Skip to content
Part 42 of 67 in the Series Aminaina Ko Ita? by Rasheedat Usman

Shurun da Haidar yaji Al’ameen yayi shine ya sashi zama tare da ture system ɗin dake gaban Al’ameen yace.

“Magana nake maka kayi min shuru, ita Nafeesa tace na tambayeka kaine ka gayyaceta Office ɗinka da magiyar dan Allah tazo.”

Cike da munguwar mamakin ta Al’ameen ya saki murmushi lallai wannan Yarinyar cikakkiyar makira ce ta bugawa a jarida.

“Ehh nine na kirata nace tazo saboda ina son nayi Magana da ita akan makomar soyayyarku, na gaji da ganinka cikin halin damuwa Haidar damuwarka tawa ce taya zan samu nutsuwa kai kana cikin damuwa kaine abokin shawarata kuma jigona a wannan rayuwar bayan shaƙuwa ta abota karka manta da jini ɗaya yana yawa a jikin mu, Haidar shin ka yarda dani?”

Murmushi Haidar yayi tare da cewa.

“Na sani Al’ameen ka damu dani ƙwarai a rayuwa babu abinda bazaka iya min ba domin samun farin ciki na, Al’ameen kai abokine kuma ɗan uwa na gari duk da wannan Companyn naka ne baka taɓa nunawa duniya cewa nakane kai ɗaya ba duk duniya ɗauka suke cewa Companyn Three friend ne, ko iya haka ya isa ya nuna kai mutum ne mai nagarta, Al’ameen ƙwarai na yadda ɗari bisa ɗari, bazaka taɓa cutar dani ba a rayuwa haka bazaka yadda wani ya cutar dani ba, ya kukayi da Nafeesa duk da banga alamun Nasara ba a idanunta.”

Numfashi Al’ameen ya saki yana kallon sa cike da tausayi domin kuwa abun tausayi ne Haidar a yanzu, ɗan murmushi ya saki gudun karya fahimci wani abu yace.

“Hakane bata yadda da duk wata magiyata ba, amma karka damu insha Allah zamu shawo kan matsalar, amma meyasa ka shigo min Office babu sallama.”

Murmushi Haidar yayi tare da cewa.

“Saboda na zaƙu naji me kuka tattauna da Nafeesa, nasan tunda na ganta cikin companyn nan to Tabbas ƙoƙarin shawo kan matsalar kake kuma insha Allah na san zakayi duk yadda zakayi domin dawo min da Nafeesa gareni.”

Murmushin yaƙe Al’ameen tare da jinjina kansa alamun hakane agogon hanunsa Haidar ya duba tare da mikewa yana cewa.

“Time ɗin tashi yayi bara naje na rufe system ɗina sai na fito mu tafi.”

Da to Al’ameen ya amsa yana duban Haidar harya fice dafe kansa yayi cike da damuwa domin kuwa lallai yana cikin tsaka mai wuya, numfashi ya saki tare da rufe system ɗinsa da duk wani file daya buɗe ya mike tare da ɗaukar wayarsa da key ɗin motar sa ya fito.

*****

“Rufaida! Rufaida! Wai kina ina ne haka ina ta kira shuru?”

Rufaida dake zaune a cikin bedroom ɗinsu tayi shuru tare da haɗa tagumi tana tunanin duniya sam bata ji kiran Momma ba, ta kasa mantawa da Haidar a zuciyarta duk yadda taso koyawa zuciyarta soyayyar Barrister khalil ta kasa domin kuwa koda wayarsa ta ɗaga sai taji amon muryar sa na sa mata damuwa, Momma da ta gaji da kiran Rufaida ne ta miƙe da kanta ta shigo room ɗin nasu nan sau biyu tana Magana Rufaida bata amsa mata ba, kusa da ita Momma ta zauna tare da dafa kafaɗar ta, firgit Rufaida ta dawo cikin hankalinta tana duban Momma, ɗan murmushi ta saki tare da cewa.

“Momma yaushe kika shigo banji shigowarki ba.”

Ɗan murmushi Momma ta saki tace.

