Kuka Sosai Mai Kano yayi ganin inda Allah ya jefo mahaifiyar shi tayi Rayuwa cikin masu lalurar tabin hankali.
“Kai mahaukacin banza tashi ka tafi gida .
Ya tsinkayo muryar Halima na fada mishi Haka ya dubeta tana tsaye Bakin kofar dakin wadda akayi da Rodika.
Ya Mike da Shirin tafiya ya matso kofar dakin ya Riko hannun ta Yana fadin. “Ubangiji ya yaye Miki mama Allah ya yanke Miki.
“Ameen mahaukaci Allah yayi maka Albarka Dan bara uba shege.
Bai taba Jin mahaifiyar shi tayi zagi ba sai a yanzu sanadin lalurar ta. HAWAYE suka kasa tsayawa a fuskar shi Dole yayi Mata sallama ya juyo har ya Kai bakin kofar fita yaji ta kwado mishi Kira.
“Kai Mai Kano ! Ya juyo da sauri Jin ta kamo sunan shi ya iso Yana jiran yaji me zata ce? Sai Kuma tace jeka abinka Allah yayi maka Albarka. Ya juya ya tafi har ya kusan fita Kuma ta Kuma Kiran shi ya dawo ta kuma ce ya tafi.
Sai da tayi mishi Haka yafi sau biyar kafin ta kyalkyale da Dariya tana Fadin.
“Kai mahaukacin banza ko na Kira ka Kar ka dawo kayi tafiyar ka kawai.
“Idan Zaki kirani sau Dubu mama Zan dawo sau Dubu.
Haka kuwa tayi ta mishi sai ya tafi sai tace ya dawo har dai wata ma aikaciyar wurin tace yayi tafiyar shi.
Da haka ya fice ko gidan hajiya Bai je ba ya koma Legos inda ya nemi duk wata nutsuwa da kwanciyar hankali ya Rasa saboda halin da Halima take ciki.
Dole ya yanke shawarar Kiran yayun shi ya sanar dasu halin da ake ciki inda Mubarak din yace lallai Husna ta Rika Zuwa tana kula da halin da mamar tasu take ciki kafin Suma suzo suga halin da take ciki da Haka sukayi sallama cikin Alhini.
Sai dai Yana ganin idan Husna ta San halin da ake ciki tamkar Alh Aminu ya sani ne hajiya ma Dole zata sani shi Kuma wadan Nan mutanen sune baya son su San Halima ta bayyana don Haka sai kawai ya share sanar da Husna sai dai shi duk juma a Yana garin katsina wurin duba mahaifiyar shi Amma dai jiya iyau Babu wani ci gaba da ake samu kamar dai wannan juma ar da yazo ya sameta sai faman cizgar bandejin da ake lika Mata inda taji rauni take har ta ficzge na goshin ta jini ya tsattsafo.
Tana ganin shi ta kyalkyale da Dariya tana fadin ga D’ana ga D’ana.
Ya sunkuya Yana gaishe ta ta amsa tana tambayar shi Ina sauran suke? Ya ce suna Nan Zuwa.
“To menene cikin ledar Nan? Ya Miko Mata kazar da ya Riko Mata har da tatacciyar madara.
Ta Kuma Soma aikawa ciki har k’ashin sai da ta taune ta kuwa Kora madarar.
Kafin ta Soma koro mishi bayanin ta gaji da Zama cikin mahaukata.
“Ka gansu Nan ? Dukkan su mahaukata ne Basu aje komai ba sai barace barace da sace sace ko gaisuwar mutunci basa min ina Dalili Zama da mahaukata? Yana HAWAYE Yake Bata hakuri da cewa zai dauketa su bar gidan
Ganin kukan shi ya sata kuka itama Dole ya Rarrashe ta suka koma zaman kurame don tana Gama kukan tamkar wadda aka dadewa Baki tayi shiru ta zubawa dakin dake kallon nata ido inda ya dubi dakin don ganin abinda take wa kallo inda ya hango wasu Yan Mata su Biyu tsaye gaban dakin matar suna Mika Mata wani Abu a cikin leda.
Matar ta karba kamar ba me lalurar tabin hankali ba har suna magana da matar suna tambayar ta tana Basu amsa. Dayar budurwar ta ci gaba da karade gidan mahaukatan tana kalle dakunan inda idon ta ya fado Kan Halima da sauri ta juyo tana Kiran sunan Salma
“Salma ! Dubi wata Mata can Wallahi kamar mamar ku . Da sauri Salmar ta dubi inda ake Mata nuni sai kawai ta ga fuskar Halima kamar mamar ta da Allah yayiwa Rasuwa.
