Skip to content
Part 43 of 67 in the Series Aminaina Ko Ita? by Rasheedat Usman

Murmushi Ablah tayi tana ijiye wayar domin kuwa ko banza tasan yanzu zuciyar Nafeesa cike take da baƙin ciki miƙewa tsaye tayi tare da fitowa falo yana nan inda ta barsa wayar ta ijiye masa tare da cewa.

“Ga wayarka.”

“Har kinyi assignment ɗin kenan?”

Kanta ta girgiza tare da cewa.

“A’a banyi ba na fasa sai da daddare idan Allah ya kaimu.””Okay to Allah ya kaimu”

Yayi Maganar hankalinsa na ga News ɗin da yake kallo itama Ablah shigewa tayi bedroom ɗin Inna Jumma.

Can kuwa part ɗin su Haidar, Rufaida tana zaune ita da Momma Haidar ya fito ya zauna gefen Momma yana ɗaukar remote zai sauya tasha yaji muryar Momma

“Aliyu ɗazu na aika Madina ta kira min kai ta samu kana bacci baka farka ba, amma Rufaida tashi ki bamu waje.”

Babu musu Rufaida ta miƙe ta bar wajen.

“Aliyu ya maganar matar Aure ka fitar ne.?”

Tamkar sauƙar aradu haka yaji zancen Momma idanunsa ya ɗago ya kalli Momma tare da cewa.

“Momma meyasa zaki min wannan tambayar, a iya sanina ke da Papa baku taɓa min wannan tambayar ba?”

Murmushi Momma tayi tare da cewa.

“Ni yau na maka sannan shi papan naku shine ya sani na maka tambayar amsar nake jira.”

Shuru yayi zuciyarsa na tsinkewa tunowa da yayi bashi da Tabbas da Nafeesa a yanzu tare da cewa.

“Momma ina da ita na fitar ina sonta sosai.”

Murmushi Momma tayi tare da cewa.

“To ina baka umarnin cewa kayi gaggawar rabuwa da ita domin kuwa mun maka matar aure muna da zaɓin mu da muke so ka aura.”

A matuƙar razane ya kalli Momma tare da cewa.

“Momma na rabu da ita kuma, haba Momma wani irin kun min matar Aure bayan kuma ina da wacce nake so.?”

“Aliyu ni kake kallon idanuna kake cemin kana da wacce kake so, to zaɓin mu zaka aura ba zaɓinka ba, idan kuma zakayi jayayya da maganata ne to Bismillah.”

Wani irin tsinkewa zuciyar Haidar yayi tare da fuskantar Momma cikin wani irin yanayi na damuwa ya ce.

“Momma please bance zanyi jayayya da maganarki ba, amma ki duba ina da wacce zuciyata ke so kuma itace zaɓin rayuwata, ta yaya zanyi rayuwa da wacce bana so, ni fa namiji ne ba mace ba ta yaya za’a min Auren dole.?”

“Jayayya zakayi da maganata mana Aliyu tunda gashi yanzu kana ƙalubalanta ta, kaga Aliyu umarni nake baka baka da wata Mata idan ba *RUFAIDA* ba itace na yadda ta zamo surukata ba wata can shasha ba, Rufaida itace ta dace da kai Saboda tana da nutsuwa da kuma hankali ladabi Uwa Uba kuma tana sonka fiye da komai a rayuwarta, zaka samu jin daɗi da kwanciyar hankali muddun ka kasance da ita.”

“But Momma i s…”

Hanu Momma ta ɗaga masa tare da miƙewa tsaye tace.

“Karka min musu, na faɗa maka ne saboda ka kwana da sanin cewa, rayuwar ka da Rufaida itace zatafi alkairi a gareka domin kuwa itace zaɓin iyayenka.”

Tayi Maganar tana haura sama ta barsa zaune a wajen, cike da munguwar tashin hankali yake kallon Momma harta ɓacewa ganinsa miƙewa yayi cike da tashin hankali shima ya fice daga part ɗin nasu, part ɗin su Al’ameen ya shiga, a falo ya zauna yana fuskantar Al’ameen cikin tashin hankali tare da dafe kansa idanunsa har sun fara sauya kala, Al’ameen dubansa yayi dai-dai wayarsa na ringin SAFWAN ya gani rubuce, ɗan murmushi yayi tare da katse kiran ya tura masa text cewa yana aiki amma zai nemesa daga baya, kafin ya maida kallon sa ga Haidar tare da cewa.

