sosai Altaaf yake mamakin jin matan Yaks ɗin har biyu. Shi kam ba zai iya hango rayuwar shi da mata biyu ba, ba shi da ƙarfin zuciyar yi musu adalci. Musamman yanzun da ya tabbatar da gaske ya gama zubar da yaran shi a titi, su Hussain ne kawai rabon da ya samu, Majida ta ishe shi, tunda ta haƙura take zaune da shi da ƙaddarar shi, take riƙe da yaran shi kamar sun fito daga jikinta. Baya neman wani abu daga wajen kowace mace kuma. Har cikin gida suka shiga ya gaisa da matan Yaks ɗin, bai ga yaran shi duka huɗun ba, ɗaya kawai ya gani, ‘yar ƙaramar ‘yarshi ɗin, bacci take don ba yadda ba su yi ba ya ɗauke ta ya girgiza kai yana faɗin, 

“Ku barta ta yi baccin ta.”

Dariya Yaks yayi kawai ya sa hannu ya ɗauki yarinyar da suka kira da Anisa ya miƙa ma Altaaf ɗin da ya ware mishi idanuwa yana tallabeta da duka hannuwan shi. Kallon ta yake, kamar ta ji hakan kuwa ta buɗe ido. 

“Ka gani ko Yaks… Ta tashi wallahi…Innalillahi ta tashi fa…” 

Altaaf yake maganar a razane yana saka su Yaks ɗin dariya. 

“Don Allah ku karɓeta kar ta yi kuka.”

Ya sake faɗi. 

“Ba ta da rigima…”

Yaks ya amsa shi, riƙe yake da yarinyar yana jin yadda ƙaryar da yake gaya ma kan shi ta cewa iya su Hussain sun ishe shi rayuwar duniya na rugujewa. Har yanzun yana son ƙara samun wasu yaran, bai ƙi ko guda nawa bane ba, motsi yarinyar ta yi tana kai hannunta kan fuskar shi. Zuciyar shi ya ji kamar tana narkewa da son riƙe ƙaramin yaro kamar ta, sosai yake jin son yara na sake shigar shi. Wataƙila hukuncin shi kenan, Allah ya ɗora mishi azabar son yara saboda wanda ya zubar a waje. Ɗaga fuska yayi yana kallon Yaks ɗin 

“Kamar ku bani ita…”

Dariya Yaks yayi, yadda Altaaf ɗin yai magana a taɓare yana saka shi sauke numfashi. Baya kuma tunanin rayuwa zata taɓa sawa Altaaf ya canza. Akwai yarintar da zata kasance da Altaaf ɗin har ƙarshen rayuwar shi. Ya jima a gidan saboda bayason basu Anisa. Kafin har ƙofa Yaks ya raka shi. Daga nan gidan Jamaal ya wuce don suma duk anan garin Kano ɗin suke aiki kuma suke zaune da iyalan su. Yayi mamakin ganin yaran Jamaal ɗin biyu kawai, dukkan su mata. Da yana nufar gida ne yake jin rayuwar ta mishi dai-dai yanzun. 

Hannun shi akan ciki ya shiga gida yana kiran, 

“Majee…”

Fitowa ta yi daga kitchen da shigar kayan Pakistan a jikin ta. 

“Yunwa nake ji fa. Cikina ba komai, babu abinda na ci tunda na fita.” 

Kallon shi tayi.

“Yoo su Jamaal ɗin basu baka abinci ba?”

Kai ya ɗaga mata yana shagwaɓe fuska 

“Sun ce in tsaya in ci, ni ne dai na ƙi.”

“Ni kau ban gama ba, Tea na sha. Yanzun ma na ɗora shinkahwa…ka shigo man gida ba ko sallama.” 

Hannu shi ya miƙa yana mata alamar da ta je , ganin ta yi tsaye tana kallon shi yasa shi faɗin, 

“Zo…”

Kai ta girgiza tana murmushi

“Sanwa hwa nike.”

Haɗe fuska yayi yana sake faɗin, 

“Zo…”

A hankali take takawa tana shagwaɓe mishi tata fuskar  

“Allah nama nike soyawa…”

Kai Altaaf yake girgiza mata yana ci gaba da yi mata alama da ta je, ganin saurin ta baya mishi yasa shi ƙarasawa yana riƙo hannun ta. Dariya take tana ƙoƙarin ƙwacewa, 

“Sakar man hannu ka ji…tsaya in zubo maka to.” 

