Skip to content
Part 15 of 67 in the Series Aminaina Ko Ita? by Rasheedat Usman

“Na fahimta amma Hajiya Mansura kina ganin babu wata matsalar da za’a samu idan sukaci gubar bana son bincike ya biyo kaina ne ko zargi.”

“Ta yaya bincike zai biyo kanki, haba Amarya wai kin manta yardar dake tsakanin kune, wallahi ko kusa bazasu taɓa tunanin zarginki ba, domin kuwa sunyi imani da cewa bazaki taɓa bari wani ya cucesu ba bare kuma ke, zargin su zai ƙare ne kawai iya kan ƴan aiki, wanda mu kuma bamu da matsala da hakan muddun burin mu ya cika.”

“Hakane nasan bazasu zargeni ba, amma dole tsoro da waswasi zai shiga zuciyar kowa daga nan zasu ankara su fara saka idanu akan lamuran gidan, kinga kuwa hakan zaisa su fara ƙoƙarin gano Ni, wanda ni kuma bana buƙatar su san asalin koni wacece nafi so mu rabu da kowa a cikin su yana min kallon ta kirki.”

“Hmmm amarya kenan farar kura uwar tsoro, ba dai kin yadda da ni ba, haka kuma ban taɓa baki kunya ba.”

Ɗaga kanta Aunty Amarya tayi alamun eh, murmushi Hajiya Mansura tayi tare da cewa.
“Good to ki amince da wannan ma, domin kuwa zata miki kyau.”

Murmushi Aunty Amarya tayi tare da ɗago hanunta suka tafa da Hajiya Mansura, amarya cewa tayi.

“Na yarda dake ƙawata kuma na amince da shawararki.”

“Ko ke fa, abu ne zamuyi shi na nutsuwa da taka tsantsan, yanzu dai ki bari a kwana biyu kafin mu fara aikin, amm jiya Goggo Hali ta kirani wai ta kira layinki baya tafiya, kuɗi take so 30k wai Zainab ta haihu zatayi mata kayan fitar suna, abinda ma ya kawo ni kenan yanzu.”

“Okay ba damuwa zan karɓi account numbern Zainab ɗin zan tura mata, nima ina so insha Allah zanje na mata barka.”

“Eh to ya kamata kam gaskiya, ni kinga bara naje yanzu ma haka zanje gidan Hajiya mariya ne zamu fita.”

Tayi Maganar tana miƙewa tare suka fito da Aunty Amarya, Inna Jumma bata nan ta shige bedroom ɗinta sai Ummi da Ashfat kawai ke zaune, Hajiya Mansura cewa Ummi tayi.

“Hajiya gaji bara na gudu, ina Inna, mu ƙarisa zancen Inna tana son nayi Aure bata san kuma Alhaji Abba yafi ƙarfi na ba.”

Dariya Ummi tayi tare da cewa.

“Mace ai bata fin ƙarfin NAMIJI Hajiya Mansura, ke dai sai dai idan baki sonsa, amma dai kika faɗawa Inna haka zaki sha faɗa.”

“Ai kuwa tunda bata kusa guduwa zan idan na tafi na kira ta anjuma nace tayi hkr na manta.”

Tayi Maganar tana shigewa da sauri cikin dariya, murmushi Ummi tayi Aunty Amarya tabi bayan ta.

Yau tun fitar Al’ameen daga gidan tun safe bai samu ya dawo ba sai 8:30 na dare kasancewar aiki daya masa yawa a Office, koda ya dawo bedroom ɗinsa ya shige a gajiye tollet ya shige tare da sakewa kansa ruwan ɗumi ya juma sosai tsaye ruwan yana ratsa jikinsa kafin yayi wankan ya fito ɗaure da towel tsabar gajiyar da ta damesa, body spray kawai ya fesawa jikinsa tare da sanya wando boxer da tshed ya faɗa saman makeken gadonsa yana lumshe idanunsa, wani irin ganda ne yake jin yana ratsa gaɓoɓin jikinsa, shuru yayi tare da lumshe idanunsa, can ya jawo wayarsa numbern Afnan ya kira tana ɗagawa yace ta kawo masa lipton, ya katse kiran, babu jumawa kuwa sai ga Afnan da lipton ɗin, ta ijiye masa a table ɗin dake gefen bed ɗin kwalin sugar ta ɗauko ta jefa masa guda biyu kasancewar tasan yadda yake so.

