Skip to content
Part 34 of 67 in the Series Aminaina Ko Ita? by Rasheedat Usman

Dariya ICO yasa tare da cewa.

“Kai Abokina ka sani ko sabon kamu kayi, ko wata ƴar kyakkyawar ce take son tayi wuf da kai.”

Murmushi Al’ameen yayi tare da girgiza kansa yace.

“Oh Ibrahim kana da matsala to ai ni na daɗe da yin wuff da muradin zuciyata, ko saboda ban sanar da kai bane kake tunanin zan kula wata, kaga ita fa wannan wanda take turo min saƙon nan kallon mahaukaciya nake mata, kasan a Rayuwata na tsani naga mace tana bibiyar namiji da sunan Soyayya raina mata wayo nake na mata kallon marar aji shiyasa nake takaicin Rufaida da take bibiyar Haidar duk da ɗan uwanta ne, na rasa meyasa mata suke haka yanzu.”

Murmushi Ico yayi tare da cewa.

“Zamani ne kawai ya lalace Al’ameen duk da ba haramun bane dan Mace ta furtawa namiji Soyayya, amma yanzu muna zamani ne da maza ke yiwa mata wahala, shiyasa suke bibiyar maza, idan har naga Mutum da ƴaƴa mata da yawa a gabansa sai naji tausayin sa, saboda wahalar Aure, wallahi abokina idan har Allah ya baka ƴa Mace to ka fara mata addu’ar samun miji na gari tun sanda ta faɗo duniya, domin Jinkirin Aure masifa ce babu abinda ya kaisa baƙin ciki, Allah dai yasa mu dace.”

Numfashi Al’ameen ya saki tare da runtse idanunsa, ya furta.

“Ameen ya Allah, rayuwa sai addu’a, dan Allah Ibrahim kayi ƙoƙarin min tracker na numbern zan turo maka yanzu.”

Da to Ico ya amsa tare da yin sallama suka katse kiran, tura masa numbern Al’ameen yayi tare da kwanciya ya zubawa silin Ido yana jin zafin abinda aka yiwa Ablah, itace da ciwon amma ya fita jin ƙunar ciwon a cikin ƙirjinsa.

Haidar ko da suka tashi daga Company Office ɗin Al’ameen ya nufa, sakatariyar sa tana zaune ya shige babu kowa cikin Office ɗin sai tarin takaddun dake ajiye ga system ɗinsa a kunne.

“Ina Kuma Al’ameen ya shiga.?”

toilet ya ƙwanƙwasa shuru hanu yasa ya buɗe wayam babu kowa fitowa yayi tare da duban sakatariyar yace.

“Sadiya Al’ameen fa?”

“Oga ai tun ɗazu ya fita da sauri yana waya dan zai kai 3hours da fita.”

“3hours.”

Ya furta yana shigewa Office ɗin tare da kashe system ɗin yasa a jaka ya tattara takardun ya shirya su tare da ɗaukar jakar system ɗin ya fito yana bawa sakatariya umarnin ta rufe office ɗin kafin ya fita motar sa ya shiga yana tsaka da driving yaji shigowar saƙo, Dubawa yayi yaga Nafeesa ce ta turo masa account numbern da zai sanya mata kuɗin BIRTHDAY party murmushi ya saki tare da mata transfer na 100k kafin ya ijiye wayar yana sakin murmushi.

Koda ya isa cikin gidan nasu part ɗin su Al’ameen ya fara shiga riƙe da system ɗin Al’ameen babu kowa cikin falon ya haura sama bedroom ɗin Al’ameen ya nufa ya jiyo kuka a bedroom ɗin su Maimu fasa shiga bedroom ɗin Al’ameen yayi ya tura door ɗin su Maimu da Sallama Aunty Amarya ce ta ɗago kanta tana amsawa, yayin da Adamu mai gyaran karaya yake ɗaurewa Samira hanu tana ta kuka tamkar ranta zai fita idanunta sun dawo tamkar jan gauta tsabar baƙar azabar ɗauri da take sha.

