Skip to content
Part 31 of 67 in the Series Aminaina Ko Ita? by Rasheedat Usman

Kanta Ablah take girgizawa kamar ƙadangare, idanunta sunyi jajur zuciyarta sai hura take, har wani irin numfashi mai zafi take fitarwa Kanta ta kuma girgizawa muryarta yana rawa ta hau cewa.

“Wallahi Allah bani na kasheta ba bansan komai ba akan wannan kisan.”

Murmushi Dsp Habu Sarki yayi yana ƙura mata idanu alamun gaskiya yake hangowa ƙarara a idanunta a matsayin sa na hukuma dole yana iya bambance mai gaskiya da kuma marar gaskiya amma sai dai hakan bashi zaisa ya sassauta mata ba, Saboda ita Shari’a saɓanin hankali ne, sai kaga mutum sak na ƙwarai amma zuciyarsa baƙiƙƙirince.

“Ablah! Kina wahalar da Shari’a na sani kece kikayi wannan kisan ina hujjar hakan a hanuna ina sone ki amsa da bakinki idan kuma kinƙi zan fito da wannan hujjar kuma hukuncinki bazaiyi kyau ba, tell me ki faɗa min gaskiya idan har kika faɗa min gaskiya zan rufa miki asiri.”

Kanta Ablah ta sunkuyar ƙasa hawaye basu daina tsere saman fuskarta ba.

“Koda zaku saka a kasheni ne ko da kuwa yankar naman jikina zaku dinga yi har na mutu ƙarshen azaba bazan amsa laifin da ban aikata ba, idan har kana da hujjar na yadda ka fito dashi karkuma kumin sassauci ku munana min azaba mafi muni na yadda.”

“Okay to ya akayi kika ɗauki cup ɗin da aka sawa Hajiya Gaji guba har sau biyu a hanunki, menene dalili?”

Kan Ablah yana ƙasa har yanzu tace.

“A ranar da Ummi tasha wannan gubar na shiga cikin bedroom ɗinta, na sameta zaune ta fito daga wanka, na gaisheta har zan fita daga room ɗin sai Ummi ta kirani tamin nuni da wannan cup ɗin tace na miƙo mata, ni bansa komai ba na ɗauka na bata na fita abuna, ban juma da fita ba sai mukaji ihun Yaya Al’ameen da gudu muka haura bedroom ɗin Ummi tana kwance sai riƙe cikinta take kumfa na fita daga bakinta.”

Tayi Maganar tare da yin shuru, murmushi Dsp Habu Sarki yayi tare da cewa.

“Naji wannan tatsuniyar, sau biyu yatsunki suka fito a jikin cup ɗin na biyun kuma ya akayi?”

“Bayan Ummi ta rasu na shiga bedroom ɗin ganin yaya Al’ameen ya faɗa bedroom ɗin yana kuka a nan ma na kawar da cup ɗin gefe?”

Shuru Dsp Habu Sarki yayi yana duban agogon hanunsa, miƙewa yayi ya fice tare da bawa Sargent Merry umarnin ta mayar da ita ɗakin duhu, haka kuwa akayi ta mayar da ita cikin ɗakin duhun, wani irin kuka ta saka mai cin zuciya, ga wani tsoro da ya ziyarce ta, tana mungun tsoron duhu a rayuwarta, wani irin haushi da tsanar Aunty Amarya take ji a zuciyarta Tabbas ta ɗauki aniyar ɗaukar fansa akan Amarya dole sai ta girbi abinda ta shuka bazata taɓa barinta ta kuma samun nutsuwa ba, domin kuwa ta ɓata mata suna ta sanya mutanen cikin gidan suna mata kallon azzaluma, numfashi ta saki tare da rakuɓewa jikin bango jikinta sai ƙyarma yake, ji take tamkar wani abu zaizo ya cinyeta.

Tunda ya shiga cikin Office ɗinsa ya kasa samun nutsuwa, damuwa ne ya dagula masa zuciyarsa, ya kasa jure damuwar sa, bai san wani hali Ablah take ciki ba, amma dai yasan dole bata cikin kwanciyar hankali, idanunsa ya runtse tare da jawo wayarsa, khalil zai dannawa kira yaji an turo door ɗin Office ɗin, idanunsa ya ɗaga ya kalli door ɗin, khalil ɗin ne ya shigo numfashi Al’ameen ya saki tare da cewa.

“Yanzu kuwa nake da niyyar kiranka.”

Zama khalil yayi tare da cewa.

“Na jika shuru ai shiyasa na ce bara nazo na kawai.”

