Skip to content
Part 1 of 67 in the Series Aminaina Ko Ita? by Rasheedat Usman

Sadaukarwa

Na sadaukar da wannan littafin ga Ummana Momy Hassana marigayiya Ubangiji ya jiƙanki da rahama yasa mutuwa hutuce a gareki, ina roƙon alfarma ga duk wanda ya samu damar karanta wannan littafin daya sata cikin adduar
Sa rabbi shi mata rahama ya yalwanta haske gami da ni’ima cikin kabarin ta.

بسم الله الرحمن الرحيم

Warning: Ban yadda wani ko wata ya juya min labari, ta kowacce siga ba tare da izina na ba yin hakan kuskukure ne.

Tsokaci

Wannan labarin ƙirƙirarren labari ne ban yishi don cin zarafin kowa ba, duk wacce taga yazo dai-dai da halinta labarin ne kawai yazo da haka domin kuwa labari ne mai ɗauke da salon zamani wanda ya taɓo abubuwa da dama da suke faruwa a halin yanzu labari ne mai taɓa zuciyar mai karatu.

Ina farawa da sunan Allah, Allah ka tsare harshena ga rubuta abinda ba zai amfani al’umma ba.

Shafi Na Daya

Cikin gaggawa take ɗaura agogon hanunta tasan yanzu haka Alhaji Atiku Naira yana hanya, bata gama tunanin ba, taji ringin ɗin wayarta, kallonta ta mayar kan screen ɗin wayar, ‘ALH ATIKU NAIRA’ ɗan murmushi ta saki tare da saka hanu ta ɗauki bag ɗinta tare da Hijabin ta, niƙaf ta ɗaura, ta jefa wayarta shima cikin jakar, wasu plat ɗin takalmi ta saka kalar ja ruwan kayan jikinta, hanyar waje ta nufa, Ƙanwarta Nazifa da tun ɗazu take zaune tayi tagumi ta zubawa ƴar uwar tata idanu cike da ƙyamar ƙasƙantacciyar rayuwar da ta zaɓawa kanta, dakatar da ita tayi ta hanyar kiran sunanta.

“Aunty NAFEESAT!”

Tsayawa NAFEESA tayi tare da juyowa ta amsa kiran.

” Na’am uwar ƙorafi, yau kuma wacce da’awa zaki bani wanda ban santa ba.”

Numfashi Nazifa ta sauƙe tare da runtse idanunta cike da jin haushin ƴar uwarta tace.

“Dan Allah Aunty karki fita kibi wannan Alhajin, kin san dai abinda kike aikatawa haramunne ko? sam bai dace da rayuwarki ba.”

Taɓe bakinta NAFEESA tayi ta ce.

“Tatsuniyar taki kenan da kullum kike maimaita min ita koda karatu ne yaci ace zuwa yanzu na haddace, Nazifa nasha faɗa miki cewa ki cire idanunki a kaina kin kasa ji ko, to Wallahi na kusa naci ubanki muddun baki fita sabgata ba, kaji min yarinya da shegen shishshigin tsiya, to uwata ma da ta haifeni bata saka min wannan idon da kika saka min ba, nasha faɗa miki neman kuɗin da zan rufawa kaina asiri nakeyi na ɗaukewa kaina takaicin da ubana ya kasa ɗauke min dan haka ki kiyayeni.”

Tayi Maganar cikin faɗa tana nuna Nazifa da yatsa, shuru Nazifa tayi tana kallonta sanda ta gama sannan Nazifa cikin siririyar muryarta tace.

“Allah ya baki hkr Aunty gaskiya na faɗa miki, wannan ba ita bace hanyar neman kuɗi meyasa bazaki nemo koda ɗauken atamfofi bane kk kasa kaya ki sayar ba, saiki samu kuɗin ta hanyar da ta dace hanyar halak, Aunty NAFEESA muna da Uba fa mu ba marayu bane ubanmu yana da dukiyarsa dai-dai gwargwado yana bamu ci da sha, me kika rasa Aunty da har zaki maid…”

“Dakata dallah malama ya isheni haka, abubuwan dana rasa a cikin gidan nan suna da yawa kuma kema kin sani, Ban rasa ci da sha ba, amma na rasa sutura masu tsada da kuɗin buƙatun duniya na more rayuwa, ni macece kuma budurwa kinsan dole ina buƙatar Ado na ƙyale-ƙyalen zamani kuma duk na rasasu saboda Allah ya haɗani da mungun Uba wanda bai damu da rayuwar jin dadi na iyalinsa ba, mai kuɗin lukudu wanda bazasu amfane kiba bare kuma ni ABBA kansa kawai ya sani babu ruwan sa damu, kinga kuwa tunda ina buƙatar jin daɗin rayuwa dole naci karena babu babbaka.”

