Kafin zuwa wayewar gari Ashfat tasha jini har leda biyu yayin da koda hanunta ne baya motsi, koda gari ya waye Papa da kansa ya sanar da Daddy abinda ke faruwa, shima Daddy Sosai hankalinsa ya tashi, a ranar yace a tanada masa jirgi, zasu tafi Nigeria, Da safe Aunty da momma da kuma su Maimu suka dawo gida, ya saura sai Inna Jumma ne da Aunty da Ummi, Haidar shima ya koma gida domin kuwa zuwa Company ya kamasa dole, ga kuma case ɗin motar Al’ameen da akayi accident din dashi, Ummi har yanzu ajiyar zuciya take gashi an hana kowa shiga yaga Ashfat an maidata ma ACU, Khalifa sosai yake son ganin ƴar Uwar tasa sai ina babu halin hakan, Ummi tausayinsa yasa tace Al’ameen ya ɗaukesa suje gida ya samu ya watsawa jikinsa ruwa, babu musu kuwa ya ɗaukesa suka tafi a motar da aka kawo su Ummi.
Koda suka shigo part ɗin nasu babu kowa sai Maimu dake zaune a falo ta kifa Kanta, sai kuka take har suka shigo bata san sun shigo ba, Al’ameen duban Khalifa yayi tare da cewa.
“Khalifa ka haura ina zuwa.”
Yayi Maganar yana zama gefen Maimu tare da saka hanu ya dafe kansa, Khalifa shigewa yayi idanunsa na cikowa da hawaye, a hankali Al’ameen ya furta cewa.
“Nayi imani da Allah wannan ba accident ɗin daya faru haka kawai bane, Tabbas da gangan aka haɗa wannan accident ɗin saboda kawai akashe mu, kaina ya kulle na fara shiga ruɗu Tabbas akwai wanda baya buƙatar ganin mu a wannan duniyar, tayar motata lafiya take domin kuwa da ita na fita aiki, kuma na dawo da ita lafiya banji alamun wata matsala a tare da motar Ba, sai bayan naje airport taya ta fice, lallai wani ne ya since tayar motar.”
Yayi Maganar yana runtse idanunsa, fuskarsa tayi jajur cike da tsantsar ɓacin rai, jin kalamansa ne yasa Maimu ɗago kanta tace.
“Waye ne, waye me son ganin bayan mu yaya?”
“Nima tambayar da nake yiwa kaina kenan waye ne, amma na kasa samun wannan amsar, ina tausayin Ummi domin kuwa ita uwa ce, sai tafi kowa jin zafi, Tabbas ko waye ne sai nayi ƙoƙarin ganosa, zan dakatar da wannan faɗan anyi biyu ba za’a sake na Uku ba! Bazan juri ganin ƴan uwana cikin tashin hankali ba, bazan iya jurar ganin ana kashesu tamkar ɓera ba! Zan kare rayuwar ƴan uwana a matsayina na yayansu.”
Yayi Maganar yana jawo Maimu dake kuka sosai jikinsa ya cigaba da cewa.
“Ki share hawayen ki, domin kuwa kukanku yana ƙara ƙona min zuciyata, Allah sarki bata sani ba ta biyo ƙaddararta, meyasa meyasa ita ƙaddarar take zuwa mana a mummuna.”
Daga bayansu sukaji muryar Haidar na cewa.
“Wannan ba accident ne wanda aka haɗa ba kamar yadda kake zargi, babu wanda ya haɗa shi Allah ne ya aikosa, ka daina zargin wani domin kuwa a idanun mutane akayi wannan accident ɗin, tashin hankali da ruɗu karyasa ka fice da hankalinka.”
Ɗago kansa yayi ya zubawa Haidar idanu kafin ya miƙe tsaye cikin ɓacin rai da tsawa tamkar wanda yake jiran a tanka masa, domin kuwa Al’ameen Mutum ne wanda baya iya riƙe fushinsa musamman idan yana cikin mummunan ɓacin rai ya cewa Haidar.
“Idan kana so ka kirani da mahaukaci Haidar! Amma Tabbas wannan hatsari ne da aka haɗasa.”