“Hakane na ɗan biya unguwa ne nida Haidar, ya ake ciki?”

“Eh to gaskiya nayi duk binciken daka sani daga unguwar Durmi har zuwa primary school da secondary school da Yarinyar tayi banji abokin faɗanta ba, sannan ko ƙawa ma bata dashi ƙawarta ɗaya ce wata Hafsa ƴar maƙwaftansu itace kawai ƙawarta, asali ma Yarinyar bata yawo daga gidan su sai makaranta ta gama yawo shine taje gidan su Hafsa, itama Hafsan nayi bincike akanta kusan halinsu ɗaya basu da wani mummunan record gaskiya.”

Ajiyar zuciya mai sanyi Al’ameen ya saki, mutum Uku yasa suka masa bincike akan Ablah kusan amsa ɗaya suke dawo masa dashi sai yanzu ya ɗan samu sukuni ya kuma yarda da zuciyarsa da take nuna masa Ablah bata da laifi, duban khalil yayi tare da cewa.

“Na gode Khalil, yanzu abinda zai faru zan tura maka kuɗi ta account ɗinka zuwa dare gobe sai kaje ka yiwa gidan su ABLAH siyayyar kayan abinci naga wata tayi ƙarshe.”

Da to khalil ya amsa yana miƙewa tare da yin musabaha ya tafi. 

Sai yanzu hankalin Al’ameen ya kwanta domin kuwa yasan ƙarshen binciken dai dole za’a sake Ablah ta dawo gida wayarsa ne tayi ringin, dubansa ya kai ga wayar wannan dai numbern ne da ta turo masa saƙo, tsuka yaja tare da jawo system ɗinsa ya hau aikin gabansa baifi da kusan 15 minute ba text ya shigo cikin wayar.

“Kana azabtar da zuciyata da rashin jin muryar ka, burin masoyi yaji Muryar abun ƙaunarsa koda kuwa bai gansa ba, wannan muryar zata taimaka masa wajen samun nutsuwa, Please my dear ka ɗaga kirana dan Allah ko zanji sanyi.”

Kansa Al’ameen ya girgiza yana taɓe bakinsa.

“To wai ita wannan wayece kam take neman addabar rayuwata, to koma waye ce bazaki taɓa samun zuciyar Al’ameen ba, domin ya daɗe da malllakawa wacce ta dace da rayuwarsa.”

Yayi Maganar yana ijiye wayar ya cigaba da aikinsa.

Shi kuwa Haidar tunda ya zauna a Office ɗinsa ya gagara aikin komai tsoro da fargaba duk ya damesa domin kuwa sauyi yake hangowa a fuskar Nafeesa da alamu akwai abinda ke faruwa gashi bata sanar dashi komai ba, dole zai mata uzuri yasan Nafeesa bazata taɓa juya masa baya ba, numfashi ya saki yana dafe fuskarsa wayarsa ya ɗaga wacce yasa IB ya je gida ya ɗauko masa tare da danna mata kira 5miss call Nafeesa batayi picking ɗin Call ɗinsa ba.

“Meke shirin faruwa ne Nafeesa 5 miss Call, taƙi ɗaga min waya to ko dai bata kusa da wayar ne, mtsss ya kamata nasan meke faruwa.?”

Yayi Maganar yana kwantar da kansa jikin kujera tare da yin shuru cikin tunani, haka Haidar ya wuni cikin wannan damuwar.

“Ina jinki jameela.”

“Ba wai maganar kina jina bane kamata yayi ki tashi ki tsaya game da lamarin wannan Al’ameen ɗin domin kuwa idan kika tsaya kallon ruwa to kwaɗo zai miki ƙafa domin kuwa da alamu wannan mutumin bushashshiyar zuciyace dashi.”

Numfasawa Nafeesa tayi tare da gyara zamanta taja gauron numfashi tare da cewa.

“Jamila ni kaina fa lamarin nan yana damuna wallahi, akwai wata shawara da Amnat ta bani kwanaki akan Haidar cewa akwai wani malami yana aiki sosai kuma aikinsa yana ci da cewa tayi na kai sunan Haidar wajen Malamin duk abinda na tambaya babu musu zai bani to a gaskiya nine naƙi saboda zuwa wajen malamai bawai ya dameni bane, amma yanzu ina ji a zuciyata me zai hana kawai na kai sunan Al’ameen.”