Girgiza kanta Nazifa tayi cike da rashin gamsuwa da maganganun NAFEESA tace.

“Aunty Wannan ba hujj…”

“Kee!!! Dallah wannan soki burutsun naki ya isheni yanzu ba lokacin ɓata yawuna bane ina da abu mai mahimmanci da zanyi ki bari Allah ya dawo dani lafiya sai mu ɗaura daga inda muka tsaya, idan Mama ta dawo kice mata na fita.”

Ta dakatar da Nazifa tare da juyawa ta fice numfashi Nazifa ta saki tare da cije leɓenta tana kallon ficewar Nafeesa.

“Hmmm!!! Allah buwayi gagara misali, kowa da tasa ƙaddarar mu kuma tamu kenan ta rashin samun uwa ta gari, tabbas da Mama mai kulace da Rayuwar Aunty Nafeesa bata lalace haka ba Hmmm!!! Allah ka shirya Aunty Nafeesa.”

Duk zancen zuci Nazifa keyi tare da miƙewa ta kwanta a saman gadon nasu zuciyarta duk babu daɗi.

Ita kuwa Nafeesa tana fita, tayi bayan layin gidan su, tana dube dube sai da ta tabbatar babu kowa a wajen sannan tayi saurin shiga cikin motar Alhaji Atiku Naira, numfashi ta sauƙe tare da cewa.

“Sannu da isowa Alhajina, kayi kyau sosai tamƙar ƙaramin yaro.”

Ta ƙarisa Maganar tana kashe masa Ido tare da ɗaura hanunta saman cinyarsa, ta kwanto jikinsa, dariya Alhaji Atiku yayi cike da Sha’awarta ya jira hanunsa cikin rigarta yana dariya yace.

“Duk kyauna ban kaiki ba, ina tsantsar Sha’awarki, anya kuwa yau ba’a cikin motar nan zamu kashe arnan nan ba kuwa, dan na zaƙu.”

Dariya Nafeesa tayi tana saka hanunta ta cire nasa hanun daga cikin rigarta tace.

“Rufa min asiri tsakiyar unguwa muke ja mota kawai muje Amada hotel yafi min rufin asiri domin kuwa ana ganina da mutunci, ni ai taka ce tunda kana biya min buƙatuna kuɗi enough daga ni har jikina ai naka ne.”

Dariya Alhaji Atiku yayi yana lakace mata hanci yaja motar suka fita daga cikin unguwar.

AMBASSADOR AHMAD GIWA FAMILY ESTATE

Hommm!!!! Hommm!!! Hommm!!! Ƙarar motar da ta doki kunnen ɗan sandan dake gadi a bakin makeken get ɗin, koda jin sautin motar tamkar zai doki get ɗin ya shigo hakan ya tabbatar masa da cewa ‘HAIDAR’ ne, sanin zafin zuciyarsa ya sa sargent Samuel tashi da sauri ya wangale get ɗin hancin motarsa ya danno fara tas gwanin sha’awa ita kanta motar abun kallo ce ƙirar MERCEDES BENZ C300 MODEL wacce kuɗin ta zai kai kimanin 7million hanu Sargent Samuel yake ɗaga masa wanda shi HAIDAR baima lura ba, dreving ɗinsa kawai yake, a parking space dake cikin estate ɗin Yayi parking, hanu yasa da niyar buɗe motar ya fito sai yaji ringin ɗin wayarsa, dubansa ya kai ga wayar Helina da kamar bazai ɗaga kiran ba, sai kuma ya saka hanu ya ɗaga wayar tare da maida kansa ya jingina jikin sit ɗin motar shuru yayi ba tare da yayi magana ba, daga can Helina tace.

“My Man where are you going?”

Tamkar baya son maganar ya amsa mata da cewa.

“Meye matsalarki da inda nake, kina bina bashi ne wohoho Helina kin matsawa rayuwata da yawa, na faɗa miki idan ina buƙatar ki nida kaina zan nemeki?”

Ya jefe mata tambayar cike da gatsali, Helina shuru tayi jin yan iskan nasa suna kansa kafin cikin kwantar da murya tace.

“Sorry My Man, ina son ganinka ne, 2dys bamu haɗu ba, ni kuma gaskiya ina matse da kai bazan iya haƙurin yau ba tare da kaiba kasan son da nake maka.”

