Skip to content
Part 24 of 67 in the Series Aminaina Ko Ita? by Rasheedat Usman

Zaro idanunta Ablah tayi bata san yadda akayi bakinta ya suɓuce yayi wannan maganar ba, ta yaya zata fara sanar dashi Aunty Amarya wacce suke ɗaukarta tamkar Uwa suka bata yardar su ɗari bisa ɗari tasan koda ta faɗa ba yadda zasuyi da ita ba, kalaman Aunty Amarya ne suka faɗo mata a rai (baki san cewa baka sanin yadda zaka kifar da mutum ba, har sai ka shiga jikinsa ka gama sanin yaya yake, a lokacin zaka masa kwantan ɓauna shi kuwa zai gama baka dukkan yardar sa, da zarar ya gama yadda da kai to fa kafin ya ankara ka kifar dashi, wannan shine salon yaƙi na banyi zaton akwai wanda zaiji asirina nan kusa ba sai dai kash tsautsayi yasa kinji sannan har hakan yasa kin dakatar min da aiki na na yau hakan ba ƙaramin ciwo ya min ba, sai dai kina da zaɓi biyu tsakanin ki dani na farko tunda kinji sirrina na baki dama ki dawo gareni mu haɗe ki tayani aiki, zaki samu kuɗin da har ki mutu keda iyayenki baza kuyi talauci ba na biyu kuma idan kinƙi amincewa zaki shiga cikin uƙuba ta, zaki gwammaci mutuwa da rayuwa domin kuwa ni kaina nasan bani da imani, Tabbas zan ɗanɗana miki azabar da tafi mutuwa ciwo zaɓi yana gareki ki zaɓi tsoro ko zamanki lafiya.)

(Au naji tsoro zaki tona min asiri, yaro bai san wuta ba sai ya taka, ki tashi kije yanzu ki faɗa musu nice nake kashesu mu gani ko zasu yadda ni ce fa wacce sukafi yadda da ita fiye da kowa a cikin gidan nan duk abinda zaki faɗa bazasu taɓa yadda ba, A ƘARSHE MA KECE RESHE ZAI JUYE DA MUJIYA )

Idanunta ta runtse hawaye na zubo mata tuno da maganganun Aunty Amarya Tabbas tana da gaskiya koda ta faɗa bazasu yadda da ita ba, a ƙarshe ma dai su iya mata wulaƙanci ko su koreta suce ta yiwa Auntyn su sharri, lallai ne dole ta ɓoye wannan maganar har sai sun ga halinta da idanunsu.

“Magana nake miki kimin shuru! Ko kurma kika dawo! Nace waye ya kashe min Ummi? “

Taji muryar sa cikin tsawa tamkar zai doketa razana tayi tare da cewa.

“Ni…..Ni…ni ban sani ba.”

Tayi Maganar cikin tsoro, zaro idanunsa Al’ameen yayi yana dafe bango domin kuwa jiri yake ji tamkar zai faɗi cikin sanyin murya hawaye na cigaba da gudu a fuskarsa yace.

“Da kunnena naji kina cewa ta kasheta hankalinta ya kwanta sannan yanzu ki cemin baki sani ba, ki faɗa min wanene ki faɗa min naje na ɗauki fansar jinin Ummi na.”

Kanta Ablah ta girgiza tare da cewa.

“Ni kuma? Ni ban faɗi wannan maganar ba, ni bansan waya kashe Ummi ba ban faɗa maka haka ba ni.”

Idanunsa ya runtse tare da komawa ya zauna daɓas jiri na cigaba da kwasarsa, wataƙila shine kunnen sa baiji masa dai-dai ba, wata ƙil gizo maganar ta masa, kuka ya fashe dashi, wani irin tausayinsa ne ya kama Ablah komawa tayi ta zauna a gabansa tare da cewa.