“Idanunka sun gwada min akwai matsala meke faruwa?”

Kallon Al’ameen yayi tamkar zai danna kuka yace.

“Al’ameen wai ni kaɗai ne mutum a wannan duniyar da damuwa da baƙin ciki ko yaushe suke ƙoƙarin dabaibaye rayuwata shin ya ake so nayi da rayuwata mutuwa ake so nayi, mutanen da nafi kowa sonsu a duniya suke ƙoƙarin saka rayuwata cikin baƙin ciki, na fara gajiya da wannan rayuwar Al’ameen.”?

Al’ameen miƙewa yayi tsaye tare da tahowa kusa Haidar ya zauna ya dafa kafaɗarsa yace.

“Har yanzu na kasa fahimtar maganganun ka, ka fito ka faɗa min menene ke faruwa, nasan a duniya bayan Momma da Papa sai kuma Nafeesa sune wanda kafi sonsu fiye da kowa amma sai dai baka faɗa min menene matsalar ba.”

Kansa Haidar ya ɗago cike da sanyin jiki yace.

“Meyasa ka cire kanka a cikin waɗanda nake ƙauna fiye da kowa, Al’ameen kana cikin su domin kuwa kai tsagi ne na jikina?”

“HMMM! Ba wannan bace damuwata yanzu Haidar, abinda ya ɗaga maka hankali nake son sani?”

Numfashi Haidar ya sauƙe tare da cewa.

“Al’ameen Nafeesa taƙi ni ta juya min baya ga Soyayyarta daya kasa fita daga zuciyata, jinta nake tamkar rayuwata numfashi na Kamar haɗe yake da nata, shiyasa nake ɗaukarta rayuwata, ina cikin wannan ciwon ban fita ba, sai kuma gashi Momma tazo min da maganar da take neman juya min ƙwaƙwalwa ta, zuciyata ta tsinke hankalina ya tashi Al’ameen Momma cemin take wai na ijiye duk wani muradin zuciyata na auri Rufaida Auren dole wai ni ake shirin yiwa, na rasa meyasa Rufaida take neman lallai sai ta shige min cikin rayuwata, na Tabbata wannan makircinta ne, itace ta haɗani da Momma a saboda kawai son zuciyarta na tsani Rufaida a yau domin kuwa tana neman haɗani da iyayena ni fa namiji ne ta yaya za’ace za’a min Auren dole.”

Tunda ya fara Maganar Al’ameen ya nutsu yake sauraronsa sai da ya kai ƙarshe kafin yace.

“Haidar Nafeesa tayi nisa bata jin kira, domin kuwa duk wata hanyar da ta dace ace anbita domin sasanta tsakaninku taƙi biyo wannan hanyar, bazan ce bazata dawo gareka ba saboda bansan ikon Allah ba, ban kuma san me gobe zata haifar ba, sai dai ina maka fatan nasara akan soyayyarka, Maganar Momma magana ce da take buƙatar ayi duba akai Haidar domin kuwa Rufaida ƴar uwar ka ce ta jini, kana jin zafin ƙiyayyar da Nafeesa take maka yanzu, to ka sani itama fa Rufaida haka take jin wannan zafin a zuciyarta, bazance ka bijirewa Momma ba domin kuwa duk masoyinka na ƙwarai bazai ce ka kaucewa maganar mahaifiyarka ba, Sai dai alƙawari ɗaya zan maka gobe insha Allah zanje na samu Momma.”

“Da akwai banbanci tsakanin zafin da nakeji da wanda Rufaida keji, Al’ameen kamin adalci nifa munyi Soyayya da ita mun shaƙu sosai har ta zamo jinin jikina kafin ta juya min baya, ita kuma Rufaida babu shaƙuwa tsakanin mu domin kuwa ban furta mata kalmar so ba ban kwaɗaita mata rayuwa dani ba ta yaya zaka haɗa raɗaɗin da nake ji akan Nafeesa da nata, ko kaɗan na fita jin ciwo, Bazama ka haɗa ba, bance Momma zata saurareka ba domin kuwa Rufaida ta gama tsarata, sai dai ka sani bazan taɓa yadda na rasa Nafeesa ba na shiryawa yaƙi akanta.”

