Skip to content
Part 38 of 67 in the Series Aminaina Ko Ita? by Rasheedat Usman

A mota suka taradda Haidar ya kifa kansa jikin sitiyarin motar, numfashi Al’ameen ya saki tare da cewa.

“Faruq kuje a motar Haidar, ni bara naje a tawa saboda akwai inda zan biya ba lallai mu dawo da shi ba.”

Da to Faruq ya amsa yana shiga cikin motar, Haidar baice komai ba yaja motar shima Al’ameen yabi bayan su, sunyi nisa da tafiya Faruq yace.

“Kayi hkr Haidar ka sawa zuciyarka salama Saboda yawan damuwar zai iya gadar maka wata matsala ta ciwo munyi Magana da Al’ameen yace yanzu idan jirgin mu ya tashi zai biya can wajen ita Nafeesan su tattauna akan matsala insha Allah ina ji a jikina za’a samu masalaha.”

Kallon Faruq yayi tare da cewa.

“Da gaske shi Al’ameen ɗin ne yace maka zaije ya samu Nafeesa?”

“Ƙwarai kuwa shine ya sanar dani ya damu ƙwarai akan halin da kake ciki Al’ameen yana son farin cikin ka Haidar damuwarka tana ɗaga masa hankali, amma meyasa kake son dole sai Al’ameen ne zaije ya sameta, shin kana ganin zata sauraresa?”

“Ehh zata sauraresa Saboda tana ganin mutuncin sa da alamu yana mata kwarjini mtss Faruq Soyayya masifa ce idan baka dace ba Allah ya baka wacce zata soka da gaskiya.”

Ɗan murmushi Faruq yayi tare da saka hanu cikin aljihu ya zaro wata farar takadda yace.

“Na riga dana samu domin kuwa Maimu itace zaɓina ba kuma zata bani kunya ba na sani, ga wannan dama zan baka ka bata.”

Duk damuwar da Haidar yake ciki bai hanasa ɗan sakin murmushi ba yace.

“Gaskiya ne Maimu bazata baka kunya ba Allah yasa mu dace.”

Yayi Maganar yana amsar takaddar, koda suka isa airport ɗin sun ɗan juma kafin jirgin su Faruq ya tashi cike da kewarsa suke kallon tashin jirgin harya lula sararin samaniya, kafin Al’ameen ya dubi Haidar yace masa.

“Haidar zanje na samu Nafeesa muyi magana, shiyasa na fito da motata, zanyi iya ƙoƙarina domin ganin na dawo maka da Soyayyarka, Saboda naga lamu ta tafi da kurwarka kalamanka suna bani tsoro zanje.”

Yayi Maganar yana buɗe murfin motar sa ya shige da kallo Haidar ya bisa ba tare da yace komai ba har Al’ameen ya tayar da motar yabar wajen numfashi Haidar ya saki tare da buɗe tashi motar ya shiga.

DFG Swimming Pool

Zaune take ta harɗe ƙafafunta tana taunar cingum tana kallon ɗaiɗai kun mutanen da suke shawagi a wajen kowa yana harkar da ta kawo sa, agogon hanunta ta duba 1:00 shida yace mata 12:30 zaizo, lallai wannan gayen akwai rainin hankali, tsuka taja tare da ɗaukar wayarta.

Shi kuwa Al’ameen darect DFG ɗin ya nufo parking yayi tare da ɗaukar glass ɗinsa ya sanya sannan ya buɗe motar ya fito ɗan dube dube ya fara ta inda zai hangota can ya hangota zaune ta harɗe ƙafafunta tana zaune a kujera, nufota yayi cikin Cool voice ɗinsa a hankali tamkar baya son Magana idan ma ba bakinsa kika kalla ba, baza kiji abinda kikace ba, yayi sallama tare da jawo kujerar dake fuskantar Nafeesa ya zauna.

“Sannu da isowa, kayi let ka duba agogo kuwa.?”

Shuru ya mata tamkar baiji ta ba murmushi Nafeesa tayi tana zuba masa idanu ta kuma cewa.

“Maganata bata da amsa kenan, okay no wonder, naji daɗin ganinka, kayi kyau sosai tamkar basarake, kai mutum ne na musamman Al’ameen I love You.”

Sai yanzu ya sanya hanu ya zare glass ɗin idanunsa tare da sakin murmushin gefen baki ba tare daya kalleta ba yace.

“Banzo nan domin ki yabani ba, bana buƙatar yabawa daga bakin mace marar daraja da kamun kai irinki, wanda ya kamata ki furtawa I love You Haidar ne ba Al’ameen ba, saboda Al’ameen ba mutum bane shasha da za’a yaudari zuciyarsa da kalaman bariki.”

