Skip to content
Part 33 of 67 in the Series Aminaina Ko Ita? by Rasheedat Usman

Dariya Aunty Amarya ta saka tana duban Ablah tare da cewa,

“Lallai kinyi kuskure idan rashin hankalinki yana gwada miki cewa, zaki iya ja da Ni, karfa ki manta cewa Amarya ce, lunbu-lunbu mai saran ɓoye.”

“Kuskure! Kuskure!”

Ablah ta furta tana duban Aunty Amarya tare da riƙe kunkumi ta cigaba da cewa.

“Idan har ja dake shine kuskure to kuwa yanzu na sanya ƙafata a cikin kuskure, kuma guguwar kuskuren da kike tunanin tana ɗaukata itace zata tashi dake.”

Dariya still Aunty Amarya tayi.

“Ina jinjinawa ƙwarin gwiwwar ki, ki sani cewa ni fa bom ce a gareki a duk sanda na tashi fashewa dake burbuɗinki ma baza’a samu ba.”

“Hmmm! Bom ai kin kwana biyu kina dasa min ko ƙurata bata ɗauka ba bare a rasa burbuɗi na, kinga Amarya wallahi sai naga bayanki dole ni ce zanyi Nasara akanki, sai na miƙe yayinda ke kuma zaki faɗi ƙasa warwas, saboda har abada gaskiya itace gaba da zalunci, wannan ƙaddara ce wacce bata sauyawa.”

“Hmmm! Ablah kenan, ba’a wannan ƙarnin da muke ciki ba, yanzu domin kuwa a yanzu zaluncin yafi Nasara fiye da gaskiyar ki jira ki ga yadda zan wulaƙanta Rayuwarki wannan alƙawari na ɗauka kuma kin sani Amarya bata taɓa faɗa ta kasa cikawa.

Dariya Ablah tasa tare da cewa.

“To shikenan mu zuba mu gani.”

Tayi Maganar tana barin wajen tare da shigewa cikin falon, murmushi Aunty Amarya ta saki ta furta.

“Yaro bai san wuta ba sai ya taka, lallai kina wasa da rayuwarki ne domin kuwa gaɗa kike a bakin rami dole juye-juye da rawar kai yasa ki afka wannan ramin.”

Tunda ta sanya ƙafarta cikin falon Samira ta miƙe a fusace tare da daka mata tsawa.

“Keeee! Ƴar matsiyata, dakata daga nan.”

Cak Ablah ta tsaya tana duban Samira cike da mamaki, ƙarasowa gabanta Samira tayi tare da riƙe ƙugu tana jefawa Ablah mungun kallo.

“Hmmm! Lallai rashin kunya yana da daɗi, uban me ya dawo dake cikin gidan nan, gidan ubanki ko na ƙanin uwarki, hmmm! Wato rashin gaskiya irin na Hukumar ƴan sanda yasa sun sako ki, shine zaki kwaso ƙafa ki dawo mana cikin gidan nan, ki kashe uwarmu kuma ki zauna a cikin mu, ai kema kinsan wannan ƙarya ne, ko ki fita kibar gidan nan kona illata ki, domin wallahi ƙona ki zanyi zan watsawa fuskarki asid yanda babu wanda zai ganeki, ki fitar mana daga gida, ƴaƴan talaka ƴaƴan tsiya.”

Tayi maganar tana huci, ɗago kanta Ablah tayi tana duban Samira idanunta duk sun cika da hawaye takaici da baƙin ciki ya danne mata ƙirjinta, numfashi ta sauƙe cikin rawar murya mai alamun kuka tace.

“Ni ban kashe muku uwa ba, ban san ya ake kisa ba bare kuma nayi, meyasa zaki ci zarafina akan laifin da bani na aikata ba.”