Ta ƙarisa Maganar cikin marairaicewar murya, HAIDAR tsuka yaja ba tare daya kuma ce mata komai ba, ya katse kiran hanunsa yasa ya buɗe motar ya fito, numfashi mai sanyi ya sauƙe tare da kai dubansa ga tarin ma’aikatan gidan dake tsaye suna jiran fitowar sa, murmushi HAIDAR yayi tare da miƙa musu hanu ɗaya bayan ɗaya sukayi musabaha kasancewar sa mutum mai tsananin daraja ɗan adam komai talaucin sa, baya taɓa ƙyamar mutum, Ga kuma uwa uba kyautar da yake dashi, kuɗi ya basu rafa guda, kafin ya danna kansa cikin wani ƙaramin get da zai sadasa da part ɗin INNA JAMMA wanda take haɗe da su UMMI tun daga bakin ƙofar da zai shigar dashi Babban falon yake jiyo hayaniyar su Minal, da Sallama ya shiga da gudu Minal ta faɗa jikinsa, tana.

“Oyoyo Yaya Haidar welcome”

Dariya Haidar yayi tare da ɗaga Minal sama yana cewa.

“Oyoyo my princess”

Ya ɗagata yana ƙoƙarin shiga cikin falon, Afnan ma dariya tayi tace.

“Sannu da zuwa yaya Haidar, tun ɗazu Daddy ke jiranka, yanzu yake cewa zai tafi kawai ba lallai kazo ba maybe uzuri ya riƙeka.”

Murmushi Haidar yayi ya sauƙe Minal tare da cewa.

“Ai kuwa kamar Daddy ya sani wallahi na biya Company ne, akwai kayan da aka kawo wanda gobe muke so a fitar dashi garmany, shine ya tsaida Ni na tsaya munyi lissafi, Ina AL’AMEEN.”

“Yaya Al’ameen yana Bedroom ɗinsa bai fito ba, ko breakfast baiyi ba, maybe ma Ina ga bai tashi daga bacci ba.”

Murmushi HAIDAR yayi tare da cewa.

“Okay Afnan kije ki tada sa, kice zamu shige da Daddy yayi maza ya fito, bara ni na ƙarasa wajen Daddyn.”

“Shikenan Yaya Haidar bara naje na tashe san.”

“Wannan ai yaudara ce baƙar cuta taya zaka shigo gidan nan baka fara nemana ba a matsayina ta uwar gida.”

Inna Jumma tayi maganar tana riƙe kunkumi, da sauri Haidar ya kai dubansa ga Inna Jumma, kyakkyawar tsohuwa fara tas mai tarin annuri a fuskarta, murmushi Haidar ya saki tare da miƙewa tsaye ya nufi Inna Jumma sanda yazo daf da ita ya tsaya yace.

“Ai koda idanuna sun makance, dole zuciyata sai ta kalleki, uwar gida sarautar mata, wai ma ya akayi yau naga kin koma min yarinya ƴar 19yrs kinyi kyau fa Zuciyata.”

Ya yi mata maganar cikin raha cike da ƙaunar kakar tasu Dariya Inna Jumma tasa za tayi Magana taji muryar *FARUQ* daga bayansu yana cewa.

“Ina kyau anan jiki duk ya tattare tsufa ya gama awun gaba ita, fata duk ta jeme, kai dai malam faɗa mata gaskiya ya akayi kaga ta tsofe ta jeme tamkar ƴar 140yrs”

Dariya Haidar yayi yana maida kallonsa ga Faruq dake shigowa, taɓe bakinta Inna Jumma tayi tare da cewa.

“To fa, ai kaga inda matsalar take kai ALIYU duk sanda kazo gidan nan sai wannan Munafukin UMARU ɗin ya biyo ka, bari kaji aini tsufana yazo da kyau ka jira na uwarka da ta ubanka ka gani bazasu sami kyawun tsufata ba.”

Dariya dukkan su sukayi Haidar na rungume Faruq yace.

“Haba dai Inna Jumma kin taɓa ganin inda mota ta tashi babu inji ko kin taɓa jin inda ɗan Adam ya rayu babu jini, Momy ai kunfi kusa ƴarki ce.”

Inna Jumma cike da ƙaunar jikokin nata tana dariya tace.

“A’a Umaru ban taɓa gani ba.”

Haidar still dariyar yayi yace.