“Hmmm! Haidar ba’a taɓa maganin matsala ta zafi kabi komai cikin sanyi na tabbata zakayi Nasara, ka dai yi hkr na fara magana da Momma kafin mu yanke hukunci.”

Kansa Haidar ya ɗaga tare da shigewa bedroom Al’ameen ya kwanta cike da matsanaciyar damuwa.

Haidar da wannan baƙin cikin da kuma haushin Rufaida ya kwana, shi kansa Al’ameen a cikin damuwa yake domin kuwa ya tabbata Nafeesa gagarumar matsala ce a rayuwarsa wacce take masa barazana.

Washe gari da safe Bayan sunyi breakfast Al’ameen ya riga Haidar fito Company, shi Haidar sanda ya biya har gidan su Nafeesa ya kuwa taki Sa’a ta fito zata shige school ta hangi motar sa, tsuka taja tare da nufar motar tasa a fusace ta tsaya a Gaban motar, buɗe motar yayi ya fito, Ƙirjinsa na dukan Uku Uku domin kuwa baisan me zaiji daga gareta ba, kallon sa tayi cikin tsawa tace.

“Me kuma ya kawoka ƙofar gidan mu?”

“Nafeesa tambayata kike meya kawo ni ƙofar gidan ku, kin sani kece rayu…..

Dakatar dashi tayi da cewa.

“Ni ce rayuwarka ba, na sani abinda zaka faɗa kenan domin ko da yaushe shine furucinka, nasha faɗa maka cewa Ni ba rayuwarka bace idan kuma ni ce rayuwarka to kuwa bazaka rayu ba zaka mutu.”

Murmushi Haidar yayi tare da cewa.

“Idan har na mutu a sanadiyyar soyayyarki wannan abun alfahari nane, duk ban san laifin da na miki ba, kike nuna min ƙiyayya, ko kaɗan Soyayyar da nake miki bata taɓa raguwa a Cikin zuciyata ba, ki faɗa min waye ne wanda kike nuna min ƙiyayya saboda shi, da me ya fini meyasa kike tsoron bayyana min shi, shin bashi da darajar da zan sansa ne, ɓoye abun da ake so wannan tsoro ne da rashin kaiwa.”

Murmushi Nafeesa tasa tare da gyara tsayuwarta sosai ta dubesa, Tabbas Al’ameen yayi kuskuren kin amsar soyayyarta duk da tasan dole ta mallakesa ko ta halin yaya amma kafin nan dole sai tayi wasa da rayuwar su, tana sakin murmushi ta dubesa tare da cewa.

“Hmmm! Rashin bayyana maka muradin ruhuna kuma farin ciki na a tunanina wannan shine kwanciyar hankalin ka domin kuwa daga ranar da kasan wanene dago lokacin tashin hankali zai hauhawa baccinka zai zamo na wucin gadi, sannan bugawar zuciyarka zai kuma yin sama.

Ɗan dariya Haidar ya saki tare da cewa.

“Nafeesa na faɗa miki tsoro kike nasan wanene malohon da kike so, tsoron me zakiji kawai ki sanar dani ɗan uban waye, meyasa zakiji tsoron karna gagara bacci, hmmm! Kina sona kenan har yanzu tunda kike tausayina.”

“Hmmm! Ba tausayinka nake ba, amma tunda ka matsa bara na sanar da kai ko wanene muradin rayuwar tawa, Haidar Ɗan uwanka Al’ameen shine wanda nake so kuma yake sona a yanzu, muna tare da Al’ameen, Kuma muna son junan mu, kasan meye tun ranar da kazo dashi wajena daga ranar ya fara bibiyar rayuwata, ya kuma sanar dani mugayen halayyar ka wanda ka ɓoye min daga lokacin na fahimci kai ba mutumin kirki bane naga kuma ya dace na rabu da kai, ban taɓa tsamanin cewa kai mashayi bane kuma mazinaci ba sai da ɗan uwanka ya sanar dani gaskiya kuma ya nuna min hujja, sanda nayi bincike akan ɗan uwanka Al’ameen kafin na fara Soyayya dashi mutumin kirki ne shiyasa naga dacewarsa dani, ko sanda ka ganni a Companyn ku wajensa naje mukasha soyayyar mu, kaga bara kaga hujjar kai mazinaci ne domin kuwa na ajiyeta ne saboda wannan ranar.”