“Kayi hkr babu mai tsallake lokacin sa, duk wanda kwanansa ya ƙare to fa babu wanda ya isa ya ƙara masa koda second ɗaya ne, nasan da ciwo dole zakaji zafi amma dan Allah ka daure ka daina mata kuka babu kyau kukan mutuwa ga mamaci tamkar azabace kake aika masa, a yanzu madadin kayi wannan kukan ka tashi kayi alwala kayi sallah sannan ka yiwa Ummi addu’a ka ɗauki ƙur’ani ka karanta mata kayi mata tawassali dashi Allah ya sa taje makwancinta cikin Nasara, na Tabbata zai isa gareta kuma zataji daɗi har tayi alfahari da kai domin kuwa daga bayan rayuwarta tun kafin taje kabari ka fara aika mata kyakkyawan saƙo, hakan zaisa tayi alfahari da kai dan Allah ka daina kukan ka tashi kayi alwala nima ita zanyi yanzu na nemawa Ummi sauƙi da afuwa gami da rahama wajen Ubangijinta.”

Inna Jumma dake tsaye bakin ƙofa tana jinsu itama hawayen take sosai taji zafi da ciwo a ranta Gaji ta rasu ikon Allah abun kamar almara lallai ne rayuwa babu tabbas, sanin tawakalli da kuma Tauhidi da sanin mutuwa wajibine akan ko wanni bawa yasa Inna Jumma bata ɗaga hankalinta sosai ba Tabbas tana jin zafi amma bazata yi kuka da kururuwa ba, idan kowa zai nuna gazawarsa a fili to waye zai rarrashi ɗan uwansa, sosai Ablah ta burgeta yarinya ƙarama sai hankali da sanin ya kamata, goge hawayen ta Inna Jumma tayi tare da ƙarasowa wajen nasu itama ta zauna tace.

“Tabbas Maganar Ablah gaskiya ne Gaji bata buƙatar kuka a garemu addu’a itace kawai gatan da zamu mata, Tabbas munyi babban rashi, ka tashi kayi alwala.”

Hawayensa yasa hanu ya goge tare da miƙewa yana tangaɗi kamar zai faɗi, ya fita ROOM ɗinsa ya shiga ya ɗauro alwala ya hau Sallah yana hawaye.

A falo kuwa, Rufaida ce ta shigo da ihu a gigice tana ambaton.

“Innalillahi wa’inna ilaihirraji’un! Wayyo Allah wayyo yau kuma mun shiga Uku me zamu gani haka, Ummi ta tafi, wayyo mun shiga Uku.”

Inna Jumma da Ablah da suka sauƙo ne ta daka mata tsawa tare da cewa,

“Baki da hankali ne Rufaida ki shigo kina wannan ihun sai kace ba musulma ba, to bamu shiga Uku ba, Allah ya fimu sanin abinda yake nufi da hakan ya ɗauki gaji madadin ki mata addu’a sai ki shigo kina cewa kin shiga Uku yau naga shashancin banza.”

Rufaida kuka ta kuma saki tare da zama a ƙasan tayels ɗin tana cewa.

“Inna Jumma, ba dole nace mun shiga Uku ba, Ummi fa muka rasa, ita ke saka Daddy ya mana komai a rayuwa, tana mana duk wata gatar duniya, sannan yau an wayi gari babu ita ba dole nace mun shiga Uku ba, Allah na tuba ka yafeni Allah ka jiƙan Ummi Allah ka bata ni’ima da salama cikin kabarinta.”

Ta ƙarisa Maganar tana cigaba da kuka Ablah kanta ta kaɗa cike da tausayin family ɗin, kowa yana son Ummi, room ɗin ta itama Ablah ta shige taje ta hau Sallah tana yiwa Ummi addu’a.

Kafin kuce me tuni mutuwar Ummi ta zagaye ko ina a cikin garin Abuja, tururuwa da taron mutane sai zuwa suke kowa yana jimamin rasuwar Uwar gidan Ahmad Giwa, ko Nafeesa ma ta gani a social media, Haidar ta kira domin ta tabbatar jin muryarsa yaci kuka ya sa Nafeesa tabbatar da gaske ne mutuwar, Haidar sosai yaji daɗi daya shigo ya samu Al’ameen riƙe da ƙur’ani yana karatu sai dai duk da haka hawayen sa bai tsaya ba, numfashi Haidar ya saki tare da zama yana sauraron ƙira’ar Al’ameen.