Ta zubawa Halima ido Mai Kano na kallon su Kuma Yana Jin su inda Kuma yajiyo Halima na fadin
“Kaga mahaukaciyar can dawo ne fa aka kawo Mata idan zaka dawo Nima ka tawo min da dawo.
Salma na Jin Haka ta dauko dawon curi uku ta nufo dakin Halima ta sunkuya cikin girmama wa ta Mika Mata ta karba tana fadin ta gode
Wannan abun ya burge Mai Kano ganin yadda ta girmama mishi mahaifiyar shi.
Ga mamakin shi sai yaga HAWAYE na bin idon Salma wadda ya Rasa ko hawayen meye. Da haka su Salma suka fice shima yayi musu Rakiya da ido.
Ya Dade kafin yayiwa Halima sallama inda take Kara jaddada mishi sakon ya taho Mata da dawo idan zai dawo
Ya taho da salma Aran shi ta Kuma Dade mishi arai Yana tunanin ta . Ba zaice Bai San Dalili ba sai dai kamar ba wancan dalilin bane na taimakon mahaifiyar shi kawai ba sai dai ya barwa Rai da zuciya.
Tun daga wannan Rana idan Salma ta Rako kawar ta ziyarar mahaifiyar ta sai tazo wurin Halima ta gaishe ta har ma ta samu abin Bata
Dawo ko lemu ko wani abun sakawa Baki acewar ta matar tashiga Ranta Kuma kamar da tayi da mahaifiyar ta yasa tana jinta Tamar mahaifiya sai hakan ya saka sabo da shakuwa tsakanin ta da Halima wani lokacin tayi Mata ADDU A wani Kuma idan soki burutsun yazo ta yi mata koma ta dura mata Ashar Amma duk Bata damuwa.
Alh Aminu Duniya ta samu fiye da zato inda kuma Zubaina ta sanar dasu cewa Halima ta haukace har ma ta shiga turu.
Sai dai abinda ya kasa ganewa Akan Husna shine duk lokacin da zasuyi Arangama da Husna to zata tafi da dukkan nutsuwar shi har yaji Yana son yayi ta kallon yarinyar.
Gane hakan yasa ya tsiri saka Husna aikin da haj wasila ce kawai ta cancanci yin shi irin su dafo Ruwan Lipton da Nemo mishi wani Abu a dakin shi. Hidima dai irin ta miji da Mata
Husna ba ta kawo komai a Ran ta ba duk abinda ya saka ta kanta tsaye take yi mishi a matsayin shi na Daddy a gareta Bata kawo komai a Ran ta ba. Wannan Kam sai Yaya muhsin shi take kallo a matsayin Rabin Rai.
Farkon farawa Hajiya wasila Bata San anayi ba sai da ta kula gata a zaune zai saka Husna aikin da ita ce ya Dace tayi mishi. Tana cikin tukukin bakin cikin hakan Kuma Amal ta Zo Mata da batun Mai Kama da tsegumi….
“Nifa Mami abinda Daddy keyi agidan Nan ya Fara Isa ta . Saboda Allah sai ya saka Husna Abu sai Kuma yayi ta binta da kallo? Ran Nan fa dakin shi ya aiketa Wai ta laluba cikin Rigar da ya cire ta dauko mishi takarda. Ina aka taba Haka saboda Allah? Yaya muhsin Yana so shima Yana so kenan? Ta fada Alamar Ranta ya motsa.
Haj wasila ta zaro ido. “Duk ki bar su shi da muhsin din ban yarda ba ba Kuma Zan yarda ba Ni dama nasan sai yarinyar can ta zame min kayar kifi a makogoro to duk ki barsu Dani suke zancen Wallahi ai ban San Yana saka yarinyar can aiki ba sai yau.
“A a Mami in Yaya muhsin ya so ta ai sun Dace ne Amma Ina Daddy Ina wannan abun kunyar?.
Har shu muhsin din sai dai ya Nemo wata Amma ba ahalin Halima.
Da Haka Amal ta fice tana bawa mamin magana Akan ta kyale Yaya muhsin da Husna tana cewa Wallahi ba zata Bari ba.
Kwana biyu da yin hakan sai ga Alh Aminu da babbar wayar hand set Mai tsadar gaske Wai ya siyowa Husna abinda ya kular da Hakiya wasila har ta tanka a zafafe.