Skip to content
Part 36 of 67 in the Series Aminaina Ko Ita? by Rasheedat Usman

“Lallai biri yayi kama da mutum to ita wannan Yarinyar meye nufinta dani, meye gamina da ita.?”

Numfashi ya sauƙe tare da komawa ya zauna yana dafe kansa duniyar tunani ya lula na menene daran gamin Nafeesa dashi, dama biri yayi kama da mutum shi dama tun can zuciyarsa bata amince da Yarinyar ba, hanu yasa ya ɗauki wayarsa tare da dannawa numbern da take kiransa dashi kira.

Nafeesa na zaune a school ita da Amnat taji wayarta tayi ringin dubawa tayi taga Al’ameen, zaro idanunta tayi cikin farin ciki tace.

“Lah Amnat kinga Al’ameen ke kirana, wayyo daɗi.”

Tayi maganar tana dariya kallonta Amnat tayi tana taɓe bakinta tace.

“Da kin dakatar da farin cikin tukunna sai kin ɗaga kinji idan ba Haidar bane.”

Tsuka Nafeesa taja tana hararar Amnat tace.

“To Uwar mungun fata ba Haidar ɗin bane domin kuwa dukkan su babu wanda ya sanni da wannan numbern.”

Tayi maganar tana ɗaga kiran ta kara a kunnenta cikin slow voice tayi sallama, Al’ameen a daƙile ya amsa sallamar yana cewa.

“Ina sauraranki kiran me kike min naga alamar kina da niyyar cinyeni me kike nema a gareni?”

Murmushi Nafeesa tayi ko kaɗan bataji zafin maganar sa ba ta ce.

“Soyayyar ka itace nake buƙata domin kuwa kamin satar zuciya, ina sonka Al’ameen domin da kai rayuwata ta dace ta yaya zan cinye abinda nake so ai ni kaina bazan moru ba.”

Murmushin gefen baki Al’ameen ya saki tare da cewa.

“Ta yaya rayuwar Al’ameen zata dace da ta ballagazar mace irinki, wacce bata san amana ba, kinsan wannan tatsuniya kike, kinga bani buƙatar sanin ko ke wacece zan ja miki kunne ki fice daga harkata karki kuma kuskuren sake kiran layina, idan kuma kika cigaba da bibiyata to babu makawa zan wulaƙanta rayuwarki ki kiyaye ko wacce ƙwarya da Abokiyar Burminta.”

Numfashi Nafeesa ta saki tana kallon Amnat tace.

“Meyasa zaka yanke min hukunci bayan bakasan koni wacece ba, hmmm! Ba’a yankewa mutumin da baka sansa hukunci ba, ina sonka shine kawai abinda na sani ban damu da kima mai zaka min ba abinda na sani kawai dole zaka soni.”

Dariya Al’ameen yasa har haƙwaransa na bayyana wai baka sanni ba ta yaya zaka yanke min hukunci.

“Okay da alamu bakya fahimta saboda kina da toshashshiyar ƙwaƙwalwa, ke da a naki tunanin bansan wacece ke ba, okay.”

Yayi maganar yana katse kiran tare da ijiye wayar yana cije bakinsa. Sosai ransa ya ɓaci wai wannan yarinyar tama raina masa hankali tsaranta ne shi da zata nemi danganta rayuwarta dashi, lallai ɗan uwansa Haidar yana cikin babban ƙalubale domin kuwa ya saka wannan tantiriyar ƴar iskar a zuciyarsa ba lallai bane a iya rabasa da ita amma tabbas zata bawa rayuwarsa wahala, ɗan uwansa shine abun jinsa domin kuwa baya ƙaunar abinda zai ɗaga masa hankali ya zamo dole ya nemi mafita kafin Haidar ya fahimci wani abu, idanunsa ya runtse tare da jawo system ɗinsa ya cigaba da aiki.

Tuƙi yake cikin rashin ƙwarin jiki ransa duk a jagule, Gwagwalada University Abuja ya nufa, parking space yayi parking tare da fitowa ya nufi inda yasan zai sameta kamar yadda yayi zato dai suna zaune ita da Amnat da Jamila sallama ya musu Amnat ce ta ɗago kanta tare da amsawa cikin fara’a tace.

“Haidar kaine har cikin school sannu da zuwa Bismillah ga waje.”

Murmushi Haidar yayi tare da jawo kujarar ya zauna yana cewa.