Kai Altaaf yake girgiza mata.

“Na fasa ci…ai na zama abokin wasan ki.”

Kai take girgiza mishi ganin yana janta jikin shi sosai, juyata yayi yana rungumeta ta baya tare da ɗora kanshi a kafaɗarta. Numfashi ya sauke yana lumshe idanuwan shi 

“Yaks yana da ‘yar baby. Anisa…”

Hannuwanta Majida ta ɗora kan nashi, tana kula da shi har yanzun, da yadda son samun wasu yaran yake cin shi, zata yi ƙarya idan ta ce itama bata so. Amma tasan haihuwa kyautar Allah ce, idan Ya so zai basu suma. 

“Majee ba kya son samun naki yaran?”

Muryarta can ƙasa ta ce, 

“Ina da yara…”

Sake matse ta yayi a jikin shi. 

“Kinsan me nake nufi fa. Bazan iya rabuwa dake ba, duk da Ina jin muna raba ƙaddarata ne a tare, ina son kaina da yawa Majee, ina sonki a kusa da ni…” 

Hannun shi ta murza da yake zagaye jikin ƙugunta tana faɗin, 

“Babu ƙaddarar da muke rabawa hwa, ka daina hiɗin haka don Allah. Haihuwa kyauta ce, idan Allah ya so zai bamu. Idan alkhairi ce ina fatan mu samu, idan ba alkhairi bace Allah ya raya mana su Hussain cikin aminci…” 

Sumbatar gefen fuskarta yayi. Soyayyarta na cika mishi zuciya fal. Basu zo inda suke yanzun cikin sauƙi ba, sai dai yana fatan su wuce sauran shafukan da Alƙalamin Ƙaddara ya rubuta musu.

* * *** 

ABUJA

Saukowa yake daga benen da sauri, hannun shi riƙe da hula ruwan ƙasa mai haske, yanayin shaddar da ke jikin shi. 

“Aroob…”

Ya ke kira, kwanan shi biyu da dawowa kenan, da ƙyar ya sha kansu suka daina mishi fushi, sai da ya haɗa da zare ido da hargagi kafin suka sauko. Isah ya ce mishi mukullan motar shi na hannunta, sauri yake fita za su yi, ya kuma yi mata magana ta ɗauko mishi. 

“Aroob mana!”

Ya sake kira, yana mayar da hankalin shi kan ƙofar jin an yi sallama cikin wani irin sanyin murya. Zuciyar shi ya ji ta yi wani irin tsalle cikin ƙirjin shi ganin Huda, tsaye suka yi a bakin ƙofar ita da wani matashin saurayi da yake kyautata zaton sunan shi Zaid, din Maman su ta faɗa mishi tana da wasu yaran guda biyu. Macen zata kai Aroob, namijin ne baya jin zai ƙarasa shekarun Fawzan. Yasan dole wata rana za su haɗu, dole zai fuskance su, bai ɗauka ranar zata zo da wuri ba. Yafindo kanta yasan dole ne zai nemeta, ko baya so dole zai nemeta, ba yanzun ba kam, amma wata rana yana fatan ya tashi da safe ya ji ya yafe mata, ya tashi da safe ya ji ƙirjin shi babu nauyin tabon da tai mishi. 

Kallon su yake, musamman macen da yake ganin yanayin fuskar shi sosai a tata. A daburce ta ce mishi. 

“Ina….Ina kwana…”

Kai ya iya ɗaga mata. Kallon su kawai yake yi yana jin wani irin yanayi a ƙasan zuciyar shi. A ɗan tsorace namijin ya ce, 

“Za mu fahimta in baka son magana da mu. Yafindo bata ma san za mu zo ba… Mun kasa haƙuri ne…” 

Hannun shi Huda ta kama tana faɗin, 

“Hamma…”

Juyawa yayi ya kalleta, kai ta girgiza mishi alamar ya bari, tukunna ta kalli Rafiq ɗin. 

“Zamu tafi… In kana son magana damu ga inda muke…” 

Tayi maganar tana janyo jakar da ke rataye a kafaɗarta ta sa hannu a ciki, ɗan kati ta fiddo, a hankali ta tako inda Rafiq ɗin yake ta miƙa mishi. 