A matuƙar razane Nafeesa ta ɗago kanta tana duban Al’ameen kalaman Bariki ina Al’ameen yasan tana rayuwar bariki, meya sani akanta ita da ko a unguwar su babu wanda yake mata kallon marar kamun kai kowa kallon mutumiyar kirki yake mata amma shi kuma ya kirata da kalmar Bariki.

“Kina tunanin ina nasan sirrinki da kike ɓoyewa duniya ba, hmmm! Na faɗa miki ni ba gama garin mazajen nan bane da kike iya yaudara, idanuna a buɗe suke tar ki fahimta, shiyasa nake nuna miki cewa ki fita daga rayuwata kafin ki fusata zuciyata, domin kuwa kika yadda na hasala Tabbas zakiyi nadamar sanina a rayuwarki domin kuwa nasan komai a kanki.”

Baki buɗe take kallonsa kafin ta runtse idanunta, (Lallai wannan cikakken ɗan duniya ne) tayi Maganar cikin zuciyarta tare da jefa masa tambaya.

“Meka sani a kaina.?”

Murmushin gefen baki Al’ameen yayi tare da amsa mata da cewa.

“Abubuwa da yawa ciki harda yawon iskancin da kike karuwa ce ke.”

Wani irin ƙuna Nafeesa taji a zuciyarta ranta ya ɓaci, (Karuwa ce ke) ta maimaita kalmar a ranta, numfashi ta saki tare da ɗago idanunta a hankali ta dubi Al’ameen, murmushi yayi tare da cigaba da cewa.

”Kina da kwarto zance ko dadiro ne ban sani ba, wanda kika fi ƙauna acikin abokan watsewar taki Alhaji Atiku Naira kinfi hurɗa da shine Saboda yafi sake miki kuɗi, kina da bala’in son kuɗi zaki iya aikata komai akan kuɗi, kwatakwata ke ba mutumiyar kirki bace, amma sai dai abinda ya kulle min kai meyasa kike son ki aure ni, bawai ki lalace dani ba kamar sauran, amma fa kai kawai ya kulle min bawai amsa nake nema daga gareki ba, Nafeesa ban damu da karuwancinki ba saboda ba rayuwata bace iyayenki ma sun zuba miki idanu bare kuma ni, kawai ki fita daga rayuwata shine Abinda ya dameni na tsaneki bana sonki.”

Murmushi Nafeesa tayi duk waɗannan maganganun da Al’ameen yayi basu ɗaga mata hankali ba domin kuwa tasan dole dama za’ayi haka zai binciko rayuwarta saboda shi mutum ne mai taka tsantsan ba irin Haidar da babu abinda ya damesa ba, abinda yake gabansa shine kawai yake yi cikin nutsuwa tana sakin murmushi ta fara magana.

“Gaskiya na jinjinawa ƙwaƙwalwarka domin kuwa da lissafi kake komai, na yarda ni ba mutumiyar kirki bace, amma me zai hana kai ka zamo sanadin shiriyata, domin kuwa Soyayyar gaskiya nake maka ba kuɗi ko wani abu nake nema daga gareka ba, Soyayyar ka kawai nake so ka Aure ni zan daina komai na saɓon ubangiji na dawo mutumiyar ta ƙwarai, ana ganin karuwa a titi harma da ɗan shege, a kuma sota a sata tayi istibira’i a aureta, ina sonka Al’ameen karka juya min baya ka soni domin Allah.”

Tayi Maganar cikin salon yaudara fuskarta cike da ban tausayi murmushi Al’ameen yayi tare da cewa.

“Kalamanki baza su iya tasiri a ƙwaƙwalwata ba, bazanji salon yaudarar ki ba, idan kin haukace ni ina da hankali, karki manta da ɗan uwana kike Soyayya, hmmm! To kuma me zaisa ni na shiga tsakanin ku, kinso Haidar koda ma da yaudara ne idan kina da kunya bazaki dubi tsabar idanuna kice kina sona ba, bama wannan bane ya kawo ni nan, ganina ma da kikayi anan kinci albarkar shi wanda kika raina ɗin Haidar domin kuwa shine yasa nazo kika ganni, ki saurareni da kunnen basira Nafeesa mu tattauna akan abinda ya kawo ni nan?”

“Taya zan saurareka bayan baka amsa min soyayyata ba, bani da hankali da tunani yanzu muddun baka furta min kalmar ka amince da Soyayyata ba, domin kuwa bazan samu nutsuwar sauraronka ba.”

