Skip to content
Part 37 of 67 in the Series Aminaina Ko Ita? by Rasheedat Usman

Bedroom ɗin Momma ta shiga tana bacci bata tasheta ba ta buɗe wadrop ɗin ta inda tasan tana ijiye magani ta ɗauka tare da komawa bedroom ɗin Haidar maganin ta ɓare tare da tsiyayar ruwa ta miƙa masa tana cewa.

“Yaya Haidar gashi ka daure ka tashi kasha maganin.”

Da idanunsa Haidar yabi Rufaida da kallo cike da tausayin ta da kuma tausayin kansa babu musu ya tashi ya zauna tare da amsar maganin yasha, komawa yayi ya kwanta tare da rufe idanunsa yayi shuru, numfashi Rufaida ta saki tana kallon sa jin ciwon take tamkar a jikinta, gagara barin bedroom ɗin tayi, ta zauna ta zuba masa idanu kawai, sun kai kusan awa daya Haidar bai buɗe idanunsa ba, bawai kuma bacci yake ba, cikin sanyin murya Rufaida tace.

“Yaya Haidar meke damunka hankalina ya tashi da alamu ciwon kan damuwa ne please dan Allah ko bazaka iya faɗa min damuwarka ba, dan Allah ka rage yawan damuwar?”

Idanunsa ya buɗe still bai tanka mata ba, wayarsa yaja tare da dannawa Nafeesa kira, harta gama ringin ta katse ya kuma kira bata ɗaga ba, ijiye wayar yayi yana runtse idanunsa, zuciyarsa na tsinkewa, a hankali ya tashi ya zauna tamkar baya son Magana ya cewa Rufaida.

“Rufaida zaman ya isa haka ki tashi kije naji sauƙi.”

Kallon sa tayi tare da ɗaga kanta tace.

“Shikenan amma dan Allah ka rage yawan damuwar Allah ya ƙara sauƙi.”

Tayi maganar tana miƙewa tabar bedroom ɗin, tana fita hawaye na zirarowa daga idanun haidar tamkar mace, ya rasa nutsuwar sa da sukuni ya rasa wani irin soyayya yake gwadawa Nafeesa, “meyasa zata gujeni meye na mata meye aibunna mena rageta dashi, waye ne wannan wanda Nafeesa take guduna akansa lallai ko wayene na tsanesa na tsanesa, domin kuwa yayiwa rayuwarta kutse ya mini karan tsaye yana ƙoƙarin rabani da farin cikina, bazan rabu da Nafeesa ba domin itace rayuwata, duk yadda zanyi domin ganin ta dawo gareni sai nayi na ɗauki alƙawarin dawo da Soyayyata koma waye yake ƙoƙarin shiga tsakanina da Nafeesa sai naga bayansa bazan taɓa ƙyalesa ba?”

Ya furta yana dukan bed ɗin tare da cije bakinsa.

Tare suka shigo bedroom ɗin Ablah da Maimu tana zaune tayi shuru Rufaida ta zauna tana cewa.

“Ya dai Ablah tunanin me kike haka kinyi shuru, ko kinsan ba’a son yawan tunanin yana jawo mutum matsala a ƙwaƙwalwa yana kuma gadar da mantuwa, waima tunanin me kike haka.?”

Ɗan murmushi Ablah tayi tare da cewa.

“A’a ba tunani nake ba, kawai dai nayi shuru ne, saboda ni kaɗai ne.”

Murmushi Maimu tayi tace.

“Saboda ke ɗaya ce, sai ki dinga tunani ka tv bazaki kunna ba, ya jikin naki?”

“Da sauƙi sosai.”

Ta amsa mata a taƙaice kasancewar Ablah Mutum marar son Magana, murmushi kawai Rufaida tayi tana duban Maimu tace.

“Maimu yaya Haidar fa kwana biyun nan ina kallon sa cikin matsala da alamu kuma damuwarsa bata rasa nasaba da wannan shegiyar buduwar tasa Nafeesa.”

Duban Rufaida Maimu tayi cikin alamun mamaki tare da cewa.

“Matsala kuma, to amma meyasa zaki danganta matsalarsa da Nafeesa, shine ya faɗa miki hakan?”