“Kar laifin Yafindo ya shafe mu. Don Allah…muna son kasancewa a rayuwar ka ko yaya ne in babu matsala…” 

Ta ƙarasa muryarta na karyewa, hannu Rafiq ya miƙa ya karɓi katin yana dumtsewa a hannun shi. Juyawa ya kamata su yi ta sani, amma ta kasa ko motsa ƙafafuwan ta, amsa take jira ya basu, tunda Yafindo ta basu labari suke son su yi magana da shi, ita ta hana su zuwa, don su barta ta huta ne ta basu address ɗin gidan su Rafiq ɗin da sharaɗin ba za su je ba. Ita ta san shi, ƙila shi yasa take jin kusanci da shi fiye da Zaid ɗin, duk da shima yana so ya ganshi. 

Kallon su kawai Rafiq yake, baida amsar basu, yanzun yake ƙoƙarin nutsar da hargitsin da yake cikin rayuwar shi, ba zai janyosu ciki ba sai yana da tabbacin akwai space ɗin da zai iya basu, ba zai kuma ɗaga musu buri ba sai ya tabbatar zai iya zama Yayansu. Baisan Aroob ta fito ba saida ya ji an riƙe hannun shi. Ɗan juyawa yayi ya ga ita ce, amma idanuwanta na tsaye kan Huda ne, kallon yarinyar take tana tunanin abinda suke yi a cikin gidan su. 

Yadda Huda ta yi kama da Rafiq ɗin na mata wani iri. Muryarta a shagwaɓe ta ce, 

“Me sukeyi anan Yaya?”

Tana ƙara matsawa ta riƙe Rafiq ɗin sosai, kamar tana so ta shiga tsakanin shi da su Huda, zata basu mamaki idan suna tunanin za su ƙwace musu Rafiq ne. Abu ne da ba zai yiwu ba. Muryar Rafiq ɗin can ƙasa ya ce, 

“Manners Aroob…”

Turo laɓɓanta ta yi tana zabga ma Huda da tai mata murmushi harara. Murmushin Huda ta sake yi, ba sai Aroob ta riƙe Rafiq haka bane zata san Yayanta ne, tasan hakan tun kafin ta zo, ita ba wai tana son samun space a rayuwar Rafiq ɗin mai girman na Aroob ba, ko ya ta samu zai mata, itama tana da nata Yayan. 

“Huda mu je…”

Zaid ya faɗi yana da na sanin zuwan da suka yi, a idanuwan Yafindo yake ganin yadda samun space ɗinsu a rayuwar Rafiq yake da muhimmanci mai yawa a wajenta. A watannin nan yana kula da ita, ranaku kaɗan ne bata kuka, ga wata irin ramewa da ta yi da baya so. Shi yasa ma ya biyo Huda suka zo, yana ji idan ya samu kusanci da Rafiq ko yaya ne zai samu damar da zai roƙe shi ya yafe ma Yafindo ɗin, ƙaddararta ce ta zo da hakan, ya fahimta ya yafe mata. 

Rafiq Huda ta sake kallo tukunna ta juya, ita da Zaid ɗin suka fice daga ɗakin, Rafiq baisan ya motsa ba sai da ya ji Aroob ta riƙo hannun shi. 

“Ina za ka je Yaya? Kabar su mana, su yi ta tafiya. Ko ka kirasu ne dama?” 

Hannun shi Rafiq ya zame daga na Aroob ɗin yana bin bayan su Huda da sauri. Gabansu ya sha yana sauke numfashi tukunna ya ce, 

“Bansan me kuke so da ni ba…”

Ɗan ɗaga kafaɗa Huda ta yi tana amsa shi da 

“Zumunci…”

Ya ji nata, don haka ya kalli Zaid da yake girgiza mishi kai. 

“Ban sani ba, wallahi bansan me nake so da kai ba. Ina jin kusanci da kai kamar na sanka tuntuni, amma bansan me nake so da kai ba. Ka zama ɗan uwan mu? Mu duka kamar bamu da wannan zaɓin tunda jini ya haɗa mu. 

Amma kai kana da zaɓin bamu waje a rayuwar ka idan kana so… Na so in jira in samu kusanci da kai kafin in roƙe ka, amma na gaji da ganin damuwar da ke cikin idanuwan Yafindo am, na gaji da ganin kukan da take a kowace rana…” 

Wani abu da yai ma Zaid tsaye a wuya ya haɗiye yana ci gaba da faɗin, 

“Ko baka yafe mata yanzun ba, ka bata hope cewar zai faru wata rana… Zata jira, na san zata jira, amma kuma zata samu nutsuwar sanin za ka yafe mata ɗin. Bansan me kake gayama kanka a kanta ba. Amman ba za ka iya tsanarta ba, ko yaya ne akwai wani abu a tare da kai da yake doka mata, ka kwanta a cikin ta, dole akwai wani abu…kusancin nan ba abu ba ne mai sauƙin ɓacewa…” 

Numfashi Rafiq ya ja mai nauyi yana saukewa, maganganun Zaid ɗin na taɓa shi fiye da yadda yake tunani. 