“Ina kuwa zakiji shigowata Rufaida kin shiga duniyar tunani, Rufaida na juma da fahimtar matsalarki amma ke naga ƙoƙarin ɓoye min abinda na fahimta kikeyi, hakan sam bashi da amfani, jin daɗin Uwa shine ƴarta ta dinga sanar da ita damuwarta rashin jin daɗin Uwa kuma shine ƴarta ta ɓoye mata damuwarta, ni uwace a gareki Rufaida meyasa zaki dinga ɓoye min damuwarki, Rufaida kina son Aliyu shine dalilin damuwarki.”

Shuru Rufaida tayi idanunta suka ciko da hawaye wato soyayyar da take yiwa Haidar har tayi girman da kowa zai fahimta duk da ɓoyewa da take, lallai ba’a taɓa ɓoye sirrin zuciya haka kuma labarinta baya ɓuya a fuska, kanta ta girgiza tare da cewa.

“Momma ba ɓoye miki damuwata nake ba ita wannan damuwarta tawa faɗarta bashi da wani amfani Saboda wanda nake damuwar saboda shi, shi ba tani yake ba, bana cikin rayuwarsa baya sona wata dabam yake so Momma, nayi takaicin rashin samun yaya Haidar a matsayin abokin rayuwata Saboda mutum ne na gari wanda zai kula da mace yadda ya kamata, Momma meyasa nazo Duniya ina takaicin haihuwata domin kuwa ji nake bazan iya rayuwa babu shi ba, a zuciyata yake Momma yaƙi ya fice duk ƙoƙarin da nake Saboda na ciresa na kasa, wannan Wacce irin munguwar ƙaddara ce, zuciyata tana cutuwa Momma, anya kuwa zanji daɗin rayuwata, da ana gayyatar mutuwa ba tare da cikar lokaci ba, da na gayyaci mutuwa tazo ta ɗaukeni ko zan samu sauƙin ciwon da yake damuna.”

Tayi Maganar hawaye na sauƙa a kumatunta, tare da sunkuyar da kanta ƙasa, cike da tausayinta Momma ta girgiza kai tare da cewa.

“Rufaida! Haihuwarki alkairi ne garemu, babu danasani a cikin rayuwarki macece ke mai tsananin ladabi da girmama na gaba dake, baki da wani illa a tattare da ke, Rufaida babu wata Uwa da zataƙi ki kasance Surukarta, muddun nice UWAR Aliyu bashi da wata matar da ta wuceki, ki nutsu Rufaida Aliyu zai zamo miji a gareki nice zan tabbatar da hakan bazan barki kiyi kuka ba Rufaida domin kuwa ni uwace ta gari.”

Ɗago idanunta Rufaida tayi da har yanzu hawaye ke gudu a fuskarta ta girgiza kanta tare da cewa.

“A’a Momma karki tursasa saboda ni, domin kuwa ba nice a ransa ba, bana son ki takura masa ki barsa da wacce yake so ni zanyi hkr na rungumi ƙaddarata, koda kinsa ya aureni ba lallai bane ya soni.”

“Karki kuma dakatar dani game da wannan maganar domin kuwa ni na haifi Aliyu ina da ikon zaɓa masa matar Aure kuma dole ya aura ko baya so, kamar yadda kema nake da ikon tursasaki ki Auri wanda nake muradi bana buƙatar musu kin sani karki sake min shi idan kuma kika kuma to ranki zai ɓaci nasan Aliyu dole zai soki saboda biyayyarki da haƙurinki kuma nasan zaki basa kulawa, duk namijin daya samu wannan komai ƙiyayyar da yake miki dole zai sassauta ki fara shiga ransa, karki damu insha Allah komai zaiyi dai-dai surukata.”

Tayi Maganar tana sakin murmushi tare da jawo Rufaida jikinta tana rarrashin ta tare da faɗa mata maganganu masu daɗi sosai Rufaida taji daɗin maganganun Momma, ko ba komai ta nuna mata Soyayya sun juma sosai suna hira da Momma har sai da Rufaida tayi bacci sannan Momma ta fito tana murmushi cike da ƙaunar Rufaida.