“Innalillahi wa’inna ilaihirraji’un! Subahanallah, Samira karyewa kikayi garin yaya?”

Yayi naganar yana zuwa gabansu da sauri ya ijiye system ɗin a gefe Aunty Amarya ne ta tauye fuska alamun damuwa tace.

“Ka gani dai Aliyu yadda Al’ameen ya yiwa ƴar Uwar sa akan wata bare can.”

“Al’ameen kuma, Aunty Al’ameen ne ya karya Samira?”

Haidar ya tambayeta cike da mamaki cikin damuwa, kanta Aunty Amarya ta ɗaga tare da cewa.

“Eh shine ya karyata kat ka gani, nayi ƙoƙarin dakatar dashi amma da alamu yanzu Al’ameen ya rainani baya jin maganata ko dan saboda babu ran Ummin su ne.”?

Duban Samira da ke shan wahala Haidar yayi ransa ya ɓaci tare da miƙewa ya nufi bedroom ɗin Al’ameen ko sallama baiyi ba ya wurga system ɗin kan bed a fusace yace.

“Al’ameen me ka aikata haka, da hanunka zaka karya Samira saboda baƙar mugunta wani irin baƙin laifi ta aikata maka da ta cancanci wannan hukuncin tamkar ba ƴar uwar ka ba?”

Idanunsa Al’ameen ya runtse tare da buɗe su ya zubawa Haidar su tashi yayi ya ɗauki system ɗinsa tare da ijiye ta a gefe ya dawo ya zauna yana jawo wayarsa ya danna game ba tare da ya tankawa Haidar ba, abinda ya tsana kenan tattare da Al’ameen wani lokacin yana da ƙyaliya da maida mutum shasha, zama Haidar yayi ya kuma cewa.

“Babu laifi idan ka maidani mahaukaci Al’ameen, amma ka sani bazan fasa sanar da kai gaskiya ba, a matsayina na ɗan uwanka kuma AMININKA.”

Al’ameen kansa na ga wayar sa yace.

“Tabbas bani da wanda nafi kusanci dashi a duk faɗin wannan duniyar daya shigeka ko Daddy da Faruq ban shaƙu dasu yadda na shaƙu da kai, ina wuni harna kwana ba tare dana saka Faruq a idanuna ba, amma kai bana iya jure wunin rana guda ban ganka ba, bana iya ɓoye maka damuta saboda tsantsar ƙaunar dake tsakanin mu, sai dai kash A ko yaushe Haidar baya taɓa fahimtar ɗan uwansa, baya taɓa masa tambaya ta cikin sauƙi domin jin ba’asi wajen fayyace mai gaskiya da marar gaskiya, ko yaushe sai dai faɗa, ya kamata ka dinga fahimta ta, domin kuwa duk inda akaje aka juyo zance na ke tabbata gaskiya, Samira tayi laifi na hukuntata daidai da laifin da ta aikata a haka ma na mata sassauci.”

Numfashi Haidar ya saki tare da zama yace.

“Ba faɗa nake maka ba Al’ameen kaine wani lokacin kana da ban haushi, amma wani irin laifi Samira ta maka haka wanda ta cancanci wannan hukuncin.?”

Wayar sa Al’ameen ya ijiye tare da ɗago kansa ya bawa Haidar labarin abinda Samira ta yiwa Ablah, zaro idanunsa Haidar yayi tare da furta.

“What! Ita samiran ce tayi wannan rashin hankalin, mtsss na rasa me yake damun Samira baƙar zuciyarta tayi yawa, amma duk da haka bai kamata ka karyata ba, gara ai ka daketa sannan ka ja mata kunne, akan ka karyata?”

