Numfashi likitan ya saki cikin sanyin jiki yace.
“Ta farfaɗo sai dai kuma akwai matsala gaskiya tunda ta farfaɗo take bige bige tana ƙoƙarin miƙewa, wanda hakan da take kan iya jawo mata matsala a yanzu ƙafarta guda ɗaya ce, kuma har yanzu ciwon ɗanye ne, girgiza jikinta da take kan iya sawa jini ya ɓalle, zamu fito da ita zuwa special ROOM, zaku iya zuwa ku rarrasheta, mu samu ta nutsu da alamu ta cikin firgici ne har yanzu.”
Kansa Daddy ya kaɗa yana sakin ajiyar zuciya, Ummi ma hamdala tayi da Allah yasa ƴarta ta farfaɗo, Aunty Amarya kuwa takaici taji domin kuwa bata so farfaɗowarta ba, komawa likitan yayi cikin ACU ta baya suka fitar da Ashfat zuwa word kafin aka bawa su Daddy umarnin su shiga, Inna Jumma tsabar saurin ta shiga har gudu takee, tana kwance sai famar fisge fisge take tana ihu, Ummi da sauri ta ƙarisa tare da riƙota tana sakin kuka cikin kukan take ce mata.
“Ashfat kiyi haƙuri dan Allah ki nutsu, ba fa lafiya bane dake ki tsaya karki sake dawo da ciwon baya.”
Fisgewa take daga jikin Ummi tana cigaba da ihu tana kiran.
“Ƙafata! Ina ƙafata! Banga ƙafata ƊAYA, ku sakeni na tashi, ni ku sakeni.”
Runtse idanunsa Al’ameen tare da juyar da kansa yana kallon window, Daddy ƙarasowa yayi bakin gadon tare da duban Ummi ya mata alamun ta matsa a wajen miƙewa Ummi tayi hawaye na zuba mata, zama Daddy yayi tare da saka hanu ya danne kafaɗar Ashfat da ƙarfi yanda bazata iya ƙwacewa ba, idanu ya zuba mata tare da cewa.
“Kiyi shuru nace! Kiyi shuru ki kalleni! Daddyn kine fa Ashfat dubeni kinji kalleni.”
Ashfat ƙin yin shuru tayi ta cigaba da ihu tana kiran ƙafarta, Al’ameen ihun nata sosai yake ci masa zuwa da ƙuna, jin Daddy sai Magana yake mata taƙi tayi shiru yasa Al’ameen daka mata tsawa mai sautin gaske sai zuciyar kowa ta girgiza a wajen.
“Ki mana shuru! Ki mana shuru!”
Wani irin shiɗewa Ashfat tayi tare da haɗiye kukan nata, tayi shuru sai ajiyar zuciya take, nufota Al’ameen yayi idanunsa sunyi jajur ya fara magana cikin ƙunar rai.
“An faɗa miki ke kaɗai ce kike jin zafi a cikin zuciyarki, muma zuciyarmu cike take da ƙunan abinda ya sameki Tabbas ciwon a jikinki yake amma muma muna jin zafin, meyasa bazakiyi haƙuri ba.!”
Yayi Maganar yana jawo kujerar roba tare da zama ya kamo hanun Ashfat cike da tausayawa cikin sanyin murya ya sassauto da muryar tasa tare da cigaba da cewa.
