"Lallai biri yayi kama da mutum to ita wannan Yarinyar meye nufinta dani, meye gamina da ita.?"
Numfashi ya sauƙe tare da komawa ya zauna yana dafe kansa duniyar tunani ya lula na menene daran gamin Nafeesa dashi, dama biri yayi kama da mutum shi dama tun can zuciyarsa bata amince da Yarinyar ba, hanu yasa ya ɗauki wayarsa tare da dannawa numbern da take kiransa dashi kira.
Nafeesa na zaune a school ita da Amnat taji wayarta tayi ringin dubawa tayi taga Al'ameen, zaro idanunta tayi cikin farin ciki tace.
"Lah Amnat kinga Al'ameen ke kirana. . .