Juyowa Ablah tayi a nutse ba tare da tsoro ko firgici ba fuskarta kuma cike da murmushi take kallon Aunty Amarya tare da cewa.
“Ban shiga komar taki ba bare nayi tunanin wahalar fitowa, shi kuwa zaren zana a ba dole sai an zugesa ba, akan iya waresa da ɗaɗɗaya a tsigesa ba dole sai an zuge ba bare kuma yayi mungun illa, ban faɗa tarkonki ba bare kuma na shiga danasani da tunanin yadda zan fito, ke koda ma faɗa ƙafata dutse ce ƙaya bazai iya soketa haka zan taka waɗannan ƙayoyin tamkar na taka biredi na fito lafiya, na yarda na amincewa zalunci ki wannan shine na faɗa tarkonki, wani irin zargine zan shiga gaskiya ta kasa fitar dani, da akwai zargin da gaskiya bata haskasa to Tabbas da izuwa yanzu wannan duniyar ta gama rufewa da duhu, gaskiya itace sama da zalunci babu ta inda ƙarya zata taɓa danne gaskiya, nine da gaskiyar ke kuma kece azzalumar dole dai nice zan danneki, yanzu kin shigo ne ki razana ni, hmmm to bazan tsorata ba Saboda zuciyata kyakkyawa ce duk halin da na shiga sai kyawun zuciyata ta fito dani, Saboda na riga da nasan cewa dole zan shiga cikin zargi tun ranar da mukayi gwajin finger domin kuwa nayi arba da cup ɗin har sau biyu da hanuna, abinda na sani kike maimaita min, amm kin ce na tanadi kalaman da zan kare kaina ko? To ai abinda ke baki sani shi mai gaskiya baya tanadar kalaman faɗi ko nace kare kai domin kuwa cike suke a zuciyarsa da bakinsa saboda shine yasan komai kuma yake da gaskiya, marar gaskiya shine yake tanadar kalaman kare kai domin kuwa a dabaibaye yake da duhu zuciya kuma babu kyau, shiyasa zai rasa abun faɗi, ki koma gefe kiyi kallon ya zata kasance domin kuwa duk tsananin zan shiga sai gaskiya ta wankeni.”
Zaro idanunta Aunty Amarya tayi cike da munguwar razana da maganganun Ablah take kallonta madadin ta tsorata shine ma murmushi take to meta taka, meye nufinta da waɗannan maganganun tana nufin zata tona mata asiri ne ko yaya, Numfashi ta saki tare da harɗe hanunta tace.
“Kina ja dani kenan har yanzu, baki saduda ba, hmmm ke mai gaskiya ko, to fa mu gani kafin gaskiyar ta fitar dake wace kalar wahalar zakisha, dole dai jiki zaisha laushi koma za’a dawo, amma ki sani yau dai *Kere ya haɗu da zabuwa, kinsan kuwa baza’a kwashe da kyau ba* bara na koma gefen nayi kallo muga ya wasan zai ƙare.”
Tayi Maganar tana murmushi tare da ficewa daga bedroom ɗin Ablah, tana fita Ablah ta zauna daɓas zuciyarta na mungun bugawa hawaye ne suka wanke mata fuska, cike take da tsoro, ko wannan amsar data maidawa Aunty Amarya tayi ne kawai saboda kar Aunty Amarya taga kasawarta taji daɗi, wai ita ake zargi da kisan kai, ” innalillahi wa’inna ilaihirraji’un meyasa za’a zargeni bayan ansan bazan iya kishe koda sauro bane bare kuma ran Mutum, yanzu kenan duk gidan nan suna min kallon munguwa ce, waye zai yarda dani gashi bani da gata wani irin kallo Inna Jumma da Al’ameen zasu min, ba kowa bane zai yadda dani, Innalillahi wa’inna ilaihirraji’un! Ya Allah kana kallon halin da nake ciki, ban zalunci kowa ba, Allah karka bari a zulunce ni, ya Allah karka nunawa maƙiyana tozarta na, ya Allah ka zamo gatana Allah ka rufa min asiri na, ya Allah karka bari a cutar dani bani da haƙƙin kowa”
Tayi addu’ar tana jinginuwa jikin drowern sosai take kukan harda ajiyar zuciya, domin kuwa hankalinta yayi mungun tashi, ta ina zasu iya Shari’a da ahalin *AHMAD GIWA* Idan har aka amince da sharrin Aunty Amarya a kanta, Aunty Amarya zata iya komai domin ganin laifin ya tabbata a kanta, idan kuwa tayi haka Tabbas rayuwarta ne zai salwanta a banza kuma baza’a fasa kisan ba, sosai ta cigaba da rera kukanta cike da damuwa wayar da Hafsa ta bata ta raruma da sauri tare da dannawa numbern Hafsa kira switch off hakanne ya tabbatar mata bata ɗaura layin akan waya ba, numfashi ta saki tare da kuma sakin kuka mai sauti numbern ummanta ta kira shima akashe yasar da wayar tayi ta saki kuka mai sauti tana rufe bakinta da tafin hannunta.