“Hmmm! Kuji wani rainin hankali, to dan ubanki sai kin bar gidan nan ki sani tunda kika kashe Ummi to wallahi bazaki taɓa tsira ba karkiyi tunanin cewa saboda kin bar hanun hukuma shine kin tsira baki tsira ba, domin kuwa alhalin *AHMAD GIWA* kika taɓa shure shuren ki bazai taɓa hanaki mutuwa ba, ki fitar mana daga gida tsinanniya matsiyaciya.

Runtse idanunta Ablah da tayi hawaye na gudu saman fuskarta lallai Aunty Amarya ta goga mata mungun tabo a cikin zuciyarta, juyawa tayi zata bar gidan ta ci karo da Aunty Amarya tsaye ta harɗe hanunta tana sakin murmushi, tare ƙofar tayi ta yadda Ablah bazata samu hanyar shigewa ba tace.

“Samira me kikeyi haka, bai dace ba, ki barta ta shiga wataƙila su masu gidan su hukuntata da hanunsu, ki daina ɓata bakinki akan wata bushashshiyar mage wacce maganinta bazaiyi wuya ba, ko ta nama zamu iya kasheta.”

Kallon Aunty Amarya Ablah takeyi idanunta na ɗigar hawaye Samira tace.

“Na barta Aunty har sai Daddy ko Yaya Al’ameen sunzo, haba ai bazai yiwu ba dole tabar gidan nan yanzu.”

Tayi Maganar tana ɗauke Ablah da mari tare da cakwamo ta, da ƙarfi ta hankaɗata jikin bango wani irin buguwa kan Ablah yayi ya fashe jinine ya fara zuba yana wanke mata fuska, jiri ne ya fara ɗaukarta idanunta na ƙoƙarin rufewa, Samira ta kuma haɗata da ginin, wannan karon ƙara Ablah ta saka mai cike da azaba, ga babu kowa cikin falon daga Afnan har Maimu basa gidan ihsan ce kawai ke zaune, Aunty Amarya kuwa murmushi ta saka tare da shigewa tabar wajen, Rufaida ce ta sako kanta cikin falon idanunta suka sauƙa akan Samira dake neman illata Rayuwar Ablah.

“Innalillahi wa’inna ilaihirraji’un! Samira baki da hankali ne, kisan kai kuma zakiyi.”

Tayi maganar tana ƙarisawa da gudu ta shiga tsakanin su tana nuna Samira da yatsa.

“Kasheta zakiyi ki duba ki ga yadda jini ke fita daga kanta, wai Samira meyasa ke a rayuwarki baki da haƙuri ne zafin Zuciya ya miki yawa, ke har abada bazakiyi hankali ba.”

Tsuka Samira taja cike da masifa tace.

“Dole kice haka tunda ba uwarki ta kashe ba, na rantse da Allah muddun bata bar gidan nan ba sai nayi ajalinta.”

Kanta Rufaida ta girgiza cike da takaicin zafin Zuciya da rashin kunya irin na Samira, bata kulata ba ta kai dubanta ga Ablah wacce ta suma, zaro idanunta Rufaida tayi cike da tsoro tana ƙwalawa Aunty Amarya kira, shuru babu amsa yayin da Aunty Amarya take jin kiran Rufaida tayi shuru tana dariyar mugunta, Samira ƙara yiwowa kan Ablah tayi da wuƙar da ta ɗauko a daining ɗin dake falon na yanka fruit a haukace, Rufaida ƙara ta ƙara danna tare da yiwa Ablah runfa ta tareta, a hanun Rufaida Samira ta yanketa da wuƙar, cije bakinta Rufaida tayi cike da azaba ta miƙe cikin ƙarfin hali ta hankaɗa Samira ta faɗi ƙasa, wuƙar ma ta faɗi da sauri ta ɗauki wuƙar tana haki duk wannan dambarwar da ake Inna Jumma bata gidan itama sun fita unguwa tare da su Maimu gidan Goggo Hari, da hanu Rufaida ta kuma nuna Samira tana cewa.

“Kasheta zakiyi baki da imani ne ki dakata haka zan ɗauketa zata bar gidan nan yanzu ya isa haka Samira.”