“Meyasa kike wannan ihun kike neman butulcewa ubangijinki, domin kuwa dashi kike neman kokuwa kina gwada masa cewa bazaki ɗauki wannan ƙaddarar daya aiko miki ba, haba Ashfat kin bani kunya domin kuwa koda Daddy ya fitar dake ƙasar waje ba turaki yayi kije ki karanci yahudanci ba, babu ilimin addini, EGYPT ya turaki karatu cikin Jami’ar AL’AZHAR domin ki karanci SHARI’A Wanda kuma duk wanda ya shiga wannan jami’ar musulmi ne, kuma dole ne garesa ya haddace duk wani littatafan Addini, ya kuma san ma’anar sa, anan Wajen gabaki ɗaya idan aka cire Khalifa, gabaki ɗayan mu, kin fimu ilimin addini, ban ware kaina ciki ba, domin kuwa ke gagara badau ce a fagen ƙur’ani, babu ta inda za’a iya ƙureki, kinsan Tauhidi amma a yanzu kike nuna cewa bazaki iya amfani dashi ba, meyasa kike neman kiyi faɗa da ƙaddara, ki sani wannan rashin ƙafar itace ƙaddararki, kamar yadda bazaki iya kaucewa mutuwarki ba, to itama wannan bazaki iya kauce mata ba, ana riƙeki kina ƙwacewa zaki tashi, idan har aka barki kika tashi, sai kinfi kowa cutuwa, domin kuwa ƙafarki tabar gangar jikinki duk ihu da ƙarajinki bazai dawo miki da ita ba, ki dubi Ummi tun da kikayi wannan haɗarin kuka take bata daina ba, tana ta miki addu’ar ki farfaɗo ta rayu dake koda babu ƙafar, sanda akace kin farka sai taji farin ciki har murmushi sai da tayi, amma yanzu ki duba ihun da kike ya dawo mata da hawayenta, meyasa bazakiyi haƙuri kici jarabawar nan ba?”
Tunda ya fara Maganar kowa ya nutsu ya sanya masa ido, Faruq kusa dashi ya tsaya tare da dafa kafaɗarsa, Ashfat Ummi ta kalla cikin sanyin jiki, tare da duban dungulmin ƙafarta idanunta na zubar da hawaye, cikin rawar murya tace.
“Na yadda da ƙaddara Ya Al’ameen, sai dai ina ihu da takaicin na dawo nakasasshiya wacce ba komai zan iya amfanawa kaina ba, abubuwa da yawa a yanzu bazan iya su, ba komai zan iyarwa kaina ba, rayuwata ta duƙushe na zamo tamkar marar amfan…”
Saurin saka hanu yayi ya toshe mata baki yana girgiza mata kai tare da cewa.
“NAKASA BA KASAWA BACE saboda kin rasa ƙafa ɗaya bashi ke nuna komai naki ya tsaya ba, da wannan ƙafar taki guda ɗayan zaki cika dukkan burin Rayuwarki babu abinda zai sauya daga ƙudirinki, cikar buri a zuciya yake ba’a ƙafa, ki godewa Allah a bisa jarabawar daya miki, shi kuma sai ya taimakeki, Ashfat burinki na rayuwa zai cika, zakiyi alfahari da kanki muma zamuyi alfahari dake, haka duniya ma zasuyi alfahari dake ki sani fa ke ƴar gata ce gaba da baya, ga Umminki ga kuma Uwar mu mai jin ƙanmu wacce bata ƙaunar kukan mu, Aunty Amarya ga kuma Daddy, ga yayunki Faruq Haidar da sauran ƴan uwa na Tabbata bazasu taɓa bari ki tozarta ba.”
Kanta ta jinjina sai yanzu zuciyarta ta ɗan samu nutsuwa da jin maganganun yayan nata, murmushi mai haɗe da kuka tayi tare da cewa.
“Bazan kuma kuka ba daga yanzu na rungumi ƙaddarata, sai dai Ya Al’ameen bana son zaman Nigeria, Please a maidani Egypt zamana anan zai dinga sani cikin damuwa na tsani Nigeria bana son zama a cikin ta.”
Bakinsa ya cije tare da ɗan sakin murmushi yace.
“Karki damu zaki koma Egypt insha Allah da zarar kin warke ko dan karatunki ma.”
Kanta ta kaɗa tare da kwanciya jikin Daddy tayi shuru tana ajiyar zuciya, kowa yaji daɗin yadda Al’ameen ya sawa ƴar Uwar tasa tawakalli tare da ƙarfafa mata gwiwwa, tashi yayi yana kama hanun faruq suka fita waje tare da tambayarsa ina Haidar, shima kansa Faruq yau tun safe bai haɗa idanunsa dana Haidar ba, kansa Al’ameen ya kaɗa tare da cewa.