“Tun tana ƙarama Samira haka take bata da daɗi zuciyarta yayi yawa, bata da haƙuri sau dubu gara Afnan da Samira domin kuwa ita Afnan rashin ji ne kawai da ita amma bata da taurin kai, ka rabu da ita hakan dana mata shine zaisa gobe idan zatayi kuskure makamancin wannan ta farga.”

“Hakane amma dai banji daɗin hukuncin naka ba, bara naje na dubo Ablar.”

Haidar yayi Maganar yana tashi, Al’ameen baice komai ba har HAIDAR ya fita, bedroom ɗin Ablah ya shiga da Sallama Rufaida dake zaune gefen Ablah ne ta amsa dubanta yayi tare da kawar da kansa gefe, murmushi Rufaida tayi cike da takaicin Haidar wai gaba yake da ita yanzu saboda kawai tana sonsa shine laifinta, kanta ta kawar gefe ba tare da ta masa magana ba, tsayawa yayi akan Ablah da take bacci, bai wani juma ba ya juya tare da ficewa da kallo Rufaida ta bisa tana goge hawayen daya taru a idanunta tana jinjinawa rashin zuciyar ta da ta kasa cire mutumin da baya ƙaunarta daga rayuwarta.

Da misalin 4 na yamma su Maimu da Inna Jumma suka dawo kusan a tare suka shigo da Daddy a falo Daddy ya zauna har Inna Jumma da Afnan Maimu ce kawai ta haura sama, basu wani juma da zama ba Aunty Amarya ta fito ranta a haɗe.

“Sannu da dawowa Daddyn Al’ameen.”

Murmushi Daddy yayi tare da amsawa.

“Yauwa sannu Amina, meya faru na ganki rai ɓace kina taɓe fuska?”

Zama tayi tare da cewa.

“Wallahi yau abinda ya faru a gidan nan sam baiyi daɗi ba, ga can Samira a sama Al’ameen ya karya mata hanu.”

Inna Jumma ce ta riga Daddy cewa.

“Iyyee! Ya karyata to akan me meye ta masa?”

“Akan bare ya karyata akan wannan ƴar aikin Ablah.”

“Akan Ablah to meya haɗata da Ablah da bata nan?”

Inna Jumma ta jefa mata tambayar cike da nutsuwa, Aunty Amarya labarin abinda ya faru ta basu, Inna Jumma guɗa tasa tare da cewa.

“Masha Allah! Alhamdulillah! Allah ya yiwa Aminu albarka yamin dai-dai banji daɗi bama da bai karyata a ƙafa ba tunda ita shegiya ce tacacciya.”

Daddy shuru yayi cike da jin ɓacin ran Al’ameen,Yasha faɗa masa a duk sanda ƙannan sa suka ɓata masa rai ya daina musu mungun duka ko mungun hukunci domin kuwa duka bashi yake gyara ba, yasan da dawowar Ablah tunda Dpo ya sanar dashi komai, numfashi ya saki tare da miƙewa yace.

“Ina Samiran take?”

“Tana room ɗinsu.”

Aunty Amarya ta amsawa Daddy tashi yayi ya haura dukkan su suka rufa masa baya har Inna Jumma, tana kwance saman bed sai kuka take tamkar ranta zai fita, gefen ta Daddy ya zauna tare da kiran sunan ta.

“Samira!”

Ɗago idanunta tayi ta kalli Daddy sai ta kuma saka kuka, numfashi Daddy ya saki tare da cewa.

“Kukan ya isa haka, baki kyauta ba abinda kikayi Samira haka shima yayanki bai kamata ya miki wannan hukuncin ba, amma tunda ya riga ya faru sai kowa yayi haƙuri ko da gaba karki kuma ɗaukar hukunci a hanunki, ita Yarinyar hukuma sun tabbatar da bata da laifi cikin mutuwar mahaifiyarki, bari zanje na samu yayanki zan masa faɗa karya sake irin wannan hukunci kema kuma ki kiyaye.”