Tayi maganar tana jawo Ablah gagara ɗaukarta tayi, runtse idanunta Rufaida tayi cikin tashin hankali ga hanunta dake mata wani irin azaba wayarta da ta faɗi gefe harta tsage ta ɗauka tare da dannawa Haidar kira, kusan miss Call 5 Haidar yana kallo yaƙi ɗauka shi duk a zatonsa damunsa Rufaida zatayi runtse idanunta tayi tare duban Samira dake huci, numbern Al’ameen ta kira yana zaune cikin Office ɗinsa yana aiki, yaji ringin ɗin wayarsa dubansa yakai ga wayar Sister Rufaida, hanu ya saka tare da ɗaga wayar Rufaida jin an ɗaga wayar ba ta jira sallama ba tace.

“Ya Al’ameen, Samira zatayi kisan kai, zata kashe Ablah, jininta na zuba sosai yaya Al’ameen ko motsi batayi karta mutu yaya Al’ameen.”

A matuƙar firgice Al’ameen ya furta.

“What?”

“Ehh yaya Al’ameen wallahi da gaske Samira kashe Ablah zatayi wuƙa ce a hanunta nima ta yankeni, babu kowa a cikin gidan ban san yaya zanyi ba, tsoro nake kar jininta ya ƙara.”

Wani irin zuciya Al’ameen yayi take idanunsa suka sauya kala daga fari zuwa ja, hankalinsa yayi mungun tashi.

“Bawa Samira wayar.”

Yayi maganar yana miƙewa tsaye ya ɗauki key ɗin motarsa da sauri har yana kamar gudu ya fita, Rufaida wayar ta miƙawa Samira tare da cewa.

“Gashi yaya Al’ameen yana magana.”

Kauda kanta Samira tayi taƙi amsar wayar tana huci.

“Yaya Al’ameen taƙi amsar wayar.”

Bakinsa Al’ameen ya cije yana buɗe motarsa ya shiga tare da ja da ƙarfi ya fita daga Companyn.

“Matsa kusa da ita ki Danna handsfree.”

Ya faɗi yana sharara uban gudu a tsakiyar titi, Rufaida handsfree ta danna tare da tsayuwa gaban Rufaida tace.

“Na danna yaya Al’ameen.”

Idanunsa Al’ameen ya runtse cikin mungun tsawar da hatta Rufaida sai da ta razana yace.

“Idan kika kuma motsi daga inda kike har kika kuma takawa gaban Ablah,na rantse da Allah yau sai na illata rayuwarki, katse kiran Rufaida gani nan zuwa.”

Katse wayar Rufaida tayi tana dafe kanta tare da riƙe hanunta dake mata azaba, tasan yanzu Samira bazata tunkari Ablah ba tunda har Al’ameen yayi magana, cike da takaici Samira ta zauna a ɗaya daga cikin kujerun falon tana haci.

17 minute ne suka kawo Al’ameen gidan ko parking bai daidaita ba ya buɗe murfin motar ya fito da sauri da gudu ya shiga falon nasu yayinda ma’aikatan gidan suke binsa da kallon mamaki domin kuwa bai taɓa shigo musu a birkice haka ba, door ɗin falon ya saka hanu ya buɗe ai kuwa a gabansa yaga Ablah yashe jini har yanzu bai bar fita daga goshinta ba, idanunta na rufe babu abinda ke motsi a jikinta, da sauri ya sunkuya yana ambaton.

“Innalillahi wa’inna ilaihirraji’un! Ablah! Ablah, ki buɗe idanunki.”

Yayi maganar cikin gigita yana saka hanu a hancinta ko zaiji numfashi amma shuru kike ji, a matuƙar ɓacin rai ya ɗago ya kalli Samira tare da runtse idanunsa.

“Rufaida jeki kawo min ruwa.”