“A’a Al’ameen ya kamata ka dawo hankalinka ka daina wannan tunanin domin kuwa sam hasashen ka ba gaskiya bane, dan Allah kabar wannan maganar na roƙeka domin kuwa baka da hujja a cik…”
“Ya isa! Ya isheni haka jin kalamanka, idan har ba zuwa kayi ka tayani tunani akan wannan lamarin ba, dan Allah ka fita ka koma inda ka fito Domin kuwa bazan jure ka dinga ƙalubalanta naba.!”
“Bafa ƙalubalantarka nake ba Al’ameen iya gaskiya nake faɗa maka, ya kamata ka gane, sanda aka kashe Khairi ya kamata ka nuna wannan fushin naka, ka tsananta wannan binciken naka domin kuwa wannan shine kake hujja da dama, amma sai ka nuna ko in kula, ƙarshe ma wanda ake zargin sa kasa aka sakesa tare da rufe file ɗin case ɗin, a wannan accident ne ya kamata ka fahimta ka daina zargi gaskiya ce nake faɗa maka.”
“Naji kuma ban amince ba, har sai na tabbatar da gaskiyar.”
“Amma fa Al’ame…”
“Ya Isa haka! Ka riƙe gaskiyar taka bana buƙata, Please ka tafi na daina ganinka.”
Numfashi Haidar ya saki sanin halin Al’ameen mutum ne shi wanda Magana bata damesa ba yakan kauda kansa akan komai sai muddun ya fusata baya jin muryar kowa koda kuwa ta iyayensa ne, abinda zuciyarsa ta sashi kawai shi yake aikatawa, juyawa yayi yabar part ɗin Al’ameen shima a fusace ya haura ROOM ɗinsa.
Haidar kuwa tunda ya koma part ɗinsu ya shige ROOM ɗinsa tare da yin shuru yana tunanin halin da amininsa ya shiga ciki lallai yau Al’ameen ya fusata tunda harya nuna fushinsa, (amma ta yaya zaike biyewa ruɗun da zuciyarsa ke masa, wannan accident ɗin kowa ya sani accident ne daya faru da kansa, ko dai halin da Ashfat take ciki ne yasa Al’ameen ya ruɗe mtsss) duk cikin ransa yake Maganar, miƙewa tsaye yayi tare da goya hanunsa a baya yana kaiwa da kawowa a cikin room ɗin nasa, Rufaida ce ta turo room ta shigo itama cikin sanyin jiki zama tayi gefen bed ɗin nasa tace.
“Wai tunanin me kake ne haka tun cikin dare, ya kamata ka rage yawan wannan tunanin.”
Numfashi ya saki tare da cewa.
“Taya zan daina tunani acikin wannan halin da muke ciki, bazan taɓa farin ciki ba, muddun Al’ameen yana cikin damuwa, bazan taɓa iya dariya ba muddun yana kuka, zanyi dariya ne kawai sanda na tabbatar yayi dariya, a yanzu Al’ameen yana cikin fargaba da ruɗu, wannan hatsarin yasa Al’ameen cikin tsoron cewa ana neman rayuwarsu ne, na rasa ya zanyi Al’ameen ya nutsu.”
“Babu yadda zakayi dashi domin kuwa kasan halinsa, hmmm! Ya Al’ameen baya jin maganar kowa a duk sanda idanunsa suke rufe abinda yake ransa kawai shine yake yi, ƙyalesa zakayi yayi binciken ya gani amma dan Allah ni dai ka daina damuwa, ɗazu Maimu tace min Daddy ma yana hanya shida ya Faruq wataƙil idan sunzo su su dannesa ya haƙura.”
Zama Haidar yayi gefen Rufaida tare da fuskantar ta yace.
“Babu fa ta yadda hankalina zai kwanta a wannan yanayin domin kuwa duk Mutum mai imani dole ne hankalinsa ya tashi idan yaga wannan lamarin, Rufaida bafa fitar ƙafar Ashfat bane yanzu abun damuwar rayuwarta domin kuwa likita yace ba tabbacin zata farfaɗo, tana ACU fa room ɗin da yake wuya marar lafiya ya shiga cikin sa ya fito da rayuwarsa, sannan a wannan halin kice hankalina ya kwanta, ba abinda zai yiwu bane.”