Yayi Maganar yana duban Maimu tare da cewa.

“Jeki kira min Al’ameen.”

Da to ta amsa tana ficewa Inna Jumma hararar Samira tayi tare da cewa.

“Shegiya maganinki kenan, ni Aminu dai-dai ya min da yaci ubanki.”

Tayi maganar tana barin wajen, ba’a juma ba kuwa sai ga Al’ameen ya shigo gefen Daddy ya zauna tare da cewa.

“Daddy sannu da dawowa.”

“Yauwa sannu, Zakina kwanan baya ban hanaka yiwa ƴan uwanka mummunan hukunci ba?”

Murmushi Al’ameen yayi yace.

“Daddy wannan ai ba mummunan hukuncin ba ne abinda ta aikata yafi ƙarfin duka shiyasa na mata wannan hukunci kuma ko gobe ta kuma aikata laifi makamancin wannan hukuncin da zan mata sai yafi wannan muni.”

“Zakina wai kai…”

“Oh Daddy please mubar wannan maganar ina aiki ne.”

Ya dakatar da Daddy tare da tashi ya fice daga ROOM ɗin, da kallo Daddy yabi Al’ameen tare da miƙewa shima ya fita, Aunty Amarya duban Maimu tayi tace.

“Ki kula da ita nima zanje na huta.”

Da to Maimu ta amsa cikin zuciyarta tana madalla da abinda Al’ameen ya yiwa Samira, zama sukayi ita da Afnan Aunty Amarya ta fice, wunin ranar cikin kuka Samira ta yisa.

Da yamma DOCTOR Saleem ya dawo har lokacin Ablah bata farka ba, maganin ya karɓa a wajen Rufaida tare da mata bayanin yadda Ablah zata sha, sannan ya tafi Inna Jumma ranar wuni tayi tana zagin Samira akan Ablah, tare suka kwana da ita da Rufaida a ROOM ɗin Ablah, Ablah bata buɗe idanunta ba sai ƙarfe 1 na dare kanta ta dafe dake mata nauyi a hankali ta buɗe idanunta tana ƙarewa ROOM ɗin kallo abubuwan da suka faru ne suka fara dawo mata, hawaye ne ya zubo daga idanunta (ina jinjinawa ƙwarin gwiwwar ki, ki sani cewa ni fa bom ce a gareki a duk sanda na tashi fashewa da ke ko burbuɗinki baza’a samu ba) maganar Aunty Amarya ya faɗo mata a zuciyarta.

Tabbas amarya masifa ce kuma sharri ga al’umma, tayi iƙrarin dasa min bom gashi kuwa ta fara saboda duk makirci da sarƙaƙiyar da ta sani a ciki yasa yau Samira tamin wannan cin mutuncin, lallai wannan Duniyar cike take da ƙunci, hawayen ta saka hannu ta share tare da ƙoƙarin miƙewa ta zauna Rufaida ce ta buɗe idanunta taga Ablah zaune, tashi itama tayi tare da cewa.

“Kin farka, sannu ya jikin dai babu inda yake miki ciwo?”

Da kallo Ablah tabi Rufaida cike da ƙaunarta domin kuwa ta ceceta daga mutuwa.

“Da sauƙi, kaina kawai yake min nauyi.”

“Alhamdulillah! Nauyin kan buguwar da kikayi ne dole sai a hankali komai zai daidaita bara na haɗa miki tea sai kisha.”