Bayan Sati Uku

Al’ameen yana zaune a falo Aunty Amarya ta sauƙo tana sakin murmushi tare da zama gefen sa kallonsa tayi cike da kissa da kuma son shawo cikin sa tace.

“Al’ameen ya akayi ne naga kayi shuru kamar wanda kake tunani meke faruwa ne?”

Murmushi Al’ameen ya saki domin kuwa tamkar Ummin sa haka yake kallonta kansa ya kwantar a kafaɗarta tare da cewa.

“Babu komai Aunty kawai ina nazari ne game da hanun jarin da na saka watanni huɗu da suka wuce, na amshi kuɗaɗen da suka bani Matsayin riba so nake na rabawa gajiyayyu da kuma marayu domin kuwa saboda haka na saka hanun jarin.”

Murmushi Aunty Amarya tayi tare da cewa.

“Wannan tunani ne mai kyau Al’ameen domin kuwa burin mahaifiyarka kenan ka taimaki masu tsananin buƙata, akwai wata acan unguwar su Hajiya Mansura bata da lafiya tana fama da matsalar ƙwaƙwalwa, za’a mata aiki ana neman kuɗi 150k wanda su iyayenta basu da wannan kuɗin jiya na tura musu 30k tunda zakayi taimako sai ka sakata a ciki.

“Shikenan Aunty insha Allah zan ɗauki nauyin jinyarta.”

“Allahu yasha” tayi Maganar cikin fara’a tare da jefo masa tambayar da take buƙatar ya amsa mata.

“Ni kuwa Al’ameen yau ina Ablah take ban ganta ba tun safe kuma dai bata da school.?”

Ɗan murmushi Al’ameen yayi tare da cewa.

“Aunty kya min Wannan tambayar, ni da ba gadinta nake ba, Inna Jumma ya kamata ki tambaya domin kuwa itace uwarta a gidan nan komai da izinin ta take aikatawa.”

Yayi Maganar a taƙaice, Aunty Amarya murmushi ta kuma ta fara magana dai-dai Ablah ta sako kanta idanu biyu sukayi da Al’ameen wanda ita Aunty Amarya bata ma lura da ita ba, idanu ya kanne mata, murmushi tayi tare da saurin komawa ta laɓe jikin bango tana sauraronsu.

“Al’ameen yarinyar tana da hankali ga kuma ladabi, kasan me kuwa?”

Girgiza mata kai Al’ameen yayi alamun a’a murmushi tayi ta cigaba da cewa.

“Sai nake ganin kamar kana sonta, shin ɗana kana son Ablah.”

Tayi Maganar tana maida kanta ga wayarta tana jiran amsarsa Saurin toshe bakinta Ablah tayi tana zaro idanunta bata son Aunty Amarya ta fahimci akwai Soyayya tsakaninsu, Al’ameen murmushi yayi tare da kallon inda Ablah ke tsaye, kanta ta ɗan leƙo tare da girgiza masa kai alamun yace mata a’a, cike da mamaki ya mata juyi da hanu alamun meyasa kanta ta mayar ba tare da ta masa alamu ba, Aunty Amarya ce tace.

“Kayi shuru Al’ameen baka amsa min ba.?”

Murmushi yayi tare da amsar wayar hanunta ya miƙe zaune ijiye wayar yayi a gefe tare da fuskantar ta yace.

“Meyasa kika min wannan tambayar Aunty, gaskiya baki fahimceni dai-dai ba domin kuwa babu alaƙar Soyayya tsakanina da ita, inai mata kallon ƙanwata ne kamar yadda nake kallon su Afnan, Aunty ban taɓa jin soyayyar ta ba, saboda bana tunanin tayi dai-dai da zaɓin zuciyata.”

Wani irin sanyi Aunty Amarya taji a cikin ranta domin kuwa amsar da take buƙata kenan ga kuma tuggun da suke niyyar farawa Ablar.

