Littafi Na Biyu
Tunda ta shiga adaidaita sahun hankalinta bai kwanta ba, ita dai kawai ta shiga ne saboda Haidar ne yace a ɗauketa kuma bata tunanin zai cutar da ita, sunyi nisa sosai da tafiya sai taga mai adaidaitan ya sanja hanya zaro idanunta Ablah tayi tare da cewa.
“Malam ya naga ka sauya hanya Ambassador Ahmad Giwa Estate fa zaka sauƙe ni, kaga malam dama fa ban yarda da kai ba, kaga sauƙeni a nan dan Allah zan ƙarisa da ƙafata.”
Dariya mai adaidaitan ya saki tare da zaro bindiga ya saita ta dashi tare da cewa.
“Karki yadda kiyi motsi ko yunƙurin fita kinayi wallahi zan fasa miki kai.”
Cike da tsoro zuciyarta na tsinkewa tace.
“Malam waye kai, meye na maka.?”
“Babu abinda kika min ni kawai ɗan aika ne dan haka ki nutsu na kaiki lafiya idan ba haka ba kuma zan kai gawarki.”
“Innalillahi wa’inna ilaihirraji’un! Innalillahi wa’inna ilaihirraji’un! Tabbas ina tare da ubangiji kuma nayi yaƙini dashi na riƙe littafinsa kuma na riƙe zikirinsa ubangijina ko yaushe yana tare dani nasan bazai bari a cutar dani ba, bazanyi motsi ba domin kuwa baza kumin abinda ubangiji bai ƙaddara min ba.”
Bai kulata ba kuma bai fasa tafiyarsa ba, ita dai Ablah babu abinda take ambato a cikin zuciyarta sai kalmomin ubangijinta amma duk da haka zuciyarta cike take da tsoro domin kuwa bata san ƙaddararta ba, kuma bata san wacce irin ƙaddara bace take kiranta.
Wani haɗaɗɗan gida wanda yaji kyau taga ya danna hom cikin minti biyu aka buɗe makeken get ɗin, shiga sukayi cikin gidan, Ablah sai da ta tsorata da ganin kyawun gidan domin kuwa tunda take a rayuwarta bata taɓa ganin gida mai kyawun sa ba, ya ninka ambassador Ahmad Giwa Estate kyawu nesa ba kusa sai dai banbancin shi wannan ƙaramin gida ne bai kai Estate ɗin Ahmad Giwa girma ba, tsayuwa yayi tare da ce mata ta fito, babu musu Ablah ta fito daga cikin adaidaitan, wata ƙofa suka nufa tare da tsayuwa, waya ya ɗaga ya kira tare da cewa.
“Oga mun iso.”
Yayi maganar yana katse kiran cikin ƴan wasu daƙiƙu sukaga ƙofar ta buɗu da kanta, nuni ya mata da cewa ta shiga cike da tsoro ƙirjinta na dukan uku uku Ablah take kallon ƙofar, ta gagara shiga, tsawa ya daka mata wanda ya kaɗa mata hantar cikinta, da sauri ta saka kai ta shiga tana addu’a cikin zuciyarta tana shiga ƙofar ta koma ta rufe, duk tsoron da yake zuciyar Ablah hakan bai sata ganin tsaruwar falon ba, turus ta tsaya tun daga ƙafarsa ta bisa da kallo har zuwa sama yana tsaye jikin kujera ya bata baya bata ga fuskarsa ba, ta juma a tsaye bai juyo ba, sai can ya juyo a hankali, fuskarsa a ɗaure babu alamun fara’a, Ablah idanunta ta ɗaga ta kallesa kyakkyawa ne ajin farko harma ya zarce Al’ameen kyau, idanunta ta sauƙar ƙasa cikin dakewar zuciya tace.
“Malam kai waye meyasa ka sa aje a ɗauko ni, ban sanka ba amma kamar kana bibiyar rayuwata tunda gashi harka saka a kawo ni nan?”
Numfashi ya saki tare da sakin murmushi har dimple dinsa suna loɓawa zama yayi saman kujerar ya ɗaura ƙafarsa ɗaya akan ɗaya cike da izza da alamu yafi Al’ameen izza idanma bai fisa ba to zasu zuba, cikin slow voice ɗinsa wanda sai da yasa zuciyar Ablah tsinkewa yace.