“A’a ko ɗaya bashi ya faɗa min ba, nine kawai na fahimci hakan domin kuwa damuwarsa tafi kama da ta Soyayya, yau kamma yana can bedroom ɗinsa harda ciwon kai kamar zaiyi kuka.”

Tsuka Maimu taja tare da cewa.

“Mtsss! Nayi zaton ma faɗa miki akayi ashe hasashe kawai kikayi, to gaskiya hasashen ki ba dai-dai bane shi dai kawai damuwar sa ta dabance banda soyayya domin kuwa yarinyar tana sonsa fiye da yadda kike zato babu fa macen da zata bawa NAMIJI kamar yaya Haidar mai ilimi kuɗi kyau tausayi ace ta basa matsala, amma bama wannan ba, wai ya ake ciki ne har yanzu yaya Haidar baya baki attention ɗinsa ko kaɗan ne.”

Shuru Rufaida tayi tare da cije bakinta sai kuma ta ɗago ta kalli Maimu tace.

“Maimu nifa na cire rai akan yaya Haidar zai soni domin kuwa banga alamar hakan ba, shi fa bashi da wani tunani ko burin daya wuce wannan Nafeesan lissafin sa komai nasa tana ciki, ta ina kike tunanin zai kalleni, ina son ya Haidar sai dai na barwa Allah lamuransa duk yadda yayi dani dai-dai ne.”

Numfashi mai ƙarfi Maimu ta sauƙe tare da cewa.

“Hakane ni kaina yanzu bansan wacce irin shawara zan kuma baki game da lamarin nan ba, Allah dai kawai ya mana mai kyau, amma ni a nawa tunanin tunda Barrister Khalil yana ra’ayinki yana sonki mai zai hana ki basa dama, karkiyi wasa da damarki Rufaida akan Haidar da baya take kizo kina kuka daga baya, ko baki so Barrister khalil a waje ba zaki sosa idan kin auresa, ubangiji da kansa a cikin littafinsa mai tsarki yana cewa zamu so abu sai ya zamo ba alkairin mu bane haka zamu ƙi abu sai ya zamo shine alkairi a garemu Allah shine ya fimu sani, wataƙil Barrister khalil alkairi ne a gareki Rufaida kiyi tunani akan wannan maganar tawa, tunda hagu taƙi gara ki koma dama.”

Shuru Rufaida tayi idanunta ya ciko da hawaye cikin murya mai alamun kuka tace

“Allah ya sani Haidar shine a zuciyata dashi nake kwaɗayin rayuwa shine nake muradin Aure sai dai ƙaddara taƙi haɗa hakan, bani da ƙaddarar farin ciki dashi sai ta baƙin ciki, amma duk da haka ina godewa ubangijina daya ɗaura tawakalli ban bijirewa ƙaddarar sa ba, bazanƙi maganarki ba Maimu ya kamata naso Khalil ko ba komai ya nuna min Soyayya a yayin da ɗan uwana yake guduna, masoyi duk inda yake yafi maƙiyi na yarda da shawararki sai dai bana tunanin iyayena zasu amince da Khalil saboda kinsan ba’a ƙasar nan yake zaune ba.”

“Wannan ba damuwa bace Rufaida domin kuwa ko jiya da daddare munyi chat dashi yace next week ma zai dawo Nigeria gaba ɗaya ya gama aikin daya kaisa US.”

Ablah shuru tayi tana sauraronsu, cike da mamaki domin kuwa ita tana mamakin ace wai Mace tana son NAMIJI shi baya sonta, ita kuma abinda ubangiji bai ɗaura mata ba kenan Soyayya kuma bata ra’ayinsa, shigowar Inna Jumma itace ta katse masu zancen nasu.

“Au ja’irai wai dama nan kuka shigo, to ke Maimu Amarya tana can tana neman ki, ke kuma Rufaida aikenki zanyi gidan Hajja Safiya kice ta baki saƙon sai ki kawo min.”

Rufaida murmushi tayi duk da bata cika son zuwa gidan ba, gidan su khalil inda Inna Jumma ta aiketa Amma bata cewa Inna Jumma bazataje ba da to ta amsa tare da miƙewa tana cewa Ablah.

“To Allah ya ƙara sauƙi.”

Da ameen Ablah ta amsa sannan suka fice tare da Maimu.