“To kuwa ki saka a ranki duk inda kikaga Haidar sai kinga Al’ameen Da Faruq domin kuwa tsintsiya ne maɗauri ɗaya, kaga Faruq rabu da Inna Jumma haura ka tashi wannan ɗan son baccin tsiyar ni bara nayi wajen Daddy time na ƙurewa.”

Ya ƙarisa Maganar yana sakin Faruq ya haura step ɗin cikin hanzari Faruq ido ya kashewa Inna Jumma tare da ce mata.

“Aje a zauna a cigaba da zaman jiran bazawarin tsoho HAIDAR dai ya tsere miki anga sabon jini ana neman liƙewa.”

Yayi maganar yana dariya Inna Jumma itama dariyar tayi ta saka hanu zata jawo Faruq ya ruga da gudu ya nufi part ɗin Al’ameen, murmushi Inna Jumma tayi ta furta.

“Ja’iri ɗan nema, hmmm Alhamdulillah!! Har cikin raina ina jin daɗin yanda kan jikokina yake haɗe suna ƙaunar junansu Allah ka tabbatar da ƙauna da zumunci tsakanin su har abada.”

Tayi adduar tana zama cikin ɗaya daga cikin kujerun dake falon kusa da Minal dake famar game da system ɗin Maimu.

Hankalinsa kwance yake baccin sa cikin blanket ɗin, ga sanyi ac daya gauraye Bedroom ɗin gami da ƙamshin turaren ɗaki, Afnan da ta shigo ne ta zauna bakin bed ɗin tana tashinsa a hankali.

“Yaya Al’ameen!! Yaya Al’ameen!! Yaya Al’ameen.”

Jin sautin kira cikin kunnuwansa ya sashi buɗe idanunsa a hankali yana ambaton.

“Bismillahillazi ahyana ba’ada ma amatana wa ilainnushur.”

Ya ƙarisa adduar tare da sauƙe sexy eyes ɗinsa masu kalar ruwan toka Ash color tamkar idanun mage ya zubawa Afnan ba tare da yayi magana ba, kasancewar sa miskilin gaske wanda shi kwatakwata bai cika magana ba, koda da iyayensa maganarsa bata yawa, mutum ne mai wuyar gane halinsa wanda idan bakasan halinsa ba, sai kace yana da wulaƙanci.

” Yaya al….”

Hanu ya ɗaga mata ba tare da ta ƙarisa Maganar ba, ya nuna mata hanyar ƙofa alamun ta fita, babu musu Afnan ta fita domin kuwa tasan halin Al’ameen sarai zai ma iya maketa, idanunsa ya ɗaga ya kalli makeken agogon bangon dake manne cikin Bedroom ɗin, 11:30am ɗan ƙara ware idanunsa yayi yana kallon agogon tabbas yau ya makara.

“Daddy.”

Ya furta a hankali tare da tashi da hanzari yana sauƙe ƙafarsa ƙasa takalmin dake gefen bed ɗin ya saka tare da miƙewa tsaye daga shi sai gajeren wando da bes, daidai da shigowar faruk, da Sallama juyawa Al’ameen yayi yana kallon Faruq sai kuma ya saki murmushi ya amsa sallamar, zama Faruq yayi bakin bed ɗin tare da cewa.

“Meyasa wai kake hakane taya zaka kori yarinya bayan aikota akayi ta tashe ka.”

Kansa Al’ameen ya kauda gefe tare da nufar tollet ba tare da yayiwa Faruq Magana ba, shima Faruq sanin hali ya sashi taɓe bakinsa, kusan 30 minute kafin Al’ameen ya fito daga tollet ɗin kunkumin sa ɗaure da towel ya rayata ɗaya kuma a kansa yana tsame ruwan dake jikinsa kan dest ɗin dake jikin dressing mirror Al’ameen ya zauna, Faruq ya kalla da hankalin sa ke kan wayarsa cike da nutsuwa Al’ameen yace.

“Hmmm!! Har abada baka taɓa fuskanta ta, Faruq sai kace ba tare muka taso ba, sanin kanka ne, na haramtawa Afnan shigowa Bedroom ɗina amma tsabar ganganci kuka turota, muddun baku daina aikota cikin Bedroom ɗin nan ba, ina tabbatar maka wata rana sai dai ku shigo ku ɗauketa a karye.”

Faruq dake kwance saman bed ɗin Al’ameen yana jinsa yayi shuru bai kulasa ba, tamkar baya wajen, Al’ameen ganin Faruq bai tankasa ba, yasa shima yayi shuru, sai da ya gama shiryawa cikin wata ɗanyar gezna baƙa wacce ta ɗauki fatar jikinsa kasancewar sa farin mutum ƙal, gashin kansa ya gyara ba tare daya saka hula ba, ya manna siririn glass ɗinsa a Idanunsa.