“Okay muje ka rakani faculty area ina son haɗuwa da NAJIB.”
Tashi Faruq yayi suka shiga mota tare da ficewa daga asibitin basu juma da fita ba sai ga Haidar ya shigo shida Nafeesa tazo ta gaida ta, tare suka shiga da sallama Aunty Amarya ce ta amsa tana sakin murmushi tace.
“Haidar kaine tafe.”
Kansa ya ɗaga tare da ƙarasawa kusa da Daddy, ya gaishesa gabaki ɗaya gaishe su yayi, Nafeesa dake tsaye kanta sunkuye ne ta sunkuya har ƙasa ta gaishe su tare da musu ya jiki fuskarta ɗaure da niƙab, babu abinda ake hangowa sai idanunta, Aunty Amarya ce tace.
“Haidar waye wannan?”
Murmushi yayi tare da ce mata.
“Ƙawata ce, kishiyar Inna Jumma idan Allah ya amince.”
Ummi ne ta saki murmushi tare da cewa Nafeesa.
“Ayya ki ƙaraso ki zauna anan ko ƴata.”
Cike da nuna kunya Nafeesa ta ƙariso kusa da Ummi ta zauna, Daddy tashi yayi ya fita ba tare da yace komai ba, Inna Jummo ce ta matso kusa da Nafeesa tana saka hanu ta ranƙwasheta cikin zolaya take cewa.
“Au waike nan mijin nawa zaki ƙwace ai kuwa kinyi kaɗan ɗamararki ma tayi ƙarama, domin kuwa tsaye nake da ƙafafuwana ƙyam, idan har kinga kin ƙwace wannan ɗan ƙwal uban Aliyu a hanuna sai kinyi babban shiri, ke tsabar tsoro ma ɓoye fuskarki kikayi, ko dai na fiki kyau ne shiyasa kike tsoron buɗe fuskar.”
Dukka wajen dariya akayi, ita dai Nafeesa kanta na ƙasa taƙi tayi Magana ga hijabi har ƙasa, Haidar ne yace.
“A’a fa Inna Jumma, waya faɗa miki yanzu ana yayinki ai kin riga da kin zama cus yanzu ƴan saffa ake yayi irinta ba irinki ba.”
Murmushi Ummi tayi tare da cewa.
“Yauwa shikenan ma ka ramawa ƴata.”
Inna Jumma dariya tayi tace.
“Oh halin mazan zaka nuna min kenan, to ai shikenan zakazo ka sameni nikam zanyi maganinka.”
Dariya Haidar yayi tare da cewa.
“Taki akeji, Ina Al’ameen ne Ummi.?”
Yayiwa Ummi tambayar yana kallon ta.
“Yanzu dai ya fita shida Faruq bansan inda suka nufa ba, ka kirasa mana.”
Wayarsa Haidar ya ciro tare da kiran Al’ameen a waya, suna tsama da tafiya yaji ringin ɗin wayarsa, ɗagawa yayi tare da cewa.
“Ya akayi Haidar kan Company ne?”
Daga can Haidar yace.
“Ina asibiti yanzu haka, na kawo Nafeesa ne ta duba jikin Ashfat wai da so nake ku gaisa da ita.”
Murmushi Al’ameen yayi tare da cewa.
“Kace mata na gode ina inda bazai yiwu na juyo ba saboda ita, Ashfat tazo dubawa bani ba, so meye kuma zakace sai mun gaisa, bana buƙatar haɗuwa da ita.”
Yayi Maganar yana katse wayar tare da duban Faruq dake dreving yace.
“Kaji wani shirmen banza, wai da budurwarsa zamu gaisa nazo, ko meye haɗina da ita oho.”
Murmushi Faruq yayi kansa na titi yace.
“Bai kamata ka masa magana a haka ba, bazaiji daɗi ba, na rasa meke damunka game da mata kai baka son kulasu, sannan kuma kace wani ma karya kulasu, ya dai kamata a nema maka magani da alamu aljana ta aureka.”
Tsuka Al’ameen yaja tare da cewa.
“Kana iya nema min maganin sai ka ɗauki ɗamarar ɗura min ɗan rainin wayo.”