Da sauri Rufaida ta miƙe tare da shiga kitchen da sauri ta fito da ruwa a cup ta miƙa masa, karɓa yayi tare da watsa mata a fuskarta, wajen sau uku amma shuru, ganin da yayi ruwa bazai farfaɗo da Ablah ba dole sai anja mata numfashi ga jininta dake zuba ya sashi duban Rufaida yace.

“Bani kallabin ki Rufaida.”

Cirewa tayi babu musu ta basa, kanta ya ɗago tare da saka kallabin ya ɗaure goshin nata inda jinin ke zuba sosai tare da cewa.

“Rufaida zaki iya jawowa Ablah numfashi ta baki?”

Kanta Rufaida ta girgiza tare da cewa.

“Yaya bazan iya jawo numfashi ta baki ba, ban san yadda akeyi ba sai dai ko na dubo maka Momma ko zata iya.”

Kansa Al’ameen ya girgiza tare da cewa.

“Ki haura sama ki dubo Aunty ko tana bacci ne.”

Yayi Maganar yana haɗa idanu da Ihsan dake tsaye saman step.

“Ihsan ina Aunty?”

Hawaye ne na tausayin Ablah ya zubo a idanun ihsan yarinya ce ƙarama amma taji zafin abinda samira ta yiwa Ablah.

“AUNTY tana room ɗin ta.”

“Tana room ɗin ta amma duk wannan tashin hankalin da ake bata jiyo ba.

?”

Rufaida tayi maganar zucin cike da mamaki tana haurawa saman da sauri, room ɗin Aunty Amarya ta tura, tana.

“Aunty Aunty!”

Jin muryar Rufaida yasa Aunty Amarya saurin rufe idanunta alamun tana bacci, jin shuru yasa Rufaida shigowa ganin Aunty Amarya kwance ya sata tashinta a hankali Aunty Amarya ta buɗe idanu tare da mutstsike idanuwa tamkar mai bacci.

“Bismillahil lazi ahyana ba’ada ma amatana wa ilaihinnushur.”

Tayi addu’ar tashi daga bacci tsabar makirci irin na Aunty Amarya tare da duban agogo tace.

“Oh bansan lokacin da wannan bacci mai nauyin haka ya ɗauke niba, Rufaida yaushe kika shigo.”

Ɗan murmushi Rufaida tayi tana riƙe da hanunta mai ciwo tace.

“Ai tun ɗazu nake nan part ɗin, ina ta kiranki ma naji shuru ashe bacci kike, wata ƴar hayaniya ce ta faru tsakanin Samira da Ablah shine yaya Al’ameen yace na kiraki.”

AUNTY Amarya sauƙowa tayi daga bed ɗin tana duban hanun Rufaida da ke yanke tace .

“Subahanallah! Meya sameki a hanu haka yake zubar da jini, Wai dama ashe dana hana Samira taɓa Ablah bataji ba, ai kuwa muje.”

Tayi Maganar tana fita Rufaida ta bita da sauri, gaban Ablah Aunty Amarya ta sunkuya tana salati tare da ɗago kan Ablah ta ɗaura a saman cinyarta tana cewa.

“Wai Samira ce ta mata wannan aikin, Oh ni Amina wannan baƙar zuciya irin ta Samira ban san a ina ta ɗaukosa ba, sai da na hanata taɓa Ablah amma Yarinyar taƙi ji.”

Numfashi Al’ameen ya saki yana huci yace.

“AUNTY yanzu ba wannan bane numfashi take buƙatar a jawo mata ki taimakeni ki jawo mata numfashin nan, dan Allah Aunty kar ƴar mutane ta mutu ba ita bace tayi kisan nan, hukuma sun gano waɗanda suka kashe Ummi yanzu haka suna hanun hukuma shiyasa aka sake ta, bata da hanu cikin wannan case ɗin.”

Murmushi Aunty Amarya ta saki cikin zuciyarta tana furta.