“Ga lipton ɗin Ya Al’ameen.”

Kansa ya ɗaga mata alamun to ba tare daya mata Magana ba, ta fice abinta, tashi yayi ya ɗauki lipton yana sha a hankali.

Inna Jumma da Ablah kuwa har sun ɗan saba tun da sukayi sallar isha’i suke fira, sai tara Inna Jumma ta fita falo, Aunty Amarya bata nan tana bedroom ɗin Daddy kasancewar itace take dashi, Ummi da Maimu ne sai ihsan kawai suke zaune, duban ihsan Inna Jumma tayi tare da cewa.

“Ke ihsan jeki cewa Daddyn ku ina kiransa maza.”

Tashi ihsan tayi ta haura sama da gudu, duban Ummi tayi tare da cewa.
“Idan ya fito ina ɗakina kuzo dukkan ku har amarya da yaran naku ku sameni.”

“To shikenan Inna”

Ummi ya amsa Inna Jumma ta koma room ɗin nata, haka kuwa akayi Daddy jin kiran mahaifiyarsa ya sashi tashi cikin gaggawa ya nufi bedroom Inna Jumma, ya taradda ita a falon ta, suna zaune a tsakiyar kafet ita da Ablah, gefe Daddy ya samu ya zauna tare da cewa.

“Barka da hutawa Inna.”

“Yawwa barka Amadu, ina iyalan naka da nace kuzo tare.?”

“Suna zuwa yanzu insha Allah.”

Ablah ce ta rusuna kanta tare da cewa Daddy.

“Ina wuni.”

Murmushi Daddy yayi tare da amsawa da.

“Lafiya Alhamdulillah! Yarinya.”

Ya amsa mata yana kallon ta cike da yabawa da tarbiyyar Yarinyar, su Ummi ne suka shigo tare da Aunty Amarya da su Maimu har Khalipa da Afnan, zama sukayi gefen iyayen su, Inna Jumma ne tayi gyaran murya tare da cewa Daddy.

“Amadu ga yarinya na ɗaukota daga gidan iyayen ta, Saboda yabawa da nayi da tarbiyyar ta, zata dinga mana ƙaramin aiki, zan haɗata da Ladiyo sai su dinga girki tare, ko kuma su dinga shiften ɗin girkin na kuma yanke shawarar cewa zaka dinga biyanta 50k a wata.”

Numfashi Daddy ya saki tare da cewa Inna Jumma.

“Inna duk abinda kika yanke a cikin gidan nan bani da ja dashi, ba damuwa Allah ya bamu ikon riƙeta.”

Da ameen Inna Jumma ta amsa tana saka masa albarka kafin ta maida dubanta gasu Ummi tace.

“Gaji ke da Amarya kun daiji abinda nace duk da bani da shakku daku, sai dai ke Afnan kece zanyiwa karariya domin kuwa kece baki da mutunci, kin dai ga wannan Yarinyar Magana ma bata dameta ba, to wallahi karki kuskura kice zaki sakata a gaba a cikin gidan idan kika sata a gaba to wallahi nima zan saki a gaba, domin kuwa zan iya ɓatawa da kowa a cikin gidan nan akan wannan baiwar Allah, ina shima babban shegen yake Aminu na masa kashedi domin kuwa nasan dashi zamu samu matsala.”

Tura bakinta Afnan tayi tare da cewa Inna Jumma.

“Harkar waye kikaga ina shiga a cikin gidan da zaki zageni, ko ƴan uwana Kinga ina shiga harkar su ne bare kuma wata can ƴar aiki.”

Tayi Maganar tana miƙewa tabar wajen, Ummi murmushi tayi kasancewar dama tasan Afnan da Inna Jumma sun saba tace.

“Al’ameen yana bedroom ɗinsa da alamu baya jin daɗi ne maybe shiyasa bai fito ba, dan ko abinci bai ciba.”

“Zai fito ne ya sameni dan wallahi dole na masa gargaɗi, sannan Aminu wancan bedroom ɗin na gefen nawa anan wannan Yarinyar zata zauna bazata boss cutter ba.”

“Nifa Inna duk abinda kikace dai-dai ne bani da ja akai.”

“Okay shikenan zaka iya tafiya, kuma zaku iya naku tafiyar dama abinda yasa na tara ku kenan.”

