Shuru yayi zuciyarsa cike fal da tunani ya rasa meyasa ko yaushe abokinsa baya taɓa gane farsafarsa, shine ya kamata ace ya fi kowa fuskanta ta a rayuwa amma kash ya gagara gane ɗabiata tun ta yarinta, Faruq kawai da Daddy ke yadda da lissafina amma Banda Haidar, ina bazan taɓa yadda na zuba idanu ina gani a cutar da rayuwar Idi ba, dole na fitar dashi daga wannan zargin, numfashi ya sauƙe tare da daga wayarsa numbern Daddy ya kira kusan 3miss call kafin Daddy ya ɗaga Al’ameen murmushi ya ɗan saki tare da cewa.
“Barka Daddy, Daddy ka manta dani baka kirana sai kwana biyu saboda yanzu ka samu Faruq ko.”?
Murmushi Daddy yayi yana zama kusa da Faruq yace.
“Kashe wayar bara na kiraka video Call.”
Katse wayar Al’ameen yayi yana murmushi system ɗinsa ya jawo tare da buɗe data, yana buɗewa kiran Daddy na shigowa, amsa yayi, fuskar Faruq ya fara gani yana murmushi daga can Daddy ya sako kai tare da cewa.
“Ya akayi zakina, da alamu dai yau da ƙorafi ka tashi.”
Ɗan dariya yayi yana kallon Faruq yace.
“Daddy ya naga wancan yaro ya ƙara haske ne harda wani ƙiba.”
Daga Daddy har Faruq dariya sukayi Faruq yace.
“Kaji ɗan rainin wayo kaji Daddy wai tambaya yake nayi ƙiba, to an faɗa maka zama kusa da Uba wasa ne, kaga ko missing ɗin ku banayi saboda Daddy ya ɗebe min duk wani kewa.”
Dariya sosai Al’ameen yayi tare da cewa.
“Ƙarya kake yaro kace baka kewar mu, kai Hausa fa na maka ina nufin ka rame ne.”
Yayi Maganar cike da zolaya Daddy ne yace.
“Kunga wannan shirmen naku bazai ƙare ba, bara dai nayi Magana na wuce na barku, Zakina kana lafiya dai ko.?”
“Daddy ina lafiya, sai dai kuma akwai matsala wanda nasan kaine kawai zaka fahimce ni Daddy.”
Gyara zamansa Daddy yayi tare da cewa.
“Ina sauraronka yarona meke faruwa.”?
“Daddy akan wannan kisan ne dai na Khairi, kowa yayi shuru akan Idi drever babu wanda yayi tunani a kansa, sannan har zuwa yanzu police suna nan suna masa azaba, kuma har yanzu babu wata shaida da ta nuna cewa yana da hanu ciki, Daddy kai kanka kasan Idi bazai kashe wani daga cikin Ahalin mu ba, da kuwa daya juma dayi, Daddy na tsaya nayi tunani gami da lissafi babu hanunsa a cikin wannan kisan amma Haidar da Papa sun kasa fahimta, Daddy kaine kake da damar da zaka iya sakawa a saki Idi ka duba wannan maganar da idanun basira Daddy so nake a saki Idi.”
Murmushi Daddy ya saki tare cewa.
“Dama wannan kake kira da matsala Zakina, ni kuwa me zaka nema a wajena na kasa maka, nifa na juma da yadda da tunaninka zaki na domin kuwa ko wacce irin magana ta fito daga bakin ka, takan iya zama gaskiya, duk shawarar daka bani takan mini amfani haka kuma idan ka faɗi Magana akan abu shima ƙarshe sai ya zamo gaskiya, ni kaina koda akace min an kama Idi ana zarginsa zuciyata bata amince da hakan ba, sai dai kasan sha’ani na rayuwa da mutum komai yana iya sauyawa mutum ya juye daga yadda ka sanshi, zanyi Magana da Dpo insha Allah za’a sakesa amma a bisa sharaɗin za’a cigaba da bincike akansa.”
“Hakan ma yayi min Daddy, domin ina yiwa Idi kallon ubane ba mai gadi ba, zuwa yanzu yaci ace yabar tuƙi domin kuwa tsufa ya fara cimmasa, ƙarfinsa ƙarewa yake shiyasa na yanke shawarar zan basa aiki a Companyn mu, a matsayin shugaban clener na Companyn hakan zaifi masa tuƙin, amma ya ka gani Daddy.”