“Ai dole nayi zuwan bazata Amnat Duniyata na fushi dani ai ko kinga banga ta zama ba.”

Ɗago idanunta Nafeesa tayi ta kallesa tare da haɗa fuska tana kawar da kanta gefe, murmushi Amnat tayi tare da cewa.

“To fa ehh lallai dole ka ziyarce mu to ga nan zinariyar taka ai zaune.”

Murmushi yayi yana mai da dubansa gareta yace.

“Duniyata wai meke faruwa ne.?”

Nafeesa ranta ranta a haɗe tace.

“Meke faruwa kamar yaya meka gani.?”

Numfashi ya saki yana ƙura mata idanu cike da Soyayya tamkar zai cinyeta saboda so yace.

“Naga abubuwa da yawa Duniyata domin kuwa hankalina ya tashi bacci gagarata yakeyi kwana biyun nan, bana gane miki duk kin sauya min a yanda na sanki kin daina bani kulawa wayata ma bakya ɗagawa Nafeesa Why?”

Kafin Nafeesa tayi Magana Amnat ta miƙe tana cewa.

“Jamila mu basu waje suna buƙatar tattaunawa.”

Ba tare da Jamila tace komai ba ta miƙe tare da taka Nafeesa tana ɗago idanunta ta kanne mata idanu, kafin suka bar wajen, Nafeesa kallonsa tayi tare da cewa.

“Haidar a wannan taƙin da muke ciki na zauna nayi duba ga ni ga kuma kai naga sam ban dace da rayuwar ka ba, gara kawai mu rabu kowa yaje yayi rayuwarsa na tabbata zaka samu wacce ta fini ka gafarceni bazan iya rayuwa da kai ba.”

Wani irin sarawa kan Haidar yayi da ƙarfi tamkar sauƙar aradu yaji maganar ta idanunsa da suka sauya kala ya ɗago yana kallon ta wani yawu mai ɗaci ya haɗiye cikin nauyin baki yace.

“Nafeesa wacce irin magana kike min wannan, idan wasa kike ki bari domin kuwa zuciyata bazata iya amsar kalmar rabuwa dake ba, rayuwata ce ke bazan taɓa iya moruwa babu keba, numfashina bazai busu ba dole sai da tallawafar numfashin ki, zuciyata bazata harba ba dole sai da ke cikin rayuwata rasaki tamkar rasa rayuwata ne ina matuƙar sonki Nafeesa ki daina min irin wannan wasan domin kuwa nasan bazaki iya rayuwa babu ni farin cikin ki ba.”

Numfashi Nafeesa ta sauƙe tana duban Haidar tare da sakin murmushi tace.

“HMMM! Haidar ni ba rayuwarka bace, tabbas a kwanakin baya naji soyayyar ka a zuciyata amma lokaci ɗaya ina haɗuwa da masoyina na haƙiƙa na gane cewa ashe ba sonka nake ba, dan haka ka rabu dani ka daina kulani, ka manta dani a cikin rayuwarka, ka daina dangantani da numfashin ka domin kuwa idan sai dani zakayi numfashi to wallahi Haidar numfashin ka zai tsaya ka fahimta idan so cuta ce haƙuri magani ne kar mu cutar da kanmu gara kayi hkr.”

Miƙewa tsaye Haidar yayi idanunsa yayi jajur ya kalli Nafeesa tare da cewa.

“Nafeesa kin san me kike cewa kuwa yau ni kike cewa na fita daga rayuwarki?”

“Wai Haidar mahaukaciya kake ɗaukata ne duk sanda na maka magana sai kace min nasan me nake cewa kuwa, tunda ba mahaukaciya bace ni ai nasan abinda nake faɗa , Haidar na sake maimaita maka ka fita a rayuwata ba’a Soyayya dole ka gane.”

Tana Maganar taja tsuka tare da ɗaukar bag ɗin ta tabar wajen, Haidar kansa dake mungun Sara masa ya dafe tare da miƙewa jiri na ɗaukarsa ya nufi motarsa, daƙyar ya iya hawa motar tare da mata key idanunsa na rufe, ikon Allah ne kawai ya dawo dashi gida, babu kowa cikin falon hakanne ya basa damar shigewa bedroom ɗinsa ya faɗa bed ɗinsa tare da danƙe kansa dake mungun sara masa runtse idanunsa yayi ya rasa meye yake masa daɗi sai famar juye-juye yake a saman bed ɗin.