Kanta Ablah ta ɗaga alamun to sannan Rufaida ta miƙe tea ɗin ta haɗa mata ta bata tasha, tare da magani Ablah harta riga Rufaida komawa bacci, shuru Rufaida tayi tare da kwantar da kanta jikin filo tana tunanin Haidar yadda ya juye mata daga yadda ta sansa zuwa mutum marar tausayi duk alƙawarin daya ɗauka mata ya kasa cika mata ko guda ɗaya, Tabbas zuciyarta marar kishin kaine domin kuwa da zuciyarta tana kishinta tabbas da ta juma da cire Haidar a rayuwarta sai dai kash ta kasa hakan a maimakon taji haushinsa sai ma sonsa da take ƙaruwa a zuciyarta, tana da hanyoyi da yawa da zata iya mallakar Haidar ya sota dole ko baya so, sai dai Soyayyar gaskiya take buƙata daga garesa ba ta tilas ba, shiyasa bazata bi wannan hanyar ba, domin kuwa koda tabi itace zata sha wahalar zama dashi suyi zama na cutar kai da kai, zata dage da addu’a tana kaiwa ubangijin ta kukanta shine ya ɗaura mata son Haidar kuma shi yasan yadda zaiyi da ita. Tabbas Haidar shine abokin ƙaddararta kuma jarabawarta tana fatan cinye wannan jarabawar.

Numfashi ta saki tare da rufe idanunta hawaye na gangarowa, da ƙyar bacci ɓarawo ya saci Rufaida a Wannan daren.

Washe gari da safe tunda Nafeesa ta farka take jin wani iri a ranta, domin kuwa da ciwon kai ta farka ga tunanin Al’ameen da ta kwana dashi, shine kawai a zuciyarta duk wasu maza yanzu basa gabanta burinta kawai ta mallaki Al’ameen tsuka taja tana dafe kanta tare da kallon Nazifa dake kwance gefenta tace.

“Ke! Dallah ki tashi kije ki saka mana ruwan zafi wanka nake son yi.”

Shuru Nazifa ta mata tamkar ba da ita take ba.

“Nazifa bada ke nake Magana ba, kina jina zakiyi kunnen uwar shegu dani.”

Bakinta Nazifa ta taɓe tare da gyara kwanciyarta tace,

“Kin san hanyar kitchen ɗin ai.”

Bakinta Nafeesa ta cije tare da jawo wayarta tana cewa.

“Idan kin ɗaura min ma kinci ubanki dama ai idan da sabo yaci ace na saba da wannan tsinannen baƙin halin naki.”

Tayi Maganar tana dannawa Al’ameen kira, wajen 8 miss Call bai ɗaga ba tsuka taja tare da wurgi da wayar tana furta.

“Wannan dai akwai shege wallahi, yau naga marar imani wai ace duk saƙwannin da nake tura masa a banza, sai kace ba mace ba, mtsss! Ai kuwa Wallahi baka isa ba dole ka soni ko ta tsiya ko ta arziki dani kake zancen.

Tayi Maganar tana miƙewa a fusace cikin ɓacin rai, kusan dariya ce taso ƙwacewa Nazifa tare da cewa.

“Iska na wahalar da mai kayan kara.”

Afusace Nafeesa ta juyo tare da cewa.

“Da wa kike.”

Tashi Nazifa tayi tare da ficewa da gudu tace.

“Da wanda ya tsargu.”

 Juyawa tayi zata bita da gudu taji wayarta tayi ringin, dawowa tayi tana cije baki ta ɗauki wayar My HAIDAR ta gani rubuce tsuka taja tana furta.

“Ya kamata na kawo ƙarshen wannan alaƙar da ke tsakanin mu da kai, mtsss.”

Ɗaga wayar tayi tare da yin shuru, daga can Haidar yayi sallama bata amsa ba tace.

“Ka cika yawan kira Haidar dan Allah ka dinga barina ina samun sukuni ni aiki nake yanzu.

Tayi Maganar tana tura baki, daga can Haidar baki buɗe kusan suman tsaye yayi a razane yace.

“Duniyata kin san wa kike faɗawa wannan maganar kuwa?

Hararar wayar Nafeesa tayi tamkar Haidar ɗin a gabanta tace.

“Na sani mana bakaji na kira sunan ka ba Haidar…”

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Aminaina Ko Ita 33Aminaina Ko Ita 35 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×