“Ummi zatayi kwanan keso Daddy yace sai gobe 11am za’ayi mata Sallah.”

Rufe ƙur’anin Al’ameen yayi tare da ɗaga hanunsa ya juma yana yiwa Ummi addu’a kafin ya sauƙe hanunsa tare da matsowa jikin Haidar ya kwantar da kansa a kan ƙafar Haidar hawaye na zubo masa ba tare da yace komai ba.

Aunty Amarya kuwa idan kunga yadda take gigice idanunta duk suka kumbura da kukan munafurci sai ku rantse da Allah cewa tafi kowa jin ciwon mutuwar Ummi ko kaɗan bazaka taɓa zargin itace ajalin Ummi ba.

Washegari da misalin 11am aka yiwa Ummi Sallah tare da kaita makwancinta, Al’ameen gagara zuwa makabartan yayi saboda zuciyarsa bazai iya ganin yadda za’a saka Ummi cikin rami a rufeta ba.

Wunin ranar haka kowa yayi sa babu daɗi yayinda gidan ke cike da ƴan ta’aziyya ƴan uwan Ummi duk sunzo, hatta su Khalipa sun sami labarin mutuwar Ummi sai dai Ashfat ne ba’a sanar da ita ba saboda an mata aiki, Khalifa a ranar yayi bukin ɗin jirgi da niyar gobe zai taho shima sosai yayi kuka tamkar ransa zai fita, Samira tafi kowa shiga cikin tashin hankali na rasuwar mahaifiyarsu domin ita a ranar ta taho.

Aunty Amarya na zaune ita da Hajiya Mansura a falon da kuma sauran masu karɓar gaisuwa ƴan sanda suka shigo, ganin su sai da yasa zuciyar Aunty Amarya ya tsinke, kallon Hajiya Mansura tayi tare da cewa.

“Mansura police kuma a cikin gidan nan?”

“Kema ai kinsan dole police zasu shigo cikin lamarin karfa ki manta da guba aka kasheta, amma na tambayeki ina dai baki kama abinda Hajiya Gaji tasha maltinan dashi ba?”

“No ban riƙe cup ɗin ba gaskiya, da na zuba gubar da ƙasan brush ɗinta na juya sa.”

Numfashi Hajiya Mansura ta saki tare da cewa.

“Alhamdulillah! Kin tsallake wannan tarkon, ki saki jikinki babu wanda zai zargeki.”

Sukayi Maganar cikin murmushi, su kuwa police bayan su Haidar ne da Daddy bedroom ɗin Ummi suka shige.

Sosai sukayi bincike tare da ɗaukar cup hanunsa sanye da handglab, suka wurga a cikin leda, sannan suka fita daga cikin gidan gabaki ɗaya ba tare da sunyiwa kowa Magana ba.

Washegari Khalifa shima yazo yasha kukansa tare da ɗan uwansa.

Nafeesa itama ranar sadakar Uku sukazo ita da Jamila, Nafeesa hankalinta bai tashi ba sai da taga daular dake gidan Ahmad Giwa, a harabar gidan suka tsaya ta kira Haidar ta sanar masa sunzo da kansa ya fito ya shigar da ita ciki, fuskarta rufe da niƙaf, wajen Aunty Amarya ya fara Kaita suka gaisa, kafin ya kira Maimu ya haɗa su yace ta kaita wajen Momma ta mata ta’aziyya, sanin ko wacece yasa Maimu jin haushi domin duk ta dalilinta ƴar Uwar ta take shan wahala, Maimu duban Nafeesa tayi tare da cewa.

“Muje.”

Suka jera tare Momma suna zaune tare da Rufaida da kuma Samira sai Aunty Zuwaira ƙanwar su Daddy Maimu ta shigo tare da su Nafeesa zama Maimu tayi gefen Rufaida tare da cewa Momma.