Dariya Faruq yasa yana juyowa ya kalli Al’ameen zai Magana Al’ameen idanunsa suka sauƙa akanta ta shigo tsakiyar titi, zaro idanunsa yayi tare da saurin saka ƙafarsa ya taka burki, shima Faruq saurin juyawa yayi yana tsayar da motar, cikin huci Al’ameen ke kallon bayan Yarinyar, buɗe motar yayi ya fito a fusace tare da shan gabanta, ya ɗaga hanu zai ɗauketa da mari, ta ɗago kanta cike da munguwar mamaki ya sauƙe hanunsa ƙasa yana jefa mata mungun kallo yace.
“Kece!”
Itama Ablah cikin tsoro taja baya tana kallon sa, Faruq parking yayi a gefen hanya tare da fitowa ganin suna tsaye tsakiyar titi har sun fara haɗa go slow, ya nufo su, kanta ta sunkuyar ƙasa zatayi Magana taji ya fisgi hanunta da ƙarfi tare da jawo ta, kayan wankin dake hanunta yayi wurgi dashi gefe, ya fisgota Faruq idanunsa ya zaro cikin mamaki yana kallon ina Al’ameen zai Kaita bisa mamakinsa sai yaga ya buɗe mota ya wurgata tare da rufe murfin motar da ƙarfi ya zagaya ya shiga gaba, da sauri Faruq shima ya shiga bakinsa buɗe yake kallon Al’ameen, motar yaja da ƙarfi tare da juyawa yayi baya, Figar motar yayi da ƙarfi, ransa a matuƙar ɓace, ita kuwa Ablah cike da zaro ta zaro idanunta, zuciyarta sai famar tsinkewa take, hawaye kuwa sosai ya fara gudu a kuncinta, Faruq ne yace.
“Wai meye hakane Al’ameen, ya zaka jawo ƴar mutane cikin mota ba tare da kasan waye ita ba, duba fa kaga yanda kake gudu damu akan titi, kashemu zakayi ne, ka dakata ka sauƙe ƴar mutane!”
Banza Al’ameen ya masa tamkar bada shi yake Magana ba, Ablah fashewa tayi da kuka juyowa Faruq yayi ya kalleta sosai ta basa tausayi, ƙara duban Al’ameen yayi tare da cewa.
“Al’ameen Magana fa nake maka, wai bazaka tsaya bane?”
Wani irin wawan parking Al’ameen yayi tare ɗago jajayen idanunsa ya kalli Faruq cikin tsawa yace masa.
“Fita min daga mota!”
Cike da mamaki ya kallesa yanda jijiyoyin kansa suka tashi tsabar masifa, muryar Al’ameen ne ta kuma dukan kunnen Faruq.
“Ka fita min daga mota nace maka! Idan kuma bazaka fita ba, to karka kuma min Magana ka dameni akan wannan fitinanniyar ƴar neman masifar!”
Shuru Faruq yayi har yanzu mamakin Al’ameen yake kansa ya kawar gefe bai kuma ce masa komai ba, Al’ameen motar yaja ita kuwa Ablah sai famar kuka take, shi dai Faruq idanu ya zuba masa yana kallon ikon Allah.
Al’ameen babu inda ya tsaya sai cikin asibiti, motarsa na shigowa ta Haidar na fita, still suka kuma yin saɓani, motar ya buɗe bayan yayi parking tare da buɗe bayan ya fisgota da ƙarfi, jawo hanunta yayi Faruq yabi bayansu babu inda Al’ameen ya tsaya sai room ɗin da Ashfat take Ummi Daddy Inna Jumma Aunty Amarya sai Aunty suna zaune suka ga an wurgo mutum tsakiyarsu, kanta ne ya gwaru da jikin gadon da Ashfat ke kwance, wani irin kuka Ablah ta saka mai shiga zuciya, Tabbas yau an wulaƙanta rayuwarta wulaƙanci mafi muni, kowa dake cikin ROOM ɗin sai daya ɗago kai ya kalli Al’ameen, Daddy miƙewa tsaye yayi yana cewa.