“Taimakonki shiyasa na saka a kawoki nan domin kuwa a yau rayuwarki tana cikin haɗari, na jima ina bin rayuwarki tun sanda kika saka ƙafa a cikin gidan AMBASSADOR AHMAD GIWA domin kuwa nasan babu alkairi a cikin gidan akwai mugaye da yawa waɗanda zasu cutar da rayuwarki, mafi rinjayen mutunan gidan bana ƙwarai bane duniya kawai suke yiwa pritending da cewa su mutanen kirki ne.”
Ablah dariya tasa, tare da girgiza kanta lallai ma wannan ɗan rainin hankali ne, wai ita zai rainawa hankali koma shiɗin wayene oho.
“Rayuwata tana cikin haɗari, to meye damuwarka da hakan Ni ce fa nake cikin haɗarin to ina ruwanka koma meye ya faru dani rayuwata ne ba taka ba, kaga ka daina aibata ahalin da zuciyarsu take cike da ƙaunar talakawa mutanen kirki ne babu abinda zaka faɗa akansu ya ɓata su a idanuna dan haka ka buɗe min ƙofa na tafi bana buƙatar taimakonka ahalin AHMAD GIWA mutanen kirki ne bana banza ba.”
Murmushi ya saki tare da saka hanu ya shafa sajensa, cikin kwanciyar hankali ya furta.
“Tabbas ba mutanen kirki bane ko baki yadda ba, LOKACI SHINE ALƘALI.”
“Lokaci shine ALƘALI me kake nufi da hakan?”
“Ina nufin lokaci ne zai nuna mai gaskiya tsakanin ni dake akan Familyn Ahmad Giwa”
“Naji buɗe min na tafi.”
“Ba zaki tafi yanzu ba domin kuwa ana farautar rayuwarki a wannan lokacin.”
“Bazan tafi yanzu ba, saboda ka ijiye ni, bara kayi iko dani, naga kana min Magana da iko da kuma izza shin wanene kai?”
Tayi maganar a fusace cike da ɓacin rai murmushi ya sakar mata ya amsa mata da.
“ABBAS ISA ABBA ɗan gidan ministan Wutan lantarki na Nigeria gaba ɗaya.”
“ABBAS ISA ABBA ɗan gidan ministan Wutan lantarki na Nigeria gaba ɗaya, wow yayi kana faɗa cike da alfahari da kuma izza, saboda kana ɗan minista shiyasa kasa a sato ni a kawoni gidan ka, hmmm! To ina ruwana da kai ɗan minista ne, kaga idan bazaka buɗe min ƙofa ni zan buɗe da hanuna tunda ba kuturuwa bace ni.”
Tayi maganar tana jan tsuka tare da nufar ƙofar murmushi Abbas yayi tare da zuba mata idanu sanda taje har jikin ƙofar taga babu ta inda zata iya buɗe ƙofar domin kuwa ko ta ina glass ne kuma a shafe babu ta inda zata iya saka hanu ta buɗe, juyawa tayi ta kallesa a fusace dariya yasa a wannan karon har haƙwaransa na bayyana ya furta.
“Bazata buɗu ba muddun bani bane na buɗe domin kuwa da password yake amfani.”
“Idan na fasa glass ɗin fa?”
Tayi Maganar cike da haushi still dai dariyar ya kuma tare da cewa.
“Bazai fasu ba koda kuwa ƙarfe kika doka masa, latest glass ne.”
Haushi da takaici yasa Ablah dawowa tsakiyar falon ta zauna domin kuwa taga alama wannan mutumin bashi da sauƙi yana da taurin kai idan ba a hankali ta bisa ba to bazai barta ta tafi gida ba cikin sanyin murya tace.
“Dan Allah kayi hakuri ka buɗe min na tafi gida, ƙarfe uku da rabi yanzu, hankalin su zai tashi idan suka ga har yanzu ban dawo ba.”
Murmushi ya saki tare da gyara zamansa yace.
“Har kin gama masifar taki, banyi zaton zaki saƙƙo da wuri haka ba, kinga Ablah ba wai fa na kawo ki nan da gangan bane ko saboda na cutar dake ki yarda dani wallahi rayuwarki tana cikin haɗari shiyasa na saka a ɗauko ki domin kuwa a nan ne kawai zaki samu tsira.”
Cike da nutsuwa Ablah take kallon sa domin kuwa a yadda taga fuskarsa shi da gaske yake iya gaskiyarsa yake faɗa lallai ya kamata ta sauraresa domin kuwa bata ga alamun zai cutar da ita ba, kanta ta kaɗa tare da cewa.