“Amsa min tambayata meyasa kika juyawa Haidar baya, Haidar yana sonki sosai kina da mahimmanci fiye da komai a rayuwarsa.?”

Shuru Nafeesa tayi tare da ɗago idanunta ta lumshe su tare da kuma buɗe su a fuskar Al’ameen ta amsa,

“Saboda kaine tunda na ganka na fahimci bana son Haidar, kaine wanda nake so rayuwata bata dace da Haidar ba dakai ta dace, shiyasa na rabu dashi.”

“Hmmm! Saboda ni zaki guji mutumin da nafi ƙauna fiye da komai a duniya kuma kiyi tunanin zan soki, har abada babu soyayya tsakanin mu, saboda tun sanda Haidar yake bani labarin ki kafin ma na kai ga ganin wannan baƙar fuskar taki na tsaneki, kije ki bawa Haidar kulawa domin kuwa shine mai miki Soyayyar gaskiya yana sonki zai iya fuskantar mutuwa saboda dake, kin samu wannan damar na Soyayya da mutumin daya fi ƙarfin ajinki, karkiyi wasa da wannan damar sau ɗaya ake samun dama a rayuwa, baya fahimtar komai Indai akanki ne, kije ki lallaɓa Rayuwarki dashi ni ki rabu dani domin kuwa bana sonki, shima Haidar da ace ina da damar da zan cire Soyayyar ki daga zuciyarsa da ƙarfi zan fisge shegiya na yasar sai dai bani da wannan ikon saboda zuciyarsa tayi nisa akanki baya jin kira komai za’a faɗa masa akanki baya yadda, hmmm! Nafeesa Haidar zai iya rabuwa da kowa a duniya saboda ke, dan Allah karki shiga tsakanina da aminina muna ƙaunar junanmu babu abinda ya taɓa haɗamu na ɓacin rai dan Allah ke karkiyi sanadiyyar shiga tsakanin mu dalilin dayasa nazo wajenki kenan Idan kuɗi kike buƙata daga gareni ki faɗa min ko nawa ne zan baki kije ki cigaba da Soyayya da Haidar ni ki ƙyaleni.”

Murmushi mai sauti Nafeesa tayi tare da miƙewa tsaye ta ɗauki bag ɗin ta tace.

“Bana buƙatar kuɗin kuma bana buƙatar Haidar kai nake buƙata kuma kai zan aura wannan dole ne ka saka a ranka, idan ni zan bawa Haidar kulawa to bazai samu ba, kaine zaɓina i love You.”

Tayi Maganar tana ɗaga masa gira tare da barin wajen da idanu Al’ameen ya bita harta ɓacewa ganinsa idanunsa ya runtse tare da miƙewa tsaye zai bar wajen mai kawo drink ya dakatar dashi da cewa.

“Ranka shi daɗe baku biya kuɗin shigowa dana drink ba.”

Hanu yasa cikin aljihun sa ba tare da yayi magana ba ko ya tambaye sa nawa ne kudin ba ya zaro rafar 100k ya basa godiya mutumin ya hau masa bai amsa ba yabar wajen cike da ɓacin rai, baya ƙaunar Haidar yasan dalilin da yasa Nafeesa ta gujesa yana tsoron matsalar da zata shiga tsakanin sa da ɗan uwansa domin kuwa idanun Haidar a rufe suke akan wannan Yarinyar lallai HATSABIBIYA ce dole sai yayi taka tsantsan da ita numfashi ya saki tare da jan motar yabar wajen.

Zaune suke cikin bedroom ɗinsa, momma ce ta ɗaga idanunta ta dubi Papa tare da cewa.

“Baban Aliyu akwai Maganar da nake son muyi da kai mai mahimmanci na kwana biyu da wannan maganar a bakina ina son mu tattauna kai kuma baka samun time.”

“Okay ina sauraranki.”

“Baban Aliyu Magana ce akan Rayuwar Aliyu akwai abinda na fahimta dashi game da Rufaida ya kamata mu haɗa su Aure kaga zumunci zai ƙara danƙo, yarinyar tana sonsa sosai ni ina ga dalilin daya sa kenan Rufaida ta dawo part ɗin nan da zama tana bani tausayi sosai ta damu da Aliyu haka wani sa’in zata shiga bedroom ta dinga kuka ita kaɗai ya kamata mu duba wannan lamarin.”

Shuru Papa yayi kafin yace.

