Skip to content
Part 26 of 67 in the Series Aminaina Ko Ita? by Rasheedat Usman

Daddy ne yayi gyaran murya tare da cewa.

“Dpo ba damuwa kuyi duk abinda kukaga ya dace mu dai burin mu shine a gano gaskiya, dan Allah kuyi bincike cikin nutsuwa domin kujewa cutar da wanda baiji ba bai gani ba, mu zamu shige.”

“Okay insha Allah ALHAJI zamuyi abunda ya kamata a gaida gida.”

Musabaha suka sake tare da miƙewa shima Al’ameen cike da sanyin jiki ya miƙe ya gagara koda furta kalma ɗaya suka fice kowa ya hau motar daya zo dashi sun ɗauki hanya Haidar yace.

“Duniya babu yarda kaga mutum kawai ka barsa inda ka gansa domin kuwa ba kowa bane yasan alkairi sai ka ɗauki mutum ka kaisa inuwa harma ka sashi a firji shi kuwa ya fara ƙoƙarin jefaka cikin wuta, ba’a gane mungu a fuska, yanayin ta sak na mutanen kirki banyi zaton baƙar kububuwa bace Ablah.”

Runtse idanunsa Al’ameen yayi yana jin ƙunar maganar Haidar a cikin zuciyarsa duk da sanin halin mutum sai Allah amma bayaji a ransa cewa Ablah zata aikata abinda ake zarginta, shuru yayi ba tare daya tankawa Haidar ba ya cigaba da dreving ɗinsa cikin dagulewar zuciya, Haidar jin Al’ameen yayi shuru baice komai ba ya sashi cigaba da cewa.

“Idan Banda matsiyaciyar yarinya, a taimaki rayuwarki a fidda ki daga ƙangin wahala amma ki nemi tozarta mutum, Allah Yarinyar nan yau sai tabar mana gida tunda butulu ce ita, Tabbas tayi babban kuskure a rayuwarta domin kuwa ta taɓo jinin da bazai taɓa barinta ta zauna lafiya ba, yadda ta kawar da Ummi a duniya dole itama sai fuskanci mutuwa mafi muni.”

Still dai Al’ameen baice komai ba har yanzu, jin Al’ameen yayi shuru yasa Haidar dubansa tare da cewa.

“Al’ameen ya kayi shuru ka barni sai Magana nake bakace komai ba.?”

“To me kake so nace Haidar, wannan fa Yarinyar zarginta ake ba wai an tabbatar da cewa itace tayi wannan kisan ba, dan haka maganganun da kake akanta sam basu dace ba harda tsinuwa, ka bari tukunna idan aka tabbatar da cewa itace tayi kisan sai kayi duk abinda zuciyarka ta baka.”

Cike da mamaki Haidar yake duban Al’ameen domin kuwa kwatakwata baya hango yarda da cewa Ablah itace tayi kisan ba, cikin mamaki yace.

“Me kake nufi kenan dayin shurunka?”

“Ina nufin ban yarda itace tayi kisan ba, domin kuwa bana tunanin ko ɓera zata iya kashewa bare kuma Mutum, zuciyata bata amince da ita bace.”

“What! Al’ameen kasan abinda kake faɗa kuwa, ta yaya zaka san cewa ba ita bace, ka sani fa ba’a gane mungu a fuska, idan har ba ita bace tayi kisan meyasa aka samu shatin yatsun ta har sau biyu kuma yafi na kowa fitowa, hmmm da mamaki amma meyasa kake ƙoƙarin kare mai laifi, karka manta akan fansar jinin Ummi ake magana?”

Numfashi Al’ameen yayi tare da saka hanu ya goge guntun hawayen daya zubo masa yace.

“Na sani akan jinin Ummi na ake magana Haidar, duk wanda zanso a duniya bayan Ummi ne, ba kareta nake ba, domin kuwa bazan kare kowa akan Ummina ba koda kuwa maimu ce ko Khalifa, kai koda ace Daddy ne da kansa, zan tsaya har sai naga hukuma tayi musu hukunci dai-dai da laifin su, bare kuma Ablah, wata can daban wacce na santa daga baya, Tabbas ina sonta domin kuwa itace tamin dai-dai da matar da nake buƙatar na aura amma wallahi! Wallahi! Wallahi! Kaji rantsuwar musulmi ba Soyayyar da nake mata yasa nake kareta ba, a’a ina faɗin hakane Saboda bana tunanin zata aikata kisan kai.”