“Kayi magana da ita, don girman Allah ka fahimci babu yadda za mu yi mu guje ma abinda Alƙalamin Ƙaddara ya rubuta mana. Kama yadda Huda ta ce, in zamu yi zumunci da kai ko yaya ne zai mana daɗi…” 

Ya ƙarasa maganar yana kama hannun Huda suka ƙarasa inda suka ajiye motar su, Rafiq na kallon su har suka shiga motar suka juyar da ita, aka buɗe musu gate suka fice, sai da ya ga an mayar da gate ɗin an rufe tukunna ya iya takawa ya koma cikin gida. Aroob ya samu tsaye tana kallon shi kamar ya mata wani abu. Numfashi ya sauke a gajiye ya ce, 

“Ba za su taɓa zama kamar ku ba, ba ni da wasu ‘yan uwan da suka wuce ku Aroob, don Allah karki min rigimar nan.” 

Idanuwanta cike taf da hawaye take kallon shi. 

“Sun haɗa jini dakai Yaya, ya zamu fara haɗa kanmu da hakan?” 

Takawa yayi ya ƙarasa inda take tsaye, hannunta ya kama yana ɗagawa ya ɗora a inda zuciyar shi take. 

“Ba za su haɗa kansu da inda kuke a nan ba Aroob… Ki ce min duk sa’adda zan gansu ba sai na sake miki bayanin matsayin ku ba, don Allah…” 

Kai ta ɗaga mishi a hankali, in dai ba zasu ƙwace musu shi ba, bata da matsala da su. Numfashi Rafiq ya sauke yana jinjina mata kai. 

“Good… Ina mukullin motata?”

Ya ƙarasa yana sakin hannun ta, ɗayan hannun ta ɗago tana miƙa mishi mukullan motar. Komawa yayi yana nufar hanyar ƙofa ya koma, har wajen motar shi ya ƙarasa ya miƙa ma Isah mukullin. Ko da yai tafiyar nan sai da ya sake ganin wani likitan ƙwaƙwalwar kan matsalar shi, kamar yadda aka faɗa a India nan ɗin ma haka suka faɗa mishi, memories ɗin shi zasu iya dawowa gaba ɗaya, za su kuma iya dawowa ba gaba ɗaya ba, zai kuma iya yiwuwa ya rasa su kenan har abada. PTSD ɗin da yake tare dashi ne kawai suka bashi tabbacin komin tsawon lokaci zai iya rabuwa da shi gaba ɗaya. Kar dai ya yi gaggawa, zai iya samun matsala Babba in yayi haka. Rashin tuƙin nashi bai dame shi ba, duk inda yake so za a kaishi. Yana son ya tuna matar shi da yarinyar shi ne wata rana, duk da hotunan su da suke cike da wayar shi yanzun, amma yana so ya tuna kalar rayuwar da yayi da su . Yana fatan faruwar hakan wata rana. 

Mota Isah ya buɗe mishi don ya shiga, hango shigowar motar Muneeb da yayi yasa wani murmushi ƙwace mishi. Da kanshi kafin ya tafi ya je ya faɗa ma Muneeb ɗin mutuwar auren Zafira, son da yake mata sai da ya ba Rafiq ɗin mamaki, don sosai ya nuna girgizuwar shi da mutuwar auren nata, duk da hakan dama ce ya samu da zai iya auren ta, sosai ya nuna rashin jin daɗin shi, har sai da Rafiq ya gaya mishi dalili. Miƙewa yayi yana rokon Rafiq da ya kai shi wajen Omeed ɗin. Dariya Rafiq yai mishi a lokacin, har yanzun in ya tuna girman Omeed da na Muneeb, da yadda Muneeb yake faɗin in zai ga Omeed sai ya ramawa Zafira dukan da yai mata sai abin ya bashi dariya. Zai iya rantsewa Muneeb yana ƙirga kwanakin da Zafira zata fita iddarta. Tunda da ya dawo yake ganin yana zarya gidan. 