Tayi Maganar tana jawo wayarta hoton sa wanda gashi nan Tabbas fuskarsa ne da kuma gangar jikinsa kwance da mace haihuwar uwarta, saurin runtse idanunsa Haidar yayi hango ƙazantar abun ko kaɗan bai taɓa zina ba, ko sanda yake tare da helina wallahi baiyi zina da ita ba amma wai shine aka nuna masa pictures ɗinsa tsirara shida wata wacce bai taɓa ganinta ba a rayuwa Tabbas dole Nafeesa ta tsanesa Kuma ta gujesa da farko ya ɗauka duk Maganar Nafeesa ƙarya ce da kuma hauka, sai da ta nuna masa hujja sanna ya fahimci shine mahaukacin meyasa yanzu duniya ta baci da yaudara da cin amana meyasa shaƙiƙinka kuma makusancinka shine wanda zai cutar da rayuwarka, meyasa Al’ameen zai yi masa haka, ya ɗauki dukkan wata yadda da yaƙini ya ɗaura akansa ashe shi ba haka bane a zuciyarsa Mace ta sauya masa ra’ayi ta sauƙesa daga turbar gaskiya ta ɗaurasa ata ƙarya lallai duniya cike take da macuta samun wanda zai soka da gaskiya bayan iyayen ka abune da yake matuƙar wahala, lallai wannan mummunan ƙaddarace wacce take da niyyar tarwatsa masa rayuwarsa, wani irin hukunci zai yiwa Al’ameen da wani ido zai iya kallonsa, lallai rama cuta ga macuci ibada ne tunda har Al’ameen zai iya cin amanarsa to babu makawa zai iya kashesa, hawaye ne suka zubo daga idanunsa take idanunsa sukayi jajur ya gagara yiwa Nafeesa Magana domin kuwa zuciyarsa suya take masa bakinsa ya masa nauyi, ƙurjinsa dake bugawa da ƙarfi ya danne, Nafeesa ganin yanayin da Haidar ke ciki ya sata sakin murmushi tare da cewa.

“Ya akayi Aliyu Haidar ka gagara Magana ne, ko ka girgiza ne, mena faɗa maka jin wanda ke sona a zai iya buga maka zuciyarka, amma kace ba haka ba, kasan wata hujjar kuma” tayi Maganar tana kuma sakin murmushi pictures ɗin ta ne ita da Al’ameen a Office ɗinsa suna dariya ta nuna masa idanunsa ya runtse tare da dukan motarsa da ƙarfi cikin tsawa ya furta.

“Stop Nafeesa! So kike ki kasheni, Al’ameen mena maka a rayuwa zaka nemi tarwatsa min rayuwa meyasa bazaka nemi na bar maka ita ba, Nafeesa banga laifinki ba, domin kuwa kina da duk wata hujjar da zaki tsaneni amma ki sani wannan hujjar duk ta ƙarya ne domin kuwa ni ba mashayi bane ba kuma mazinaci bane, laifinki ɗaya da kika amincewa Al’ameen, mtsss! Nafeesa Nafeesa! Ina sonki ina sonki rayuwata ce ke Al’ameen…”

Ya gagara ƙarisa Maganar tare da dunƙule hanunsa murmushi Nafeesa ta saki tare da cewa.

“Okay na Yarda da shi domin kuwa yana da hujja, ka sani har abada bazan soka ba, Al’ameen shine nawa na barka lafiya.”

  Tayi Maganar tare da juyawa tabar wajen, harta ɗan fara tafiya ta tsaya tare da juyowa tace.

“Ammm sorry fa nace kayi tuƙi a hankali karka jiwa rayuwarka ciwo idan kuma bazaka iya ba, ka tafi a ƙafa ko ka tari adaidaita sahu Mister love…”

<< Aminaina Ko Ita 47<< Aminaina Ko Ita 43<< Aminaina Ko Ita 42<< Aminaina Ko Ita 49Aminaina Ko Ita 45 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×