“Naji to amma ka faɗa min waye ne zai cutar dani bawai ka ijiye ni a nan ba kawai idan har da gaske taimakona zakayi, domin kuwa nima nasan yadda zanyi na kare kaina.”
Da murmushin saman fuskarsa yace.
“Na kasance mai saka idanu a duk wani taku da ke zakiyi saboda ina jinki a cikin raina bazan kuma iya jurar wani ya cutar da ke ba, an shirya a miki fyade a yau ɗin nan bayan kin tashi daga school dalilin kenan da yasa nayi gaggawar sawa a ɗaukoki kafin su cimmiki.”
Zaro idanunta Ablah tayi cike da munguwar tsoro ta furta.
“Fyaɗe kuma innalillahi wa’inna ilaihirraji’un! Wa yake shirin lalata min rayuwata, Please ka sanar dani dan Allah.”
“Hajiya Amina wacce kuke kira da Amarya, itace ta haɗa miki wannan gadar domin ki kauce ki bata waje ko zata samu damar ƙarisa aikin da ta dauko kika tare mata gaba ba.”
A matukar razane ta miƙe tare da cewa.
“Aunty Amarya! Eh lallai biri yayi kama da mutum, amma kasan komai game da abinda yake faruwa a cikin gidan ne?”
Murmushi ya saki tare da furta.
“Kwarai na sani, shiyasa ma na samu damar kareki daga sharrinta.”
Cike da munguwar mamaki Ablah take kallon sa bata taɓa ganinsa ba a rayuwarta ko a cikin gidan amma kuma yana nuna mata yasan komai game da Aunty Amarya wannan abun mamaki ne.
“To amma ta yaya kasan wani abu akan amarya wanda su waɗanda suke GIDAN ma basu sani ba, kai aljanine?”
Sosai ta bawa Abbas dariya numfashi ya saki yace.
“Saboda ni MAYENKI NE duk wani abinda ya shafeki ya zamo wajibi na sani Sallah ake kira ni zan shige masallaci yanzu ba lokacin amsa waɗannan tambayoyin bane na amsa miki wata rana, sannan idan na fita bazan dawo ba zaki kwana anan keda Farida saboda kare lafiyarki.”
Yayi maganar yana juyawa tare da bi ta wani korido da idanu ta bisa cike da mamakinsa da kuma tsoron sa wai MAYENKI ko me yake nufi da hakan, ta furta cikin zuciyarta tana dafe kanta.
Tana nan zaune wata matashiyar budurwa ta shigo wacce bazata wuce 21 yrs ba da ganinta ba bahaushiya bace kamar Irin yaren ibo ne, zama tayi tana yiwa Ablah sannan tare da gabatar mata da kanta, murmushi Ablah tayi ganin Farida tana da sakin fuska cikin mintuna kaɗan suka hau zance tamkar sun san juna.
*****
Shi kuwa Al’ameen yana fita garden ya nufa tare da zama yana dafe kansa sosai ransa ya ɓaci ji yake zuciyarsa tamkar zata faso ƙirjinsa ko cikin mafarki bai taɓa zaton Haidar zai tozarta sa haka ba, bai taɓa tsamanin akwai wanda zai iya shiga tsakanin su ba, yayi imani da Allah cewa da shine bazai taɓa yadda wani ko wata ta shiga tsakanin su ba, ashe dama duk rayuwar da suke Haidar bai fahimci abinda zai iya aikatawa da wanda bazai iya aikatawa ba, ashe dama Haidar bazai fahimce sa ba a rayuwa, ashe akwai abinda zai iya shiga tsakanin Amintar su, kansa ya kuma dafewa da ƙarfi dake sara masa idanunsa sunyi jajue lallai takobin Nafeesa yayi tasiri a jikin HAIDAR wai yau karuwa itace ta shiga tsakanin sa da AMININSA kuma ɗan uwansa, idanunsa ya runtse hawaye ya gangaro masa, kafaɗarsa yaji an dafa saurin saka hanu yayi ya goge hawayen sa domin kuwa baya so a fuskanci rauninsa, dubansa ya kai ga inda aka ɗaura hanu a kafaɗarsa, Maimu ce ɗan murmushi ya sakar mata cikin dauriyar zuciya domin kuwa ya hango rauni da damuwa sosai a fuskarta harda hawaye, zama tayi gefensa sai kuma ta saki kuka, girgiza mata kai Al’ameen yayi tare da jawota jikinsa yana rarrashinta.