Bayan Sati Uku

A cikin waɗannan kwanakin sosai Ablah ta samu lafiyar jikinta, a yayin da Haidar yake cikin matsanancin damuwa domin kuwa koda zai kira Nafeesa sau goma a rana bazata amsa kiransa ba, kuma koda zaije neman ta bata yadda su haɗu, wannan halin da ta sa Haidar a ciki yayi mungun tarwatsa masa tunanin sa, komai nasa yayi baya, a yayinda Nafeesa ta sako Al’ameen a gaba kira text, ganin sa ne kawai bata samun dama, sai dai ko kallon banza bata ishesa ba, a yayin da ya tsaurara bincike akan Rayuwar Nafeesa domin yana son lallai ya gano ainihin kalar yarinyar.

A kuma wannan satin duk wani ƙullin su Aunty Amarya akan waɗannan wanda tasa suka kaiwa Al’ameen hari ya cika domin sai da suka tabbatar da laifin kisan Ummi ya rataya a wuyan su, koda aka kaisu kotu babu wani ƙwaƙƙwaran bincike ko jayayya aka kaisu prison ɗaurin rai da rai, hakanne yasa aka kulle duk wani zargi da tantama akan kisan Ummi, bayan mutuwar Case ɗin Daddy ya koma American yayin da Faruq zai biyosa washegarin ranar daya koma.

Haka kuwa washegari da safe bayan sunyi breakfast Faruq na shirin tafiya zai tashi jirgin 11:30pm suna zaune a falo Faruq ya dubi Haidar da yayi shuru tare da cewa.

“Haidar meke faruwa ne da kai a waɗannan kwanakin bana ganewa lamuranka?”

Faruq ya jefawa Haidar dake zaune yayi shuru tambaya Al’ameen idanunsa ya ɗago ya kalli Haidar tare da mai da kansa gefe domin kuwa koda bai tambayesa ba yasan damuwarsa, numfashi Haidar ya sauƙe tare da lumshe idanunsa ya furta.

“Faruq damuwata bata da mafita domin kuwa na rasa matallafi da aso samu ne Al’ameen nake buƙatar yaje ya jiyo min ba’asi da alamu shi zata iya sauraron sa sai dai shi nasan bazaije ba shiyasa ma ban masa magana ba, amma ina cikin matuƙar tashin hankali da barazana domin kuwa bazan iya rayuwa babu Nafeesa ba, ina sonta fiye da komai na rayuwata Faruq bansan ya rayuwata zata kasance ba, Nafeesa bata sona yanzu?”

“Ka rabu da ita mana kaima tunda bata ra’ayinka, da nine kai da na juma da yin fatali da ita kamar yadda tayi fatali dakai, ka rabu da wannan Yarinyar ka samawa rayuwarka salama Haidar.”

Al’ameen yayi maganar kafin Faruq yayi, murmushi Haidar yayi tare da cewa.

“Bari na tambayeka kafin na kai ga baka amsa, na sani kana son ABLAH fiye da kanka shin zaka iya rabuwa da ita?”

Murmushi Al’ameen yayi duk da tambayar Haidar tazo masa a bazata,kafin yace.

“Zuciyoyi sun bambanta kamar yadda tawa ba irin taka ba ce kowa da yadda yake ijiye Soyayya a zuciyarsa wani yana ijiye tane yacce zata basa wahala wani kuma yana ijiyeta yacce ko ta zo masa da matsala zai iya riƙe kansa, to ni a wannan ɓangaren nake, ina son Ablah tabbas amma duk Soyayyar da nake mata gashi na iya riƙe zuciyata tunda har yanzu na kasa furta mata saboda ina gudun me zaije ya dawo min, amma tabbas idan Ablah zata min butulci irin wadda Nafeesa ta maka bayan rabuwa da ita har tsanarta sai nayi.”

Faruq da idanunsa yake binsu da kallo, Haidar cewa yayi.

