Daddy ne yayi gyaran murya tare da cewa.
"Dpo ba damuwa kuyi duk abinda kukaga ya dace mu dai burin mu shine a gano gaskiya, dan Allah kuyi bincike cikin nutsuwa domin kujewa cutar da wanda baiji ba bai gani ba, mu zamu shige."
"Okay insha Allah ALHAJI zamuyi abunda ya kamata a gaida gida."
Musabaha suka sake tare da miƙewa shima Al'ameen cike da sanyin jiki ya miƙe ya gagara koda furta kalma ɗaya suka fice kowa ya hau motar daya zo dashi sun ɗauki hanya Haidar yace.
"Duniya babu yarda kaga mutum kawai ka barsa. . .