“Hmmm! Amsar tambayata ta fito dama biri yayi kama da mutum duk rantsuwar da zakayi min Al’ameen bazan yadda da kai ba Saboda ka ambato kalmar Soyayya, hmmm! Amma fa ka sani Wallahi muddun zuciyata tana bugawa babu alaƙa tsakanin ka da Wannan tsinanniyar Ablah, sai na dakatar da duk wani abinda zai shiga tsakaninka da ita, domin kuwa Tabbas itace ta kashe Ummi idan zuciyarka bata baka haka ba ni tawa ta bani, kuma ina tabbatar maka cewa sai na tabbatar da ta fuskanci wulaƙanci kafin ta mutu.”

“Haidar ban sanka da kuskuren fahimta ba, karka fara yanzu kayi hkr mubi komai a hankali har sai mun tabbatar da gaskiyar lamari idan harya tabbata itace ta aikata sai nafi kowa tsanarta sai nasa an wulaƙanta ta fiye da wanda kake da niyar mata, na fika jin zafin mutuwar Ummina, amma dole muna buƙatar muyi bincike a hankali, kar muyi hukunci cikin fushi, ba’a yanke hukunci cikin fushi Haidar, idan har zuciyarka ta fusata kayi ƙoƙarin kwantar da hankalin ka ka kawo nutsuwa ka ijiye cikin zuciyarka domin gudun danasani, babu ruwanka da Ablah kabar hukuma suyi aikinsu gaskiya baya taɓa ƙasƙanta sai dai ƙarya ta ƙasƙanta ka fahimce ni, gaskiya itace sama da zalunci.”

Idanunsa Haidar ya runtse zuciyarsa na masa ƙuna wani haushi da tsanar Ablah yakeji a cikin zuciyarsa, Al’ameen bazai fahimce sa ba domin kuwa akwai Soyayyarta cikin zuciyarsa mutum marar imani irin Ablah suna iya komai domin ɗaukewa namiji hankali duk yadda akayi Al’ameen baya cikin hankalinsa.

Ni fa bazan haƙura ba dole sai na nunawa yariyar nan kuskurenta a yau.”

“Wato dai bakaji abinda nace maka ba Haidar meyasa ka koyi taurin kai ne, mtsss! Babu ruwanka da ita kabar hukuma suyi aikinsu.”

“Bafa zan bari ba dole sai tabar gidan mu a yanzu idan yaso hukumar suje su kamata acan gidan ubanta.”

Numfashi Al’ameen ya saki tare da kallon Haidar yana dafe kansa yace.

“Ka sani fa unguwar su area ne idan har police sukaje suka kamata acan zai zamo musu abun kunya domin kuwa unguwar cika zatayi da mutane ka dai san area, karka wulaƙantata a samu kuma ba ita bace tayi laifin.”

“Wai kai Al’ameen Soyayyar wata mace har tafi ta mahaifiyarka ne domin kuwa nunawa kake ka manta da soyayyar Ummi saboda Soyayyar wannan matsiyaciyar.”

“Enough! Enough! Haidar ya isa! Karka kuma danganta Soyayyar mahaifiyata da ta wata mace ina son Ummi fiye da kowa da komai a duniya, karka faɗa min Magana Haidar hatta Daddy na fi son Ummi sama dashi, naga alamar kana neman lallai saika tilasta ni nabi ra’ayinka, kuma bazan bi ba, saboda kai lalube kake acikin duhu, hukuma zan bari suyi aikinsu, domin kuwa koda suma suna lalube a cikin duhu to basa taɓa yanke hukunci har sai sunga haske dan haka ka bar maganar nan haka babu ruwanka kabar hukuma suyi aikinsu.”

Al’ameen yayi Maganar cikin fushi da tsawa idanunsa sun kaɗa sunyi jajur, ji yayi mutuwar Ummi ta dawo masa sabuwa dal a ransa, Haidar shima cike da hasala yace.

“Tsawa kake min Al’ameen Saboda na faɗa maka gaskiya, okay to ƙarya nayi baka fifita Soyayyarta fiye da ta ummin ban…………..”Ya isa! Ya isa!”

Yayi Maganar da wani irin tsawa mai shiga ƙwaƙwalwar mutum tare da taka burki a gefen titin yayi parking idanunsa sunyi jajawur tamkar gauta kansa na wani irin bala’in sara masa ba tare daya dubi Haidar ba yace.

“Ka fita min a mota! Na ce ka fice daga Mota.!”

Kallon Al’ameen cike da mungun mamaki ya nuna kansa da yatsa yace.

“Ni zaka wulaƙanta a tsakiyar titi Al’ameen ka koreni cikin motar ka?”

“Haidar i say get out of my car get out!”