“Sai nake ganin rashin furtawa Ablah Soyayyar ka tamkar datse kanka kake da wuƙa domin kuwa ita macece dole wani zai sota ina gudun wani ya rigaka karɓar zuciyarta, ina baka shawara a matsayina na abokina da kaje ka furtawa Ablah Soyayyar ka, sannan Al’ameen ka dubi cikin idanuwa da kyau ka gani, wallahi bazan iya rabuwa da Nafeesa ba. Zan iya mantawa da kowa da komai a rayuwata harma dani kaina amma bazan iya mantawa da Nafeesa ba, koda zanyi rayuwa babu ita to zan rayu ne cikin mutuwa domin kuwa bazan moru ba, gangar jikina ne kawai zaike amfani amma zuciyata ta riga da ta mutu, Al’ameen a yanzu haka da nauyin ƙirji da kuma zafin zuciya nake kwana bansan me zai faru dani gaba ba, na rayu cikin ƙasƙantacciyar rayuwa kona mutu gabaki ɗaya dole ɗaya zai faru.”

Yana Maganar hawaye na zuba masa Al’ameen a razane ya ke kallonsa cike da tashin hankalin maganganun sa marar misaltuwa, yana ƙare maganar ya tashi ya bar wajen yana saka hanu ya goge hawayen sa, Faruq ne ya dubi Al’ameen tare da cewa.

“Wai waye ce wannan Nafeesan kan shin babu zuciya a ƙirjinta ne, bata da imani ne, ta yaya zakayi watsi da mutum mai nuna maka Soyayyar gaskiya kamar Haidar, shifa a cikin mu mutum ne na daban wanda kowa ke ƙaunar sa, yake burge kowa amma yau rana ta farko naji wata ta nuna masa ƙiyayya Why?”

Numfashi Al’ameen ya sauƙe tare da dafe kansa duk wannan abubuwan da suke faruwa saboda shine, saboda shine Nafeesa take wahalar da rayuwar ɗan uwansa ya zamo dole ya haɗu da ita domin kawo ƙarshen wannan fitinar domin kuwa yau Haidar ya basa tsoro lallai rayuwar ɗan uwansa tana cikin hatsari muddun bai yiwa tufkar hanci ba, kallon Faruq yayi tare da cewa.

“Faruq a wannan rayuwar samun wanda zai soka tsakani da Allah muddun kana da kuɗi abune da yake matuƙar wahala, matan yanzu son duniya da buri ya musu yawa zasu so mutum ba dan Allah ba sai dan abinda yake dashi daga baya kuma suna hango wani wanda ya ɗaraka sai su zame daga gareka babu ruwansu da halin da zaka shiga su dai kawai su samu cikar burinsu shiyasa har yau nake tsoron furtawa Ablah kalmar soyayya duk da na santa na kuma yarda da tarbiyyar ta, amma ina cike da tsoro, da kuma fargaba saboda ni mutum ne wanda ban iya Soyayya haka kuma ban iya ƙiyayya ba, saboda duk ina tsananta su, babu makawa ita yarinyar da Haidar keso taga wani ne wanda yafi Haidar cancanta a gareta, amma ba komai zanje nayi magana da ita kamar yadda ya buƙata.”

Girgiza kansa Faruq yayi tare da cewa.

“Yau jirgina zai tashi da na rakaka domin ceto rayuwar ɗan uwanmu.”

“Karka damu, zanji da komai Daddy yana buƙatar ka kaje kawai, tashi muje yana jiran mu Haidar idan jirginka ya tashi ni zanje na sameta.”

Yayi Maganar yana miƙewa, shima Faruq miƙewa yayi tare da yin gaba, Al’ameen bayan Faruq ya fita ne ya ɗago wayarsa tare da dannawa Nafeesa kira cike da zafin zuciya, ringin ɗaya kuwa ta ɗaga cike da farin ciki domin kuwa a yanzu babu abinda take buƙata sama da taga kiran Al’ameen a cikin wayarta.

“Amincin Allah ya tabbata a gareka farin cikina, yau rana ce ta musamman a gareni domin kuwa naci karo da kiran abun ƙaunata.”

Idanunsa ya runtse tare da cije bakinsa cike da tsanarta yace.

“Ina son mu haɗu da ke a ina zan iya samunki idan hakan zai yiwu.?”

Dariya Nafeesa tasa domin kuwa gani take tarkon ta ya kama kurciya tace.

“Me zai hana, mu haɗu a gidan hutawar DFG swimming pool.”

“Okay 12:15.”

Yana Maganar ya katse kiran tare da bin bayan Faruq…

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Aminaina Ko Ita 36Aminaina Ko Ita 38 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×