Ƙarasawa yayi don su gaisa da Muneeb ɗin, har ƙasan zuciyar shi yana samun nutsuwa, tunda har Daddy yayi ma magana kuma ya tabbatar mishi babu wata matsala, sai dai ba zai yarda da auren ba sai yaji daga bakin Zafira cewar Muneeb ɗin ne zaɓinta. Hannu ya miƙa mishi suka gaisa. 

“Baka da aiki ne?”

Rafiq ya buƙata. 

“Malam yau Asabar, in ma ina da aikin me yasa kake tambaya?” 

Ware idanuwa Rafiq yayi yana faɗin, 

“Allah ya baka haƙuri, zaka balbaleni ni kam. Zan wuce ne ina da hidima da yawa…” 

Sake gaisawa suka yi Rafiq ɗin har ya juya, ya dawo yana faɗin, 

“Muneeb…”

Kai Muneeb ya ɗago yana kallon Rafiq ɗin da ya ce, 

“Kayan gidan yari ba zasu min kyau ba na sani, amma zan kasheka idan kai mata wani abu…” 

Dariya Muneeb ya kwashe da ita yana sa Rafiq daƙuna fuska. 

“Ban baka tsoro ba kenan ko?”

Hannu Muneeb ya ɗaga mishi, har lokacin yana dariya. 

“Don Allah jeka… Ka tafi inda zaka kawai.”

Dariya Rafiq ɗin yayi, kafin muryarshi can ƙasa ya ce, 

“Amanar ƙanwata Muneeb, don girman Allah karka bamu dalilin da za mu yi dana sani.” 

Kai Muneeb ya jinjina. 

“Bazan maka alƙawarin bata farin ciki duk rana ba, amma zan maka alƙawarin yin iya ƙoƙarina wajen zama da ita yadda addini ya tsara. In sha Allah ba za ku yi dana sani ba.” 

Numfashi Rafiq ya sauke yana jinjina kan shi kafin ya juya yana ƙarasawa wajen motar shi. Shiga yayi, Isah ya zagaya shima ya shiga, saida suka fita daga gidan tukunna ya duba ɗan katin da yake hannun shi, address ne, daga baya kuma lambobin waya guda biyu. Address ɗin ya kira ma Isah da cewar nan za su fara biyawa. Kafin ya gyara zaman shi sosai cikin motar yana lumshe idanuwan shi. Ya daina guje ma ƙaddarar shi, zai fuskance ta da wuyan shi a dage, sanin ba zai taɓa wuce rubutun da Alƙalamin ƙaddarar shi yai mishi ba. 

*******

Amma kamar ya ba hawayen ta damar ci gaba da zubowa ne, kuka take da ta jima tana riƙewa cikin zuciyarta don bata taɓa tunanin zai dawo ba. 

“Neem na ce ki jira ni, na faɗa miki, me yasa kike min kuka kamar kin yi zaton ba zan dawo ba?” 

Rafiq yai maganar muryar shi na karyewa, confusion yake gani cikin idanuwanta yana jin wani irin yanayi mai wahalar fassaruwa. 

“Na faɗa miki a cikin takardar dana baki, baki duba ba?” 

Kanta da ke cikin hannuwan shi ta girgiza mishi, wasu hawayen masu ɗumi na zubo mata. 

“Na… Nasan ka sake ni, bana so in gani a rubuce…” 

Take faɗi tana kokawa da numfashin ta. Cikin tashin hankali Rafiq yake kallonta, baisan ya akai wannan tunanin ya zo kanta ba, ko don yana kallon yadda su Nuri suke binshi da ido akan maganarta, suma ɗin sun ɗauka sakin ta yayi kenan, shi bai sake ta ba, baisan ta yaya zai fara sakinta ba, ya sa an dawo da itane don ya samu nutsuwar hargitsin da yake cikin rayuwar shi, don in yana ganinta kullum ba zai tuna duk wani dalili da yasa ya sota ba, yafe mata zai mishi wahala in yana ganin ta. 

“Oh Allah na…”

Ya faɗi yana tsintar kanshi da sumbatar ta, tukunna ya kalli fuskarta yana janta jikin shi, gam ya rungumeta, cikin kunnenta yake faɗin, 

“Me ya kawo miki wannan tunanin? Na yi nisa da ke ne don in tuna dalilin da yasa na soki, don in samu zuciyar yafe miki, babu abinda ya samu igiyar auren mu… Babu abinda ya sameta, na ce ki jirani ne…” 

Wani kukan ta ji ya ƙwace mata, kafin ta zame jikinta daga riƙon da Rafiq ɗin yai mata tana kai mishi dukan da bai isa da ƙarfin da take so ba. 