“Maimu kukan me kike haka sai kace wanda akayi mutuwa meya faru?”
Ya mata tambayar tamkar bashi da damuwa, cikin kuka da munguwar damuwa Maimu tace.
“Yaya Al’ameen bana so saɓani ya shiga tsakaninka da yaya Haidar, yau hankalina ya tashi na hango tsana da kyamarka a idanun yaya Haidar, kullum Soyayya da shaƙuwa ne a tsakanin ku, meyasa sai yanzu mace zata haɗaku, bazan iya jure ganinku cikin saɓani ba dan Allah kuyi haƙuri ku dawo dai-dai yaya Al’ameen.”
Murmushi Al’ameen yayi tare da cewa.
“Waya faɗa miki zamu kasance cikin saɓani, ki daina ɗagawa kanki hankali Haidar ransa ne yake ɓace shiyasa yake faɗa amma zuwa nasan zai huce Haidar fa abokin rayuwata ne aminin da bazan taɓa iya rabuwa dashi ba, ku masa uzuri yana cikin mayen Soyayya ce, idan harshi ya haukace idanunsa ya rufe ni nawa bazasu taɓa rufewa ba, ina son ɗan uwana karki damu zamu daidaita.”
“A’a yaya Al’ameen bana tunanin zai huce, domin kuwa ya ɗauki zafi da yawa fa, kuma ni abinda ya ke ɗaga min hankali irin zagin da yake maka anya kuwa Yarinyar nan ba asiri ta masa ba, nikam zan faɗawa Daddy ya dawo gida ya yiwa tufkar hanci.”
Sakinta Al’ameen yayi yana haɗa fuskarsa tamau tare da cewa.
“Karki kuskura ki sanar da Daddy ki ɗaga masa hankali, komai yayi zafi zaiyi sanyi ni na ɗauki wannan a matsayin jarabawa kuma zai shige, dan haka bana buƙatar ki sanar dashi idan kuwa kika sanar dashi wallahi ranki sai ya ɓaci, ki tashi kije ki wanke fuskarki.”
Kanta ta ɗaga tare da miƙewa tabar wajen numfashi ya saki ganin ta tafi hawayen da yake riƙewa suka zubo, duk Nafeesa ce silar wannan tashin hankalin lallai a yanzu ne ya kamata ya fara nuna mata kuskurenta, miƙewa yayi tamkar an tsikaresa ya fito daga garden ɗin motar sa ya shiga ya jata da karfi get aka wangale masa ya fice.
Momma tana zaune cikin falon taga Haidar ya shigo a fusace yana huci, baima kula da ita da take zaune ba ya haura cikin sauri da kallo ta bisa tare da miƙewa domin kuwa tasan ba dai lafiya ba.
“To me yake faruwa dashi?”
Ta furta, ƙarar fashewar abu da taji a bedroom ɗinsa ya sata haurawa cikin sauri itama Rufaida da shigowarta kenan ta hango Momma na ƙoƙarin shiga bedroom ɗin Haidar ne ta kirata tare da dakatar da ita cikin sauri domin kuwa tasan muddun taji damuwarsa akan budurwa ce to ransa ne zai kuma ɓaci, ƙarisawa tayi gaban Momma tace.
“Momma ɗan saɓani suka samu a Office da wani ma’aikacinsu yanzu yaya Al’ameen yake sanar dani kinsan yaya Haidar da zuciya ki bari kawai ni na shiga na basa hkr.”
“Saɓani kuma to saboda sun sami saɓani da ma’aikacinsu shine zai ɗebo mana fushi ya dawo dashi cikin gida har yana mana fashe fashe saboda iskanci zuciyar banza, haƙurin uwar me zaki basa, ni bani waje kiga naje naci ubansa.”
Kanta Rufaida ta dafe domin kuwa tasan masifar Momma shiyasa ma bata son tasan ainihin abinda ke faruwa.
“Oh Momma dole mana zaka dawo gida da ɓacin rai tunda an hasala ka dan Allah Momma kiyi haƙuri ki tafi karki shiga please, nasan zuwa zakiyi ki ƙara ɓata masa rai.”
“Ke kuma bakya so na ɓatawa ɗan gwal ɗinki rai ko, yayi kyau duk ɓacin ran da yake ciki sai ya manta da sallama umarnin Ubangiji.”