“Momma ga budurwar Yaya Haidar yace a shigo da ita zata miki ta’aziyya.”

Rufaida wani Irin tsinkewar zuciya taji take taji takaici da haushin Nafeesa duk da bata ga fuskar Nafeesa ba sakamakon rufeta da tayi da niƙaf amma sosai taji zafin ta, miƙewa Rufaida tayi tare da jan tsuka mai ƙarfi ta bar wajen, Momma idanunta ta ɗaga ta dubi Rufaida tsantsar kishi ta hango a cikin idanunta dama ta juma tana zargin Rufaida na son Aliyu sai dai bata tabbatar ba sai yau, suma su Nafeesa da kallon mamaki suka bi Rufaida, numfashi Momma ta saki tare da cewa.

“Ayya sannunku da zuwa.”

Nafeesa kanta a sunkuye ta gaishe da Momma tare da mata ta’aziyya, babu yabo babu fallasa sun ɗan juma kaɗan kafin su fita, Maimu Haidar ta nema ta mayar masa da Nafeesa, kafin ya kira Al’ameen.

Nafeesa cike da tausayawa tace.

“Al’ameen ashe abinda ya faru kenan Ummi anzo ƙa’ida, Allah ya jiƙanta da rahama.”

Da ameen Al’ameen ya amsa, ko kafin Nafeesa ta kuma Magana yaseer yazo ya kirasa anzo masa ta’aziyya ba tare da sunyi Sallama ba ya juya yabi bayan yaseer.

Sun ɗan juma kaɗan da Haidar kafin suma suka tafi.

Tunda police ɗin suka tafi basu kuma dawowa ba, har akayi sadakar bakwai na Ummi a yayin da kowa ya watse sai Samira da Khalifa da basu tafi ba.

Zaune yake yayi shuru fuskarsa cike da damuwa har yanzu mutuwar Ummi bata bar jikinsa ba, hanu yasa tare da ɗago wayarsa sai yau ya fara duba saƙwannin da aka turo masa, wajen 50 message ya ci karo dasu, a hankali yake duba saƙonnin har yazo kan saƙon Nafeesa, karanta saƙon yayi tare da kuma maimaita karantawa yana zaro idanunsa sai kuma yaja tsuka tare da taɓe bakinsa, turo ƙofar akayi da Sallama ɗaga idanunsa yayi yaga Daddy ne amsa sallamar yayi Daddy ya shigo ya zauna a gefe bed ɗin Al’ameen tare da dubansa yace.

“Zakina har yanzu kana cikin damuwa ko, ka rage yawan tunanin nan domin na fahimci kwana biyun nan kana yawan keɓewa gefe kana tunani Please ka rage Saboda karka jawowa kanka ciwo.”

Duban Daddy yayi yana runtse idanunsa, ya gagara daina tunanin Ummi, numfashin ya saki tare da cewa.

“Insha Allah Daddy zanyi ƙoƙarin naga na rage.”

”Ya kamata kam, ka tashi muje muyi breakfast sai mu shige station Dpo ya kirani yana buƙatar ganin mu, na yiwa Haidar magana zamu je tare.”

Miƙewa Al’ameen yayi tare da cewa.

“Okay to shikenan muje Daddy.”

Ƙasa suka sauƙa Aunty Amarya Al’ameen ya hango zaune a gefe tayi shuru cikin tunani da alamun kamar tana cikin yanayin damuwa, domin kuwa tun rasuwar Ummi take Cikin wannan yanayin, kansa Al’ameen ya girgiza cike da tausayin Aunty Amarya ya ƙarisa ya zauna a gefenta tare da cewa.