“Muna iya tafiya.”

Ya furtawa Faruq tamkar bai son maganar murmushi Faruq yayi ya ɗauki wayarsa tare da dukan kafaɗar Al’ameen yana dariya.

“Shege Abokina, wannan kwalliyar kuwa anya ba wajen budurwa zaka ba.”

Taɓe bakinsa Al’ameen yayi tare da furta.

“Kaine suke gabanka har kake tuna su, ni ko kaɗan basa gabana, Faruq ƙwaƙwalwata bata shirya ɗaukawa kanta damuwa ba, domin kuwa mace matsala ce.”

Murmushi Faruq yayi hanunsa na kafaɗar Al’ameen suna tafiya yace.

“Anya kuwa Al’ameen aljana bata aureka ba, wannan ƙyayyar da kake yiwa Aure yayi yawa, gaskiya ya kamata a fara nemo maka magani, naga kai ko kaɗan mata basa burgeka duk kuwa kyan mace da adonta, abokina kana da matsala duk yanda akayi.”

Murmushi Al’ameen yayi ya ɗaga kansa ya kalli Al’ameen tare da cewa.

“Aljani baya taɓa kusantar mai yawan ambaton Ubangiji, ko ta nan ya kamata ka fahimci nafi ƙarfin jinni.”

Yayi Maganar daidai sun shigo tsakiyar falo, wannan karon babu Inna Jumma a falon da alamun ta shige Bedroom ɗin ta, sama suka haura Wajen Daddy, da Sallama suka shiga shiga cikin Bedroom ɗin, wani kyakkyawan tsoho mai kimanin shekaru 75 zaune idanunsa manne da farin glass ga wani farin saje daya zagaye fuskarsa yana sanye da farar shadda duk da ɗan tsufar da yayi hakan bazai hana kaga tsantsar kama dake tsakanin sa da Al’ameen ba, HAIDAR ne zaune gefen sa yana tausa masa ƙafarsa *AMBASSADOR AHMAD GIWA* kenan adalin tsoho mai matukar tausayin talaka da taimakon su Wakilin Nigeria na ƙasar *AMERICAN* tsohon ɗan siyasa daya riƙe manyan maƙamai cikin Nigeria. Fuskarsa ɗauke da murmushi ya amsa sallamar tasu, gefen Haidar suka zauna Al’ameen a hankali ya furta.

“Good morning Daddy hw ws th dy”

Har yanzu fuskarsa ɗauke da murmushi ya amsa.

“Fine my son, sai yanzu gari ya waye kenan, da har zan tafi ba tare da munyi sallama ba, sai naji bazan iya tafiya bamu gana ba dalilin kenan da yasa na dakata da tafiyar sai tomorrow in Allah ya kaimu.”

Murmushi Al’ameen yayi yace.

“Sorry Daddy na ɗan makara ne, amm Daddy sai yaushe kenan zaka dawo idan ka tafi?”

Murmushi Daddy yayi tare da kallon Al’ameen yace.

“Just one years kawai zanyi, sannan ina son na sanar daku cewa da Faruq zan tafi yau saboda ayyuka sunmin yawa ina buƙatar mai taimaka min kuma sai naga faruk ne ya dace daya tallafa min idan yaso kaida Haidar sai ku kula da Companyn mu dake nan.”

Kusan a razane Al’ameen da Haidar suka ɗago kansu cike da mungun mamaki.

“Whattt!!!!” Suka furta kusan a tare shi dai Faruq kansa yana ƙasa kasancewar yasan da zancen tafiyar tun jiya da safe Daddy da Papa suka sanar masa tare da hanasa sanar dasu Al’ameen gudun sasu cikin damuwa, murmushin manya Daddy yayi cikin kwantar musu da hankali yace.

“Dama dole nasan hankalin ku zai tashi dalilin kenan da yasa na hanashi ya sanar daku, tafiyar ta kama dole dashi ne shiyasa zan ɗaukesa sannan nima ina buƙatar mai tayani hira, hmmm ana tare dama dole wata rana a rabu, sannan ai tafiya ba mutuwa bace, muna zamanin da waya kan sada zumunci, facebook twitter Instagram Whatsapp telegram etc gasu nan dai da yawa hanyar da zaaga juna ta video call da kuma magana ta chart, dan haka ku masa fatan alkairi kawai baku tada hankalin ku ba.”