“Momma ɓacin rai babu abinda baya sawa ke dai kiyi hkr.”
Ɗan ranƙwashin Rufaida Momma tayi cike da ƙaunarta domin kuwa tana da tsananin biyayya uwa uba tana ƙaunar Aliyun ta bata son abinda zai ɓata masa rai cewa tayi.
“Na dai ga alama kin dawo lauyar Aliyu domin kuwa duk laifin da yayi sai kin karesa naji zan sauƙa amma fa albarkacinki yaci.”
Dariya Rufaida tayi Momma kuma ta sauƙa tana murmushi, bedroom ɗinsa ta buɗe ta shiga yana tsaye ya dafe kansa, kamar kuma wanda aka fusatasa ya saka hanunsa ya naushi madubin mirror da ƙarfi ji kike ras ras ya fashe hanunsa glass ɗin ya caka take jini ya fara biyo hanun, amma tsabar tashin hankali da damuwar da yake ciki ko kaɗan baiji zafin yankan ba, sai huci kawai da yake saukewa tamkar mayunwacin zaki hanu ya kuma sawa ya yaye bedsheet ɗin bed ɗinsa yayi wurgi dashi Rufaida bakinta ta toshe cike da tsoro tare da nufarsa da gudu ta saka hanu ta kama hanunsa dake jini.
“Ka dakata haka ya Haidar kana jiwa kanki rauni shin baka jin zafin ciwon a jikinka ne jini ne fa yake zuba sosai a hanunka ka duba ka gani.”
Tayi maganar cikin tashin hankali tana jin zafin kishin Nafeesa a cikin zuciyarta wai duk wannan abun da yake saboda wata mace ce ba ita ba, tsawar da Haidar ya daka mata ya sata razana tare da saurin sakar masa hanu.
“A zuciyata a zuciyata! Anan nake jin zafin ba a jikina ba, hmmm yarda da amana da kuma nuna kulawa ga aboki kuma makusanci ko ɗan uwa ya ƙare domin kuwa dukkan su mugaye ne ciki kuwa harda ke da kike ƙoƙarin zamo min masifa a cikin rayuwata!”
Ya ƙarisa maganar da ƙarfi yana nunata da yatsa, runtse idanunta Rufaida tayi tare da girgiza kanta ta furta.
“Masifa! Masifa fa kace nake ƙoƙarin zamowa ga rayuwarka.”
“Ƙwarai kuwa masifa domin kuwa kin shiryawa shiga cikin rayuwata ta ƙarfi da yaji, kina shirin haɗani sa’insa da mahaifiyata, kin shiryawa shiga cikin rayuwata domin ki musgunawa zuciyata, ki faɗa min me za’a kira wannan idan ba masifa ba, mtsss a yanzu na tsani ganin wannan mummunar fuskar taki tsana kuma ta haƙiƙa a da ina darajaki da mutunta ki saboda ina miki kallon ƙanwata ashe sheɗaniyace ke, ki sani bazaki taɓa samun zuciyata ba har abada rayuwata yafi ƙarfin shiga cikin gurɓatacciyar rayuwarki, bana sonki bazan aureki ba a yau na furta miki wannan na tsaneki, Nafeesa itace rayuwata kuma zata dawo gareni duk inda taje ni na sani, kinji daɗi ina shirin rasa Nafeesa shine bara ki shigo ki cusa min kanki ko, bazaki taɓa kwarjini a idanuna ba, ki fice min daga room.”
Yayi maganar da ƙarfi yana nuna mata hanyar waje, hawayene suka biyo fuskar RUFAIDA ita zuciyata take sonsa amma shi kallon masifa yake mata a cikin rayuwarsa hanunsa dake zubar jinin ta kalla tare da juyawa bedsite drowern sa ta ɗauki tisue hanu tasa zata kamo hanunsa ta goge masa jinin ya bige hanunta da ƙarfi yana nunata da yatsa cikin ɓacin rai jikinsa har karkarwa yake.
“Ke wacce irin mayyace fitinanniya shin babu zuciya a ƙirjinki ne, ban taɓa ganin ballaga bankaura ba irinki macen da bata da class, ina ruwanki da jikina ina ruwanki na mutu ma mana meye asarar ki, na tsani wannan jakin shisshigin naki, ki fice daga ROOM kafin na raunata ki…”