Tsuka Nafeesa taja tana isa wajen da su Amnat ke jiranta.

“Mu tafi class yau dai na yarda ƙwallon mangwaro na huta da ƙuda shima Al’ameen zamu buga dashi da alamu ɗan jiji da kaine yana ji da izza da kuma raina ajin Mutun zan kuma nuna masa shi ba komai ba, ban taɓa harin abu na rasa ba dan haka bazai kufce min ba.”

“A tunaninki kin rabu da Haidar ne a yau?”

Amnat ta jefa mata tambayar.

“Ƙwarai kuwa domin kuwa komai rashin zuciyarsa yanda mukayi yau dole ne ya rabu da ni.”

“Hmmm! Nafi kenan Haidar yana miki matsanancin soyayya bazai rabu dake ta cikin sauƙi haka ba dole zaiyi yaƙi ya kuma dage domin ganin ya dawo da Soyayyarsa, Kuma nafi duk wanda zai faɗa miki gaskiya Idan kika rabu da Haidar baki masa adalci ba, Haidar ya miki halaccin da babu wani namiji daya taɓa miki ya bauta miki ba dan jikinki ba saboda kawai Soyayyar gaskiya ya ɗauki maƙudan kuɗaɗe ya baki badan ya kwanta dake ba, saɓanin samarin ki na bariki da sai kin basu kanki su baki kuɗin su, meyasa zaki shure wannan Soyayyar gaskiyar, kiyi tunani kafin aikata kuskure Nafeesa.”

Dariya Nafeesa tasa tana kallon Amnat kafin ta dubi Jamila suka kuma kwashewa da dariya Jamila tace.

“Kaji wata kalma wai ita adalci, to dama akwai adalci a wajen ɗan bariki ne, kinga da adalci da kuma Amana babu su a bariki kema kin sani Amnat to ai gara ma ace ya bata kuɗin ne saboda jikinta da yanzu ba wannan maganar ake ba.”

“Kinga Jamila rabu da ita bata ganewa ba kuma zata gane ba, amma idan kina jin tausayin sa sai ya aureki ki masa huce haushi, amma dai kin sani ba’a SO dole dan haka ko mutuwa zaiyi dole ne dai ya ƙyale ni na masa zarrah nan gani nan bari.”

Kanta Amnat ta girgiza cike da tausayin Haidar tace wa Nafeesa.

“Good kin bawa kanki mafita Nafeesa kince ba’a so dole da bakinki to meyasa kike ƙoƙarin yiwa Al’ameen dole ya soki, tunda ba’a so dole ai sai shima ki rabu dashi ko, ki jira wanda zuciyarku zata haɗu ko yaya kika gani?

Wani irin tsuka mai ƙarfi Nafeesa taja tare da jan hanun Jamila tace.

“Mu tafi Jamila ki rabu da wannan ƴar hassadar wacce bata ƙaunar cigaban Mutum.”

Tayi Maganar tana jan hanun Jamila suka bar wajen kanta kawai Amnat ta girgiza tare da bin bayansu.

Rufaida bayan ta gama nuƙurƙusonta ne ta shiga tayi wanka Ablah ce ta faɗo mata a ranta wuni guda bataje ta duba ta ba, hakanne ya sata ɗaukar wayarta ta nufi part ɗin su Maimu, a falo taga key ɗin motar Haidar a wurge tasan dai ya fita to kuma meya dawo dashi, bakinta ta taɓe tare da sunkuyawa ta ɗauki key ɗin, bedroom ɗin sa ta nufa ta tura da Sallama kusan baki Uku ta jisa shuru hakanne ya sata shiga kai tsaye yana kwance ya riƙe kansa idanunsa yayi jajur ga gumi dake famar keto masa a goshinsa, da sauri Rufaida ta ƙarisa na furta.

“Yaya Haidar baka da lafiya ne?”

Zama tayi gefen sa tana kuma cewa.

“Ko na kira Momma, Yaya Haidar meke damunka kwana biyun nan kana cikin damuwa, bara naje bedroom ɗin Momma Akwai maganin ciwon kai na kawo maka domin kuwa da gani kanka ke ciwo Sannu.”

Ta ƙarisa Maganar tana fita da gudu ba tare data tsaya ya amsa mata ba.

<< Aminaina Ko Ita 35Aminaina Ko Ita 37 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×