“Hmmm! Abun da na sani kuma ni na shirya yake sanar min, tace mu zuba mu gani, gashi kuma ta fara gani, wannan kaɗan kenan daga cikin makirci na” sannan Aunty Amarya ta ɗago kanta ba tare da tace komai ba ta sunkuya ta haɗa bakinta dana Ablah ta dinga jawo mata numfashi a hankali, har aka samu Ablah tayi wani irin ajiyar zuciya sannan Aunty Amarya ta ɗaga kanta tana sakin numfashi Ablah ta gagara buɗe idanunta sanadin jinin daya wanke mata fuska, wani irin ƙara ta saki tana kai hanunta ta riƙe kanta dake famar sara mata Aunty Amarya duban Al’ameen tayi tare da cewa.

“Ka kira DOCTOR Al’ameen yazo ya duba ta.”

Tayi maganar tana kamo Ablah ita da Rufaida suka kaita bedroom ɗin ta, Al’ameen cike da tashin hankali ya kira Doctor Saleem, ijiye wayar yayi bayan sun gama waya yana jefawa Samira mungun kallo, shi kaɗai yasan kalar hukuncin da zai yiwa Samira a cikin gidan nan, kaiwa da komowa ya dinga yi cike da tashin hankali, doctor Saleem bai wani juma ba kuwa sai gashi, bedroom ɗin Ablah suka nufa cike da tashin hankali, tana kwance sai juyi take tana mutsutsuku, tamkar ranta zai fita tare kanta gam, doctor Saleem nufarta yayi tare da yiwa Al’ameen alamar ya riƙe masa hanunta, haka kuwa akayi Al’ameen ya riƙe hanun Ablah, doctor Saleem ya sunce kallabin nata, shi kansa sai da ya tsorata da ganin raunin dake goshinta wanke ciwon yayi Ablah tana runtse idanunta, har da ɗinki, sannan ya ɗaure kan da bendeji, ruwa mai ɗumi yasa aka kawo masa ya goge mata jinin dake fuskarta tare da mata allura kafin ya dubi Al’ameen yace.

“Na mata allurar bacci ko zai rage mata zogin da kanta ke mata, sannan zan rubuta magani sai a samo kafin na dawo zuwa yamma, amma gaskiya ko wanene ya mata wannan aikin bashi da imani, domin kuwa kisan kai yaso ko haukatarwa.”

Al’ameen bakinsa ya cije tare da cewa.

“Ba damuwa muje na rakaka.”

Abunda ya faɗi kenan suka fita Aunty Amarya duban Ablah da idanunta ke rufe tayi tare da taɓe bakinta ta cewa Rufaida.

“Rufaida bara naje na gyara room ɗina ko, ki zauna tare da ita kafin na dawo.”

Da to Rufaida ta amsa tare da gyara zamanta tana duban Ablah cike da mungun tausayin ta, a rayuwarta bata ƙaunar ganin wani cikin matsala, hanu tasa ta gogewa Ablah hawayen dake zuba mata ta gefen idanunta.

A zuciye ya shigo falon, sama ya haura tare da tura bedroom ɗin su Maimu, Samira tana zaune har yanzu tana hurar zuciya, Hanu yasa ya jawo Samira tare da riƙo gashin kanta da ƙarfi idanunsa sunyi jajur yace.

“Wato kece baki da mutunci baki da kunya ko, uban me ta miki da zaki nemi kasheta, hujjar uban me kike da ita na ita ta kashe Ummi koda ita ce ta kashe Ummi wata doka ce ta baki dama ki kasheta da kanki?”

Ƙara samira ta saka tana jin tamkar zai tsige mata gashin kanta ta gagara basa amsa.

“Tambayar ki nake kin min shuru?” Sakinta yayi tare da riƙo hanunta yace “Da wannan hanun kika dinga haɗata da bango ko saboda kinci kin ƙoshi kin fita ƙarfi, insha Allah daga yau bazaki kuma marmarin koda kallon Ablah bane bare ki kai hanu jikinta.”