“Subahanallah Zakina me zan gani haka, waye wannan ɗin meta maka haka?”
Daddy ya jefa masa tambayar yana riƙe kafaɗarsa alamun cool down, Inna Jumma kuwa saurin riƙo Ablah tayi tare da jin zafin wurgota da Al’ameen tayi miƙewa Inna Jumma tayi cikin ɓacin rai ta ɗauke Al’ameen da mari tana nuna sa da yatsa tace.
“Dabba ka ɗauko ne, da zaka wurgota kamar mage, kana da hankali kuwa, ka wurgo ɗan Adam haka ka duba yanda ka kumbura mata goshi, kai kuma Amadu tsabar rashin son gaskiya da nuna masa komai yayi dai-dai ne, zaka wani riƙosa kana masa magana cikin rarrashi, ita bata da gata ne, ko shi kaɗai ne mai gata.”
Tayi Maganar cikin ɓacin rai, Al’ameen idanunsa ya runtse tare da dafe fuskarsa abinda Inna Jumma bata taɓa masa ba kenan mari sai yau akan wannan jakar, Daddy shuru yayi gudun yayi magana ran mahaifiyar tasa ya ɓaci, Ummi ce ta miƙe tare da ɗago Ablah dake kuka ta rungumeta a jikinta, duban Al’ameen tayi cikin ɓacin rai tace.
“Waye ita! Na ce waye ita! Meta maka da tsabar rashin kunya zaka jawota har gaban mu ka cimata mutunci!”
Kallon Faruq yayi, yayinda Faruq ya kawar da kansa gefe alamun babu ruwana, shima shuru yayi yana huci, Ummi tsawa ta daka masa tare da cewa.
“Ba magana nake maka ba Al’ameen kamin banza.”
Nuna Ablah yayi da yatsa tare da cewa.
“Ni fa ba wulaƙanta ta, nayi ba, na kawota wannan asibitin ne a gwada ƙwaƙwalwar ta, domin kuwa ina zargin mahaukaciya ce, domin kuwa tana bibiyar rayuwata da sharri da kuma masifa, burinta kawai shine taga na afka cikin masifa.”
Ga baki daya wajen zaro idanunsu sukayi Aunty Amarya ce tace.
“Masifa kuma, kamar yaya bamu fahimci maganarka ba.”
Cire hanun Daddy yayi daga kafaɗarsa tare da zuwa gaban Aunty Amarya yace.
“Bayan Daddy ke kaɗaice zaki fahimce ni, wannan Yarinyar da kuke gani masifa ce.”
Saurin ɗago idanunta Ablah tayi cike da jin zafin maganar sa, (masifa ce mahaukaciya ce, mai sharri ce) ta furta kalmar cikin zuciyarta duk ita kaɗai ya alaƙanta da waɗannan mugayen kalmomin, Aunty Amarya ce masa tayi.
“Naji masifar me ta jawo maka, meya haɗaka da ita shi muke son ji.”
Iska mai zafi ya fesar daga bakin sa tare da cigaba da cewa.
“Aunty Amarya wannan Yarinya sau biyu tana shiga Mota ta tsaya a tsakiyar titi da gangan saboda na bigeta ta jawo min sharri, tamin ɗaya tamin biyu, to shine nace bazan bari tamin na Uku ba, gara a fara duba min ƙwaƙwalwar ta, kafin na hukuntata.”
Murmushi Daddy yayi jin shirmen Al’ameen kansa ya kaɗa Aunty Amarya zatayi Magana Daddy ya ɗaga mata hanu tare da kama hanun Al’ameen ya fice dashi, Ummi ne tayi ajiyar zuciya tare da cewa.
“Wannan shine ma mahaukacin.”
Ablah ta kalla tare da share mata hawayen fuskarta, haka kawai taji Yarinyar ta kwanta mata a ranta, hanu tasa ta share mata hawayen tare da cewa.
“Kiyi haƙuri kinji ƴan mata, dan Allah kiyi haƙuri haka yake zafin zuciya garesa kar maganganunsa susa ranki shi ɓaci, haka yanayinsa yake harta ga ƙannensa ma hakan yake musu menene sunan ki.”