Girgiza kansa Haidar yayi tare da buɗe motar ya fita, Al’ameen da ƙarfi yaja motar yabar Haidar tsaye domin kuwa yana neman hasala shi ne ya sashi lallai sai yayi abinda bashi da niyya shi kansa baiji daɗin korar Haidar da yayi cikin motarsa ba sai dai babu yadda ya iya hakan shine kawai nutsuwarsa domin kuwa bakin Haidar bazaiyi shuru ba.

Shi kuwa sosai ransa ya ɓaci kasancewar sa ba mutum mai girman kai ba ya tari adaidaita sahu ya kawosa gida, koda ya shiga a First get yaga motar Al’ameen ajiye Numfashi mai zafi ya saki tare da shigewa part ɗin su domin kuwa a yadda ya fahimci Al’ameen bazai bari a kori Ablah daga part ɗin su ba, ƙarshe ma dai ya iya dawo musu faɗa, koda ya shiga part ɗin su a falo ya zauna tare da dafe kansa yana jin yana sara masa tsantsar tsanar Ablah yakeji a zuciyarsa, wayarsa ya ɗaga tare da dannawa Nafeesa kira kasancewar yau tun safe bai samu damar waya da ita ya kira kusan sau uku da safen batayi picking call ɗin ba, kuma har yanzu bai ga ta kirasa ba Yanzun ma sau Uku yana kira ya shiga kuma bata ɗaga ba, ƙara kira a karo na huɗu Nafeesa dake zaune ita da Jamila a compaunt ɗin gidan Jamila ne ta taɓe bakinta tare da cewa Jamila.

“Wannan ɗan wahalan ne nacacce.”

Dariya Jamila tasa tare da cewa.

“Rabu da ɗan iska karki kuskura ki ɗaga kiransa wunin yau gaba ɗaya, ya kamata ya fara fahimtar sauyi saboda ya yi ƙoƙarin ja baya, Ni mutumin ya miki reply ɗin saƙon da muka tura masa kuwa.?”

Kanta Nafeesa ta girgiza tare da cewa.

“A’a bai min reply ba, amma niyata na fara bibiyarsa gobe domin nasan wasu abubuwan akansa kafin musan yadda zamu ɓullowa lamarin.”

“Kinyi tunani mai kyau hakamma yayi sai ki ƙoƙarta domin mu samu mu kashe boss ɗin da wuri a wuce wajen, mu fara sarƙa da kuɗi ƙawata.”

Dariya Nafeesa tasa tace.

“Shegiya ƙawata badai son kuɗi ba, ai muddun na samu na Aure Al’ameen zaki warke wani ma sai ya huta a ƙarƙashin ki ƙawata.”

Tayi Maganar dai-dai wayarta na kuma ringin still dai Haidar ne, tsuka taja tare da kashe wayar gabaki ɗaya, Jamila ne ta kuma tsaki tare da furta,

“Ɗan wahala”

Haidar jin an kashe wayar ya sa hankalinsa tashi domin kuwa zato yake Nafeesa bata cikin lafiya ko kuma wayar aka sake, shi dai burinsa Allah yasa tana lafiya, miƙewa yayi ya nufi sama ya haura step sukaci karo da Rufaida zata sauƙo hanunta riƙe da kaskon turaren wuta, kanta ta sunkuyar ƙasa, kallonta yayi cike da tausayi, kansa ya girgiza tare da shigewa, Rufaida kanta ta ɗago tare da bin bayansa da kallo cike da tsantsar ƙaunar sa, idanunta ne ya ciko da ƙwalla hanu tasa ta goge tana kallonsa harya shige bedroom ɗinsa sannan itama ta sauƙa.

Zama yayi bakin bed ɗinsa tunani da damuwa ne suka cakuɗe masa waje guda gefe ɗaya ga damuwar wani hali Nafeesa take ciki gefe guda kuma ga haushin Ablah da tunanin matakin da zasu ɗauka a kanta, jin hankalinsa ya kasa kwanciya ya sashi ɗaukar key ɗin motar sa ya fito da sauri domin kuwa bazai samu nutsuwa ba Muddun baije yaji wani hali Nafeesa take ciki ba bata saba masa haka ba ya kirata bata ɗaga ba, koda bata ɗaga ba tana dawowa zata biyu kiransa amma wunin yau kas 20 miss Call no reply dole dai akwai wata damuwar.