Dariya Jamila tasa tare da cewa,

“Shegiya Amnat Uwar bin bokaye, kinga ƙawata, a yanzu bama buƙatar zuwa wajen wani boka, idan har mukaje wajen boka bamu amsa sunan mu ƴan bariki ba, menene amfanin barikin, da ƙwarewar mu da tuggun mu, zaki mallakesa, amma yanzu kinsan me zai faru ki cigaba da kiransa kina tura masa saƙwannin idan har yaƙi sauraronki to zamu fito masa a mutum.”

“To amma Jamila har yaushe zamu zauna muna jiran sai ya maido min da reply a yanda na fahimci wannan mutumin fa koda shekara zanyi ina tura masa saƙwanni bazai saurareni, gara kawai na fito masa a mutum ɗin.”

Ta ƙarisa Maganar dai-dai wayarta na ringin, dubanta ta kai ga wayar tare da jan tsuka Haidar.

“Wake kiranki ne kike tsuka.?”

Jamila ta jefa mata tambayar, bakinta Nafeesa ta taɓe tare da cewa.

“Hmmm! Wannan marar zuciyar ne Haidar.”

Murmushi Jamila ta saki tare da cewa.

“Ɗaga wayar ƙawata, muna bukatar kuɗi ma ai ko kin manta birthday ɗinki on 20 ne, ɗaga ki nemi wannan kuɗin a wajen sa.”

Bakinta ta tura tare da ɗaga wayar tana yamutsa fuska sallama tayi, daga can Haidar ya amsa yana cewa.

“Wai ina kike ijiye wayar kine nata kira bakya ɗauka?”

“Bana kusa da wayar ne, yanzu kuma da ka kira ina kusa aina ɗauka, ya aikin?”

Murmushi Haidar ya saki yace.

“Hakane dama na kira naji muryar kine, ko zan samu nutsuwa, Nafeesa ina sonki, son da bansan iyakarsa a cikin zuciyata ba, ji nake bazan iya moruwa ba idan babu ke, shiyasa hankalina yake tashi idan na kiraki baki ɗauka ba.”

Yayi Maganar dai-dai Al’ameen na da Faruq suna shigowa cikin Office ɗin nasa tare da zama suna zuba masa idanu, Nafeesa kallon Jamila tayi tare da taɓe bakinta tace.

“Na sani Haidar kana sona amma bana son kana zurfafawa da yawa cikin soyayya Saboda rayuwa takan juyawa ta hanyar ƙaddara, yanzu dai ba wannan ba, yau muna 18/07/2021 gashi on 20 zanyi birthday party na, ina buƙatar kuɗaɗe da zanyi hidima dasu.”

Numfashi Haidar ya saki tare da cewa.

“Birthday kuma Farin ciki na, me zai haɗaki da BIRTHDAY party kina kamilar mace mai nutsuwa da ilimi, amma kamar nawa kike buƙata zasu miki hidimar?”

“200k sun isa, yanzu ina unguwa zan kashe wayar sai naga saƙon.”

Tayi Maganar tare da katse kiran ba tare da ta jira taji me zaice ba, dariya Jamila tayi tace.

“Good ƙawata kinga ba sai kuɗinki ya tafi ba, nasa sun isheki hidima shima wannan tsohon najadun ki samu ki amshi wani abu wajen sa Alhaji Atiku Naira.”

“Ke kina jin ɗan iskan Haidar ɗin nan abinda yake cemin, wai me zai haɗani da BIRTHDAY party sai kace a islamiyya ya ɗaukoni.”

Dariya Jamila tasa har tana sunkuyawa tace.

“Wai da meya ɗaukeki uztaziya ƴar islamiyya, kai lallai wannan gayen yaci kai, rabu da wannan maganar time ɗin shiga class yayi kafin wannan ɗan masifar lecturer ɗin ya rigamu shiga.”

Tayi Maganar suna miƙewa tare da nufar class ɗin nasu.

Al’ameen dubansa yayi tare da girgiza kansa yace.

“Zaka haukace abanza Haidar akan wata mace marar tarbiyya.”

“Marar tarbiyya.?”

Haidar ya furta yana kallon Al’ameen kansa Al’ameen ya ɗaga tare da furta.

“Yess marar tarbiyya mace mai tarbiyya da kamun kai bazata ambaci BIRTHDAY party ba, ko da yake kai kana mata kallon kamilar macece, amma ko a idanu batayi kama da mata masu hankali da ilimi ba, zuciyarka tasa tunaninka yana neman kufce maka Haidar dan Allah ka rabu da wannan Yarinyar, kaje ka nemo ƴar mutunci, Faruq na rantse da Allah bazan maka kaffara ba, Yarinyar da Haidar ke so tafi min kama da sheɗanun ƴan barikin nan, ka rabu da ita Haidar gara ma ka sawa kanka Soyayyar Rufaida ina ga sai yafi maka alkairi.”