Shuru Ablah tayi tana sakin ajiyar zuciya, Aunty Amarya haka kawai taji ita sam Yarinyar bata kwanta mata a ranta ba, asali ma ji take tamkar zuciyarta na tsinkewa daga shigowar Yarinyar, Ablah kanta ta ɗagawa Ummi cikin sanyin murya tace.
“Sunana ABLAH, ba komai Mama ya wuce.”
Murmushi Ummi tayi cike da jin daɗi, Inna Jumma ne tayi dariya tare da zama gefen su ta shafo kan Ablah tace.
“Kunga yariyar kirki ko wacce ta fito daga gidan mutunci, harta haƙura.”
Tayi Maganar tana kama hanun Ablah tace.
“Tashi muje can wajen muyi magana shalelena.”
Tashi tayi tsaye tare da bin Inna Jumma, a gefe suka zauna Ablah kanta yana ƙasa,
Inna Jumma murmushi tayi tare da cewa.
“Menene sunan ki Shalele na?”
A hankali ta amsa da.
“Ablah!”
“Masha Allah tambayanki zanyi Shalelena dan Allah ki faɗa min gaskiya kinji.”
Kanta Ablah ta ɗaga tare da amsawa da to.
“Da gaske ne kin shiga tsakiyar titi da gangan domin kuwa nasan Aminu baya ƙarya, asali ma baya shiga harkar wani koda ƴan uwansa ne.”
Ɗago kanta Ablah tayi idanunta na cikowa da hawaye tace.
“A’a kaka ban shiga tsakiyar titi Saboda ya bigeni ba, Kaka ina da hankali fa ta yaya zan shiga titi domin na cutar da rayuwata, Wallahi kaka, Ranar daya bigeni, bana cikin nutsuwata, naje shago na sayowa ƙanina garin rogo, ina sauri zan koma na haɗa masa kafin ya dawo daga makaranta, karya dawo da yunwa Saboda babu abinda ya samu yaci haka ya tafi Makaranta, kuma na duba hanya kafin na shiga, sai dai ban kula da hanun damana sosai ba, shine ya bigeni, sannan kaka yau kuma na duba hanya na shiga, amma wallahi ban ankara ba, sai jin ƙarar motarsa nayi shine ya jawo ni ya kawoni nan, ni yanzu tashin hankali na ma kayan wankin Aunty Hafsa daya wurgar min a wajen bansan ya zanyi ba idan suka ɓata.”
Numfashi Inna Jumma tayi cike da tausayin Yarinyar domin kuwa daga ganinta macece mai kwancaccen hali, cewa tayi.
“Na yadda dake Shalelena amma ki daina kirana da kaka ki kirani da Inna Jumma kamar yadda jikokina suke kirana, kiyi haƙuri da abinda Aminu ya miki, insha Allah bazai kuma ba zan masa faɗa, sannan naji kin kira ƙaninki, shin baki da mahaifiya ne.”?
“Ina da mahaifiya, Mahaifi ne bani dashi.”
Cikin tausayi Inna Jumma tace.
“Allah sarki ashe ke marainiyace, to amma mamanku ke ciyar daku kenan, sana’ar me kuke yi tunda baku da mahaifi.”
Hawayen idanunta Ablah ta goge tare da cewa.
“Mamana ke ciyar damu komai itace take mana, mamana tana aikatau ni kuma ina wankin kuɗi dashi muke rufawa kanmu asiri.”
Inna Jumma sarkin tausayi cike da tsantsar tausayin su tace.
“To amma baku da Baffa ne ma’ana wan mahaifi da bazai ɗauki ɗawainiyarku ba.”
Girgiza kanta Ablah tayi tare da cewa.
“Bamu da kowa sai Umman mu, bamu san wasu dangi ba, har yau Umma taƙi ce mana komai game da dangin mu, sai dai tana ce mana da ita da mahaifin mu, ba ƴan Nigeria bane ƴan Niger ne buzaye, bayan nan bata ce mana KOMAI ba.”