“Me yasa? Me yasa za ka ce in jira ka a takarda? Meyasa baka faɗa min da bakin ka ba?” 

Take duk maganar tana kai ma duk inda ta samu a jikin shi duka tana wani irin kuka da yake ji har ƙasan zuciyar shi. 

“Neem…Neem… Neem!’

Rafiq ya ke kira yana so ta nutsu amma ta ƙi, hakan yasa shi kama hannuwan ta yana riƙewa, kuka take har numfashinta na tsaitsayawa. 

“Don Allah ki yi haƙuri… Ki yi haƙuri.”

Yake faɗi, kuka take har lokacin. 

“Kasan me yake riƙe da zuciyata bata tarwatse ba? Yaron da ke cikina! Saboda ka gama ruguzamin komai, na maka laifi na sani, wallahi na sani, amma da ka faɗa min da bakinka in jira ka baka bani takarda ba, me yasa za kai mun wannan horon?” 

Sosai ya sa ƙarfi yana riƙe hannuwanta da take kiciniyar ƙwacewa. 

“Tasneem!”

Ya kira cikin yanayin da yasa ta 

nutsuwa tana kallon shi, ajiyar zuciya take saukewa, hawayenta na zuba. 

“Saboda bazan iya ba! Bakina ba zai iya furta kalaman ba a lokacin, shi yasa na rubuta miki, saboda bansan iya lokacin da zan ɗauka ba… Ba lallai ki fahimta ba… Kiyi haƙuri don Allah… Kiyie haƙuri.” 

Ya ƙarasa maganar yana ranƙwafowa ya haɗa goshin shi da nata, kafin a hankali ya saki hannayenta da yake riƙe da su, tana jin hucin saukar numfashin shi akan fuskarta. 

“Idan zaki iya zama da marar asali zuwa nai mu koma Neem…” 

Cikin tashin hankali take kallon shi, sai dai idanuwan shi a lumshe suke, wannan karin numfashinta ne yake fita da sauri-sauri. 

“Ba su Nuri suka haife ni ba…”

Wannan karon yamutsin da ta ji cikinta yayi yasa ta kamo hannun shi tana haɗawa da nata ta ɗora kan cikin, bata tunanin ta fahimci maganganun shi, amma yanayin ciwon da take gani kan fuskarshi yasa takai hannu tana shafar fuskar shi, ya kuwa buɗe mata idanuwan shi da duk wani abu da zuciyar shi take ciki. 

“Bansan ko na fahimci abinda kake son ce min ba, ina son ka, shi ne kawai abinda na sani, in za ka iya samun wajen yafe min a zuciyarka zan zauna da kai.” 

Numfashi Rafiq ya sauke yana mayar da idanuwan shi ya lumshe, har lokacin goshin shi na haɗe da nata, wani irin ajiyar zuciya mai nauyi ya sauke, ya ɗaga hannuwan shi ya ɗora kan kafaɗarta, yana jin nata hannuwan na sauka kan nashi, numfashin da ta sauke kan tashi fuskar ya shaƙa, yana jin yadda wani abu yake haɗewa a zuciyar shi da baisan ya buɗe ba, tare da ita sauran abinda yake nema rayuwar shi ta dai-daita yake samuwa, rayuwa ta gwada su ta fannin da bai taɓa tunani ba, Alƙalamin Ƙaddara ya kai rubutunsu ƙarshen shafin da yai tunanin zai ƙarashe da su a ƙasa warwas, sai kawai ya gansu a wani sabon shafin mai cike da tarin abin al’ajabi. Kamar yadda ba shi da tabbas akan abinda wani shafin zai sake buɗe musu, haka ba shi da tabbas za su ɗore a wannan shafin ma, yana da yaƙinin tare da ita ko wanne shafi zai yi sauƙin karantuwa. Ba’a nan farkon labarin su ya fara ba, ba zai kuma ƙare a nan ba.

DUKKAN GODIYA TA TABBATA GA ALLAH MAI IKO AKAN KOWA DA KOMAI. 

Godiya mai tarin yawa ga ɗaukacin mutanen da suka bini a tafiyar nan. Godiya mai yawa ga mutanen da suka tabbatar tafiyar ta faru.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 4.6 / 5. Rating: 9

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Alkalamin Kaddara 51

2 thoughts on “Alkalamin Kaddara 52”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×