A matuƙar harzuke Haidar ya ɗago yana kallon Al’ameen ransa a ɓace yace.

“Sheɗanun ƴan bariki, Al’ameen Please dan Allah ka daina aibata Nafeesa Saboda kawai zuciyarka bata ƙaunarta, ni ina sonta koma yaya take ko karuwa ce, na yadda tayi istibira’i ni zan aureta ka cire idanunka a kaina da Nafeesa.”

Numfashi Faruq ya saki tare da cewa.

“Haidar bai kamata kace ya cire idanunsa akan…”

Hanu Al’ameen ya ɗagawa Faruq tare da cewa.

“Bar Maganar Faruq in dai nine na cire idanuna akanku sai dai ka sani, zaka tuno maganata wata rana.”

Yayi Maganar tare da miƙewa yabar wajen ya koma Office ɗinsa, wayarsa ya samu an masa 10 miss Call wannan dai numbern ce, tsuka yaja tare da kashe wayar gabaki ɗaya yana jinjinawa rashin zuciyar wannan mai kiran.

“Haidar bana son kuna samun saɓani da Al’ameen akan mace mtsss dan Allah ku daina irin haka.”

“Mtss kai yanzu laifina ka gani kenan, okey naji tashi mu tafi.

Tsaye Al’ameen yake ya kasa zaune ya kasa tsaye, Ablah ce take yawo a cikin zuciyarsa, zatayi kwanan cell kwanan wahala meyasa ma ya Kaita, mtss yaja tsuka tare da zama bakin bed ɗin nasa yana kallon agogon bangon dake manne cikin room ɗin 12pm idanunsa ya lumshe, tare da saka hanu ya jawo system ɗinsa ya buɗe saƙo ne ya shigo ta cikin e-mail ɗin sa dake kan system ɗin, dannawa yayi ya shiga cikin saƙon.

Meyasa zaku kama wacce bata da laifi ku saka a wulaƙantata duk gari suna muku kallon Mutanen kirki masu adalci ga talakawa ita ƴar aikin gidan ku da kuke zargi da kashe kashen da ake muku to ba ita bace, domin kuwa ina da labarin wanda yake muku wannan kisan ya shirya kasheka gobe da misalin karfe 11 na safe a hanyarka ta zuwa aiki, sai kasan yadda zaka kare rayuwarka.

Idanunsa Al’ameen ya zaro tare da miƙewa tsaye ya furta.

“What! Ni kuma ake hari yanzu?”

Wayarsa ya jawo tare da dannawa Haidar kira, kusan miss Call Uku yayi masa baiyi picking call ɗin ba.

Tsuka Al’ameen yaja tare da dafe kansa yana runtse idanunsa, wayarsa ne tayi ringin Haidar, saurin saka hanu yayi ya ɗaga wayar tare da cewa.

“Haidar akwai matsala, fito ka sameni a compound.”

Yayi Maganar yana katse kiran tare da ɗaukar wayarsa ya fito gidan shuru babu kowa kowa yana bacci.

A compaund ɗin ya tsaya, Haidar ya hango Isowa Haidar tare da tsayuwa kusa da Al’ameen yace.

“Lafiya yanzu na farka naga kiranki hankalina ya tashi da kace min akwai matsala tell me what problem?”

Numfashi Al’ameen ya saki tare da jan hanun Haidar suka koma bedroom ɗinsa, system ɗin sa ya jawo tare da nunawa Haidar saƙon da aka turo masa, sanda Haidar ya karanta saƙon ya ɗago kansa ya dubi Al’ameen tare da cewa.

“To yanzu kuma kaine next target ɗinsu, hmmm! “

Dafe kansa yayi tare da cewa.

“Ina Ablah take?”

“Wani irin tambaya kake min Haidar wannan saƙon daka karanta ya isa ya nuna maka cewa Ablah tana hanun hukuma.”

“Ta yaya zan sanar da kai Haidar bayan a halin da ake ciki yanzu kafi kowa nuna zargin Ablah dama fa ni zuciyata bata amince da Ablah ce tayi wannan kisan ba, mtsss menene solution?”

“Hakane na zargi Ablah amma wannan saƙon bashi zaisa na yarda cewa ba ita bace tayi kisan, har yanzu ina zarginta domin kuwa zai iya yiwuwa an shirya hakanne domin su ceto ta daga hannun hukuma, ƙarshe kuma kaga babu wani hari da za’a kawo maka…”

<< Aminaina Ko Ita 30Aminaina Ko Ita 32 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×