Ummi da Aunty Amarya da take jefawa Ablah mungun kallo ne suka tashi tare da ficewa, Daddy da ihsan ne suka tsaya, Daddy ya ɗan juma tare da Inna Jumma suna hira har kusan goma sannan ya tafi, a ranar tare Inna Jumma suka kwana da Ablah a room ɗinta da niyyar da safe sai a sharewa Ablah nata room ɗin ta koma.

Washegari da sassafe Aunty Amarya ta shigo room ɗin Inna Jumma,bata nan tana tollet sai Ablah dake zaune tana karatun Alkur’ani, taɓe bakinta Aunty Amarya tayi tare da cewa.

“Keee!”

Ɗago kanta Ablah tayi ta kalli Aunty Amarya cikin girmamawa tace.

“Ina kwana Aunty.”

Aunty Amarya bata amsa gaisuwar ta ba, tace.

“Zaman me kike har yanzu baki fito kin fara aikin ki, ba, ko kin manta da aikin aka kawo ki, to daga yau daga kinyi sallar asuba zaki fito kitchen ki fara haɗawa ihsan breakfast da zata shige dashi school, sannan kizo kiyi na gida duka, maza ki tashi kije ki samu Ladiyo ta nuna miki tsarin aikin.”

Kanta Ablah ta sunkuyar ƙasa tare da cewa.

“To Aunty, bansan Ladiyon ba amma.”

“Ladiyo tana kitchen muje na nuna miki kitchen ɗin ki sameta.

Da to Ablah ta amsa tare da rufe ƙur’anin ta ijiye miƙewa tayi tabi bayan Aunty Amarya, har kitchen Ladiyo suka samu tana fere dankali, cikin rusunawa ta gaishe da Aunty Amarya, Aunty Amarya cewa Ladiyo tayi.

“Ladiyo maza ijiye firar nan, ki bawa wannan tayi, duk wani aiki da zakiyi yau wannan itace zatayi, ban yadda ki ɗaga koda tsinke bane, daga nan har sati biyu, itace zatayi aiki, abinda zakiyi kawai shine ki dinga nuna mata yanda abubuwan suke, saboda karta mana shirme da alamu daga gidan matsiyatan talakawa ta fito, bata iya amfani da gas ba, kibi a hankali karta tayar mana da wuta.”

Kanta Ladiyo ta ɗaga ta amsa da to, ita kuwa Ablah runtse idanunta tayi cike da jin zafin maganganun Aunty , kallon Ablah Aunty Amarya tayi ta ce.

“Ke kuma ki tabbatar kinyi komai da kula idan ba haka ba, zaman ki gajere zai kasance a cikin gidan nan.”

Tayi Maganar tana ficewa, Ladiyo hanun Ablah ta jawo tare da cewa.

“Kiyi hkr da maganganunta, bansan meyasa take miki Magana da zafi ba, domin kuwa tana da kirki amma ke naga kamar jininku baizo ɗaya ba, yanzu ki fere dankalin kafin muje aiki na gaba.”

Murmushi Ablah ta saki ba tare da tayi Magana ba haka ko a fuska bata nunawa Ladiyo tamkar bataji zafin abinda Aunty Amarya ta mata ba, ta hau fere da dankalin cike da rashin nuna damuwa, cikin ƙanƙanin lokaci suka kammala breakfast ɗin, dankali da ƙwai suka soya sai dafaffen ƙwai guda biyu na Al’ameen wanda ya zamo masa al’ada duk wayewar gari sai yaci dafaffen ƙwai, kunun gyaɗa mai kyau suka damawa Inna Jumma tare da soya mata ƙosai sai kuma ruwan lipton da suka dafa wanda yaji citta da kanunfari da na’ana’a, a daining suka jere shaf Ablah ta mata da wannan ƙwai guda biyu da ta dafa na Al’ameen a kitchen ɗin, a cikin kitchen ɗin suka ci nasu abincin ita da Ladiyo sannan ta koma bedroom ɗin Inna Jumma, tana zaune ta sameta, gaisheta Ablah tayi, Inna Jumma ta ce ta shige tollet tayi wanka, haka kuma akayi ta shiga tayi wanka ta.