“Hajiya Hadiza ita Rufaidan ce take cikin wannan halin saboda ɗan uwanta.?”

“Ƙwarai kuwa, Rufaida tana son Aliyu, ya kamata kayi duba ga lamarin mu muka haifi Aliyu bashi ya haife mu ba, muna da ikon zaɓa masa matar daya kamata ya aura kuma dole a garesa ya mana biyayya.”

Murmushi Papa yayi tare da cewa.

“Hajiya koda bakiyi wannan maganar ba, dama shine ƙudirina haɗa Aliyu da Rufaida Aure, karki damu Aliyu bashi da mata sai Rufaida zanyi Magana da ƴan uwana.”

“Amma sai dai wani hanzari ba gudu ba, Yaron nan fa kamar shi baya son Rufaida akwai wacce yake so, ina tsoron karya bamu kunya da dai ka gama da shi tukunna kafin kuyi Magana dasu Baban Rufaidan kasan Inna Jumma idan taji magana tana ɗaukarsa ne da zafi.”

Murmushi Papa ya kuma yi yace.

“Hajiya Hadiza kenan me kika faɗa ɗazu, mu muka haifi Aliyu bashi ya haife mu ba, dole ne ya zamo Auren Rufaida a garesa, ita na zaɓa a matsayin surukuta muddun kuma nine na haifi Aliyu dole zai min biyayya ki daina saka wannan tunanin a ranki.”

“To shikenan Baban Aliyu, idan har Rufaida ta Auri Aliyu sai nafi kowa farin ciki domin kuwa bazamu samu suruka kamar Rufaida ba mai biyayya da kunya nima zan dage wajen ganin wannan Auren ya ɗauru ita Yarinyar bamu da matsala da ita saboda ina da tabbacin tana sonsa.”

“Insha Allah Auren yama ɗauru shi kuma Aminu akwai wacce yake so ne da so nake na haɗasa da Madina.”

Murmushi mai sauti Momma ta saki tare da cewa.

“Gaskiya banji wani labari ba amma gaskiya idan ka haɗa waɗannan Auren ba ƙaramin jin daɗi dangi zasuyi ba, gashi itama Madinar dama babu wani tsayayye har yanzu, kuma nasan Al’ameen bazai baka kunya ba kayi tunani mai kyau.”

“Hajiya Hadiza, a wannan lokacin ne ya kamata mu haɗa ya’yan mu zumunci domin kuwa Rayuwa ta lalace shigowar bare cikin dangi kan haifar da matsaloli idan ba’a dace ba duk da ba sosai aka cika samun hakan ba, kije ki haɗa min ruwan wanka ina son zan fita.”

Murmushi Momma tayi cike da farin ciki ta miƙe ta shige tollet ɗin Papa.

Zaune take tayi shuru bakin flower tana kallon su, tana buƙatar zuwa wajen Ummanta sai dai ta rasa wannan time ɗin ga school da zata fara tafiya gobe, ya kamata ace yau taje ta ko da la’asar ne.

Tana cikin wannan tunanin taji an zauna a gefenta, ɗaga idanunta tayi ta dubi wanda ya zauna kusa da ita Al’ameen ne yayi irin zaman da tayi ya tallafi fuskarsa tare da ƙura mata idanu, suna haɗa ido Ablah ta sunkuyar da kanta ƙasa a hankali ta furta.

“Kaine.?”

Murmushi Al’ameen yayi tare da amsa mata da.

“Umm nine na baki tsoro ko Tunani me kike haka.?”

“Bana tunanin komai.”

Ta amsa masa tana sakin murmushi shima murmushin yayi tare da cewa.

“Zuciyata ta faɗa min kina tunanin Umma, kina kewarta ba?”

Ɗan dariya Ablah tayi har haƙwaranta suna bayyana tace.

“Ya akayi ka fahimci ina buƙatar ganin Ummana.?”

“Saboda zuciyata da taki iri ɗaya ce shiyasa nake fahimtar abinda ke cikin taki zuciyar.”

“Zuciyoyinmu iri ɗaya ne kuma kamar yaya ban fahimta ba, zuciyata dabam taka dabam ta yaya zasu kasance iri ɗaya.?”

“Wannan ba abun mamaki bane Ablah dan zuciyata da taki sunzo iri ɗaya, wataƙila ma tare aka hallice su ya kamata ki fahimta.”

Cike da mamaki ta ɗago tana kallon sa har yanzu ta kasa fahimtar zancen sa…….

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Aminaina Ko Ita 37Aminaina Ko Ita 39 >>

1 thought on “Aminaina Ko Ita 38”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×