“To amma ya haida…”
Hanu Haidar ya ɗaga mata tare da cewa.
“Ya isa haka, ki tashi kije sai na fito.!”
Yayi Maganar cike da fara gajiya da Maganar Rufaida, fita Rufaida tayi ba dan ranta yaso ba, bayan fitarta ne Nafeesa ta kirasa a waya sun ɗan juma suna hira harya sanar da ita rashin lafiyar Ashfat sosai ta nuna masa tausayin ta tare da cewa insha Allah itama zatazo ta duba ta.
Al’ameen sai wajen azahar suka koma asibitin shida khalifa, har yanzu babu wani labari akan Ashfat, jirgin su Daddy ƙarfe huɗu ya sauƙa, Papa da kansa yaje ya ɗauko su, Faruq sosai yake cikin damuwa har Allah Allah yake su isa yaga wani hali Ashfat ke ciki, Daddy cewa yayi a shige dashi asibiti, haka kuwa akayi asibitin aka wuce dashi, ko da Daddy suka shigo asibitin Khalifa da gudu ya faɗa jikin Daddy sai kuma ya saki kuka, bayansa Daddy ya buga cikin alamun rarrashi Ummi tana ganin Daddy idanunta ya ciko da hawaye wani irin kuka ne taji yazo mata kanta ta kifa jkin kujera sai ta saki kuka mai cin zuciya Daddy sake khalifa yayi tare da nufar Ummi gefenta ya zauna tare da jawota jikinsa ya kwantar da ita a ƙirjinsa cikin rarrashi yace.
“Gaji meyasa bazaki bawa zuciyarki haƙuri ba,kema da kanki kike kuka ina kuma ga yaranki kene fa ya kamata ki rarrashi zuciyarki sannan ki ƙarfafawa yaranki gwiwwa amma sai ya zamo kece kike kuka, ki sawa ranki hkr, wannan jarabawa ce, Allah ya bamu ikon cinyesa, akwai wanda yake rasa dukkan iyalansa ma lokaci ɗaya, ki godewa Allah ke ɗaya ce kika rasa.”
Yayi Maganar cikin sigar rarrashi da ƙarfafawaa Ummi gwiwwa shuru Ummi tayi tana ajiyar zuciya, Daddy duban Al’ameen yayi cike da so da kuma ƙauna ya miƙo masa hanu alamun yazo kusa dashi, tahowa Al’ameen yayi tare da zama suka saka Daddy a tsakiya Daddy duban Al’ameen yayi tare da cewa.
“Zaki na kaima ka sawa zuciyarka damuwa ko, ba’a san zaki da tsoro ba, kuyi tawakkalli, shine ɗabiar mumini, gacan Faruq yana cikin mota ya kasa fitowa yace bazai iya shigowa ya ganka cikin damuwa ba, maza ka sake ranka kaje wajen ɗan uwanka, ni bara naje nayi magana da DOCTOR idan ta kama kawai gara a fita da ita India domin samun ƙwararrun likitoti.”
Kansa Al’ameen ya ɗaga tare da ɗan sakin murmushi tunda abin ya faru sai yanzu Al’ameen yayi dariya.
Tashi yayi ya nufi motar da Daddy yazo, shi kuma papa da Daddy suka nufi Office ɗin doctor yayin da security suke takewa Daddy baya, koda Daddy suka samu likita ya tabbatar musu da cewa basai an fitar da Ashfat waje ba su zasu mata komai sannan sun tabbatar da cewa ƙafar da ta fitan yanzu ta daina fitar da jini, farfaɗowarta suke jira kafin su fito da ita daga ACU, sosai suka tattauna da Daddy kafin Daddy ya fito Inna Jumma bata nan itama ta koma gida, Daddy cewa yayi Ummi tazo su koma gida tabar amarya anan, shi kuwa Al’ameen hanu yasa ya buɗe motar yana zaune yayi shuru, murmushi Al’ameen yayi tare da shigowa ya zauna kafaɗar Faruq ya daka tare da cewa.
“Kai yaro wai tunanin mai kake haka ne?”
Faruq rungume Al’ameen yayi cikin farin cikin ganinsa yace.
“Oh Al’ameen, banyi zaton ganinka da murmushi ba, ya jikin Ashfat ɗin.”
