Skip to content
Part 39 of 67 in the Series Aminaina Ko Ita? by Rasheedat Usman

“Na kasa fahimta ta yaya za’ace haka ni dabam kai dabam kuma zuciyoyinmu suzo iri ɗaya, kaima dai ka faɗa ne kawai, amma hakan ba abu bane da zai yiwu.”

“Hmmm! Ba faɗa bane kawai haka yake da’ace Mutane sun fahimci rayuwa tafe take da haɗewar zuciyoyin mutum biyu waɗanda suka haɗu kuma suka aminta, da juna suka yarda cewa ƙaddarar su tare take, da wani ba zaiyi kuskuren shiga rayuwar wani ba, Ablah da gaske zuciyata a haɗe take da naki kuma zan iya shiga cikin tunaninki kamar yadda kema zaki iya shiga cikin nawa tunanin, haɗuwar zuciyata da taki daga rabbil izzati ne shiyasa ya fara haɗani dake domin ki shigo cikin rayuwarmu har ki zauna a cikin mu.”

Still dai Ablah kallon Al’ameen take domin kuwa zantuka yake mata waɗanda suke kulle mata kai ta kuma kasa fahimtar su, numfashi ta saki tana saka hanu ta tsinki farin fure mai launin ja a tsakiyar sa tare da ɗagowa tace.

“Yaya Al’ameen ya kamata kamin magana ta yadda zan fahimta domin na kasa gane wannan zaurancen naka.”

Murmushi yayi tare da girgiza kansa hanu yasa ya amshi furen hanun nata tare da kaiwa hancinsa ya shaƙi ƙamshinsa yace.

“Ƙamshin sa gwanin daɗi shi kansa kyau ne dashi, jigon Soyayya fure, Ablah akwai wanda ya taɓa furta miki kalmar so ma’ana kin taɓa Soyayya, ko kin zauna kusa da wanda ya taɓa shiga cikin so?”

Kanta ta girgiza tare da furta.

“A’a ban taɓa ba, bani da alaƙa da Soyayya shiyasa ban damu da sanin ya ya take ba, amma meyasa kamin wannan tambayar.?”

“SABODA ina sonki ne Ablah tun ranar da idanuna suka fara ganinki zuciyata ta fara amsar dakon Soyayyar ki.”

A firgice Ablah ta ɗago idanunta cike da munguwar mamaki Ummi ce ta faɗo mata a ranta sanda take gargarar mutuwa (Ablah ki auri Al’ameen nasan zaki kula da rayuwarsa) idanunta Ablah ta runtse tare da cewa.

“Bai kamata ka ambaci wannan kalmar ba ta soyayya a gareni, ni ba tsarar Soyayyar ka bane ko wacce ƙwarya da Abokiyar Burminta, ƙwarya tabi ƙwarya sam ban dace da rayuwarka ba, kafi ƙarfin Soyayya dani yaya Al’ameen kai ɗan manyan mutane ne wanda ƙasa ke alfahari dasu duniya ta sansu suke taimakon al’umma, dan haka baka dace da ƴar gajiyayyun talakawa irina ba, dan Allah ka daina wannan maganar, koda mun dace ni bani da ra’ayin Soyayya a gabana karatuna shine burina ka nemi dai-dai kai yaya Al’ameen, ina son nayi karatu mai zurfi domin na taimaki mahaifiyata bata da gatan daya wuceni a yanzu ƙarfinta ƙarewa yake dole dai ni ce zan zamo jigonta tunda ni ce sama da Abdul.”

“Hmmm! Ablah kenan zan miki uzuri tunda kince baki san Soyayya ba kuma baki da alaƙa da mai yinta, amma tabbas baki yiwa soyayya adalci ba, da kika banbance sa da mai arziki da talaka, Ablah babu ruwan Soyayya da dacewa idan har zuciya ta kamu da Soyayya babu ruwanta da wannan mutumin yaya yake ita dai kawai burinta ya sota, Ablah zuciya tana da banbanci da sauran gaɓoɓi domin kuwa ita harbawa take da burin cikar dukkan muradin wanda ya mallaketa bata kuma samun sukuni har sai ta cika wannan muradin, zuciya mahaukaciya ce akan soyayya kuma makahuwa, babu ruwanta da cancanta, dan haka ki daina danganta Soyayya da dacewa, domin kuwa babu ruwanta da wannan, ina sonki kije kiyi tunani akan hakan sannan ki daina tunani akan goben Umma muddun ina numfashi bazan bar rayuwarta ta ƙasƙanta ba, Umma ta kwana biyu da daina kukan damuwa kuma bazata sake ba har ƙarshen rayuwarta nima uwace a wajena, koda ban sameki a matsayin mata ba, bazan daina bautawa Umma ba.”

