Shurun da Haidar yaji Al'ameen yayi shine ya sashi zama tare da ture system ɗin dake gaban Al'ameen yace.
"Magana nake maka kayi min shuru, ita Nafeesa tace na tambayeka kaine ka gayyaceta Office ɗinka da magiyar dan Allah tazo."
Cike da munguwar mamakin ta Al'ameen ya saki murmushi lallai wannan Yarinyar cikakkiyar makira ce ta bugawa a jarida.
"Ehh nine na kirata nace tazo saboda ina son nayi Magana da ita akan makomar soyayyarku, na gaji da ganinka cikin halin damuwa Haidar damuwarka tawa ce taya zan samu nutsuwa kai kana cikin damuwa kaine abokin shawarata. . .