Ɗan murmushin Al’ameen yayi tare da cewa.
“Ya muka iya da ƙaddara, jiki sai dai muce alhamdulillah! Amma tunda suka shiga da ita ACU bamu ganta ba.”
“Insha Allah komai zaiyi dai-dai ya kamata muje gida ka samu hutu.”
“Eh bara Daddy yazo sai mu tafi.”
Sun ɗan juma kafin Daddy yazo shida Ummi da Papa drever yaja suka tafi.
Tunda suka tafi Aunty Amarya ta saka dariya tare da ɗago wayarta layin Hajiya Mansura ta kira ringin ɗaya ta ɗaga, daga can Hajiya Mansura tace.
“Shegiyar wai ya akayi ne banji wani motsi ba, shuru ba labari.”
Amarya murmushi ta saki tare da cewa.
“Ke dai bari, yanzu ma labarin na kira na baki domin kuwa sun sha, babu wanda ya mutu cikin ukun, sai Ashfat ta ƙafarta ɗaya ta fita, hmmm yanzu me kike gani bai kamata fa ba ta farfaɗo ba, ya kamata ne ace ta shige ta can.”
Murmushi Hajiya Mansura tayi tare da cewa.
“Karkiyi wannan kuskuren, domin kuwa kuna cikin asibiti ne mai matuƙar tsaro sannan kuma dole kinsan za’a saka idanu akan Yarinyar saboda matsayin ubanta a wannan ƙasar, babu likitan da zai yadda a haɗa baki dashi domin kuwa yasan idan asiri ya tonu dashi zata juye ƙarshe ya rasa aikin sa, bama buƙatar wani a cikin wannan aikin, ki barta ta rayu a nakashe ko banza kin gurgunta mata rayuwa, aikin mu kuma kamae yadda muka fara sai mun gamasa dole ne burinmu zai cika, komai zaizo mana da sauƙi, da yamma zanzo nayi jajen dariya domin kuwa wannan itama rabin nasara ce.”
Dariya amarya tasa tare da cewa.
“Tabbas kin bani shawara mai kyau, uban gayyar ya shigo ƙasar mun masa kiran dole, kin san abun baƙin ciki baiyi tani ba, ta Gaji da yaranta yake baki ga yadda yake rarrashinta ba, kamae zai maida ta ciki, nafa ji haushi.”
Dariya Hajiya Mansura tayi tace.
“Karki damu duk zamu juyo kansu ke dai kici gaba da nuna musu kulawa cikin ruwan sanyi zamu dafa su, zagon ƙasa zamu musu, sai dai kawai suga suna afkawa rami su rasa ta ina akayi haƙar.”
Dariya amarya cike da jin daɗin mu’amala da ƙawar tata, sun juma Sosai suna kitsa tsiyarsu kafin sukayi sallama.
Tunda Umma ta tafi gidan aikinta, Ablah ke famar wankin kuɗi, itace bata gama ba sai la’asar lis duk tabi ta gaji, tana gamawa kuma ta ɗora musu tuwon dare, tana tankaɗe Hafsa ƙawarta ta shigo hanunta riƙe da ƙur’ani, kujera ta jawo ta zauna tare da cewa.
“Na fa yi zaton kin gama aikin ki, SHINE nazo muyi musaffa, kuma sai naga yanzu ne ma kika ɗaura girkin, ya akayi kika makara haka.”
Murmushi Ablah tayi tare da cewa.
“Wallahi kuwa, na yiwa Aunty Zarah wankin ta ne tun kwanansa wajen huɗu fa tunda nayi accident yake ajiye, shine nace gara kawai yau na mata.”
“Hakane, to bara na tayaki aikin naga ko wanke wanke bakiyi ba, bara na tayaki wanke wanke, amm ina Abdu cewa ban gansa ba.”
“Kinsan Abdu da son ƙwallo yana can ya tafi bugawa, Hafsa jiya nayi mummunan mafarki da wannan wanda ya kaɗenin, wai an biyosa za’a kashesa, yana ta kirana nazo na taimakesa.”
Duban Ablah Hafsa tayi tare da cewa.