Numfashi suka sauƙe tare da furta.

“Shikenan Daddy Allah yasa hakan yafi alkairi, zamuje muyi breakfast Daddy.”

Murmushi Daddy yayi cike da ƙaunarsu yace.

“Okay kuje Allah ya muku albarka.”

Da ameen suka amsa tare da miƙewa suka fito ƙofar Bedroom ɗin Ammi ya nufa Haidar ya dakatar dashi da cewa tana bacci fasa shiga sukayi suka fito daining, har zasu zauna Haidar yace.

“No ni bazan zauna ba zan shige Companyn Gum Arabic ya iso yanzu zanje na duba ingancin sa, dan a yau nake son a shige dashi Egypt.”

Al’ameen kansa na ga wayarsa yace.

“Har kayan sun isowa jiya naji aka ce suna gashuwa harsun iso kenan.?”

“Eh sun iso tun cikin dare shiyasa ma yau nayi sammako zuwa Companyn Ƙaron sunyi kyau sosai da alamu zasu kawo kuɗi, jiya Sadam ya kira ni yake cewa akwai waƙen sa buhu 60 yana buƙatar kuɗi, sai dai ban yanke hukunci ba, nace masa sai munyi shawara, idan kun ƙaraso Companyn sai muyi magana.”

Numfashi Al’ameen ya sauƙe tare da zama yana jawo wata farar kula ya buɗe Chief ɗin dankali ne soyayye, spon ya ɗauka da plat ya ɗebi daidai wanda zaici sannan ya cewa HAIDAR.

“Babu wani shawara da zamuyi kawai kace masa bazamu sayi kayan ba.”

FARUQ ne yace.

“Saboda meyasa kace baza’a saya ba, bayan kuma muna buƙatar wake sanin kanka ne suna cikin list odern da za’ayi zuwa Tailan?”

Haidar cewa yayi.

“Ko kaima zaka tambayesa.”

Murmushi Al’ameen yayi tare da cewa.

“Saboda Sadam bashi da amana ya cucemu sau biyu ya samu asaran maƙudan kuɗaɗe ta hanyar yaudarar mu da saka magani cikin waken sa, wanda su kuma ƙasar waje basa buƙatar wake wanda yake da sinadarin magani, ƙarshe mukayi asaran wannan waken KAFIN ya dawo gida Nigeria tuni ya ɓaci da ƙwari sannan Tailan suka daina sayan waken mu, dan haka bazamu sayi nasa ba yakai wani Companyn.”

HAIDAR ne yace.

”But amma…”

Hanu Al’ameen ya ɗaga masa.

“Karkace komai kawai bazamu saya ba na yanke hukunci.”

Numfashi Haidar ya sauƙe tare da ficewa yana cewa.

“Okay sai kun iso”

Al’ameen da Faruq tare sukayi breakfast suna ɗan taɓa hira sama sama.

Haidar Driving ɗinsa yake hankali kwance ya kunna waƙar Auta mg boy mai taken sai dake, yana sauraro cikin nutsuwa, hango wata mabaraciya ya sashi tsayawa gefen titi yayi parking, inda Nafeesa ke tsaye tana jiran adaidaita sahu, tunda yayi parking Nafeesa ta zirawa motar ido sosai motar ta mata kyau koda gani ba ƙaramin kuɗi motar zatayi ba, duk cikin zuciyarta take wannan zancen, idanunta kuma na kan motar tana jiran ganin wanda zai fito daga cikin motar, Haidar cike da nutsuwa ya buɗe motar tare da ziro kafarsa, tun daga takalmin sa, take ƙare masa kallo har samansa, ko kaɗan Haidar bai kula da ita ba, kansa tsaye ya nufi mabaraciyar tare da miƙa mata Naira dubu goma, ya juyo, Nafeesa murmushi ta saki cikin zuciyarta ta furta ” wannan damar bazata wuce ni ba, domin kuwa da ganin wannan bawan ba ƙananan kuɗi bane dashi, dole na ƙulla alaƙar zuciya dashi domin babban jari zai zamo min” tayi zancen zucin tana nufar motar sa cikin hanzari ta zauna jikin motar, tare da danna ƙara tana muƙurƙusu, ta riƙe cikin ta gam da zummar yana mata ciwo sosai take muƙurƙusu harda riƙe cikin ta, idanunta rufe gam…

Aminaina Ko Ita? 2 >>

3 thoughts on “Aminaina Ko Ita? 1”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.