Murmushi Daddy yayi tare da cewa.
“Duk abinda ka yanke dai-dai ne, domin kuwa wannan abu mai kyau ne zakayi, Allah ya maka albarka ka kula da kanka ni zan wuce Office.”
Murmushi Al’ameen yayi yace.
“Na gode Daddy fatan alheri.”
Murmushi Daddy yayi tare da barin wajen Faruq ne yace.
“Abokina, wai da gaske ne kam Haidar ya samu matar Aure.”
Haɗa fuska Al’ameen yayi tare da jan tsuka yace.
“Mtsss! Zancen banza shiɗin ne ya faɗa maka haka.”?
“Waye kuwa zai faɗa min idan ba shiba yace min kyakkyawa ce, wai da harma zaije gidan su, akayi wannan mutuwar amma dai yace yau insha Allah zaije, kaga nima fa ina dawowa zan nemi matar nan, gara kaima ka fara nema tun yanzu kawai a haɗa gaba ɗaya lokaci guda asha biki.”
Dariya ce ta kwacewa Al’ameen tare da cewa.
“Marassa aikin yi, ku damuwar ku kenan mace mace, to ni dai wannan shiriritar baza kuyi dani ba, ban tashi ɗaukawa kaina kayan da zai dameni ba, bance bazanyi Aure ba, amma dai a yanzu nafi jin daɗin rayuwata a haka koda zanyi Aure sai na tantance wacce ta dace da zama Abokiyar rayuwata wanda bazata zamo min matsala ba a rayuwata, bazata dameni ba haka nima bazan dameta ba, mai cikakkiyar nutsuwa mai addini ƴar babban gida, wacce tasan mutuncin kanta, a duk sanda na samu wannan matar zanyi Aure babu ruwana da kyau ko fari, a’a tarbiyya kawai da hankali gami da ilimin addini nake nema, nasan samun wannan matan a yanzu yana matuƙar wahala shiyasa na ajiye lissafin aure yanzu dan haka kuje kuta Auren ku wannan ba matsalata bace.”
Bakinsa Faruq ya taɓe tare da cewa.
“Itafa mace babu ruwanta da wannan jiji da kan naka, idan har kace da wannan izzarta ta iko zaka tsaya neman matar Aure to fa sai ka zama tuzuru kafin kayi Aure wata ƙil ma lokacin yaran mu cin kusa kai shekara goma.”
Murmushi Al’ameen yayi sanin halin tsokanar Faruq yace.
“Naji na zamo tuzurun, kaga gimtse waya da alamu maganganun ka shirmene.”
Faruq shima dariya yayi yace.
“Ai dole kace maganganuna shirmene tunda na kira Aure maƙiyinka.”
Yana Maganar ya katse yana dariya, Al’ameen shima dariyar yayi tare da rufe system ɗin, ya miƙe ya nufi tollet.
Kusa dashi ta zauna tana amsar wayar hanun sa tare da cewa.
“Ya Haidar.”
Ta kirasa cikin slow voice ɗin ta, sosai taci kwalliya cikin less mai ratsin ƙore yayin da ɗinkin ya amshi jikinta, dubanta Haidar yayi tare da cewa.
“Ina zakije haka da daren nan kinci kwalliya kamar mai zuwa gidan biki, sai dai fa kinyi kyau sosai ba kaɗan ba.”
Murmushi Rufaida tayi cikin jin daɗin yaba kwalliyar da tayi domin kuwa saboda shi tayi.
“Na gode Ya Haidar, Ya Haidar, amm wannan game ɗin da naga kanayi jiya ita nake son ka cire min securityn wayar nayi.”
Murmushi yayi tare da kamo hanunta da wayar ke riƙe, wani irin zubawa tsikar jikin Rufaida yayi jin yanda ya kamo hanunta idanunta ta lumshe, shi kuwa ko a jikinsa baiji komai ba domin kuwa bai kawo komai cikin ransa ba yadda ya ɗauki Madina ƙanwarsa ta ciki ɗaya itama haka ya ɗauketa, yatsarsa ya saka wayar ta buɗu tare da cewa.
“Sai kita fama tunda da alamu yau baki da aikin yi.”
Murmushi kawai Rufaida tayi ba tare da tace masa komai ba ta hau buga game ɗin, suna nan zaune Ammar ya shigo da gudu yana cewa
“Aunty Madina!! Wai kije inji Uncle yaseer yana compaunt yana tsaye.”