“Kina cikin damuwa Aunty kin kasa sakewa tun rasuwar Ummi, damuwa tana son ta miki yawa, Aunty Ummi ta tafi bazata dawo ba, dan Allah kiyi hkr ki rage tunani, na Tabbata baza muyi kukan rashin Uwa ba a cikin gidan nan, domin kuwa muna dake tamkar Ummi haka kike a garemu bazaki barmu muyi kuka ba, kina kaunar mu kamar yadda Ummi ke ƙaunar mu, Aunty na sani kin shaƙu da Ummi kuna son junanku babu mugunta tsakanin ku, dole zaki shiga cikin damuwa, amma Aunty idan muna ganinki a cikin wannan halin ta yaya mu hankalinmu zai kwanta, bana buƙatar ganin damuwarki domin kuwa tana ɗaga min hankalina, dan Allah Aunty ki daina damuwa muyi hkr mu yiwa Ummi addu’a, shi kuma wanda ya kasheta Allah ya tona masa asiri.”

Hawaye Aunty Amarya ta goge a idanunta tare da kama hanun Al’ameen tace.

“Bansan sanda damuwar take zuwar min ba, a duk sanda na tuna da cewa a yanzu babu Ummin Al’ameen a cikin gidan nan ta barmu bari na har abada, sai naji zuciyata ta dugunzuma hankalina ya tashi, sai naji tamkar nima na yanki jiki na faɗi, Al’ameen bana jin daɗin rayuwa a cikin gidan nan babu Ummin Al’ameen, hankalina yana tashi.”

“Babu wanda yake jin daɗi a cikin mu sai dai Aunty dole zamuyi hkr tunda bazamu iya dawo da ita ba, ki tashi muje kiyi breakfast.”

Miƙewa aunty Amarya tayi cikin sanyin jiki suka shige daining, Aunty Amarya tsabar makirci ƙin cin abincin tayi sai hawaye shar a fuskarta, Daddy ijiye spoon ɗin dake hanunsa ya dubeta tare da cewa.

“Amarya meyasa ne da zarar kinsa abinci a gabanki sai ki hau kuka, meyasa kika kasa haƙuri da rasuwar Gaji ne, ta fa riga ta rasu mtsss! Babu yadda muka iya dole zamuyi hkr idan baki ci abinci zaki sawa kanki ciwo ya kamata ki rage wannan damuwar.”

“Daddyn Al’ameen dole hankalina zai tashi idan na kalli wajen babu Ummin Al’ameen, shine yake ɗaga min hankali.”

Ta ƙarisa Maganar dai-dai wayar Daddy na ringin, ɗaga wayar Daddy yayi Dpo ne.

“Hello Dpo ya aiki.”

“Aiki alhamdulillah Alhaji, amm yau zamuyi gwajin yatsu akan wannan cup da aka zuba gubar a ciki so ya kamata idan zakuzo sai kuzo da dukkanin mutanen da suke cikin gidan ka, Saboda zamuyi gwajin yatsu Saboda mun samu tambarin hanun mutum Uku a jiki, so muna son mu gwada mu tabbatar da masu yatsun yanzu zan tura Sargent Joshua asibitin Dgs hospital sai ku samesa a can.”

“Okay to shikenan insha Allah muna tahowa yanzu.”

Yayi Maganar tare da katse kiran duban su Aunty Amarya yayi da Inna Jumma tare da cewa.

“To kunji abinda Dpo yace zamuje za’ayi gwajin yatsu to su masu gadin flower da suke waje bazamu sasu ciki ba Saboda doka ne akansu su basa shigowa cikin falon nan dan haka iya mu da muke rayuwa a cikin wannan falon da mu da ƴan aiki mata dake cikin falon nan zamuje Samira kije ki samu Ladiyo da Ablah ki sanar dasu cewa su shirya su fito yanzu zamuje asibiti karki sanar dasu abinda zamuje muyi.”

“Okay to shikenan Daddy bara naje.”

Tayi Maganar tana tashi taje ta sanar dasu.

Haka kuwa akayi suka shirya mota biyu suka nufi asibitin, koda sukaje basu wani sha wahala ba aka musu gwajin tare da basu umarnin suna iya tafiya, Daddy dpo ya kira ya sanar dashi sunje sunyi test ɗin.

