Dariya ICO yasa tare da cewa.
"Kai Abokina ka sani ko sabon kamu kayi, ko wata ƴar kyakkyawar ce take son tayi wuf da kai."
Murmushi Al'ameen yayi tare da girgiza kansa yace.
"Oh Ibrahim kana da matsala to ai ni na daɗe da yin wuff da muradin zuciyata, ko saboda ban sanar da kai bane kake tunanin zan kula wata, kaga ita fa wannan wanda take turo min saƙon nan kallon mahaukaciya nake mata, kasan a Rayuwata na tsani naga mace tana bibiyar namiji da sunan Soyayya raina mata wayo nake na mata kallon marar aji. . .