Yayin da shi kuwa Al’ameen tunda ya shiga bedroom ɗinsa ya kasa nutsuwa sai kaiwa da komowa yake zuwa yanzu ya fara shakku akan Ablah to meyasa za’a samu shatin yatsun ta har sau biyu a jikin cup ɗin.
“Mtsss! Sannan ai sanda yake ihun mutuwar Ummi kafin ya sanar da ita Ummi ta rasu ita fara tambayarsa cewa Ummi ta mutu ko? To meyasa ta min wannan tambayar idan ba tana da alaƙa da mutuwar ba? Hummm! Shikenan ta kasheta ta huta! Ta faɗa min wannan kalmar ma, sannan tace ita bata faɗa min haka ba, kuma Tabbas naji ta faɗa tayi amfani da ruɗun da nake ciki tace bata faɗi haka ba, koma ba ita tayi kisan ba tasan wanda yayi! Amma dai bari mu jira binciken hukuma.”
Yayi Maganar yana zama jin ya kasa nutsuwa ya sashi tashi ya shige tollet tare da sakawar kansa shower ko zai samu nutsuwa Saboda zuciyarsa ta kasa gida biyu wani ɓangaren na nuna masa yarinyar bazata iya kisan kai ba, wani ɓangaren kuma yana gwada masa zai yiwu ita ɗin ce.
Tunda Aunty Amarya ta shigo bedroom ɗinta hankalinta ya tashi domin kuwa bata ga Ablah ta shiga wani hali ba, babu alamun tsoro a zuciyarta hakan yana nufin akwai abinda ta taka karfa yarinyar nan ta kira sunanta a station zargi ya fara biyowa kanta, lallai akwai matsala, wayarta ta jawo ta dannawa Hajiya Mansura kira miss Call ɗaya ta ɗaga tare da cewa.
“Ƙawata ya akayi kwana biyu na jiki ɗib kamar anyi fari, ya akayi domin kuwa idan naga kiranki ta ɓaci ne, menene matsalar?”
Numfashi Aunty Amarya ta saki tare da cewa.
“Ke dai bari ƙawata bata ɓacin ba dai tukunna amma tsoron ɓacin yasa na kiraki, Yarinyar nan fa ita ake zargi da kashe Hajiya gaji, Ablah, sannan tamin wasu kalamai wanda suke nuni da kamar zata tona mana asiri, yanzu ya kike ganin za’ayi domin kuwa babu tsoro afuskarta na wanda ake zargi da criminal Case.”
Murmushi Hajiya Mansura tasa tare da cewa.
“Sanar dani me tace miki da ta saka miki tsoro a ranki?”
Numfashi Aunty Amarya ta saki tare da sanar da Hajiya Mansura yadda sukayi da Ablah dariya Hajiya Mansura ta saka tare da cewa.
“Ɗan wannan maganar itace ta ɗaga miki hankali, ta yaya zata iya ambaton sunanki a cikin Case ɗin bayan tasan babu wani shaidar da zai nuna akwai hanunki aciki koda kuwa ta faɗa babu abinda za’a samu a tattare dake, ke dai abinda zakiyi yanzu kiyi taka tsantsan da kowa ki zamo a ankare karki yadda koda da wasa kiyi kuskuren wani motsi na aikin da kike, kiyi ɗib ki bar komai har sai ƙura ta lafa anrufe wannan babin Case ɗin, sannan zamu duba mu gani ta wacce hanya zamu fidda ita Ablah domin kuwa muna da buƙatar ta a cikin gidan, idan har tana cikin gidan to fa ko wani yayi muka kwaso akanta zamu watsa, ni nasan yacce za’ayi ta fito koda ta shiga hannun hukuma, saboda zamu maida ita juji ne wajen zuba sharar mu, ki jira har ta dawo kafin mu ɗaura a inda muka tsaya, karki damu asirinki bazai ta ɓa tonuwa ba ina tare da ke a sannu zamu jefa zazzafar ƙyayyarta a zuciyoyin masu gidan ta yacce zasu ƙyamace su da kansu zasu ɓatar da ita, bata da damar magana a kanki saboda koda ta faɗa reshe ne zai juye da mujiya.”