Share Ammar Madina tayi tamkar bata jisa ba, yayi Maganar wajen sau uku bata kulasa ba, Ya Haidar ne ya juya tare da cewa.
“Madina wai baki jin yana miki Magana ne yace miki saurayinki yazo.?”
“Yaya naji sa mana tsabar iskanci ke damunsa nace masa duk sanda aka aikosa ya daina kirana daga nesa yazo har inda nake ya faɗa min, amma tsabar taurin kunne ya kasa ganewa, kuma Allah na riƙeka ko, hmmm!! Sai na cire maka harshe.”
Dariya Haidar ya saka yana duban Madina yace.
“Dama kun saba faɗan ai, kinga malama daina alaye tashi kawai kije idan ma Al’ameen kike tsoron ya ganki, sai kiyi addu’a Allah ya hanasa fitowa har ki dawo.”
Bakinta ta tura tare da miƙewa ta haura sama, Rufaida ce tace.
“Ba dole taji tsoronsa ba, mutum kullum kamar dodo, shi dai a rayuwarsa babu wasa na tsakanin ƴan uwa dashi kullum cikin haɗewar fuska yake.”
Dariya Haidar yayi yace.
“Wai ke baki da saurayi ne, ban taɓa ganinki kina hira ba, ko dai baƙin jini ke gareki ne.?”
Yayi mata Maganar cike da zolaya, murmushi Rufaida tayi tana ɗago idanunta ta kallesa tare da cewa.
“Ni kuwa nake da farin jini malam, samarin koransu nake saboda ina da gwanina, haskena shiyasa bana tsayawa ɓata lokaci da wasu.”
Dariya Haidar yayi yana nuna ta da yatsa yace.
“Kaji wata ƙarya ina samarin suke da har zaki koresu, ke dai faɗi gaskiya kice, Ya Haidar bani da saurayi sai na taimaka na nemo miki koda lebura ne.”
Itama Rufaida dariyar tayi tare da ijiye masa wayarsa akan cinyarsa tace.
“Na faɗa maka ai ina da gwanina bar neman kai dani.”
“To ina gwanin yake, bamu shaida ba ai tunda bamu gansa ba in da gaske ne sai ya fito mu shaida.”
Rufaida raurau tayi da idanunta tamkar zatayi kuka idanunta suka ciko da ruwa ta ɗago ta kalli ya Haidar sai kuma hawayen suka zuba, zaro idanunsa Haidar yayi ya saka hanu tare da goge mata hawayen yace.
“Meye kuma na kukan nifa wasa nake miki, kawai daga wannan maganar sai kuka Rufaida.?”
Cikin raunin murya Rufaida tace.
“Ya Haidar kullum zuciyata cikin tsinkewa take, domin kuwa ni ina sonsa amma shi baya sona baima san ina sonsa ba, kuma ni shine nake so, na rasa ya zanyi ya fahimta.”
Tunda take Maganar ya zuba mata idanu cike da tausayi, hanunta ya kama tare da cewa.
“Na fahimce ki Rufaida, hmmm!! Amma shi wannan wanda kike son waye ne?”
Shiru tayi kanta na ƙasa ta kasa furta masa cewa shine, a hankali tace.
“Ya Haidar baka sansa ba a school ɗin mu yake.”
“To amma Rufaida ni a nawa tunanin mai zai hana kije ki samesa kuyi magana ta fahimtar juna,. Ki bayyana masa gaskiyar abinda yake zuciyarki, ba haramun bane dan mace tace tana son namiji, idan har yana imani da tausayi zai amince da ke muddun yayi duba da halin da kike ciki, duk inda masoyinka yake yafi maƙiyinka, a wajen mutum mai hankali bazai taɓa zubawa masoyinsa ƙasa a idanu ba, kije ki gwada sa’ar ki, nasan kuma insha Allah zakiyi nasara, domin kuwa baki rasa komai wanda ɗa namiji yake buƙata a wajen mace ba, kina da kyanki dai-dai gwargwado kina da ilimi da tarbiyya ga asali, to me kika rasa, kije da ƙwarin gwiwwarki ki nemo Soyayyar ki, ina miki fatan Nasara.”