Shi kuwa Al’ameen tunda ya shigo ya tsaya tsakiyar falon yake nazari da tunani sosai hankalinsa yake tashe, to meya kai Ablah bedroom ɗin Ummi harta samu alaƙa da wannan cup ɗin, idan har da gaske Ablah itace ta kashe Ummi meye ribarta akan hakan mezata ƙaru dashi, kisan rai ba wasa bane me zaisa Ablah ta aikata idan kuma Maganar Haidar ya tabbata sakata akayi to waye ne, lallai wannan lamarin akwai lauje cikin naɗi duk wanda ya tabbata shine ya kashe Ummi to yana da alaƙa da kisan ƙanwarsa, hmmm! Yaja gauron numfashi tare da cije bakinsa, meyasa yake jin soyayyar Ablah a cikin zuciyarsa! Yaushe ne ma yayi sake son wata mace ya shiga zuciyarsa gashi yanzu har yana neman ya hanasa ganin laifinta, anya kuwa zai iya jurar gani anyi Arresting ɗin Ablah, lallai akwai matsala domin kuwa na bari zuciyata tayi sakaci? Tsuka yaja tare da dafe kansa, Aunty Amarya ce ta fito sai masifa take hango Al’ameen ya sata kwaɗa masa kira, idanunsa ya ɗago cikin sanyin jiki ya kalleta.

“Kazo ka shiga tsakanina da wannan fitsararriyar Yarinyar Samira domin kuwa ta rainani acikin gidan ban isa na faɗa mata Magana ba sai taimin rashin kunya, tana neman zagina bazan ɗauki wannan iskancin ba.”

Al’ameen cewa yayi.

“Ita Samiran ne zata zageki, kiyi haƙuri zan haura na sameta yanzu kaina ciwo yake min.”

Sai yanzu Aunty Amarya ta kula da yanayinsa duk jikinsa na sanyaye da alamu yana cikin damuwa ne tambayarsa tayi.

“Al’ameen lafiya na ganka haka meke faruwa da kukaje station ɗin.”

Numfashi Al’ameen ya saki tare da jinginuwa jikin kujerar yace.

“Labari ne marar daɗi Aunty wai wannan Yarinyar Ablah suke zargi da kashe Ummi, abin duk ya ɗaure min kai wallahi ta yaya Ablah zata iya kisan kai sun gano shatin hanunta har sau biyu jikin cup hakanne yasa suke zargin itace criminal ɗin.”

Zaro idanunta Aunty Amarya tayi tare da sakin murmushin zuci good job, lallai Ablah ta shiga cikin matsala mai fidda ita sai Allah, to amma garin yaya Ablah ta taɓa wannan cup ɗin, tayi Maganar zucin tana sakin numfashi tare da cewa.

“Tirƙashi yanzu ita Ablah ake zargi da kashe Ummin Al’ameen ɗin, kai baka yadda ba kenan, babu mamaki idan ma itace tayin kisan domin kuwa sanin mutum sai Allah, ba kuma gane mungu ake a fuska ba, amma dai wannan Yarinyar tayi asara wallahi to meye tsamarta da Ummi da zata kasheta, hmmm! Lallai mutum mungun icce, yanzu ya akayi meye matakin da za’a ɗauka akanta.”

“Police zasuzo suyi Arresting ɗinta da daddare domin ƙwarara bincike akanta domin gano gaskiya.”

Miƙewa Aunty Amarya tayi tare da cewa.

“Hakan yayi domin kuwa ya kamata ta fuskanci mummunan hukunci, kaga ka tashi ka shiga bedroom ɗinka ka kwanta da alamu kana cikin damuwa.”

Miƙewa Al’ameen yayi tare da haurawa sama Aunty Amarya dariya ta saka tare da nufar bedroom ɗin Ablah.

A bakin door ɗin ta tsaya tare da kama handle ɗin tana naɗe kayanta ta bawa door ɗin baya taji muryar Aunty Amarya.

“Shiga komata yana da matuƙar sauƙi sai dai fitarsa akwai munguwar wahala domin kuwa cike take da ƙayoyi a cikin ta, ta yadda take soke ƙafofi, ga kuma ƙullin zarena yana da wahalar warwara saboda zaren zana ne ba’a ware sa a tsaye sai dai a zugesa a kuma duk sa’ilin da kayi kuskuren zugewa zai zugewa da fatar mutum, kin faɗa tarkona ba tare da ni ko ke mun ankara ba, kawai afkawa kikayi komata, gashi kuma kin shiga cikin zargin da bazaki iya taɓa fitar da kanki ba kuma babu mai iya fitar dake koda kuwa duka duniyar nan gatanki ne, hmmm nayi shuka gashi kuma kece zaki gurbi abinda na shuka, ke ake zargi da kashe Hajiya gaji sai ki tanadin kalaman da zaki kare kanki dama na faɗa miki muddun baki dawo zagi na ba, to kuwa zaki ƙare rayuwarki ne a cikin garari domin kuwa azaba da wahala su zaki ta fuskanta, ba dai kince da Amarya zaki gabza ba to mu zuba mu gani…”

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Aminaina Ko Ita 25Aminaina Ko Ita 27 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×