Sai Yanzu Aunty Amarya ta samu nutsuwa numfashi ta sauƙe tare da sakin murmushi tace.
“Na fahimta ƙawata, na kuma kwantar da hankalina domin ina da ke, amma ki sani Yarinyar nan idan ta cigaba da takura min zansa ayiwa shegiya fyaɗe.”
“Karki damu ƙawata mu dai bi komai a sannu za’a kai wannan matakin ma, amma dai ba yanzu ba.”
“Shikenan sai munyi waya.”
Dariya Hajiya Mansura ta saki tare da katse kiran.
Shi kuwa Haidar a ƙofar gidan su Nafeesa ya tsaya tare ƙara gwada numbern ta switch off ta kasheta, Numfashi ya saki ya ɗan juma tsaye kafin ya hango wani yaro kiransa yayi tare da aikansa ya shiga cikin gidan su Nafeesa ya ce wai Haidar yana Sallama da ita, yaron shiga yayi bai juma ba ya fito yace masa.
“Wai inji mamanta bata nan ta fita unguwa tun safe ita da ƙawarta.
Shuru Haidar yayi yana nazari to anya kuwa suna lafiya.
“Okay amm dan Allah koma kace wai a bani numbern Amnat.”
Da to yaron ya amsa yana komawa bai juma ba ya fito da Number a rubuce a takadda ya bawa Haidar karɓa yayi tare da bawa yaron ɗari biyar ya masa godiya numbern Amnat ɗin ya saka a cikin wayarsa ya kira ringin ɗaya ta ɗauka.
“Hello! Dawa nake Magana?”
“Sorry kina Magana da Haidar ne, Allah yasa dai da Amnat nake Magana?”
Shuru Amnat tayi jin Haidar ne, cike da tausaya masa domin kuwa tasan maybe akan Nafeesa ya kirata.
“Kinyi shuru.”
“Sorry Haidar ehh dani kake Magana ya kwana biyu ka ɓuya mana fa da yawa kasan ku manyan nan wahalar gani kuke.”
Ɗan murmushi Haidar yayi jin muryar Amnat cikin farin ciki ya sashi zaton itama Nafeesa tana halin lafiya.
“Ko dai ke kinyi wahalar gani ba, amm ina mutumiyar kuna tare ne, na kira numbern ta batayi picking ba, daga ƙarshe dai sai ma naji an kashe wayar, so nazo gida yanzu sai Mama tace kun fita tun safe shine na karɓi numbern na kira naji ko lafiya.”
Girgiza kanta Amnat tayi, tana tausayawa halin da Haidar zai shiga sanda ya gano Nafeesa ba sonsa take ba yaudarar sa take saboda abin duniyarsa, domin kuwa da alamu yana mata matsanaciyar Soyayya.
“A’a ba tare muka fita da Nafeesa domin kuwa yau tun safe bamu haɗu ba, sai dai muyi waya da ita da safe ta sanar dani zasuje ƙauye da ƙawarta Jamila anyi musu rasuwa sunje gaisuwa maybe suna cikin ƙauyen ko ba service ne kasan ƙauye ba’a cika samunsu da sarvice ba, amma insha Allah da zarar ta dawo nasan komai dare zata neme ka amma dai tana lafiya.”
Tayi masa ƙaryar Saboda bata son yaji komai a bakinta numfashi Haidar ya saki sai yanzu hankalinsa yaɗan kwanta.
“Okay to shikenan ba damuwa na gode Amnat ki gaishe da Mama.”
Yayi Maganar yana katse kiran, Amnat numfashi ta saki tare da turawa Nafeesa text message.
Haidar ya kirani hankalinsa yana tashe yace tun safe yake kiranki bakiyi picking call ɗinsa ba, ƙarshe ma dai wayar kin kasheta, na masa ƙaryar kinje ƙauye keda Jamila gaisuwar mutuwa, so idan kinga sako na, na dai sanar dake yadda mukayi dashi, a ƙarshe ina tuna miki da cewa kiji tsoron Allah ki guji ranar sakamako domin kuwa babu makawa Jamila sai ta ci amanar ki domin kuwa ita ɗin maciji ce bata ramin kanta sai na wani kibi a hankali.
Ta tura mata sakon tana ijiye wayar shi kuwa Haidar Company ya shige cike da tunani.