“Subahanallah! To Allah ya sawwaƙa shirmen mafarki ne kawai.”
“Nima ashirmen na ɗauka, amma dai yau da safen nan sai da na masa sadaka nayi tawassali idan har akwai musibar dake bibiyarsa to Allah ya karesa ya maidawa maishi kansa.”
Ɗan dariya Hafsa tace.
“Kuma kin kyauta da kika masa sadaka tunda ko banza ai kema ya taimakeki tunda da kuɗin da suka baku kika samu zaki shiga jami’a.”
“Hakane amma badan wannan wannan na masa sadaka ba, na masa ne kawai saboda Allah da kuma ƴan uwantaka ta musulunci.”
Dariya Hafsa tayi suka ci-gaba da aikin su tare sukayi har suka gama ana kiran sallar magaruba sannan Hafsa ta tafi mussafar da basuyi ba kenan saboda aikin da ya yiwa Ablah yawa.
Umma itace bata dawo gidan ba sai 7:30 ta samu Ablah da Abdu suna ta karatu, sannu da zuwa Ablah ta mata, murmushi Umma tayi tare da zama gefen Ablah tana dubanta tace.
“Kunci abinci ko?”
“Ehh Umma munci, dama jira nake ki dawo sai na shiga na kaiwa Aunty Zarah wankin ta, na gama tun kafin na ɗaura girki.”
Murmushi Umma tayi tare da cewa.
“Oh Ablah agogo Sarkin aiki yanzu ke da baki gama warewa bane kikayi wanki, kinga yanzu dare yayi ki bari sai da safe idan Allah ya kaimu sai ki shiga ki miƙa mata.”
“To shikenan Allah ya kaimu,. Umma kin bayar da kuɗin registration ɗin nawa ne?”
Dariya Umma tayi tace.
“Sarkin gaggawa ai tun jiya na bawa Salisu, yaje ya miki, sai dai kuma kuma makarantar ne, nake ji Ablah kinsan bamu da ƙarfi karmu fara kuma karatun yazo ya gagara shine Abinda nake ta tunani, kinga kuɗin aikin nawa kwatakwata dubi shida ne suke bani a wata, bazai isa muyi uzurin rayuwa dashi kuma mu biya kuɗin makaranta ba.”
Ɗan murmushi Ablah tayi cikin ɓoye damuwarta Saboda karta karyawa mahaifiyarta gwiwwa tace.
“Umma karki damu indai Maganar kuɗin makaranta ne, Allah zaiyi wannan na registration ɗin ma, bamuyi zaton zamu samu ba, kuma sai Allah ya kawo, shima insha Allah kuɗin makarantar zamu samu mu dogara ga Allah Umma na Tabbata bazai barmu mu tozarta ba, zai kawo mana agaji.”
Murmushi Umma tayi tare da cewa.
“Hakane ABLAH Allah ya mana jagora, bara na watsa rayuwa kafin a kira Sallah.
Da to Ablah ta amsa tare da cigaba da karatun ta.
Bayan Kwana Biyu
Gabaki ɗayan su suna zaune a harabar ACU, suna jiran likita, domin kuwa yau suke saka ran farfaɗowar Ashfat, Ummi zuciyarta sai tsinkewa yake domin kuwa bata san wani irin sakamako zataji ba, shi kansa Daddy cikin tsoro yake, Al’ameen da Faruq da Haidar suma suna zaune a gefe, Aunty Amarya suna zaune ita da Aunty suma a gefe guda, Inna Jumma kuwa gagara zama tayi, likitan tunda ya shiga suke jiransa kusan awa huɗu bai fito ba, hakanna ya ƙara ɗarsawa Ummi tsoro a cikin ranta, Aunty Amarya kuwa addu’a take Allah yasa kar Ashfat ta farfaɗo burinta kawai ace ta shige ta can doguwar suman, sunan har wajen azahar likitan ya fito fuskarsa duk ta jiƙe da gumi jikinsa yayi mungun sanyi kafafunsa daƙyar suke ɗaukarsa, Daddy ne ya tashi da sauri tare da nufar DOCTOR Ummi tsabar tsoro gagara tashi tayi Daddy ne ya cewa likitan.
“Doctor ya ake ciki, ta farfaɗo kuwa?”