Yayi Maganar dai-dai Haidar na ƙarisowa wajen kafin Ablah takai ga bawa Al’ameen amsa.

“Tun ɗazu nake kiran wayarka baka ɗauka ba, kuma mai gadi ya sanar dani ka kai 1hours da shigowa cikin gidan nan nayi zaton zaka nemeni kuma naji shuru mtsss kasa duk na firgita?”

Ɗago idanunsa Al’ameen yayi ya kallesa tare da maida dubansa ga Ablah da take tsaye ta buɗe baki tana kallon sa, da ganin idanunta bakinta cike yake da magana baiso ace Haidar yazo ya katse masa hanzari ba, iska ya fesar daga bakinsa tare da cewa.

“Wayar tana bedroom ni kuma ka ganni a nan, gani yanzu, Ablah jeki zamuyi magana daga baya.”

Kanta Ablah ta girgiza tare da shigewa daga wajen, Haidar sunkuyawa yayi gefen Al’ameen tare da cewa.

“Ka haɗu da Nafeesa kuwa?”

“Eh na haɗu da ita.”

“Al’ameen naga fuskarka da alamun sauyawa, kamar baka son maganar Nafeesa, amma ka sani hankalina bazai kwanta ba har sai naji ya kukayi?”

Bakinsa Al’ameen ya cije cike da ƙunar rai gami da tausayin Haidar na son Yarinyar da bata dace da rayuwarsa ba, idanunsa naga furen da ya karɓa daga hannun Ablah yace.

“Hmmm! Akan wani dalilin zanƙi son maganarta, Haidar naje na samu Nafeesa munyi Magana da ita, amma sam ta nuna min bata buƙatar tayi rayuwa da kai, Haidar tunda har ta furta bata buƙatar ka cikin rayuwarta Haidar kaima ka rabu da ita mana, ganan mata da yawa cikin gari waɗanda suka fita komai na rayuwa kaje ka nema ka rabu da wannan yarinyar bata da imani.”

Idanunsa Haidar ya runtse yana jin maganganun Al’ameen tamkar wuta a kunnensa, idanunsa ne ya kaɗa yayi jajur domin kuwa koda wasa baya ƙaunar yaji an ambaci kalmar rabuwa tsakanin sa da Nafeesa ya tsani kalmar tana sanya masa nauyin ƙirji, cikin alamun rashin jin daɗi ya fara Magana.

“Har sau nawa zan sanar da kai cewa Nafeesa rayuwata ne, ka taɓa ganin wanda ya rabu da zuciyarsa kuma yayi rayuwa, bazan taɓa rabuwa da Nafeesa ba har abada domin kuwa itace numfashi na dole sai da ita zanyi rayuwa idan babu Nafeesa to Tabbas babu ni, rayuwata mutuwa zatayi idan babu ita Al’ameen ka daina danganta rabuwa tsakanin mu, komai wahala komai rintsi sai na mallaki Nafeesa!.”

Idanunsa Al’ameen ya runtse ya tsani shouting a rayuwarsa miƙewa yayi tsaye tare da zuba hanunsa cikin aljihun sa ya ce.

“Menene abun tsawa anan, ka sani na tsani shouting, please ka daina ɗaga min murya akan wannan marar mutuncin yarinyar wacce bata san menene hallaci ba, Haidar ka dage akan wannan Yarinyar to ka sani bata da imani bazata taɓa tausaya maka ba, koda kuwa gani tayi zaka mutu, kai idan har ta samu dama zata iya kasheka da hanunta domin kuwa tafi buƙatar duniya fiye da Soyayya.”

Yayi Maganar yana juyawa zai bar wajen cike da haushin Haidar, muryar Haidar ce ta dakatar dashi.

“Da Nafeesa zata kasheni da na huta da zafin Soyayyar ta kuma kafin numfashi na ya tsaya zan yafe mata domin kuwa koda ita bata sona yanzu, ni har abada ina sonta kuma da Soyayyarta zan koma ga mahalicci na, Al’ameen bazan taɓa daina ɗaga maka murya ba Muddun baka daina aibata Nafeesa ba, ina jin haushin duk wani mai faɗar mummunan kalma a kanta ciki kuwa harda kai, ka sani bazan daina son Nafeesa bazan cireta daga rayuwata ba kamar yadda kake buƙata na faɗa kuma zan maimaita Nafeesa tana zuciyata har abada bazata taɓa fita ba har ƙarshen rayuwata, sannan baka sanar dani abinda Nafeesa ta faɗa maka ba ka juya zaka tafi ka barni ni ga mahaukaci ko?”