Misalin sha ɗaya dai-dai kowa ya hallara a daining ɗin kasancewar yau babu aiki asabar sai Al’ameen kawai da bai sauko ba, Maimu ne tayi seving ɗin kowa itama Inna Jumma ta fito, yayin da tabar Ablah a bedroom ɗinta, Inna Jumma da Daddy Sosai kunu da ƙosan da Ablah ta musu ya tafi dasu Daddy gagara haƙuri yayi sai da ya dubi Aunty Amarya yace.

“Amarya, amma kece da kanki kika dama wannan kunun, na juma bansha kunun daya min daɗi irin wannan ba.”

Tuno da Ablah ce tayi yasa Aunty Amarya haɗa fuska tare da jin baƙin cikin yabon kunun da Daddy yayi taso ace Ablah tayi kuskure, waskewa tayi tare da sakin murmushi cikin kissa da makirci tace.

“A’a Daddyn Al’ameen bani bace nayi, Ablah ce Yarinyar da Inna ta kawo, gaskiya dai Inna ta iya zaɓe yanda Yarinyar take da hankali haka kuma ta iya komai a rayuwarta.”

Afnan ce tace

“Daddy ai da kasha wannan tea ɗin to fa da kaji banbanci da na ko wanne rana, yayi daɗi sosai ba’a taɓa haɗa tea mai daɗinsa a cikin gidan nan ba, gaskiya girkinta na mussaman ne.”

Murmushi Daddy yayi tare da cewa.

“Lallai kuwa ƴar Inna ta amshi yabo yau, dama waya faɗa muku mamana zatayi zaɓen tumun dare.”

Dukkan su dariya sukayi har Ummi, Inna Jumma ce tace.

“To an faɗa muku niɗin ta wasa ce, Wai ko dai ma a saka muku waiji ne, domin kuwa da alamu dukkan ku, kun tafi santi.”

Ummi ce tayi dariya tare da cewa.

“Gaskiya dai kam Inna mussaman ma ni Yanda kunu da ƙosan nan ya tafi dani idan babu waiji gaskiya za’a samu matsala.”

Tayi Maganar suna dariya, cike da raha cikin farin ciki suka kammala breakfast ɗin nasu, Daddy bai juma ba a wajen ya fice, itama dai Ummi bedroom ɗinta ta koma, haka Inna Jumma, ya saura a falon daga Aunty Amarya sai su Afnan da Maimu da kuma ihsan.

Misalin 12:00am dai-dai Al’ameen ya fito daga bedroom ɗinsa, sanye da baƙar jallabiya wacce ta amshi fatar jikinsa, ba tare daya nufi Aunty Amarya ba ya shige daining kasancewar da yunwa ya kwana, dankali da ƙwai ɗin ya jawo ya buɗe yamutsa fuska domin kuwa bai fiye son da ƙwai haɗe ba, yafi gane chiefs ɗinsa ƙwai ɗin dabam, ture kular gefe yayi yana tsuka tare da sake jawo ɗayar, ƙosai ya gani, murmushi ya saki tare da ɗiba a plat lipton ɗin ya tsiyaya a cup, a hankali ya kai ƙosan bakinsa idanunsa ya lumshe jin daɗin ƙosan yana ratsa kansa, cike da nishaɗi yake cin ƙosan, lipton ɗin ya kurɓa, idanunsa ya lumshe domin kuwa tea ɗin yayi mungun daɗi, sosai yaci ya ƙoshi rabon da yayi breakfast haka harya manta, dube dube ya fara ta ina zaiga dafaffen ƙwai ɗinsa, babu shi babu alamun sa, Aunty Amarya ya kira.

“Aunty! Aunty! “

Amsawa Aunty Amarya dake zaune tayi tare da cewa.

“Lafiya kuwa Al’ameen.?”

“Ina ƙwai na yake.?”

“Ka duba baya wajen ne.?”

“Indai ba idanuna bane suka samu matsala to gaskiya babu.”

Tashi Aunty Amarya tayi tana murmushi, dama kuwa nema take Ablah tayi kuskure, daining tazo tare da dubawa bata gani ba.

“Aunty anya kuwa yau an dafa ƙwai ɗin nan.”

Dafa kanta Aunty Amarya tayi tare da cewa.

“Sorry sabuwar ƴar aiki Inna ta kawo itace tayi breakfast yau, ina ga bata dafa ƙwai ɗin ba, amma kuma ai nace Ladiyo ta nuna mata komai, wannan yarinya bata kyauta ba.”