“To ina ga ni ce ban fahimta dama nayi wannan tunanin Ablah bata dace da Rayuwarka ba saboda ko wacce ƙwarya da abokiyar burminta, ɗan arziki ai sai gidan arziki, bara naje sama.”

Murmushi ya mata tare da ɗaga mata kai alamun to, cike da farin ciki kuwa Aunty Amarya ta haura, Al’ameen numfashi ya saki gani Aunty Amarya ta shige bedroom ɗinta ya sashi cewa Ablah.

“Sai ki fito ai.”

Fitowa Ablah tayi tare da zuwa ta tsaya gefen sa.

“Meyasa kikasa na yiwa Aunty ƙarya kinsan dai soyayyata bazata ɓuya ba, amma ke ƙoƙari kike ki ɓoyeta.?”

“Kaji wata tambaya to meye dan ka ɓoye, ni fa bana son kowa ya fahimci wannan Soyayyar har sai nan da wani lokaci.”

“Shine na ce meyasa to menene dalilin?”

Murmushi Ablah tayi dai-dai wayar Al’ameen na ringin dukkan su kallon wayar sukayi Nafeesa ce tsuka Al’ameen yaja yana ɗagowa ya kalli Ablah tare da cewa.

“Ina jinki.”

“Nafeesa ce ta kiraka ko, ka ɗaga mana kaji me zata ce maka.”

“Na ɗaga kikace saboda bakya kishina, Ablah ni fa na tsani wannan yarinyar domin kuwa annoba ce a cikin rayuwarmu, tasa Haidar cikin mungun hali nima tana nemana da masifa.”

Ɗan murmushi Ablah tayi tare da zama gefensa ta ce.

“Yaya Al’ameen na juma da fahimtar damuwarku akan wannan Nafeesan, amma ni ina ganin laifinka saboda ya kamata ka sanar da yaya Haidar abinda yake faruwa domin yasan komai daga bakinka sannan kusan abun yi, amma sai kaƙi yin hakan kake ɓoye masa kuma wannan matsalar bata ɓoyewa bace, matsalace daya kamata Haidar ya santa zuwa yanzu kafin ya fara zarginka.”

Ɗan murmushi Al’ameen yayi tare da cewa.

“Bazan taɓa sanar da Haidar wannan matsalar ba, Saboda matsala ce da zata iya tarwatsa zuciyar abokina, ni kuma bazan yadda na yi abinda zai cutar da rayuwarsa ba, kin san irin soyayyar da yake mata kuwa, tunda nake ban taɓa ganin irin wannan Soyayyar ba, da kaina zanyi maganin matsalar ba tare da Haidar ya sani ba.”

Numfashi Ablah ta sauƙe tana kallon sa tare da cewa.

“Matsala tun tana ƙarama ake magance ta ba sai ta girma ba, amma ka gagara fahimtar haka, Nafeesa macece mai tsananin wayo sau ɗaya na ganta na fahimci hakan, Nafeesa zata iya cin riba akan…..”

Hanu Al’ameen ya ɗaga mata tare da cewa.

“Bana son ki sare min gwiwwa akan abinda nake ganin zan iya, ni na sani zan shawo kan wannan matsalar ba tare da Haidar ya fahimci Nafeesa tana sona ba, kamar yadda kika faɗa na yadda tana da wayo dalilin haka yasa nake taka tsantsan saboda kwalba ce ita uwar sharri zata iya sawa zuciyar Haidar zargi na ta hanyar min sharri, idan nayi ƙoƙarin sanar dashi saboda yana sonta Soyayya zai gagara fahimta amma ita zai fahimce ta, sannan zai iya bin duk wani layi da zata ɗaurasa, dalilin kenan da yasa nake tsoron sanar da shi Saboda za’a iya samun akasin lissafi ki fahimce ni Ablah.”