Tunda ya fara Maganar ta zuba masa idanu cike da matsanaciyar Soyayyar sa, Tabbas Ya Haidar mutumin kirki ne duk macen da ta samesa a matsayin miji Tabbas tayi dace, kafin tayi Magana wayarsa tayi ƙara hanu yasa ya ɗago wayar *NAFEESAT* murmushi ya saki tare da kallon Rufaida yace.
“Kinga nima Auntyn ki ke kira, kyakkyawa ce ga kunya, ina sonta sosai, Kuma nasan na samu matar Aure.”
Wani irin tsinkewa zuciyar Rufaida yayi, take ranta ya ɓaci farin cikin da ta samu yanzu ya gushe, saurin sunkuyar da kanta tayi ƙasa jin hawaye na ƙoƙarin zubo mata, ɗaga wayar Haidar yayi tare da cewa.
“Kin jini shuru ko.?”
Daga can cikin shagwaɓa da narkewar murya Nafeesa tace.
“Baka son zuwa ne ko, tun ɗazu nake jiranka harna fara gajiya, ni dai dan Allah kazo na ganka ko zan samu nutsuwa, ina tsananin buƙatar ganin kyakkyawar fuskarka, gashi kuma nacewa Mama kana zuwa ni dai kazo.”
Murmushi Haidar yayi yana jin maganganunta suna shiga har cikin ransa lumshe idanunsa yayi tare da kwantar da kansa jikin kujera, Rufaida zuba masa idanu tayi cike da takaici.
“Haba dai waya faɗa miki bazan zo ba, ai yau bazan iya bacci ba idan ban ganki ba, gani nan zuwa yanzu zuciyata.”
Murmushi Nafeesa ta saki cike da hango cikar burinta domin kuwa yanzu ta gama yadda cewa Haidar ya faɗo hanunta.
“Ka kula da hanya Allah ya iso min da kai lafiya.”
Da ameen Haidar ya amsa yana katse kiran dubansa ya kai ga Rufaida da yaga ranta a haɗe cike tausasa zuciya yace mata.
“Oh kinga Rufaida dan Allah karki bari Soyayya ta saki a damuwa, kije ki gwada amfani da shawarar dana baki, ina tabbatar miki da zakiyi nasara zai soki.”
“Ya Haidar! Ka tabbata zai soni idan na sanar masa, ina tsoro karya kware min ina ganin yana da wacce yake yaso ita yaya zaiyi da ita idan ni ya amshi Soyayya ta.”
Ɗan dariya Haidar yayi tare da cewa.
“Kin jiki da wata magana, shifa namiji ne wanda Auren mata biyu zuwa huɗu ya wajaba akansa, idan har yana da ƙarfi na Tabbata bazai ƙiki ba, zai haɗa ku biyu ya Aura muddun ke zaki yadda kije masa a ta biyu.”
“Ya Haidar idan kuma bashi da ra’ayin mata biyu fa.?”
Goshin sa Haidar ya dafe tare da cewa.
“Kuma kinyi Magana Tabbas ba kowa ke da ra’ayin mata biyu koni nan bani da wannan ra’ayin nafi son na zauna da mace ɗaya ta isheni rayuwa, amma kije ki gwada idan har bai amince da soyayyarki ba, idan so cuta ce hakuri ma maganine, ni bara naje sai na dawo.”
Yayi Maganar yana kwasar wayoyinsa da key ɗin motar sa ya fice daga part ɗin wani irin kuka mai cin rai Rufaida ta saki, sosai take hango rashin Nasara a lamarin Soyayyar ta, gudun kar momma ko Mansura su zo su sameta a wannan halin ya sata goge hawayen nata tana jin zuciyarta na tafasa.
Shi kuwa Haidar tunda ya shigo maitama yayi parking a gefe tare da kiran Nafeesa ya sanar da ita inda yake babu jumawa kuwa ta fito, tun daga nesa ta hango motar tasa, dariya tasa tana ƙiyasce iya kwanakin da itama zata mallaki irin wannan motar, hijabinta har ƙasa ta isosa tare da kwankwasa glass ɗin motar, a hankali ya zuge glass ɗin tare da zuba mata idanu yana sakin murmushi, kallonta yayi daga sama har ƙasa tasa dogon hijabi ga safa a ƙafarta, baka ganin komai a jikinta sai fuskarta da tafin hannunta, Tabbas yayi dace da mace ta gari, abinda ya furta a cikin zuciyarsa kenan ya buɗe mata mota ba musu ta shiga tana murmushi tace.