Juyowa Al’ameen yayi yana kallon sa tare da girgiza kansa, gani yake anya kuwa Haidar bazai haukace ba akan wannan fitinanniyar Yarinyar, baice masa komai ya cigaba da tafiyar sa runtse idanunsa Haidar yayi tare da dafe kansa wai meke shirin faruwa dashi ne lallai maganganun Al’ameen sun tabbatar masa Nafeesa bata basa amsa mai kyau ba, ba ƙaramin abu bane yake saka Al’ameen ya hasala da yiwuwar Nafeesa bata sauraresa ba, numfashi ya saki tare da kuma runtse idanunsa ya jingina jikin bangon wajen, hanunsa yasa a cikin aljihun sa ya ciro wayarsa Nafeesa ya kuma kira 4miss call bata ɗaga ba sai a na 6 Nafeesa ta ɗaga wayar cikin tsawa tace.

“Wai kai bazaka rabu dani ba, ka dameni da kira malam, kasan dalilin da yasa na ɗaga kiran ka, gargaɗi zan maka karka kuma turo min wani domin kuwa koda ubana ka turo bazan sauraresa ba akanka, na faɗa maka a yanzu bana sonka na samu wanda nake so fiye da kai kuma dashi zanyi rayuwa, dan haka dan ka bawa wannan marar lissafin zuciyar taka haƙuri kace mata Nafeesa tafi ƙarfin ta.”

Tana Maganar bata bari Haidar yayi magana ba ta yi saurin katse kiran, wani irin raɗaɗi da ƙuna zuciyar Haidar ta fara, duk da yaji daɗin jin muryarta ƙwarai sai dai yanayin amon kalamanta sun ƙona masa zuciya, a fili ya furta.

“Zanyi haƙuri na jure tsanani da wahala akanki Nafeesa nasan kina sona duk yadda akayi wannan tsinannen da kike min magana akansa shine ya hure miki kunne kika juya min baya, zaki dawo gareni Nafeesa saboda nine masoyinki na haƙiƙa, Allah ya nuna min wannan matsiyacin daya shiga rayuwata idanuna idanunsa sai naga bayansa na tsanesa koma waye shi.”

Yayi maganar yana dukan bango idanunsa na ziraro da hawaye hanu yasa ya goge hawayen tare da miƙewa yabar wajen.

Tunda ya shiga bedroom ɗinsa hankalinsa ya kasa kwanciya, sai kaiwa da komowa yake, cike da tunani (ina jin haushin duk wani mai faɗar mummunan kalma akanta ciki kuwa harda kai) kalaman Haidar suka dawo masa.

“lallai Haidar zai iya aikata komai akan soyayyar wannan karuwar, me zai faru idan Haidar yasan nine Nafeesa take so yarinyar makira ce zata iya aikata komai domin shiga tsakanin sa da Amininsa anya kuwa Haidar zai fahimce ni, kai ina Haidar bazai taɓa min mummunan fahimta ba, dole zai fahimce ni, to kona sanar dashi, kai idan na sanar dashi yanzu akwai matsala domin kuwa baya cikin hankalinsa gara na bari na kawo ƙarshen matsalar ba tare daya sani ba, mtsss! Wannan yarinyar wacce irin rayuwa take haka ƙazama sai kace bata da mafaɗi, ya zamo dole na kawo ƙarshen wannan fitinar kafin ta girmama.”

Yayi Maganar yana dafe kansa tare da zama bakin bed ɗinsa, yana kulle idanunsa (saboda kaine tunda na ganka na fahimci bana son Haidar, kaine wanda nake so, rayuwata bata dace da Haidar ba da kai ta dace shiyasa na rabu dashi)

Still maganar Nafeesa ta kuma dawo masa, idanunsa ya buɗe tare da furta.

“Koda na rasa matar Aure a duniya bazan taɓa auranki ba, da dai na Auri ƙazamar mace irin Nafeesa mai cike da dauɗar zina gara na mutu babu Aure, wannan wata irin rayuwace ta jahilci kiyi Soyayya da abokina kuma ɗan uwana sannan ki dawo kice shi kin fahimci bai dace da Rayuwarki ba, dani kika dace, yau naga shegiya jaka.”