Shuru Ablah tayi tana nazarin maganganun su, ita dai a nata lissafin wannan ba hujja bace da zaisa Al’ameen ya ƙi sanar da Haidar domin kuwa tana iya hango matsala da zata faru nan gaba, sai dai zatabi Al’ameen a yadda yake so, zata ɗauki kasadar fuskantar Nafeesa domin ta ƙalubalence ta, ba tare da Al’ameen ya sani ba bare ya dakatar da ita, Tabbas wannan hali ƙaddarar su bata ƙarewa daga wannan sai wannan bai fita daga na amarya ba gashi ya kuma faɗawa na Nafeesa meyasa ƙaddarar tarwatsa rayuwa take ƙoƙarin bibiyar rayuwar Al’ameen ana neman lallai sai ya shiga cikin mungun yanayi muddun tana numfashi bazata taɓa barin burin ko ɗaya daga cikin su ya cika ba, ta yadda da zancen Umma soyayyar ta da Al’ameen ne kawai zai bata damar karesa duk da bata isa sauya ƙaddara ba, amma zatayi ƙoƙarin ganin ƙaddarar tazo da sauƙi za kuma ta roƙi ubangiji daya sauya ƙaddarar, numfashi ta saki bayan gama zancen zucin ta tare da cewa.

“Hakane maganganun ka ka fini gaskiya Allah ya baka ikon daidaita komai ni bara naje na bawa Inna Jumma aikenta, wai da so nake ka ara min wayarka zanyi assignment ne.”

“Ya dai kamata zuwa yanzu ace kina da waya taki ta kanki, zanje na samu Umma na nemi iznin ta idan ta yarda kema zakiyi taki na huta.”

Yayi maganar yana miƙo mata wayar murmushi kawai Ablah tayi ba tare da tace komai ba ta amshi wayar, tana barin wajen, shima Al’ameen tashar aljazira ya sauya.

Aunty Amarya tunda ta shiga bedroom ɗinta ta saka dariya tare da ɗaukar wayarta cikin sauri ta kira Hajiya Mansura tana ɗagawa amarya tace.

“Mansura yau na tabbatar babu wata alaƙa ta Soyayya tsakaninsu.”

Dariya Hajiya Mansura ta saka tare da cewa.

“Na faɗa miki dama babu ta yadda za’ayi Al’ameen yaso wannan yarinyar yadda yake da jin kai da izza ai yafi ƙarfinta, Amarya yanzu aikin mu zai fara akan wannan Yarinyar yanzu ne zamu sakata cikin bala’i ita da Uwarta kuma yanzu ya kamata tasan dalilin mu na wannan yaƙin zamu yanke mata hunkuci na shiga cikin abinda bai shafeta ba yacce gaba ko wani ta gani mai irin halinta zata dakatar dashi.”

Dariya Aunty Amarya tayi tare da cewa.

“Haka nake so ƙawata mummunan hukunci nake son a yanke mata yacce idan taji an ambaci sunana sai zuciyarta ta tsinke, wani hukunci zamu yanke mata kafin mu dawo kan shegen?”

Dariya Hajiya Mansura ta saka cikin ɗaga murya tace.

“FYAƊE shi zamu sanya a mata domin kuwa shine kaɗai abinda zai lalata mata rayuwa, kuma shine zai sanya musu ciwon zuciya ita da uwarta, zasu mutu cikin takaici da baƙin ciki.”

“FYAƊE Mansura hakan yamin kuma shawara tayi dai-dai abinda za’ayi ki bada oder ni kuma zan baki bayanan ta na shiga da fita tabbas watan baƙin cikin su ya fara yanzu ma aka fara labarin yanzu zai fara.”

“Ƙwarai kuwa yanzu ne labarin zai fara domin kuwa naɗaɗɗan zare ne mai wahalar warwara, Tabbas Ahalin AHMAD GIWA yanzu zasu fara ɗanɗana kuɗarsu, zuwa gobe zan shirya komai ke kuma ki tabbatar mana da shige da ficenta.”

Murmushi Aunty Amarya tayi tare da cewa.

“Hakan yayi”

Tayi Maganar suna katse kiran zama Aunty Amarya tayi tare da sakin dare ta furta.

“Ablah kenan, ke ko yaushe gani kike dai-dai kike dani baki san na kware a fannin tuggu ba, a gobe zaki fahimci wacece Amarya.”

Tayi maganar tana kuma sakin dariya.