Yayi maganar yana lanƙwasa hanun Samira da karfi kat kuwa ya karya mata hanu wani irin mungun ƙara Samira ta saka mai gigitarwa, lokaci guda ta fita a hayyacinta tare da yamkar jiki ta faɗi a sume, Aunty Amarya dake bedroom ɗin ta ne ta jiyo sautin ƙarar Samira ya sata fitowa da mungun gudu a tsorace ta faɗo bedroom ɗin nasu, a sume ta ganta, duban Al’ameen tayi da ko a jikinsa ya ciro wayarsa tare da dannawa Adamu mai gyaran karaya kira yana ɗagawa Al’ameen yace.”Kazo gidan mu yanzu akwai wacce ta karye zaka ɗaurata.”

Ya yi maganar tare da katse kiran zai bar bedroom ɗin Aunty Amarya ta dakatar dashi da cewa.

“Me kayi haka Al’ameen?”

“Hukunci na mata dai-dai da abinda ta aikata sai suyi jinyar tare.”

Yayi Maganar ransa a haɗe Aunty Amarya cewa tayi.

“Al’ameen ƴar Uwar ka ka karya Saboda bare anya kuwa kasan abinda kayi me zaka cewa Daddyn ku idan ya dawo?”

Murmushi Al’ameen yayi yace,

“Hmmm! Dalilin kenan da yasa na sassauta mata albarkacin aifayya da wata ce hanu da ƙafa zan karya mata, abinda na faɗa miki kuma shine zan maimaitawa Daddy.”

“Amma Al’ameen…”

Saurin ɗagawa Aunty Amarya hanu yayi tare da cewa.

“Ya isa haka tambayar Aunty.”

Yayi Maganar yana shigewa yabar ROOM Aunty Amarya sheƙewa tayi da dariya bayan ya fita tare da furta

“A sannu dai duk sai na hargitsa muku rayuwa.

Bedroom ɗinsa ya shige tare da zama yana dafe kansa ƙirjinsa sai zafi yake masa, Tabbas sai ya takawa kowa burki a gidan nan akan Ablah domin kuwa idan yayi wasa to zasu illata masa rayuwarsa, tamkar numfashin sa yake jin Ablah a cikin rayuwarsa, zuwa yanzu zuciyarsa bazata jurewa ganinta cikin tashin hankali ba, bakinsa ya cije yaji wayarsa tayi ƙarar shigowar saƙo, ɗaga wayar yayi tare da duba text ɗin Nafeesa ce dai.

“Meyasa zaka kasa bawa zuciyar dake muradinka amsar saƙon ta, karka manta kaine bugun numfashi na, kuma duniyata, bazan iya haƙurin rasaka ba, ina sonka kuma dole ka zamo mallakina sunan mu sun dace da rayuwar mu har ma na raɗa mana sabon inkiya Al’ameen da kuma Feenat, zai bamu ALFEENAT ka bani rayuwarka zan riritata tamkar ƙwai zan shagwaɓa ka tamkar jaririn yaro zan kula da kai tamkar yadda uwa zata kula da ƴarta ina sonka Hubbina.”

Tsaki mai ƙarfi Al’ameen yaja ya fara gajiya da wannan banzan saƙon da ake turo masa, wayar tasa ya ɗaga tare da kiran ICO bayan ya ɗaga yace.

“Abokina kwana biyu ka ɓuya.”

Murmushi Al’ameen yayi tare da cewa.

“Kai dai bari Abokina bamu da kirki ya aikin dai.”?

“Aiki alhamdulillah! Rabona da kai tun rasuwar Ummi.”

“Wallahi kuwa bamu sake haɗuwa ba, yanzu ma wani ɗan ƙaramin aiki nake son na baka kayi taimako.”

Ɗan dariya ICO yayi tare da cewa.

“Okay ba damuwa Abokina menene aikin.?

“Wata number ce ta addabi rayuwata da kira da kuma turo saƙo, so nake zaka min tracker ɗin layin domin gano wacece take neman kuskuren shiga rayuwar da bata da hurumi a ciki, ina son sanin wacece..”

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Aminaina Ko Ita 32Aminaina Ko Ita 34 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×