Yayi Maganar yana kuma komawa ya zauna shifa yau kansa ya kulle damuwa ta damesa ya rasa ta wacce hanya zai fara ƙoƙarin kawar da wannan matsalar da ta taho masa, ganin tunani na neman masa yawa ya sashi ɗaukar wayarsa tare da maƙala airpies a kunnensa ya kunna suratul Hud ƙira’ar shek munshawi.

Itama Ablah tunda Al’ameen ya furta mata kalmar Soyayya ya sata cikin tunani domin kuwa bata taɓa zato ko tunanin kalmar zata fito daga bakinsa ba, sai gashi ya furta mata, bata taɓa jin Soyayyar sa ba koda da second ɗaya ne, amma wai shi cewa yake ya juma da Soyayyarta, bazata yadda ta amince da Soyayyarsa ba, domin kuwa Al’ameen yafi ƙarfinta ta ko ina, gara ta ijiye kanta inda Allah ya ijiyeta tasan koda zata amince da Soyayyarsa iyayensa bazasu taɓa yadda ya aureta ba, Koda ma kuwa iyayensa zasu amince, to ita ina ma ruwanta da wani Soyayya ita da karatu ne a gabanta, numfashi ta furzar tare da gyara kwanciyarta ta furta.

“Hmmm! Ita kuma wannan kwana biyu tayi shuru ko me take shiryawa domin kuwa na Tabbata shurunta ba alkairi bane, Allah sarki Ummi ankashe ki a karon banza wai tsabar makirci irin na amarya ta ɗaurawa wanda baiji ba bai gani ba kisan kuma har a yanke musu hukunci lallai wannan matar abun tsoro ce, bai kamata na sakankance haka ba dan kawai naga tayi shuru ya kamata na cigaba da bibiyar lamuranta domin kuwa nasan ƙudirinta bai cika ba dole da akwai abinda take shiryawa.”

Tayi maganar tana tashi ta zauna sai yanzu ta ankara da Aunty Amarya tana shirya wani abun domin kuwa yanzu bata shiga sabgar ta hakan yana nufin tana shirya mata zagon ƙasa ne saboda karta dakatar da ita, (lallai kuwa zan bibiyeki domin kuwa a wannan karon bazan taɓa bari haƙarki ta cimma ruwa ba).

Tayi maganar zucin tana sakin numfashi tare da miƙewa ta nufi bedroom ɗin Inna Jumma tana son sanar da ita gobe daga school zata biya wajen Umman ta.

Tun daga falon take sallama shuru tamkar babu kowa dube dube take cikin falon, hakanne ya sata shiga bedroom ɗin Hajiya Mansura darect tana kwance tana bacci, murmushi amarya tayi tare da saka hanu ta ɗan daketa, buɗe idanunta tayi tana hamma tare da kallon Aunty Amarya tace.

“Wai dama kece amarya yaushe kika shigo.?”

“Yanzu na shigo kina ta baccin asara, falonki kuma babu kowa sai tv dake kunne.”

Tashi Hajiya Mansura tayi ta zauna tare da cewa.

“Nabar Najib a falon kafin na shigo maybe fita yayi, daga ina haka.?”

“Daga gidana mana zuwa naki, Malama gani nayi kwana biyu shuru babu ke babu waya, sannan kuma abubuwa sunyi sanyi amma banji kince komai ba?”

Murmushi Hajiya Mansura ta saki tare da cewa.

“Kai Amarya rashin haƙuri, ina sane sarai wai ke meyasa bakya abu da lissafi ne, naji abubuwa sunyi sanyi, amma baza muyi wani yunƙuri yanzu ba dole muna buƙatar ƙarin lokaci Saboda har yanzu basu gama sakin jikinsu ba, mu kuma muna bukatar su saki jininsu su fara mantawa da wani tsoro, kafin mu cigaba daga inda muka tsaya karki manta fa ko yaya ne mun ɗan samu nasara domin kuwa mun kashe babban jigo Hajiya Gaji, sai sauran ne zai bamu wahala ki kwantar da hankalinki ki ƙara jawo su a jikinki da nuna musu tsantsar ƙauna domin kuwa yanzu salo zamu sauya saboda kiɗan ya sauya dole salon ma ya sauya, shiƙa zamuyi wanda babu zargi a cikin sa.”

Shuru Aunty Amarya tayi kafin tace.

“Ban gane ba wani irin kisa ne wanda babu zargi?”

<< Aminaina Ko Ita 38Aminaina Ko Ita 40 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×