Ablah babu wani assignment da zatayi kawai ta amshi wayar ce domin ta kira Nafeesa haka kuwa akayi ringin ɗaya Nafeesa ta ɗaga cike da farin ciki ita duk a tunaninta Al’ameen ne ya kirata daga can tace.

“Assalamu alaikum, amincin Allah ya tabbata a gareka masoyina, nasan wannan kiran daka min ta amincewa ne, domin kuwa na sani dole zaka dawo gareni.”

Murmushi Ablah ta saki tana girgiza kanta kafin cikin slow voice ɗin ta tace.

“Ba daraja da kimar mace bane bibiyar namiji duk da ya furta mata kalmar ƙiyayya, ba ajinki bane barazana a soyayya, domin kuwa soyayyar gaskiya ba’a mata barazana a cikin ta, wai ma na tambayeki shin wacce irin zuciyace da ke wacce bata san ya kamata ba, Allah wadaran zuciya irin taki wacce take da kwaɗayi da son abun duniya, meye ribarki idan kin raba AMINAI kin san meye kina bani tausayi domin kuwa duk macen da ta rasa Haidar a matsayin miji tayi babbar asara, hmmm! Nafeesa ki dawo ga soyayyarki ta farko domin kuwa nan ne kike da matsuguni kafin lokaci ya ƙure miki a nan wata ta maye gurbinki, kizo kiyi biyu babu domin kuwa idan kik…”

“Ke dalla shasha rufe min baki, wacece ke da zaki ɗauki wayar mijina har ki kirani kina ƙoƙarin faɗa min wata maganar banza, ki sani Al’ameen nawa ne kuma wallahi dole ya soni kuma ya aureni na kuma yi sarauta a cikin gidan sa, wai ma tukunna bansan wacece keba da har kike da zarrar faɗa min maganar banza anya kin san wacece Nafeesa kuwa?”

Dariya mai sauti Ablah tasa har sai da Nafeesa ta jiyo sautin kafin tace.

“Au haba ashe har kin zamo matar sa, sorry na ɗauki wayar mijinki ko, Hajiya Nafeesa kenan haka kike so na faɗa miki ko Nafeesa ni ce asalin matar tasa wacce ake so ba wacce take so ba wacce ake bi ba wacce take bi ba, ni mace ce mai daraja da aji ba irinki ba da kika ijiye darajar ki a gefe, gargaɗi na kira na miki ki fita a hanyar Masoyina idan ba haka ba kuma zakisha wahala wacece ni ba shi bane abinda ya dace ki sani fita a hanyata shine abinda yafi dacewa a gareki Al’ameen numfashi nane kuma duk wanda yayi ƙoƙarin rabani da numfashi na shima sai na rabasa da nasa numfashin kika tsaya a hanyata to fa Tabbas zan kawar dake daga wannan hanyar ni ce dai Ablah wannan wanda muka haɗu a school ɗin har ya wurgar dake gefe saboda kin zauna a sit ɗin sarauniyar sa, kinga kuwa ko iya wannan ya kamata ki gane bazaki taɓa samun Al’ameen ba.”

Tana gama maganar bata tsaya taji me Nafeesa zata faɗi ba ta kashe kiran, tana sakin murmushi tasan ko iya waɗannan kalaman sun isa su sanya hantar cikinta kaɗawa.

Wani irin baƙin cikin maganar Ablah Nafeesa taji zuciyarta ne ta mata wani tuƙuƙun baƙin ciki gami da razana domin kuwa bata san me wannan yarinyar ta taka ba da har take faɗa mata waɗannan maganganun, koma menene zata nuna mata cewa ruwa ba sa’an kwando bane sai tayi danasanin kalamanta akanta zata dasa mata baƙin cikin da zai sanya zuciyarta fashewa.

Tayi zancen zucin tana wurgar da wayar a hasale idanunta sunyi jajur ita kaɗai tasan sukar da ƙirjinta ke mata lallai Ablah ta janyowa kanta faɗan da bazata taɓa iyawa ba…

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Aminaina Ko Ita 41Aminaina Ko Ita 44 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×