“Barka da isowa duniyata.”
Murmushi Haidar ya saki tare da cewa.
“Sai naji sunan yamin daɗi MUSSAMAN daya zamo kece kika raɗa min, muje kenan.”
Kanta ta kaɗa masa tace.
“Muje”
Motar yaja Suka nufi ƙofar gidan su tana masa kwatance a ƙofar gidan yayi parking suka fito yace taje ta sanar da maman tukunna kafin ya shiga babu musu ta shiga, shi kuwa da kallo yabi gidan nasu, gida ne mai kyau kana kallon gidan zaka tabbatar da mai gidan attajiri ne, ya ɗan juma tsaye kafin ta fito suka shiga da sallama Haidar ya shiga falon mama tana zaune tasha hijabi a ƙasa Haidar ya zauna kansa a sunkuye yace.
“Barka da hutawa Mama.”
Mama murmushi tayi tana duban Haidar da kansa yake sunkuye tace.
“Barka ɗana, sannu da zuwa, Nafeesa ai tana ta bani labarin ka, ka ceci rayuwar ƴata mun gode sosai Allah ya saka da alkairi.”
Murmushi Haidar yayi cike da kunya yace.
“Ba komai Mama ai yiwa kaine, na gaisheki mama ni zan koma.”
Yayi Maganar yana miƙewa tare da zaro rafar kuɗi a cikin aljihun sa ya ajiyewa Mama a gabanta.
“A sayi sabulu Mama.”
Yayi Maganar yana tafiya, murmushi Mama tayi tace.
“Harda ɗawainiya haka to nage Allah ya ƙara buɗi.”
Da ameen ya amsa yana fita nafeesa tabi bayan sa, a jikin mota ta samesa murmushi tayi tace.
“Kuma harda ɗawainiya haka.”
Ɗan harararta ta tayi tare da cewa.
“Laifine idan ɗa yayiwa uwarsa kyauta.”
Kanta girgiza alamun a’a, to ki rufe bakinki a duk sanda na kyautatawa mamana, dariya tayi tace.
“To na rufe, wai yama naga ka ƙara kyau fiye da yanda na ganka kwanaki.”
Dariya Haidar yayi tare da cewa.
“Kwanaki dai kinmin kallo tsoro ne Malama saboda baki sanni ba kina tunanin ko zan sace kine.”
Dariya sosai Nafeesa tayi tace.
“Ai kuwa gashi ka sace nin, tunda ka sace min zuciyata.”
Dukkan su dariya sukayi sun juma sosai suna hira sai tara da kwata Haidar yace.
“Kinga dare yayi idan na biyeki to zamu kwana ban gaji da jin muryar kiba, gara ki shiga gida kar mama tayi miki faɗa.”
Yayi Maganar yana jawo wata ƙaramar leda daga cikin motar sa, ya miƙa mata tare da cewa.
“Karki ce min komai ki amsa wannan itace kyauta ta ta farko a gareki.”
Murmushi Nafeesa tayi tare da saka hanu ta amsa tana cewa.
“To na gode Allah ya ƙara buɗi bara na shiga sai munyi waya.”
Murmushi Haidar yayi yana kallonta sai da ta shiga sannan yaja motar sa ya bar unguwar cike da farin ciki.
Ai cikin sauri Nafeesa ta shiga bedroom ɗin Mama tana zaune tasa kuɗin da Haidar ya bata a gaba tana kallon su gefenta Nafeesa ta zauna tare da cewa.
Nawa ne ya baki?”
“Dubu ɗari ne gasu.”
Dariya Nafeesa ta sheƙe dashi tare da juye ledar daya bata a gadon Mama, sarƙar gwal ce sai sheƙi take da kuma rafar dubu ɗari, zaro idanunta Nafeesa tayi ta ɗaga sarƙar tare da cewa.
“Mama sarƙar gwal ce fa.”
Itama Mama baki buɗe take duban sarƙar tace
“Ƙwarai kuwa da gani kuma babba ce, sai Allah ne yasan bawa ya saya amma ababu zata iya kai 350k wannan kuma sana’ar me yake da zai samu waɗannan kuɗin, anya kuwa ba ɗan satar mutane ba, karfa ki jawo mana bala’i Nafeesa….
Ummu Nasmah ✍🏻
Mashaa Allah