8:30pm
Da misalin ƙarfe takwas da rabi na dare gabaki ɗaya suna zaune cikin falon suna hira Haidar da Faruq suna zaune tare suna hira yayin da Al’ameen ke gefen su yana aiki da system ɗinsa, can gefe kuma su Aunty Amarya ne da Maimu Afnan samira da kuma ihsan Inna Jumma suna gefe itama da Daddy suna tattaunawa akan matsalolin gidan ko kaɗan Inna Jumma bata da labarin cewa Ablah ake zargi da kisan Ummi.
“Ina sauraranka Amadu, ya kukayi da kawun naka, yamin magana cewa za’ayi Auren ƴarsa hindu yana buƙatar ai mata kayan ɗaki kasan dai ba ƙarfi garesa ba, dan haka sai kayi ƙoƙarin ka aika masa da kuɗin da kuma wanda zaiyi hidimar Auren dasu?”
“Ehh Inna ya kirani jiya ya sanar dani harma ɗazu naje na masa TRANSFER na 1m ta account ɗinsa mun gama dashi.”
Murmushi Inna Jumma tayi tare da cewa.
“To to masha Allah ka kyauta Allah ya maka albarka ya maida sabon samu.”
Tana rufe bakinta police suna sallama, Daddy da kansa ya amsa yana musu iso tsakiyar falon suka shigo.
“Ranka shi daɗe Dpo ne ya turo mu zamuyi Arresting ɗin Ablah Yahya Sani, wacce hukuma ke zargi da kisan Gaji Ahmad Giwa, ga nan takaddarar umarni.”
Tunda suka fara Maganar Inna Jumma ke kallonsu cike mungun mamaki wai Ablah ake zargi da kisan kai, miƙewa tayi a hasale tare da furta.
“Kai me naji kuna faɗi ita ablar ake zargi da kashe Gaji.?”
Kansa police ɗin ya ɗaga tare da cewa.
“Yes Ma ita ake zargi muna son ganinta zamu tafi da ita.”
Al’ameen ɗago idanunsa yayi yana kallon Inna Jumma, a yayin da Maimu da Afnan suke mamaki, Aunty Amarya kuwa murmushi ne ke bayyana a fuskarta, tsalle Inna Jumma tayi ta dire tare da cewa.
“Ai kuwa ƙarya hukumar taku take domin kuwa banda dai Ablah kam ku dai tuno wacce aka aiko ku ku tafi dashi badai Ablah ba.”
Haidar ne ya miƙe tsaye ba tare da yace komai ba ya shige bedroom ɗin Ablah Faruq taɓa Al’ameen yayi tare da cewa.
“Ban gane abinda ke faruwa ba, is true Ablah criticism criminal Case, anya kuwa binciken su yayi dai-dai abun da mamaki mtsss! No gaskiya ƙarya ake yiwa wannan Yarinyar bana tunanin zata aikata wannan laifin yaushe ma tazo gidan.”
“Kaima ka faɗa Faruq,ni kaina lamarin ya sarƙe min amma nasa a min bincike zan gano komai insha Allah zuwa gobe idan ma tana da laifi ko bata dashi zan gano, suje da ita dan Allah karkayi magana domin da alamu Haidar baya aiki da lissafi zaku iya samun matsala dashi yanzu idan kayi Magana.”
Kafaɗarsa Faruq ya ɗaga tare da furta “well”
Inna Jumma ce tace.
“Ku koma wajen wanda ya aiko ku ku kamata kuce masa ni Inna Jumma nace bazata zo ba saboda binciken ku ƙarya ne sabida…”
“Ku rabu da ita kuzo kuyi aikin ku gata nan na fito muku da ita.”
Sukaji muryar Haidar kafin Inna Jumma ta idda maganarta, Ablah da kallo take bin Haidar zuciyarta na tsinkewa domin kuwa ta masa uzuri baisan gaskiya ba da bazai ci mata mutunci ba, nufar Ablah police din yayi yana zaro ankwa Inna Jumma tayi saurin tare gabansu tana nuna Haidar da yatsa.
“Ka fita a idona na rufe dan ubanka baƙin munafuki, wato gaka tantiri bara kaje ka fito da ita ko ta naga ta yacce za’ayi a tafi da ita”
Tayi Maganar tana huci tare da kallon police ta cigaba da cewa.
“Ku kuma na dawo kanku, Uwar kuturu ma tayi kaɗan balle ta makaho ku tozarta wannan Yarinyar ku fita kubar gidan nan tunda bana hukumar bane.”
Daddy miƙewa yayi tsaye zai yiwa Inna Jumma Magana Al’ameen ya girgiza masa kai tare da miƙewa ya nufi wajen nasu hanun Ablah ya kama zuciyarsa na masa suka yace….