“Okay doctor ya sanar dani zuwa yamma misalin 5:30pm kazo ka sameni a station results ɗin zaizo zuwa wannan lokacin.”

Da to Daddy ya amsa tare da masa godiya ya katse, gida suka koma ita dai Ablah haka kawai take jin zuciyarta na tsinkewa wanda bata san dalili ba da wannan sanyin jikin suka iso gida.

A falo Al’ameen ya zauna tare da yin shuru yana nazarin rasuwar Ummin sa, shi dai har yanzu yana cikin matsanancin damuwa, tagumi ya zuba tare da furta.

“Na rasa mai bani shawara a rayuwata na rasa mai gwada min ina ne gabar inane yamma na rasa mai dawo dani hanya idan na ɓata, shin yanzu wa zan faɗawa damuwata waye zai bani shawara mai kyau a bed ɗin waye zan kwanta nayi baccin rana, uwata mai ƙaunata ta tafi ta barni da kewarta.”

Ablah da ta shigo ne ta tsaya tana sauraransa sosai ya bata tausayi dama ta sani dole yana cikin damuwa kawai yana ɓoyewa ne Saboda ƴan uwansa karsu shiga wani hali, gashi suna tare da wacce take cutar dasu a matsayin Uwa basu sani ba, numfashi ta saki tare da zuwa gabansa ta sunkuya tace.

“Yaya Al’ameen.”

Ɗago idanunsa yayi da sukayi jajur ya dubeta cikin ɓoye damuwarsa.

“Meya faru Ablah, gobe zaki fara zuwa school koh”?

“Eh gobe zan fara zuwa school, amma bashi bane ya kawo ni yanzu, hmmm yaya Al’ameen gani nayi kamar kana cikin damuwa, har naji kana wasu maganganu.”

Murmushi Al’ameen sosai yaji daɗin yadda ta damu da lamarinsa har take kulawa dashi.

“Babu wata damuwa da nake ciki, kawai ina wani nazari ne.”

“A’a yaya Al’ameen, Tabbas damuwar Ummi kake ciki, yaya Al’ameen ka yadda da ubangiji.”?

Idanu ya zuba mata cike da ƙaunarta ya ɗaga mata kansa alamun eh.

“Na yadda da ubangiji domin kuwa shine wanda ya halicceni ya halicceki ya hallici samai da ƙassai da dukkan abubuwan dake cikinsu to ta yaya bazan yadda da ubangijina ba.”

“To amma ƙaddara fa ka yadda dashi.?”

“Ƙwarai kuwa na yadda da ƙaddara mai kyau ko akasin haka.”

“Yaya Al’ameen idan har da gaske ka yadda da ubangiji kuma ka yadda da ƙaddara, to kuwa ya kamata ka daina shiga cikin damuwa Saboda rashin Ummi ka ɗauka cewa ubangijin da yayini ya yika yayi Ummi ya fimu sonta ne ya ɗauketa, ka ɗauka cewa rashin Ummi ƙaddarar kace daga ubangiji wataƙil ya ɗauketa ne domin ya nuna maka cewa zaka iya rayuwa ba tare da taimakon wani ba, kuma domin ya gwada ƙarfin imaninka yaga ko zaka gode masa ko akasin haka dan Allah kayi hakuri kaci wannan jarabawar.”

Tunda Ummi ta rasu Al’ameen bai ji nishaɗi ko farin ciki ba kamar yanzu Tabbas samun Mutum kamar Ablah a kusa dakai babbar kyauta ce daga ubangiji, ɗan murmushi ya saki tare da cewa.

“Hakane ABLAH naji daɗin kulawarki gareni, insha Allah daga yau na daina tunani zan dage da yiwa Ummi addu’a aduk sanda naji kewarta zanyi ƙoƙarin ambaton kalaman ubangijina domin ya danne min zuciyata.”

Murmushi ta saki tare da miƙewa tabar wajen, shima murmushin yake yana kallon ta cike da Soyayya harta ɓacewa ganinsa…

<< Aminaina Ko Ita 23Aminaina Ko Ita 25 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×