Ɗago idanunsa yayi cike da ɓacin rai ya furta.

“What sabuwar ƴar aiki kuma? Aunty yanzu kina nufin ba abincin Ladiyo naci ba, amma dai an cuceni sanin kanki ne bana cin abincin wani idan ba naki kona Ummi ko Ladiyo ba, shine zaku barni naci abincin wata, wataƙil ma ƙazama ce, wama yace ana buƙatar wata ƴar aiki a cikin gidan nan, koma wayece a kira min ita dole tabar gidan nan yanzu.”
Yayi Maganar a fusace, murmushi Aunty Amarya ta saki, cikin zuciyarta tana furta (dai-dai kenan, ai kuwa yanzu zansa ayi kiranta.) Tayi Maganar zucin tana ƙwalawa ihsan kira da gudu ihsan ta taho, cewa tayi taje ta kira baƙuwar dake bedroom ɗin Inna Jumma, da gudu ihsan ta tafi aikan.

Ba’a juma ba kuwa sai ga Ablah da ihsan sun fito tare, daining ɗin ta iso tare da risinawa tace wa Aunty Amarya.

“Gani Aunty.”

Muryarta ta doki dodon kunnensa, ras zuciyarsa ta tsinke, kamar yasan muryar, kafin Aunty Amarya ta yi Magana Al’ameen ya juyo tare da sauƙe idanunsa a fuskarta ido biyu suka haɗa, cike da munguwar mamaki Al’ameen ya nuna ta da yatsa.

“Dama kece?”

Idanunta ta sunkuyar ƙasa cike da jin haushin sa domin kuwa tun zagin daya mata take jin zafinsa, murmushi Al’ameen ya saki tare da cewa.

“Kin biyoni har gidan mu kenan, yayi kyau na yabawa nacinki wato dai ke a rayuwarki baki ƙaunar ganina cikin farin ciki, ai kuwa ke bazan koreki ba, ina miki barka da shigowa *AMBASSADOR AHMAD GIWA ESTATE)* “

Yayi Maganar yana sakin murmushin mugunta tare da miƙewa ba tare daya kuma yin zancen ƙwai ɗin ba, ya ɗauki wayarsa yabar falon gabaki ɗaya.

Aunty Amarya wani irin baƙin ciki taji domin kuwa bata so haka ba, taso ace Al’ameen ya wulaƙanta Ablah tsuka taja itama tare da barin wajen, Ablah da kanta ke sunkuye ne, ta juya cike da zullumin Rayuwar wannan gidan, (anya kuwa zamanta zai yiwu da waɗannan mutanen, bata san me ta yiwa Aunty Amarya ba ta jefa mata karar tsana gefe guda kuma ga wannan baƙin azzalumin.) Numfashi ta saki ta shige ROOM ɗin Inna Jumma.

*****

Tagumi Rufaida ta zuba cike da damuwa da tunani, ita dai Soyayya ta zame mata ƙaddara a rayuwarta, soyayyar ɗan uwanta na shirin zame mata ciwo shin meyasa bazata sanar dashi gaskiya ba idan yaso ayita kawai ta kare domin kuwa bata hango Ya Haidar zai rabu da wannan Nafeesan wannan wacce irin masifa ce.

Tayi Maganar zucin tana sakin tsuka hawayen da bata san dashi bane ya gangaro daga idanunta, Haidar daya juma tsaye a kanta ne bata san yana tsaye a kanta ba, ya zauna gefenta tare da saka hanu ya dafa kafaɗar ta, a firgice Rufaida ta ɗago idanunta ta sauƙe su akansa, numfashi ta saki tana dafe ƙirjinta.

“Rufaida! Wani irin tunani kike haka, ki duba kiga yanda kike cikin damuwa ga tunani, kuma kina zuci, so kike ki kashe kanki, wai meye matsalarki ne ma yanzu.?”

Idanunta ta zuba masa cikin zuciyarta tana furta kaine matsalata, anya kuwa bazata faɗa masa gaskiya ba yanzu, mtss! Kai gara kawai ta faɗa masa ko zaiji tausayinta….

<< Aminaina Ko Ita? 14Aminaina Ko Ita? 16 >>

2 thoughts on “Aminaina Ko Ita? 15”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×