Shuru Inna Jumma tayi sai can tace.
“Hmmm! Rayuwarku abar tausayi ce, duk sanda akace Uwa itace ke ɗaukar ɗawainiyar da Uba ne ya kamata yayisa to Tabbas wannan Uwar abar a jinjina mata ne, Ablah ki bani numbern wayar mamanki, zanyi Magana da ita, insha Allah da zarar an sallame mu daga wannan asibitin zanzo har gidan ku, amma Ablah zakiyi aiki a gidan mu.”
Ɗago idanunta Ablah tayi tare da cewa.
“Ni makaranta zan cigaba, bazai yiwu nayi aiki ba.”
Murmushi Inna Jumma tayi tare da cewa.
“Bafa wani tsanantaccen aikin da zai hanaki karatu zakiyi ba, aikin da zakiyi bazai hanaki karatu ba, ni da kaina zan ɗauki nauyin karatunki kiyi tunani kuma nima zan nemi mahaifiyar ki.
Jinjina kanta Ablah tayi sun ɗan juma suna tattaunawa da Inna Jumma, kafin tasa drever ya ɗauki Ablah ya Kaita wannan titin ta duba kayanta sannan ya maidata gida, dubu goma Ummi ta bata tare da bata hkr sosai akan abinda Al’ameen ya mata.
Koda Al’ameen suka fita waje da Daddy Sosai ya masa faɗa tare da nuna masa abinda yayi sam bai kyauta ba, shi kam Faruq sosai abinda Al’ameen yayiwa Ablah ya basa mamaki domin kuwa baisan Al’ameen da wulaƙanta mutum ba, koda ya sanar da Haidar ma baiyi mamaki ba Domin kuwa a gabansa akayi na farko.
Kwanan Ashfat shida a asibitin yayin da jikin ta keta samun sauƙi haka kuma ta sawa zuciyarta haƙuri, su Ummi duk sun koma gida Aunty Amarya kawai aka bari a wajenta take kula da ita, haka kuwa take kula da ita tamkar yadda Ummi zata kula da ita, Daddy Sosai yake jin daɗin yanda Aunty Amarya ke kula da yaransa tamkar itace ta haifesu babu mugunta ko baƙin hali rayuwa take dasu da zuciya ɗaya wannan dalilin yasa Daddy ke matuƙar ƙaunar ta, kowa a gidan ƙaunar Aunty Amarya yake mussaman Al’ameen, yafi kowa shaƙuwa da ita, haka rayuwa ta dinga tafiya jikin Ashfat na samu sauƙi.
Lamarin Haidar kuwa da Nafeesa sosai Soyayya da shaƙuwa yayi ƙarfi tsakanin su, inda Haidar yake jinta tamkar rayuwarsa, a yayin da ita kuwa Nafeesa take son kuɗinsa, yana kuma sake mata kuɗi sosai duk abinda ta nema yana bata, harta gidan da ta roƙa da sunan ƙanwar mamanta ya saya musu, sosai suke tatsarsa a yayin daya gama yarda cewa Nafeesa Auren sa zatayi.
A gefe guda kuma har yanzu Rufaida ta gagara sauraron wani saurayi, ita dai Haidar take so, wanda take masa son maso wani hausawa sukace ƙoshin wahala, Inna Jumma ta kira Umma mahaifiyar Ablah kamar yadda tayi alƙawari sun tattauna sosai, takan kiranta duk bayan kwana biyu har shaƙuwa ta ɗan shiga tsakanin su, Inna Jumma har yanzu tana da ƙudirin dawo da Ablah cikin gidan AMBASSADOR AHMAD GIWA.
Watan Ashfat ɗaya da sati ɗaya aka basu Sallama yayin da sosai jikinta ya samu sauƙi, likitocin sun bata sanda ɗaya, wanda shine zai kasance a madadin ƙafarta ɗaya, koda suka dawo Aunty Amarya tsabar iya kissa da munafurci, ɗakinta ta ajiye Ashfat take kulawa da ita.
Naji dadin kasan cewa daku
Masha allah allah ya